ya karanta zuciyar abokin nashi ya karaso gaban tebur din shi yana fadin wani abu ya faru ne na ganka haka.
Tsuki yaja tare da juya kujeran da yake zaune sama yace may ye ma bai faru ba Yusuf wai kasan matar nan bata gida tun ranan da muka tafi kaduna.
Ba ita ta dawo ba sai karfe biyu da wani abu ta shigo gida jiya da sauri Yusuf yace ina taje haka ko da sanin ka ta tafi yace idan na sani abin zai damay ni haka ne ?
Kai wai may yasa wasu matan samun wuri ke sa su wuce limit din su ne na mata akan may mace mai ciki zatayi irin wanan tafiya haka ba tare da sanin mijin ta ba.
Bata tsoron wani abu yaje ya samay ta a can yace ma Yusuf ni ba wanan ne damuwa na ba damuwa na shine ina taje ?
Jiya jiyan nan Khadija taban wani mugun labari wai buzaye sukan baro mazan su na gado su shigo nan suyi auren bugi don kudi ni wanan abin shi abinda ya tsaya min a rai na.
Ita Khadija ta fada ma hakana sosai kuwa jiya muna tare da ita tana zayano min halin buzaye sai naga babu abinda ta rage daga cikin halin Nafisa har ma da wasu da ban sani ba takara min haske akai.
Lalai Khadija jarumar gaske ce tunda har ta tsaya ta iya fahintar dakai wanan abin yace ka san hauka irin nata ita bata dauka maganan ai zaiyi tasiri a raina ba haka.
Yanzu fa har na fara zargin yawan tafiyan Nafisa kasan su akai akai da takeyi tunda gashi har yakai ta fara satan tafiya haka.
Da fa shi yayi yace kada ka zargeta da wanan don ta fadi haka ba lallai ne haka ya zamo gaskiya ba akan Nafisa din sai dai idan wasu sun su suna yin hakan bance a a ba don son kudin su yayi yawa.
Kai ina bazan yar da ba Yusuf ko na yarda da komai ba zan yarda da wanan gantalin da Nafisa ta dauko yi ba dole ne in dauki mataki a kai.
Tunda ta fara haka maganin abin kawai ya kamata kayi don tana ganin ita kadai ke gare ka yasa take abinda taga dama a gidan.
Yanzu zabi biyu shine nake ganin mafita a gare ka na farko walau Fati ta dawo ko nabiyu ka kara aure don ganin da takeyi ita kadai ce yasa take wa yan nan abubuwa haka.
Ido ta kura wa Yusuf dake magana sai da yayi shiru yace Fati ita ta kasa zama saboda rashin hakkurin ta.
Kai ya girgiza mashi yace ka daina fadin Fati bata da hakkuri halin Nafisa dai ya kori Fati gidan ka wanda a lokacin baka ganin haka kai.
Zaka iya bata wani daman a yanzu ko abin zai gyaru a tsakanin ku amma fa sai ka jajirce wa hakan kafin komai ya zama dai dai don Nafisa shuumace ta kwarai.
Ba zata taba bari kuyi zaman lafiya da Fati kawai a gidan ka dole sai da wace mace a tsakani mai kwato mata nata hakkin idan kun cuta mata.
Bai iya magana ba sai jawo file din gaban shi yayi ya fara aiki ba tare da ya san abinda yake yi ba.
Fita yayi ya bar mashi office don yasan halin tunda yayi haka ba amsan maganan shi zai samu ba a lokacin.
Ya kai wani lokaci yana aikin da zuciyar shi raki sakewa don haka ya rufe files din ya mike tare da nufar hanyar fita office din.
Gida ya nufa kai tsaye lokacin sha biyu da wani abu na rana tun daga kofa yake jin tashin sautin wakan yan yaren su cikin harshen buzaci ya karade gidan.
Bai ko kali gefen da suke zaune ba ya hau sama ya shige dakin shi tare da rufo kofan da karfi zuwa yanzu sun fara isan shi a gida.
Mutane haka ba kimsi ko kadan sai bakin ci da ihu yau ma don samun wuri kidan suka sake mai haka a gida anya ma suna wani cikaken ibada kuwa tunanen da yake kenan Nafisa ta turo kofan dakin ta shigo.
