yayi ya bata min lokaci na ina zaune kalau.
Don Allah ko may ya kawo shi kije ki saurare shi ba dadi mutum yazo wurin don ka ka wullakanta shi haka muje in zaba maki kayan da zaki saka in maki rakiya.
Dole na mike muka tafi dakina ita da kanta ta zaba mi wani dogon riga mai ruwan ganye da dan karamin gyale shi sai da na shirya tsab a cikin rigan tabi jikina ta feshe da turararuka masu kamshi muka rufo kofan muka fito tare.
Yana zaune a cikin motar shi riga da wandon shadace mai guntun hannu rigar ma iya ciya dinkin yake light green kayan su matukar karban jikin shi da dinkin .
Wurin dirkekiyar motar shi da ke fake a kofan can dan nesa kadan damu muka nufa ko ganin maryam ya hana shi fada ban sani ba sai cewan da yayi.
Ita ko maryam tunane take a ranta ina tasan fuskan nan nashi ne ya katse mu da cewa kin san ina waje zaki shanyani a wanan wurin naku mai kazantar tsiya haka ?
Nayi dan dariya tare da cewa cikin wayance abinda yafa da nace ga kawata maryam tazo gaida kai don ma ita ta matsa min in fito yanzun haka.
Anyway maryam ga yayan mu Abdulsamad Abdulrahim nan ku gaisa tace dama nace kamar nasan fuskan nan ai tace ina wuni yayan mu anzo lafiya yaya iyali.
Yace lafiya kalau yaya karatu koda yake exam kukeyi yanzu ko yana wani kauda kai yana basarwa .
Tace karatu Alhamdullahi mun kusa cin ma karshen shi da yardan Allah ai a huta gajiya dama nace barin zo mu gaisa ne kawai yace to na gode kwarai da alama kin fi kawar taki kirki sosai.
Dariya tayi tace a a wallahi ai kirkin khadija na daban ne wallahi tana da kiki matuka shiyasa ma nake jin dadin zama da ita wallahi.
Baki ya tabe ta juya ta tafi tana mashi a huta gajiya ta nufi hanyan shiga hostel din namu sai lokacin na sauke ajiyan zuciya bayan tafiyan ta.
Katse ni yayi da fadin tsaye zaki min sai kace wanda tazo tadi da buduruwar shi haka bude kofan motar shi yayi na zagaya na shiga sai naji ya rufe motar.
Shiru daga ni harshi ba wanda ya iya magana a lokacin sai ma gyara kwanciya yayi a motar bansan lokacin da nace dashi baka da lafiya ne Yaya Samad.
Shiru yayi kamar baiji ni ba sai can yace may kika gani a tare da ni nace yau na ganka so weak ne ba miskilancin nan naka yasa na gane bakajin dadi ko baka cikin good mode.
Wai ke aljana ce ko may dazun kin fada min magana akan ahalina ya zama gaskiya yanzu kuma waya fada maki banjin dadin jikina ?
Nace yanayin ka ya nuna min haka sai ya dago da sauri ya na kallo na nima kallon shi nake yi sai dai ba zan iya jimirin kallon nashi ba a lokacin saboda kwarjin shi da ya cika min fuska a lokaci daya dukar da kaina nayi kasa ina wasa da yan tsun hannu na.
Yau ina bakin naki ya shiga nace ko don Yusuf ne dama kike da bakin a gaban shi nace da sauri ko daya wallahi gani nayi yau kana bukatan kulawa don baka cikin hayacin ka sosai.
Don jikina ya bani baka da lafiya sai naga ya koma ya kwanta kamar yadda yake da farko ya fadi a kasalance cewa kaina kamar zai rabe biyu nake jin shi khadija.
Kasha magani na tambaye shi da sauri yace ban sha ba wani magani kake sha yace panadol extra nakan sha wani lokaci.
Wayana na fara dannawa ina neman layin maryam ta dauka nace fito min da panadol extra din nan da goran ruwa don Allah yaya Samad bai jin dadin jikin shi tace to da sauri na kashe wayan.
Motar shiru ba a dauki lokaci ba sai ga maryam ta iso da maganin ta kwankwasa glass din motar ya bude mata karba nayi ina mata godiya tace babu komai mana Allah ya bashi lafiya.
Maida marfin motar nayi na rufe na fara kokarin bare mashi maganin tare da bude goran ruwan nace mai gashi ka sha.
