Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MIJIN Buzuwa Complete Complete Hausa Novel by Nil

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   140 / 144

417K to 420K   out of 431K words

tawagan su anan anty Fati ta shigo ta samay mu gidan sukayi kanta da korafi.
Sai buda baki tace ai ga amaryan ku nan tana maku yadda kuke so ko don haka ba sai mun shigo da wuri ba mu.
Ina jin su ban son abin rashin mutunci ya shiga tsakanin mu ko kadan sai nayi shiru ina dan dariya.
Taci gaba da fadin kin san ku ko wace amarya tazo maku daa kalan rawan ta wanan da alama ta shigo da kafan dama don baga yayan ku kawai abin ya tsaya ba har ku ta gama kwashe kafan ku.
Fauziya tace mu khadija kin san ta wuce matar dan uwa a gurin mu don tun kan ta shigo take yar gidan nan ita ma don haka bata yada mu muma bazamu yadda ita ba.
Faiza ta dora da fadin khadija bata son kanta bane a cikin mu don tayi kokarin abinda ku kuka kasa yi tun farko akan gidan dan uwan mu don aljihun ku kawai kuka sani.
Nan dai abin yaso ya zama masu fada a tsakanin su sai da momy da yan uwanta suka shiga tsakanin su don ta fara fada masu bakaken magana wanda duk a fakaice dani take yin zancen suna mayar mata da amsa.
Nafisa bata shigo ba sai karfe uku na rana da wani abu ta shigo gidan da yan uwan ta ba wanda ya kalle ta yadda take shigo masu da izza abaya sai gashi wanan karon ta shigo gidan bata samu kulawan kowa ba agidan duk kuwa da adon da tasha na fitar buki irin nasu na kasan su.
Bata dade da shigowa ba don ko haduwa bamuyi ba muka koma gidan don shiryawa na samu laraba ta gama girki data koma ta hada miya na karasa hadawa kafin mu shirya ina san ran ya karasa.
Dama tun safe kafin in fita na hada komai yadda nake son yi hankalina ya kasu biyu ga girki n miji ga sha,anin buki.
Laraba ta kyauta min don abinci tayi wadatattace da zai ishi kowa har a raga a gidan sai gashi ya kirani a kuraren lokaci akwai baki da zasuci abinci a gidan na dare.
Shigowan mu daidai ana wankin amarya muka shigo filin shigar mu kawai ya dauke hankalin kowa a gurin don shiga ce ta alfarma.
Alkasim na gefe a mota dake jibge da kayan da zan raba a gurin Altine da fauziya ce zasu raba don su suka san mutanen su.
Da ganin an fara rabo hankalin mutane ya koma can har ana batun rufe su dakyat na kusa nasa Alkasim rufe kofan motar gabadaya.
Nace ya koma gida kawai ta bar gurin duk wanda ya karbi jakka ko roban sai ya karanta hoton yan biyu ne da sadiya suna dariya aka dauka.
Tun maryan da sauran kawayena na nema muka wuce gida ban koma cikin gidan ba sai da muka shiga ne a cikin dare na tura laraba da duk wani gifts din bukin takaiwa matan gidan su AA wanda na ware masu.
Bayan isha,i ne bakin shi suka shigo gidan ga shirin zuwa diner da zamu banda halin zuwa don AA na gidan da bakin shi.
Bakina dasu laraba ne suka wuce a mota na don ban sa ran zuwa guri ba sai gashi yana fada muna mu shirya don tare dashi zamu tafi dukkan mu.
Shiri sosai kowan mu yayi dama akwai kayan da anty hauwa ta sayo min a dubai suna saka sai sai gashi shigan mu yazo kusan daya dashi farin yadin mazane a jikin shi mai tsada.
Anty fati ta fara fitowa sai nafisa na dan bata lokaci don tsayawa gyara sadiya data bata jikin ta da yake yarana suna da kafan su shiya rike su a hannun shi biyu zuwa wuri mota.
Ni kuma na dauko sadiya a kafada na kowa satan kallon shigan dan uwa yakeyi munzo shiga mota a raina nace zanga yadda za ayi yau.
Sai naji yace Fati ke ki shigo gaba su zauna a baya su kamar nafisa ba zata shiga ba sai dai taja ta shiga ya tayar da motar fati sai sauke ajiyan zuciya take yi.