Sau daya ya kalle ta ya kawar da kanshi gare ta ta karaso kusa dashi da shi ra tsaya cikin murya da maida hankali gare shi tace lafiya yau kadawo a wanan lokacin haka ?
Kallon ta yayi ya kawar da kan shi gefe daya ta sake cewa magana fa nake maka wai may ke damun ka ne haka ?
Ya dago ido ya sake kallon ta da idanun shi da sukayi jawur yace ban son damuwa a wanan lokacin tace haba mai gida ai wanda duk ya ganka a wanan lokacin yasan akwai damuwa a tare da kai.
Matsalar ki ce ta isheni Nafisa in ma ina da damuwa bai wuce halin ki ba tace halina na kamar yaya wani abin nayi maka ko may ?
Au baki ma san abin da kikai min ba ke nan kike nufi tace don kawai na fita na dade shine zai zama matsala haka ?
Fita nayi kuma gani na dawo lafiya sai may da zaka dauki wanan a babban matsala kuma ko nace ka barni in fita na san ba barina zakayi ba inje inyi lalurar gabana.
Ina kika je har kwana biyu baki gidan nan tayi shiru tana tunanen karyan da zata yi mashi ya yarda da ita a lokacin.
Ya sake tambayan ta sai tace na tafi bukin kawata ce da ta haihu a jos don ko na fada ma ba zaka yarda in tafi ba.
Duban ta yayi cike da zargin ta sannan yace wata kawa kike da ita haka a jos da ban santa ba har zaki iya zuwa ki kwana biyu a bukin ta ?
Ta dan zaro idanu tace dole ne sai ka san kawaye na duka wai yace da kyau Nafisa wanan halin da kika dauko a yanzu sam ba zan dauke su ba .
Tunda har kika iya tafiya na kwanaki don kawai bukin wata kawa taki buki nawa akayi a gidan mu sau nawa kika taba zuwa?
Sam yanzu zuciya ta ta soma zargin ki da aikata wani abu akaina da ba daidai ba sakamakin hurda da matan barikin da kike a yanzu.
Zargina ka fara ne Samad akan may ba zan rage ki ba halayen ki gaba daya yanzu sun gundureni baki zama gida ba yar aiki ba ba wata yar kasuwa ba amma ke kenan kulun yawo fita.
Gaba daya kin shiga rayuwana kin hana min farin ciki kin hana mata na ta zauna dakinta ke kuma ba kula nake samu a gurin ki ba.
Au matar ka kace kace dama matar ka kake son ta dawo kawai kake wanan kamay kamay haka idan zata dawo zaki hana ne ko may ? ,
Ta dube shi a hasale to ta dawo din mu gani mana sai may yadda ta dawo haka zata koma da kafan ta.
Yace haka kika ce tace na fada sai may ?
Baya ya bata batare da ya kara juyawa kanta ba ta tsaya tana ta jidali wai ai dama ta sani zuwa kadunan da yakeyi yanzu saboda fati yake zuwa da yaran shi.
Mamaki yayi sosai da ta iya karfin halin furta hakan lallai yasan ya cuci Fati da yawa ita da tazo daga baya ta iya fadan haka ?
Ina ga Fatin da zaman gidan ya gagare ta da yaranta dole suka bar mata gidan har diyan shi ita ko tana zaune yan uwan ta da yarta a cikin salama.
Lalai ya tabka babban kuskure a rayuwan shi dole kowa nashi ya tsane shi yanzu don sam shi bai taba hango wanan abin ba sai yanzu da taimakon Yusuf da khadija suka ganar dashi gaskiyar hakan.
Ido ya rufe kamar yana barci don bai son hayaniya ko kadan gashi ya jawowa kanshi yar hayaniya a rayuwan shi bai taba nadamar auren nafisa ba sai wanan karo.
Mikewa yayi ya shiga ban daki ya dauro alwala yazo ya tayar da sallah azahar ya gama ya dade zaune a gurin anan wayan Yusuf ya shigo mai yana tambayan shi yana ina ne ?
Yace gida sai ya kashe wayan yasan damuwa ce taimai yawa yasa ya koma gida yasan ko a gidan ba wani sauki zai samu ba, don ko yasan Nafisa ba zata kyale shi ba.