Ya dago kanshi da kyat ya kalleni ya kalli maganin da ruwan da nake mika mai sai naga ya bude min bakin shi alaman in bashi da kaina .
Dan rankwafawa nayi ina saka mashi maganin a baki na kawo goran ruwan na bashi ya hadiye da kyat yana wani lumshe idonun shi yana bata fuska.
Komawa yayi ya kwanta tare da fadin thanks nace Allah ya baka lafiya amin yace da kyat ni dai komawa nayi na zauna na zuba mai ido.
Wasu irin jijiyoyi naga sun fito rada rada saman goshin nashi wanda ban taba kula ko yana dasu bane dama tsoro ne ya kamani kada wani abu yazo ya samay shi fa a nan wurina nawa ya samay ni kuma.
Shiru daga ni har shi ba wanda yayi magana a cikin mu har mintina na shudewa a hakan suna batun zama awa daya muna nan a hakan dashi kamar mai barci.
Abu daya ne yasa hankalina dan kwantawa ganin yana numfashin shi normal a lokacin yasa nayi shiru tare da zuba mashi ido kawai ina kallon ikon Allah.
Wayan shi dake aje a motan ne ke ringing ganin anata kira bai dauka ba yasa na daga kiran don ba suna batare da na saurari mai magana ba nace mai wayan bai da lafiya please.
Naji muryan mace tana fadin ke wacece da sauri ya dago ya kwace wayan a hannu na ya katse kiran yace akan may zaki daga min waya waya baki wanan damar da ikon daga min kira a wayana.
Zanyi magana yace get out tunda ka samu lafiya yanzu zaka iya ci min mutunci sai dai ka sani ba zan ce ma komai a yanzu ba don yanayin da kake ciki na bukatan natsuwa.
Get out i said na bude motar na fita ba tare da na juya na kalle shi ba naji ya tayar da motar ya jata da karfi yabar gurin nashige ciki abina.
Dakina na shiga na wurgar da sauran maganin saman katifana na fara kokarin cire kaya a jikina sai ga maryam ta shigo tace ashe kin dawo.
Eh ya tafi ya samu lafiya ai nace mata ina daura zanin a jikina na nike kayan na za saman jakkunan kayana dake gefe daya a dakin.
Shiko tunda ya kama hanya yake jin wani bacin rai da bakin ciki a ranshi yana fadin wanan aljanan yarinyar sai ta kasheni wata rana.
Yarinya yanzu ta sauke min bacin raina yanzu kuma ta kara sakani a wani anya ma mutnce kuwa dai , ?
Yana shiga gidan a hargitse ya samay su duk kan su Nafisa ta haukace masu daga ita sai dan buje a jikin ta tana fadin yaushe samad ya fara cin amana na haka ?
Yaushe samad ya canza ban sani ba nayi sakaci da yawa har na bari haka ya faru a yau da ban dauki mataki ba.
Haka ya shigo ya samay ta tana wanan sambatun a cikin yan uwanta da suke ririke da ita kamar sabuwar mahaukaciya.
Nan ya shigo baice da kowa kalaba cikin fushi ya shigo gidan don haka basu ga fuskan wani magana a gareshi ba.
Tayo cikin shi da zagi tana fadin macuci mayaudari sai Allah ya isar min a gare ka har zaka dauki waya kabawa wata mace ta fada min wai baka da lafiya a wurin ta.
Da karfi ya banbare hannun ta da ta rike mai wuyan rigar jikin shi ya fisge ya shige dakin shi a hasale.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ganin zamu dan huta har kwanaki yasa na yanke shawaran zuwa kaduna wurin Ya Amina in masu hutun dan break din da muka samu a can.
Bayan mun fito daga lectures ne na shigo na fara shirin tafiya kaduna maryam ma da tasa rai a gidan su zamu yi dan break din sai ganin ina shiri takeyi ta tambaye ni nake cewa kaduna zan tafi in duba ya Amina kin san hutun nan ban samu zuwa can ba.
Ranta ya baci amma na bata hakkuri akan wani lokaci ai zan tafi nayi Sa,a ina zuwa na samu mota ta cika saura mutum biyu.
Bamu dade ba motar ta bar tashan motar na da gudu sosai sai dai muna wuce maraba mun dan ba kauyen dage gaba baya kadan motar tamu ta tsaya.
