nuna mata.
Laraba ne ta karbe zancen da fadi ai irin uwar dakina sune daidai da irin wanan matar ina fada kullun don macen da ke nuna masu tsoro sai su kara zama shedanu a gurin su.
Ba karin abu muka gani a wurin taba wancan zaman da mukayi da ita da hajiya uwar gidan saboda ita sam bata da baki a gurin ta.
Idan sun fara sai dai mu shige daki ba dama mu leko ko na minti daya yanzun zatace dawa Allah ya hada ta ba da mu ba.
Ba girma ba arziki muka koma kaduna da zama don abin har yaso taba ta a lokacin sosai wallahi Allah dai ya gyara da yake iyayyen miji suna bayan ta ai da yanzu basu tare.
Don gaba daya ta juya kan babangida ga kowa ko iyayyen sai da suka tashi tsaye akan shi don gaba daya ya juya masu baya ne a lokacin.
Kowa yayi mamakin jin zai kara auren uwar dakina damaganan ya fito fili sai ana ganin ko ita ba zata iya dasu ba ai.
Abin mamaki laraba na rufe baki driver ya karbe zancen ta yace ai ba karamin dadi naji ba yanzun da naga hakan don mun sha wuya a gurin wanan matar.
Kafin ta fara tuka mota irin yadda muke fita daku din da zaran mun fita da ita sai mun sha fada a gurin oga ranan don sherin da zata kulla muna tace mun mata abu kaza.
Shi kuma ya rufe ido yaci muna mutunci ido rufe a kan ta kuma fa ba gurin alheri mutum zai kai ta ba.
Matar dake tambayan mu idan musan wurin wani mai asiri mu kai ta ko nawa yake aiki zata biya mu idan mun kai ta.
Wanan mace ai shu,umace kwanaki akan oga yasa musa ya dinga kaiki school da yai tafiya Allah dai ya gyara ba a kore shi ba sai da muka bi ta kan oga yusuf muka kai maganan shi muka samu yai wa ogan namu magana aka barshi sai dai aka maida shi office.
Kinga kuma zama office ba so shi muke yi ba don irin haka mutum yafi samu don idan anyi tafiya dakai ko aike wani guri zaka samu alheri dabaka zata ba a gurin shi.
Mussanman ke hajiya da kowan mu ke son ace ya kaiki wani guri saboda Alherin ki da girmamawa a gare mu.
Laraba tace komai akace tayi zata iya ba sheri a cikin sa don halin ta ne ake fadi ko ita hajiyan tawa tace ai ba kanwar lasa bace ita ma guri ne bata samu ba dai yanzun.
Dariya driver yayi yace hajiyan can kan gaskiya akwai rowa ba abinci ba kuma kulawa a gare ta sai nakasa.
Gaskiya yanzun kan muma muna fadin oga yakai ga mata kulun muna rokon Allah yasa wanan matar ta barki ki zauna a gidan nan don tsaye take a kan ki sosai yanzu.
Emanuel yace min ya kaisu wani guri da wanan kawar nata bakar nan mai jiki ya je ya kai mata wayan da ta bari a mota yaji tsoron inda ya gansu kuma ya samu ana maganan ki a cikin bukkan da ya shiga.
Muushi nayi daga inda nake zaune sai dai ban masu magana ba illa cewa danayi malam sani kaimu sahad don Allah daga nan mu dan yo sayayya a can.
Nau,in kayan girki na gwagwani da na kwalba zuwa na leda na sayo don Azumin da muke ciki akwai yawan amfani da kaya da muke kai da kai.
Gurin kayan yara na nufa na zabo ma yaran yan tufafi da takalma don na fara rage hanya sai yar baby daa nayiwa sayayya itama daga nan muka wuce wurin kayan sha dana ci muka dan taba muka fito zuwa gida don har da maryam can zamu tafi don anty ta bata gari.
Maryam ne take cewa wai kina nufin har da yaran wanan matar kika sayawa kaya komay ?
Nace maryam da yara nake kishi ko da uwar su gani nayi na sayawa wa yan kada yaga ban sai ma nata ba kin ga ba dadi zaiga na banbanta a tsakanin su.
Shiru tayi batace dani komai ba har muka kai gida ta lura ban jin magana don duk maganan da suke tun farko ban tanka masu ba.