Sai dayayi sallah karfe hudu ya fito daga gidan kai tsaye ya yanke shawaran zuwa guri na don irin shammatan junan da mukeyi yana sashi nishadi a ranshi haka yasa ya nufi inda nake.
Bai faye son zuwa wurina tare da Yusuf ba yanzu don idan sunje tare hiran kan koma tsakani na da Yusuf ne don bai iya sake jiki yayi komai a gaban Yusuf di yanda ya samu dama a zuwan karshe.
Ya iso bakin hostel din sai da ya kare ma gurin kallon yadda mutane suke ta faman shige da fice ya daga waya ya kirani kamar kullun gani kofan hostel din ku yace ya kashe wayan.
Muna zaune girki na gama muna muna ci kiran shi ya shigo min kalon maryam nayi nace wai may wanan mutumin ke nufi ne maryam jiya fa ce min yayi zai yi tafiya ba zamu sake haduwa sai ya dawo yanzun kuma may zo nema nan ?
Dariya tayi tace ke mana don Allah tashi kije kada ki bata mai lokaci dan hararan ta nayi nace na kirashi ne ?
Sai da na tsaya shirya nasa wasu material a jikina din kin buje da riga akai min wani zuwa kaduna da nayi maron colour dinkin yadan matse min jiki kadan don dan jikin dana kara yanzu.
Sun kama min jiki tam sai kitson da mukayi satin nan na ghana wiving ya kara fito min da fuskana shar ga matsiyacin kamshin dake tashi a jikina wanda ke tafiya da imanin wanda ya shaka.
Tun daga nisa ya zuba min ido yana karewa shiga na kallo har na karaso inda yake kofan motar ya bude min wai nashiga.
Naki nace cikin girgiza mashi kaina yace common shigo don Allah mu tafi rakiya zaki min wani guri da sauri nace a hakan zan tafi wani gu.
Ko banza kuma ba zan shiga motar ka ba again agogon hannun shi ya duba yace cikin dakewa kina bata min lokaci ki shiga mutafi.
Tunda muka fara tafiya ba wanda yai magana a motar sai shi dake tuki a hankali cikin wani irin yana yi yana yi yana wani furzo iska daga bskin shi lokaci lokaci.
Sai can ya juyo inda nake yace zakici wani abune kaina yana a waya na da sauri na dago kai nace wani sai kuma ja girgiza mashi kai nace ni a koshe nake.
Ok rakani inci wani abu tun safe banci abinci ba da sauri na zaro ido nace azumi kayi ne ?
Dashi nayi ma da zai fi min sauki yace ba tare da ya dube ni ba na mayar da kaina ga titi ina kallo sai kuma can kamar an tsunkule nace matar ka tayi tafiya ne ?
Bai bani amsa ba sai karya kan motar shi da yayi zuwa wani restaurant din abinci mai kyau gurin da daukan ido ya parke a wurin .
Mun shiga naga tsarin wurin yana da kyau sosai da alama yasan wurin da kyau don wani ke bebben wuri naga yana nufa a cikin wurin.
Min zauna masu aiki gurin suka zo suna tambayan shi mai za a kawo muna ne yace ferfesu kawai zai sha bayan an mika mai dan takarda ya duba.
Koda aka kawo mai bai wani sha da yawa ba naka ya aje cibin yana goge bakin shi tare da fadin tashi muje kawai nikan mike wa nayi nabi bayan shi.
Sai da ya biya su kudin su muka fice muka bar gurin ina mamaki a raina nace yaya mutum kamar shi baici komai ba sai a wurin cin abinci zaici kuma bai tsaya yaci wani abin kirki ba.
Kasa hakkuri nayi nace amma wanan ba girman ka bane cin abinci a waje alhali kana da iya li kuma a gari.
Kamar bai jini ba yana tukin shi sai dai ban san ida muka nufa ba can naji yace dani yaya kike son inyi khadija in banci abinci a waje ba ?
Kamar yaya kuma kana da mata a gida zaka ce haka yaya Abdul yace sunana Abdulsamad ko ke ma zaki bata min suna ne ?
Yi hakkuri bani na kashe karen ba ratayan buzu ba zai zama nawa ba in bai zama naki ba wace ki dauki karen ?
Naci yau kana da magana ke nan yace da yawa khadija iam not in good mood at all.
Ayyah sorry Allah ya sauwa koma maye yayi maka mafita a kan shi yace amin na gode da adduan ki gare ni yaci gaba da tuki.