Drivern yayi tsaki yana fitowa daga motar ya fita ya bude gaban motan ya dan taba ya dawo ya tayar taki tashi bude motar yayi yace mu fita daga waje mu sha iska zai duba motar.
Abu wasa wasa muna wurin har hudu na yamma motar bata gyaru ba raina duk ya baci nayi tunane kala kala a wurin tsaye.
Wasu motoci ne guda uku tafe a jere da gudu suka wulga a gaban mu, ina jin mutanen dake cikin motar suna fadin kai jama,a akwai dai motoci a duniyan nan hadadu wallahi duba motocin nan kamar su suka kera kan su don Allah.
Kuran motan da suke magana akai nabi da kallo sai naga motan suna dawowa baya a hankali zuwa inda muke kawar da ido na nayi daga kallon su na mayar da hankali na ga waya.
Muna charting da maryam ina fada mata abinda ya faru damu a hanyar jin muryan masu hiran nayi suna fadin wai Allah yaba wasu duniya duba mutanen cikin motar nan don Allah.
Daidai nan na dago ido na in ga abinda suke magana akai Yusuf ne yake kokarin fitowa daga motar tare da AA a daidai inda sukai parking yana kallon mu.
Yi nayi kamar ban gansu ba na dukar da kaina a kasa ina ba maryam amsa ya karaso yana gaida mutane tare da sallama suka amsa mai a mutunce suma don yadda yazo masu din.
Bayan ya gaisa dasu ne yake tambayan driver motar ce ta samu matsala yace wallahi Alhaji lafiya kalau kuma na fito da ita halin karfe ne kawai.
Wurina ya mayar da hankalinshi yana fadin khadija ina zaki haka a wanan lokacin bamu sani ba kuma ?
Ko kaina ban daga na kalle shi ba nace KD a takaice wata mata da muke mota daya ta dan manyanta matar dama akwai zuba don bakin ta bai huta ba tunda muka tsaya din.
Sai cewa tayi malam hala matar ka ce matar oga nane gashi can a cikin mota zaune tace haba.
Tun shigowan mu nasan yarinyar nan diyar manya ne ko kuma matar wani babba dama ina mamakin abinda ya shigo da ita motar hanya yanayin ta kawai ya nuna min haka.
Dago kai nayi ina kallon matar da mamaki karara a fuskana zan yi magana tace in kina ma Allah kiyi hakkuri kibi mijin ki yarinyar nan kila shiya sa motar tamu tsayawa haka nata tashi ba kin ko san girman tashi (yaji)ga diya mace wurin Allah.
Aiko jin haka sauran mutanen suka sa muna baki a lokaci daya ga abin dariya abin kuma haushi har da drivern suna ta bani hakkuri.
Drivern da kan shi ya dauko jakkata wanda dan karamin traveling bag ne na saka kaya na a ciki dama, driver ya dauka yakai wurin motar tasu.
Hannu Yusuf yasa a aljihun shi yaciro kudi yaba duk mutanen dake wurin dubu bibiyu wai su shiga wani mota su tafi.
Godiya sosai sukai mashi suna kara min nasiha akan hakkurin aure anan kan dariya saida ya subce min a fuska na.
Bude min baya yayi wai in shi ga naja na tsaya a wuri daya bakin motar tare da fadin kada ka manta na fada ma bazan sake shiga motar ku ba again.
Haba khadija ai ko don idon mutane nan da nayi wa karya ki daure ki shiga ji yadda matan nan ke hada ki da Allah tana fada maki yaji fa baida kyau ga mace .
Wa nayiwa yaji din ai gara su san gaskiya tinda ban san inda zan kara haduwa dasu ba yanzu idan mun rabu don haka please sauke min kaya na in tare wani motar in tafi.
Don gidan mu a motar haya muka saba tafiya tunda bamu da motar yace please kanwa na kada mu tsaya jayayya anan kiyi hakkuri don girman Allah mu tafi yamma keyi yanzu hanyan kuma babu kyau kin sani.
Girman Allah da ya ambata ne yasa na shiga motar ba tare da nayi wani magana ba kuma sanyi da kamshin motar ne suka daki fuska na a lokaci daya.
Kira, a ke tashi a cikin motar a hankali muna shiga sauran motocin suma suka tashi muka kama hanyar kaduna ga yamma yayi.