Don irin yadda nake ji aa zuciya na ba dadi na farko yarinyar dana gani a cikin wani hali na biyu kuma zancen mu da Nafisa a asibiti yadda ta rufe ido tayi muna cin mutunci az bainar jamma,a kamar wace tayi cikin daba na sunna ba.
Zaman mu a a falon bamu jima da zama ba na fara fitar da kayan da muka sayo muna kallo daidai nan ya shigo falon fuska a daure.
Bin kayan dake baje a kasa yayi da ido sai kuma ya dago yana bi mu da kallo har lokacin fuskan shi babu walwala a cikin sa.
Nima daure fuska nayi ban ko samu gaida shi da dawowa ba sai laraba ce ta fara mai sannu da zuwa tana kokarin tatara kayan dake gurin a kasa.
Wuri ya samu ya zauna daga gefe haka yasa maryam dake daga kwance mikiewa zata shige daga ciki ya dakatar da ita da fadin zauna abin ki maryam ba wani abu bane ai.
Ya joyu gare ni yana fadin Deedar may yasa baku da hakkuri ne dukkan ku kunje asibiti kuna sayar min da hali a gaban mutane da matan abokaina.
Yaya AA nine
ma mai rashin hankalin ke nan ba ita da mukaje gaiyarwa ba ta tare mu da bakar magana yace a fusace dukkan ku baku da hankali.
Na gane ni kuke son tozartawa a idon duniya idan ita bata da hankali ke baki da shine don may ba zaki kyale ta ku fito bakin ku alaikum ba tunda kin san halin ta.
Wani irin takaici da bakin ciki ya zo min a wuya ya tokare ina jin wani bacin rai na zo min kamar zan fashe.
A cikin wani irin murya nace a fusace ni wanan abin ya isheni ya isheni wallahi kulun mutum shine mai laifi a furin ku baka ganin irin cin mutuncin da take min ko yaushe magana ya taso sai kayi kokarin dora laifi a gare ni.
Gaskiya na gaji da wanan halin abin yai min yawa a gidan nan da wannen kuke son inji wai daga ciki ?
Yace ni ba ruwa na da abinda ke a tsakanin ku mutunci nane ba zan yarda kuna zubar min a idon jamma,a ba ko yaushe.
Idan ita bata da hakkuri bata dauki girman ta ba don may ke da ilimin ki zaki tsaya kuna irin wanan sai da halin akan titi haka.
Yanzun dai nice mai laifin kake nufi ke nan tunda ance inda fata yafi taushi nan ake duka ta gama karanto maka hauka kazo ka sauke a gurina ko .
Hawaye ne ya kawo min bayan na gama maganan mikewa yayi a hasale yana fadin ban son irin wanan halin da kuke na zubar min da mutuci a baiyanan jamma,a
Har yakai kofa nace cikin daga murya mutunci kan ai koda nazo na samay shi a zube gidan nan ya juyo ya kalle ni ya girgiza kan sa ya fice.
Labara dake daga kofan kitchen tana sauraren mu tace kayya uwar dakina ai da baki biye mai kunyi haka ba shifa hakkuri bai baci.
Nace ina hawaye mama na gaji ne da abinda mutumin nan yake min yanzu fa a gaban ku akai komai da ya faru, amma yanzu kin gani akaina yake son ya maida maganan.
Tace indan wanan ne fa kinyi kuskure babba domin ba wani abin halitta da rayuwa take zuwa mai daidai a yadda yake son ta.
Ba tare da ganin akasin ta ba kuma may zaisa ki damun kanki da abinda yace yanzu ai gaskiya ya fada don ke mai ilimi ce gaba da baya.
Ke din yake gani zai wa magana yaji sanyi ke kuma din yanzu kin bultsaye masa ina kuke son ya dafa yaji saukin wanan alamarin.
Ga ya masa mara lafiya a asibiti cikin halin ka, in dana in ku kuma ga taku rikicin yanzu kin san iya irin bala,in da sukayi a bayan mu kan zancen cikin jikin ki ne ?
Sha,anin kishiya ko ba irin wanan ba sai mutum ya hada da hakkuri yakanci riba duk mai gaskiya fa ki tuna shike da riba akan komai .
Don haka kada ki kara wanan irin gangancin da kikayi yanzu ai komai ake a sane yake ina jiye mata ranan da zasu hadu mutum mai hakkuri ba a iya kaisa bango ba.
