An daura auren mu sha biyun rana a unguwar Daji unguwar da yan uwan daddy suke zaune wanda daurin auren ya samu halartan mutane da yawa daga yan uwa da abokan arziki.
Tun da na tashi nake jin jikina ba dadi ga tunanen ina maryam ta shiga da nakeyi a raina sai sha daya dawani abu suka shigo gidan dasu ya Amina da wasu mata da yawan su.
Bayan mun gaisa ne na koma dakin mu na samu maryam tana sauya kayan jikin ta nake tambayanta inda ta fito haka.
Bata kai ga bani amsa ba naji wata daga cikin matan waje tana rangada guda cikin nufanci Allah yayi auren khadija yau.
Zubur na tsaya ina sauraren abinda matar ke fadi ta juya da hausa tana kara maimaita abinda ta fadi da yaren nufancin again.
Maryam na kalla naga tana dariya tare da fadin matar nan ta iya guda wallahi bata ankara ba sai gani tayi na fadi kasa .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kwance take tana barci har zuwa wanan lokacin bata tashi ba ga kira nata shigowa a wayan ta can cikin barci take jin kiran yayi yawa.
Tsuki tayi tare da dago kiran tana zagin mai kiran nata ta dauka a hasale muryan madam taji a wayan tana fadin wai ina kika shiga ne ake ta kiran ki baki daga waya ba haka.
Barci nake walkahi may kina da hankali Nafisa da har kika samu idon barci a cikin wanan fitinar da ya kunnu muna kai ?
Da sauri tace may ke faruwa waya mutu kuma madam tace ai da mutuwane zai fi sauki don mun san may shi ya tafi ke nan .
Muna kukan targade sai kuma ga kariya ya samu yanzun haka mijin ki yai muna wanan yankan kaunar a idon jamma,a ?
Nafisa dake mamaki a ranta na abinda mijin ta yayi haka ya bata wa madam rai tace ai kin san samad miskiline bai da sabo sai ni nasan kan abina.
Madam tace ke dan Allah abin kin may can ki gyara kalamin ki yanzu kice abin ku don aure zai kara yau din nan nasan baki sani ba da naji don jiya muna tare dake har dare banji kin min zancen ba.
Nafisa da tai mutuwar tsohowa a zaune bataji sauran abinda madam din ke fadi ba a lokacin sai da madam ta kirata da karfi ta dawo a hankalin ta.
Madam tace kina jina tace madam ko dai baki gane wanda ake fadi bane kika dauka mijina ne ?
Kamar ya ban gane ba ni da akaturowa har kayin daurin aure ko bashi ma fam sec din FLAS ba na nan Abuja wani irin zufa ne ya keto ma nafisa duk da sanyin da dakin ya dauka na AC alokacin.
Madam ko dai baki karanta da kyau ba madam tace ki bincika da kyau ki gani idan kin bincika kikirani anjima tana fadin haka ta kashe wayan ta.
Madam na kashe waya nafisa ta rasa wani irin tunane zatayi yanzu ta dai san suna tare da Samad suna raya dare dashi sai sha biyu suka kwanta bata ga wani alama da ya nuna mata wani abu na faruwa dashi ba.
Ta rasa wani irin tunane zata ba a lokacin cikin karfin hali ta mike zaune daga inda take kafarta taji baya daukan ta a lokacin ta nufi dakin maigidan wanda ta bar dakin tun asuba daya ta da ita tayi sallah asuba ta gudo ta dawo dakin ta ta kwanta.
Ta tura dakin yana tsaye a bakin wardrove din shi yana ciro kayan da zai saka tun daga kofa take mashi kallon tuhuma.
Kallon ta yayi ya kawar da kai yana fadin yaya nagan ki haka kamar mara lafiya ?
Tace shine dalilin zuwa na yanzu don in tabbatar da lafiya na don amsan na wurin ka yace kamar ya tace yanzu madam ta kirani take fada min wani magana dan gane ba ?
Yace may ta fada maki yana kokarin zura wando a jikin shi takai ma kayan kallo taga sabbine full din su shi kuma ba gwanin saka kayan hausawa bane.
Ta karaso inda yake tana fadin cikin kura mashi ido wai aure za daura maka yau samad ?