Sai da muka danyi nisa da tafiya yace kin daiji abinda manyan mata suka fada maki fushi baida kyau khadija don ko wanan tafiyan ya ishe ki ki gane mu da alheri muke bin ki khadija.
Sai yanzu AA yayi magana da cewa ke kina haukane ko rashin sanin ciwon kai ne yakai ki bin motar haya cikin wa yan nan mutane haka masu yawa.
Idan wani abu yaje ya samay ki a cikin jejin nan fa kina son ki salwantar da rayuwan ki ne a banza ko may ?
Tunda ya fara magana ban dago kai na kalle shi ba kaina yana a wayata sai da naji ya fadi hakane na dago kaina nace a tsiwace .
In salwantar da kaina kamar yaya don kawai nabi motar haya zan salwantar da rayuwana yace a zurke yana kallona.
May yakai ki shiga motar haya a wanan hanyar ?
Nace ai kasan ubana tallakane ko banda motar da zan shiga inwa mutane tsiwa asan ina dashi, don banda motar ya wuce ta haya a yanzu don kowa yasan ubana ban kwadayin karaya ko abin wani a rayuwa.
Wani kallo ya watso min daga inda yake zaune ya kada kai ya koma ya zauna yana maida numfashi.
Yusuf ne yace kaunata kin san kowa ke din mai tsada ce a yanzu don Allah kibar wanan gangancin da rayuwan ki murmushi nayi nace ganganci kai nama rasa may zance dasu alokacin.
Gudu suke shararawa da mu sai can ya juyo kamar mai maganar lalama yana fuskantana yace kina jina daga yau duk inda zaki ki buga ma Yusuf waya a turo maki mota bana son shiga irin wa yan nan motocin please I hope you understand me ?
Malam bafa don na shiga motar ku bane yanzu zaisa ka dinga bani commad son ranka ina dai nike da rayuwana bawani ba.
Ya ce haka kika ce nace kwarai kuwa don may zan ka so takura min kamar wani wanda ya ajeni can a gidan shi.
Ya juyo ya kara fuskantana yace haka kike so kiga an adanaki a gida ko sanan zaki bi maganan da ake fada maki na kula da kan ki ?
Nace haka din ne ai shiya na fada haka kawai ba matar aure nake ba zaka wani kafa min doka kamar wace ke karkashin wani.
Yusuf yace kai kanwa ta ba kayau ne haka yasa kikaji ana maki magana kada ki dauki zancen da zafi mana.
Yace barta ai ka santa da bakin tsiya wanan bakin naki ya kai karshen tsiwan sa daga yau zaki kula kisan abin fadawa mutum.
Wai ma may zaki je kaduna a wanan lokacin haka kuna karatu ko kin fara wasa da karatun ki ne yanzu ?
Nace kai wanan ya dama ni gurin yar uwata zanje in dubata karatu kuma nike da abina ba wani ba.
Murmushi yayi yace yarinyar nan ina tausayawa ranan da bakin nan naki zai dinke ya koma shiru wallahi kaina na kawar wanan karon ban biye mashi ba ya koma ya jingina da kujara ya dafe kan shi da hannun shi daya.
Sai Yusuf ne ke dan jana da hira jefi jefi ban bashi amsa sosai sunyi sayayya a hanya sai ba a wani dade ba sai gamu mun shigo garin kadauna garin gwauna.
Lokacin duhun yamma ya fara a yi sosai nace ku sauke ni in karasa a motar haya wani irin kallo ya watso min daga inda yake zaune yace saboda kin saba shiga motar hanya baki mai dashi komai ba ko ?
Koda muka shigo layin mu har an fara kira a wasu wurare na magariba daidai get din gidan Ya Amina Yusuf ya tsaya da motan da muke ciki na fito tare da fadin yayana na gode sai da safe.
Ki gaida sister idan kin shiga kice muna mata yaya jikin kafin mu shigo gaida ita zataji kawai nace dasu na dauki jakata na nufi ciki.
Sai dai may daga get din har ciki a rufe na gansu waya na ciro ina kiran ta har ya katse ba a dauka ba nan dai na sake kira karo na biyu yana gab da katsewa ne aka daga wayan nace.
Ya Amina kina ina nazo gida ban samay ku ba gida a rufe khadija ce nace eh don ba muryan ta naji ba a wayan.
Tace mommy