Matsala a gun aiki ne ya taso maka yace matsala a gida na yake subbahanallahi nace dashi tare da dan kallon fuskan shi.
Yace khadija dole in ci abinci a waje ko in zauna da yunwa ko zaki taimaka ki dinga bani abinci in dinga zuwa wurin ki ina ci idan na taso office.
Kai don Allah ka daina zolaya abincin yan makaranta ne zakaci wanan ai sai mu da yazama muna dole muci shi.
Badai ke kina ci ba nace sosai kuwa yace to ni mai zai hana inci tunda ke kika iyaci sai dai idan rowa zaki min kuma beside ke kika ce na daina cin abincin waje.
Nace matar da ran ta da lafiyan ta zaka wai ni na dinga dafa ma abinci kamar wata wacce ka aje da zaman banza.
Bai kara magana ba sai horn da yayi a bakin wani gida aka bude mai muka shiga dayan motar da suke zuwa wuri na da farko ne na gani a gidan.
Maigidan na ciki ya tambayi mai gadi ya na gaishe shi bai amsa ba ya jefa mai tambayan shi sai maigadin yace yana nan bai dade da shigowa gidan ba.
Fita yayi daga motan ya zagayo ya bude bangare da nake zaune jin ya tambayi mai gidan yasa banji wani tsoron shiga gidan ba.
Sanyin A C ne ya tari fuskana da kamshin air freshner da falon ya dauka falon ya tsaru komai akwai a ciki ga wasu manyan kujeru da aka kawata falon dasu.
Yana waya koda muke shiga gidan yana fadin kafito gamu a falon gidan ka yace a wayan baifi second ba naji ana bude kofan daga cikin gidan sai ganin Yusuf ya fito yana saye da kayan shan iska irin ta maza wando dogo tare da yar riga armless a jikin shi.
Yana gani na ya bude baki da mamaki yace kace yau ina da babban bakuwa a gidana ina kafito da yar mama da yamman nan haka ?
Ya nuna mun kujera da hannu yace bissimillah zauna mana khadija bamu hadu ba sai yau nace ina wuni ya amsa da lafiya kalau ya kike ?
Ina nan lafiya yace Alhamdullahi yau sai gaki a gida na kwatsam na gan ki ba tsammani nace wallahi ga wanda ya dauko ni nan bai fada min ida zamu zo ba yace dai wani guri zan raka shi.
Yayi maki wayan manya kenan don ya baki mamaki dan hararan gefen da yake nayi mikewa Yusuf yayi yana fadin barin kawo maku abinsha sai dai kiyi hakkuri kin san gidan gwauro kika zo.
Da sauri na dago kai ina kallon shi da mamaki nace baka da aure ne dama yace eh baki sani bane yar mama ?
Ashe mutumin bai fada maki komai game da ni ba yace ma Yusuf din an fada ma kowa irin ka ne mai zuba a lokaci guda.
Yusuf yana dariya ya wuce inda fridge din shi yake ya dauko drink a ciki tare da kofuna ya kawo gaban mu ya aje nidai ido nake binsu dashi kawai.
Ya aje tare da zama yana fadin bissimillah kusha lemon shi yasha nin ban sha ba gani nake kamar plain ne suke shirya min in fada ciki.
Yayi yayi dani don insha nace wallahi na gode mai zai sa ka damu haka idan bata sha ba yace mai kasan bakuwa tace ita dole in damu idan tazo gida na bataci wani abu ba.
Daukan cup nayi na tsiyayya kadan na dan kurba na aje cup din ina fadin na gode shima tunda ya kurba sau biyu ya koma ya jingina da kujera tare da dafe kanshi da hannun shi .
Yaya dai Abdulsamad lafiya ko dan tsuki yaja tare da kara dafe kan nashi fuskan shi ya nuna alamun bacin rai da damuwa.
Juyawa yayi guri na yana fadin may ke faruwa ne khadija nace nima haka naganshi wallahi ko maganan da nayi mai ne yasa shi bacin rai ban sani ba ?
Ni kuma gaskiya na fada mai ba girman shi bane cin abinci a waje ban san ranshi zai baci da kalamina ba na fada mai haka.
Dariya ya dan yi tare da fadin see you akan dan wanan maganan zan bata