Cikin cijewa ya amsa mata ashe kin samu labari ke nan yanzu nake son fada maki dama sai gaki kin shigo dakin.
Yanzu zamu tafi daurin auren minna ai bata bari yakai karshen maganan shi ba ta sake wani irin uban ihu tayo kan shi da duka duk abin da ta samu buga mai shi takeyi akai.
Tun yana kaucewa har ya tsaya wuri daya yana mamakin ta daya ga abin ba mai karewa bane sai ya hade hannun ta wuri daya ya hankadata zuwa waje.
Yana shiri yana tunanen wanan wani irin fitina ne haka gana Nafissa ga kuma na khadija da zai tara bai san yadda zasu kwashe da ita ba don ita ma bata sani akace.
Don shi rabon shi da ita tun a kaduna da suka rabu bai karaji ko ganin ta ba yanzun dai yaga haukan nafisa saura na yar matsalan kuma ya fadi yana murmushi tare da fadi a fili kai mata dai kayyah wallahi.
Yaci gaba da shirin da yake ranshi idan yayi dubu ya baci a lokacin dama yasan da wanan abin na zuwa gare su shi da ita idan taji da haka yagama shirin shi.
Ihun Nafisa ne ya tayar da sauran mutanen gidan dake barcin safe suka firfito a razane daga na dukan nasu dake kasa.
Suka fito a sukwane suna tambayan may ya faru sai dai ba amsa daga bakin ta a lokacin don ta haukace masu gaba daya.
Yana gama shirin shi ya nufi kofa ya bude ya ji kofan a rufe haka yasa ya gane ta rufe shi daga bayane da wani makulli waya ya dauka ya kira Yusuf akan yazo ya bude shi.
Yusuf yace taji ne yace kaima ka sani ai ajiyan zuciya Yusuf ya sake yana fadin haka yayi daidai yanzu ka daina jin shakkan fada mata.
Don Allah malam kazo ka bude ni kaji ka tsaya min surutu haka dariya Yusuf yayi yace kai angon khadija mijin buzuwa uban gidan Fati.
Tsuki ya kara ja Yusuf yace ganinan zuwa sai dai kasan nima ba barina zatayi ba yau nasan akwai tsiya tsakanin mu yace kadai zo din.
Yusuf yazo gidan tun daga kofa a yadda ya samu mutanen gidan cirko cirko yasan akwai matsala a gidan haka yai kundunbalan fadawa gidan kai tsaye yana rike da master key ya shigo.
A falo ya samay su zaune da yan uwan ta zuwan shi yayi daidai da shigowan madam gidan da yan uwan nafisa suka kirata hankali tashe.
Tana ganin Yusuf tayo kanshi a sukwane da niyar bugamai flawer base din da ta raruma a hannun ta ta nufo shi gadan gadan dashi.
Su madam suka rike ta suka kwace abin flawer da kyat a hannun ta ta kwace tayo kanshi da duka da cizo tana zagi.
Mari ya kwashe ta dashi cak ta tsaya tana mamakin shi idon ta na tsiyar da hawaye take kallon shi wuce ta yayi ya nufi sama ta sake kukan kura ta bishi zuwa saman kafin ta iso yasa key ya bude kofan dashi.
AA ya fito rai bace tayo kan su gaba daya tana fadin yau sai ta kashe su sai ta halakasu sai ta illanta su a duniyan nan.
Madam na gefe sai faman buga ma abokan su na kut da kut waya take su zo gidan nafisa din ba lafiya.
Bayan sun fito ne Yusuf yace ke wata irin mace ce ba ki da hankali ne idan kin mashi rauni fa kan ki aka kishiya kema ba wata kika shigo kika sama a gidan ba.
Ganin zasu fita subar gidan ta sake yowa kansu ta fisge hannun su madam din suka sake riko ta suna bata hakkuri ta shiga surfa masu zagi har su madam din Yusuf ya kallota yace mahaukaciya.
Nan suka fice suka barta da mutanen ta a gidan da suka fara taruwa ranan kawayen ta sun nuna mata bakin cikin su kwarai da gaske kowa da abinda yake fadi a bakin shi a ranan.