Yaran suna gaba a wurin su zan iya cewa wannan ne karon farko data dauki yarana a jikin ta kota kulasu.
Mun shiga wurin wuri ya cika da mutane yana neman gurin da zamu zauna ne naji muryan Altine na fadin kawo sadiya in kama maki dama sai da nayi tunanen barin ki da mukayi da ita ai.
Ni naga karfin hali a gurin Nafisa ko kallo yar bata isheta ba wai ita ala dole ta barmin yarinyar don nawa ne dama.
Mc da yake abokin su ne ya shiga baradawa ga AA abokin ango yayan amarya da iyalin shi sun iso kallo ya dawo gare mu.
Daga can gefe gulma ya tashi yana gaba tare da nafisa ya dawo muka jera daniyar daukan mami sai yace in dauki Alamin muka jera tare da anty Fati da muke tafe tare muka sakashi a tsakiya sai da ta juyo ne ta gamun a hakan tafe ba yadda zatayi haka muka kai mazaunin mu.
Nan ma yana kusa dani sai dai mun sashi a tsakiya dani da nafisa din Fati tana daga gefe na don ban dauka wani magana yana hadata da buzuwa ba.
Dan rankwafowa yayi yana fadin yau kinga yayan ki baki yaki rufuwa Altine ne ta karaso tana rada min wai su maryam basu samu wurin zama ba.
Tambayana yake yasa ya dan duko min ina fada mai abinda ta fada min sai jin hasken wutan camera mukayi a kan mu ana dauka mu hotuna.
Wani ya yafito yazo ya danyi mai magana bada jimawa ba sai ga wani sit ana gadawa a gurin.
Aka nemo su cikin loundspeaker ana neman su suzo ga gurin zaman su kusa damu suka zauna maryam don gulma ta zauna a setin mu.
Duk wanan abinda ake sai sakon harara yake samu daga wurin nafisa itama fatin ba wani walwala a tare da ita turanci da nuna wayewa ke tashi a gurin.
Duk wanda yazo dani zamu gaisa sai fati dakan dan saka baki gefe zakaga mutum na fadin ya muke ya iyalin mu sai in buge da bada amsa.
Dinner yayi kyau sosai sai dai bai bari an tashi ba yasa mu bar gurin don yara saboda sanyi tayi yawa a gurin don haka muka bar gurin a cikin lokaci.
Baya munyi hotuna da amarya da ango muka bar gurin zuwa gida saboda laraba da muka baro gurin bukin don haka ko da muka dawo ban huta ba don shirin yaran da nakeyi na kwashe su zuwa dakin shi.
Sai gasu maryam sun dawo nadan dade a gurin su sai daina basu komsi don sunce tea zasu sha kafin su kwanta larabs na saka ta dubamin su.
Na samu ya gyara min kwanciyan yaran guri daya ya ajesu su uku don haka muka manne da junan mu a gefe daya mundanyi fira kafin komai ya kan kama muna mukai barci cikin jin dadin kasancewa da junan mu ga yan diyan mu a tsakiyan mu.
Washegari da wuri na fito don shirya abincin baki saboda ranan su maryam zasu juya Abuja ina tsakiyan aikin ne hayaniya ya taso a sama ashe fitowa na nafisa ta shiga dakin shi.
A fusace taje da tambaya may ye matsayin ta a gurin shi ne do bata gane ba don may zai ban girki bayan ita gata yace don tana matana ita din.
May kake nufi da ita matar kace nifa a matsayin may nake gurin ka yace wanan kuma yanzu ba zan iya fada maki ba sai nayi shawara nan gaba.
Nan har yakai suka fara sa in sa har yakai ya mike ya fara jibgan ta suna tonon asiri ga junan su duk wanda ke gidan ya fito.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/27/21, 6:51 AM - Xxxxx: Yanzu kokarin kammala karatun mu mukeyi wanda muna a matakin karshe haka ya jawo min rashin zama sosai a gida.
Sai yamma lis nake dawowa gidan da na dawo kuma na dan huta bayan na gama ibada sai in shege barci don gajiya.
Duk yadda Altine kan so muyi hira hakan bai samuwa a gare ni ban san may yakai Nafisa garin mu ba ranan na fito don zuwa school ina sauri sai ji nayi tana fadin iyayyen ki na gaida ke mun biya munga gidan ku .