Dama ita amarya a duk inda ta samu kanta dole sai tayi hakkuri da biyayya kan takai ga gina kanta yadda take so.
Kaina na duke kasa ina share hawaye nace nagode mama tace nice ai da godiya da kika fahince ni kikai amfani da magana ta.
Don haka kada wanan magana kice zaki rike shi a rai inda kukayi shi ku barshi gama kin ga cikin wata mai alfarma da muke.
Ita bata tsaya ta nemi falalan sa ba ke da keyi ta kawo maki cikas acikin sa dama kuma burin ta ke nan taga ta dakushe ki a wurin miji ko ta halin kaka.
Maryam da sai yanzu tai magana tace dadin zama a kusa da manya ke nan don ni har na goyi bayan yadda khadija din tai mai yanzu amma maganan ki mama ya sa na hasaso wani abu a yanzun haka.
Ganin yake idan khadija tana kyaleta a bainan jamma,a zaifi da su dinga saida hali ana masu daukan baidaya .
Kin gane ke nan yar nan ai ki rabu da shu,umar mace a gurin kishi Allah dai ya tsare ya kare kawai za a ce.
Ranan ban shiga kitchen ba su sukai aikin komai yadda ya kamata tun kan ya dawo na shiga part din na gyara na jera komai yadda ya kamata na shan ruwa.
Samira ma tazo ta dauki nasu zuwa part din su a falo ya hadu da ita dauke da kayan abinci ta fito daga part dina zuwa nasu ya shige bayan ta gaida shi a tsartsaye.
Yana shiga yaga ranan har na aje mai kayan abincin sa ko ba kamar yadda na saba ba idan nayi girki sai ya dawo nake kawowa part din.
Wanka ya shiga kafin a kira sallah sufita inda suke sallah dasu yusuf mama laraba takai masu kayan buda bakin su acan sai sun isha,i suke shigowa suci abinci su dan taba hira kafin su watse.
Sai dai yanzu da zancen asibiti yazo ne naga da sunci abinci sai su bar gidan zuwa asibitin wurin Nafisa.
Mun idar da sallah a nan falo nayi sallah kasancewar azumine ina zama nan muyi buda bakin mu gaba daya wanda bayan ruwa sai diyan ice dana kan danci sai zuwa dare kuma in dan sha tea shine abinda nakan iya ci kawai in kwanta ban dogon hira sosai don nakan gaji da ansha ruwa nakan kwanta wani lokaci a falo sai idan sun gama kallo mama ta tadani.
Ranan da nake da girki kuma ban jimawa sosai a part dina nakan shige wurin shi in kwanta yakan so matsa min da sai naci wani abu ganin idan ya matsa min din naci ina wahala yasa ya kyale ni hakana.
Yau da shan ruwan su yace suje asibiti ya duba su suna zuwa tana zaune har lokacin cikin ba sakewa tare da ita yanayin ta ya nuna tana cikin tashin hankali.
Yusuf ne ya iya gaida su tare da tambayan jikin yarinyar sauran mutanen dake gurin ne suka karba mai da sauki har tasha nono da likita yace a bata.
AA ya zagaya ya dauki yarinyar ya dan dubata ya dade da ita a hannu kafin ya mayar da ita ya shimfide ta saman gadon ya dago yana cewa Yusuf su tafi.
Sai lokacin tayi magana kamar cikin fada tana fadin ku tafi ina kuma yanzu yace zamu gida ko da magana ne kuma.
Ba laifin ka bane hakan tunda ka auro makirar mace gidan ka ana fada min ban yarda ba sai yanzu na kara tabbatar da hakan jikan mayu .
Idan suna takama da maita gida tazo don sai na nuna mata ita ba kowa bane a garin nan don sai na wullakanta ta kafin ta kai ga nufin ta a kaina.
Ganin Yusuf bada niyar tafiya ne ya fara tafiya ba tare da yayi magana ba Yusuf din yace Allah ya sauwaka yabi bayan shi ko minyi talatin basuyi ba a cikin asibitin suka fito.
Direct ciki suka shigo sai bayan sun zauna ne Yusuf ke fadin yau banga kanwata tazo gaida mu ba mana yace tana ciki da maryam.