Mamakine ya kamani don jin kalamin ta matar da ba wani hurdan arziki yake hada mu ba may ya kaita gidan mu kuma.
Nagode Allah ya bani ikon amsa mata dashi na fice ba tare dana dora wani magana ba akai sai dai a raina ina mamakin zuwan ta minna din da tayi.
Banda lokacin wanan don haka ban tsaya bin ta nata ba kuma Allah ya taimake ni mun gama komai na project nayi sumiting.
Na fara jin shakat a tare dani yasa ina dan zama gida yanzu a cikin iyalina yanzu muna da masu aiki dake girka abincin gida gaba daya wa kowa don haka ba wani aikin komai mukeyi ba mu.
Arzikin AA ya bun kasa sosai bai damu da tsayawa yayi aikin nan gida Nigeria ba ko yaushe yana waje mu kan mu ba kullun ne muke ganin shi ba nan.
Sai dai idan ya zone kasan ba mai hutu a cikin mu don yawan aikin da muke na fama dashi da bakin shi dole sai mutum ya leka kitchen din ya duba abinda sukeyi.
Na fada ma masu aiki abinda zasu girka min yau kafin in fita sai na dawo na samu wai Nafisa ta shiga tace dasu kada suyi abinda nace sai wanda ta fada masu din.
Raina ya baci gashi muna saka ran dawowan maigidan a ranan kuma nice da girki idan ya dawo ga auren maryam daya taso kwatsam a satin da zamu kare satin za a fara bukin.
Part din Nafisa na shiga wanda zance tun da akai wanan gyaran ban shige shi ba sai ranan nayi mamaki ganin part din dam da buzaye yan uwan ta wanda ban san lokacin da suka zo ba ma.
Da farko naji dan shakka yin maganan da ya kaini amma ganin sun gani nashigo ya sa na dake na karasa dakin ta don tsarin ginan iri daya ne da nawa na kwankwasa kofa na shiga.
Tana zaune da bakuwa sun baje kaya a gaban su ana mata bayani wanda ashe akan yarana akai wanan tafiyan ban sani ba ni.
Allah ya taimake ni ban wasa da ibadana duk ko da daulan da Allah ya kaini a cikin sa na dawo khadija na ta farko sosai ban yarda na shagala ba da addinina.
Shima kan shi maigidan yanzu ya canza sosai don koda zan falka zan samu ya rigani tashi yana gabatar da nafila a cikin dare.
Daz mamaki suka kalloni nan ta fara fadan borin kunya wai may na shigo mata shiya yi bata shiga girina va don may zan shigo mata.
Suna kokarin boye kayan da na samu an baje ana kula sheri farin kudine sai dodon alkwato da kan wasu mushen halittan daban san ko may ye ba.
Na gama kare ma kayan kallo a cikin second nace zuwa nayi nima inji dalilin daya sa na bada kalar abincin da za ai min kika shiga kika ce kada su girka min shi.
Jimun wanan yar matsiyatan don Allah zuwa kikayi yanzu ki makure ni ko may ta fada tana min wani irin kallo nace zuwa dai nayi in maki kashedi akaina da komai nawa.
A matsayin ki nawa a gidan nan ke yanzu fa nasan komai akan ki don haka baki da wani bakin da zaki mun maganan banza a gidan nan.
Don naje har kuryan dakin uwarki na gani naga abinda kike mun tunkaho dashi ba komai banda tsiya a gidan naku.
Alhamdullahi tunda muna da gida har kinje ashe nafiki don iyayyena dai ban barsu a kango zaune ba ko bukka ta kwashe da dariya tace karya ke nan wallahi kowa ya ganin yasan gidan dana fito ai.
Dama na nemi gidan ku ne don in kashe maki wanan alfaharin naki a gidan nan don na samu abin fada maki watarana nace nafi kowa sanin haka ai don ba zuwan alheri ya kaiki gidan mu ba.
Sai dai nasan duk yadda gidan mu yake nan yafi gidan ubanki sau dubu albarka koda banje ba ina da labarin komai a kunne na ga wayanda sukaje suka gani.
Ban fito ba sai da muka fada ma juna magana son ran mu na fito dakin da farko abin yaso ya damay ni a raina sai daga baya maryam tace dani akan dan maganan nan zaki damu kanki dashi.
Cin tuwon kishiya fa ranko ne ko birnin masar take sai munje mun gano gidan su wallahi don taji inda dadi hakan balle banga abin kushewa a gidan ku ba ai.
Sherin kishiya yanzu khadija wani iri ne baki sani ba kuma har da wanda batayi niyar yiba kin sani banga abinda zai damay ki ba ni.
Haushinta dai daya yanzu duniya ta daina yi da ita babu bakin cikin ta sai ta bude ido ta ganki a cikin gidan nan dake da yaran ki.
Da wanan maganan na maryam na manta da zancen ranan sai Allah ya taimaka bai dawo ba a ranan ya dage tafiyan sai wani sati mai zuwa zai dawo.
Tun lokacin da muka fara bukin maryam banjin dadin jikina sam zazzabi nake fama dashi sosai dole na samu time naje asibiti don a dubani sai dai result din ya ban mamaki jin wai ciki ne dani.
Sun bani magani na dawo gida na boye takardan naci gaba da ahan magani na banje kaduna na ba jos na wuce inda a can za ai bukin maryam din.
Wanan yasa hajiya umma yin korafi akaina wai na fifita gidan kawa na sama dasu don shi kanshi AA baiso in tafi jos din ba sai danayi ta magiya ya yarda na tafi.
Wahalce nakai jos kwanan mu uku ana shan shagalin buki muka juyo zuwa kaduna a dadafe na shigo kaduna don jikina daya kiya min tuncan.
Fada ya fara wai ai saida ya fada min karnayi nafiyan nan na nace sai nayi dole ya tasa ni gaba zuwa asibiti a cikin daren muka je.
Tambayan farko shine ko ina da ciki ne ya wani kura min idanuwan shi don son jin amsan da zan bayar a sanyaye na daga ma likitan kai alaman eh.
Zama ya gyara yana saurare na likitan yace wata nawa nace biyu sai ya rubuta min magani yace tafiya da jigilan bukin danayi ne ya sa min wanan zazzabi haka.
A raina nace koma may zai fada ya fadi yanzu dama don kada ya hanani sha,anin buki naki fada mai zancen cikin da wuri.
Har muka dawo gida bai min magana ba sai da zan fita mota naji yace baki son cikin jikin naki ne da alama don tunane na ya nuna min hakan.
Dan kallon shi nayi banda bakin magana don yanayin da nake ciki nace ban iya magana yanzu don Allah ina kokarin fita daga motar .
Mun samu masu zuwa gurin dinner nata kokarin zuwa nikan nasan ba halin haka gare ni ina shiga na shige dakina na dunkule.
Laraba ya kira ta hada min tea in sha insha maganin da aka bani tunda ya fita bai kara lekowa ba nasan sun tafi gurin dinner din ne sai ni da laraba kadai muka rage a gida.
Can ma hankalin shi bai kwanta ba don haka ya dawo gida sai dai ya samu ina barci na hankali kwance tare da yarana su uku a dakin.
Sai laraba data gama gyara bandakin dana bata tana saka kamshi a dakin ya shigo baidade ba tunda ta fada mai nasha maganin sai dai nayi ta amai daga baya.
Jamma suna tambayana ake fada masu na dawo banda lafiya ina gida kwance haka yasa mutane da yawa sukaji rashin lafiyan nawa.
Da safe na dan tashi jikin nawa da dama don haka nayi wanka na gyara jikina na koma na kwanta muna waya da maryam din nan nake sheda mata abindake damu na.
Tayi mamaki nace nasan ki da baki tsiya dana fada maki tun farko dayan zu ba ai bukin nan dani ba don idan ya sani ba inda zanje kema kin sani.
Shine ya shigo dakin nace zan kirata daga baya yana wani shan toka a fuskan shi ina kwana nayi mashi tare da tambayan shi gajiyan jamma,a .
Bai amsa min ba sai tambayan da yayi na karya insha magani nace laraba ta fita ta samo min kosai don shine kadai nake ci ya zauna min a ciki yanzu da dan kunun kamu.
Ina taje samuwa nace ban sani ba wallahi ta dai fita ko zata samu yanzu kina sakaci da rayuwan ki da tun farko nasan da zancen cikin nan ba inda zaki je wallahi.
Har ya kare rigiman shi ya fita ban iya tanka mai ba

140 / 144

Chapters