Au tana gidan nan ke nan har yanzu yace ina ganin haka bayan sun gama cin abincin Yusuf bai dade ba yace zai tafi don ganin yanayin abokin nasa yau ba dadi.
Jin cewa suna gida har yanzu a wurin laraba da tafita dauko kayan da sukai buda baki dashi waje yasa nayi mamaki a raina.
Har wani lokaci na kara tabbatar da yana gidan bai fita ba kamar in share shi ganin ina hamma don ranan na wuce lokacin da nake kwaciya idona biyu muna hira da maryam.
Laraba tace dani da kinje ki kwanta don barci kike ji wanan mijin nawa ko kawar daga mai son jiki ne sosai.
Ba yadda zanyi in share shi haka na daure na shiga na shirya na fito nayi masu sai da safe suka rufe kofan part din mu ni kuma na tafi wurin shi.
Koda na shiga dakin na samu shima ya kwanta sai dai baiyi barci ba don na ga fuskan shi a dum light din dake kunne a dakin dake dan haska dakin kofan nayiwa key na nufo gadon na kwata dan can nesa dashi.
Shiru ne ya biyo dakin na tsawon wani lokaci daga cikin mu kuma babu wanda yayi barci a lokacin.
Sai can naji muryan shi kamar daga sama yana fadin ya kamata ki sauke wanan fushin karki haifar min diya masu fushi irin ki ko su dara ki.
Kanzil bace dashi ba sai gyara kwanciyar danayi na bashi baya yace na dauka ke din mai ilimice da zaki fahinci saidai na manta da halin mata da haka kuke komai ilimin ku.
Shiru nayi mai yace bakya jinane dake fa nake magana Deedar ina matsayin mijin ki ina magana kin bani baya wanan tarbiyan a ina kika samo shi ?
Ya mirgino yana taba ni nace kada ka tabani don Allah ka barni inji da abinda ya damay ni please .
Dan shiru yayi sai kuma naji yace becouse of what zan daina taba ki kina matana da zaki ce in daina taba ki ina a matsayin mijin a gare ki kuma.
Nace kadai san inda matan ka suke da suke bata ma wasu rai ka goyi bayan su kuma dama ba sona ake ba nuna fin karfi da iko yasa aka kawo ni gidan nan ba don so ba.
Sai don cin ma wani manufa taka ta daban a kaina kada kuma kaga na zauna a gidan ka kace zaku hade da matar ka ku gasa ni cikin ruwan sanyi yadda kuke so.
Na zauna gidan ka ne saboda biyayya ga magabata har ka ganin haka don haka enough is enough dakai da matar ka don kun fara kaini makura kada ka dauke ni yarinya kace ko ban gane inda ka dosa bane dani.
Shiru yayi yana sauraron kalamai na da nake fadin cikin zafin rai da yaji nayi shiru yace kin gama maganar ki nace yanzu na fara yace to karya kike fada da kikace wai zaman biyayyan iyayye kike dani.
Don kowa yasan da kina so na ai ba haka ake zaman biyayyan iyayye ba dakikace kina fada a kaina kice wai ba son ki ake ba ko baki sona.
Kyale shi nayi na bashi baya ba tare da na juyo ba balle in nuna naji maganar shi yace hakkina zaki ban kafin ki kai ga barci ni shine bukata na yanzu ba wani abu ba.
Dama baka da zancen da ya wuce wanan ai a gare ni don shine kawai tsakanin mu dakai murmushi baiyanane yayi ina iya jin shi daga inda nake kwance.
Ranan dai ban yarda na bashi abinda yake so din ba duk da maganan da yake min cikin sanyin rai sai na dauka yaudara ce kawai irin ta maza idan suna son kasancewa da matan su.
Duk sayin nan bai a cikin natsuwa abubuwa sun taru sun rikice masa a kai ga wurin Nafisa ba dadi sai fitina take masa da yaje asibitin akan cewa da yayi sai an sallace zasu fita da yarinyar waje.
Nan ta haushi da masifa tana fadin don ciwon ba ajiki shi yake ba yasa yace hakan don kawai yana da ida yake rage dare a gidan sa.
Gashi kuma har lokacin ba wani sakin fuskan da nake mai a bangare na kamar baya ko magana daga eh sai a, a idan yai tsowo kuma ba mai yawa bane.
A dole nima ina son jan nawa kambun na mata ina nuna nima mace ce ban san haka halin sa yake ba