Suna fita ya sauke ajiyan zuciya Yusuf ya kalleshi yayi yayi dariya yace somi ke nan amma komai zaizo karshe insha Allah sai ka zama namijin duniya sosai kafin ka samu mafita ga haukan matar ka.
Sun samu har wasu sun kama hanya a bisa jagorancin kawu da mahaifinshi da yazo daga kaduna tare da wasu yan uwa nasu don daurin auren da daddy yasa cikin kwana uku daga zuwa magana daddy ya tsayar masu da ranan daura aure.
KHADIJA
Na falka naganin saman gadon dakin daddy kwance maryam da Ya Amina akaina suna min fitara.
Nakai kallona garesu su ukune tsaye akaina Ya Amina maryam da wata kanwar maman mu kanwar maman mu na kalla don su a matsayin makiyana nake kallon su yanzu.
Nace mama Tani da gaskiya aure aka daura min da mutumin da ban sani ba tace tana dafani yanzu ba lokacin magana bane khadija.
Barin maki allura ki samu natsuwa tukun ta dauko allura tana aunawa zata dirka min kaina na girgiza mata nace mama ba sai ki min allura ba don Allah .
Ido na rufe a hankali ina ji aka dirka min alluran dole sannu a hankali barci ya fara dauka na ban san inda nake ba kuma.
Sun rufe dakin da nake ciki kwance bamai shiga sai su ukun ke zaraya a kaina hankalin su duk a tashe sai yanzu suke dana sanin goyan bayan da sukayi aka hada kai dasu aka daura min aure da ban so.
Don sun dauka wasa ne ina son A A din barazane kawai nake masu na mata amma yanzu sin gane gaskiya nake har cikin raina.
Hankalin yan uwana duk ya tashi amma banda daddyn mu don cewa yayi a ranan za a tafi dani sabanin yadda akace dafarko aure kawai za a daura daga baya sai in tare.
Ina kwance ban san wainar da ake toyawa ba a gidan barci nake mai kamar wahala don ban iya cewa ga inda nake ba.
Maryam tayi kokarin neman Yusuf a waya tana fada mai halin da ake ciki don haka yaja AA gefe yana sheda mai abinda daddyn mu yace.
Kiran maryam sukayi su fito ita da anty Amina su damay su a waje sun iso inda suke Yusuf ke tambayan su halin da ake ciki.
Taso ta boye mashi amma sai ya Amina tafada masu halin da ake ciki bata boye masu komai ba abindake faruwa harda maganan daddyn mu.
Daga inda yake tsaye yake sauraren maganan su yaji idon shi ya rufe yana jin wani zafi a ranshi shine mace zata nuna ma wanan kiyayyan haka ?
May ta taka may khadija ke ji dashi a cikin ranta may take takama dashi muryan yusuf yaji yana cewa anty zasu ga daddy su bashi hakkuri abar tarewan har wani sati lokacin sun shirya inda zasu aje ni.
Sun sami ganin daddy inda daddy ya nuna masu bai yarda ba saida a tafi dani ranan idan mutuwa zanyi saidai in mutu akan aure bazan kwana mashi gida da igiyan aure a kaina ba .
Suka bashi hakkuri akan basu gyara inda zan zauna bane tukun abasu sati daya yace sati yayi yawa ai mutane sai su zage shi a hakan.
Sai da kyat ya yarda da kwana uku suka amince da haka sun bar wurin shi suka nemi maryam tai masu iso inda nake su ganni kafin su wuce.
KHADIJA
Koda na farka mama nagani zaune a kusa dani ta kuramin ido cikin tagumi tace dani khadija kin falka nace eh mama.
Tace tashi ki ci wani abu ko tea mai zafi ki korama cikin ki tun safe baki kai komai a cikin ki nace banjin yunwa mama tace dani a,a khadija ban son gardama fa.
Daure ko kadan ne kisha sai musan abinyi daga baya jin haka ban son gardama da mama kodon in kwantar mata da hankalin ta yasa na mike zaune ina kokarin tashi sai dai ban iyawa na koma na zauna a bakin gado.
Kofan dakin akaturo gaba dayan mu muka dago muna kallon mai shigowa dakin maryam ne a gaba sai yusuf ke bin ta daga bayan su AA ne ya shigo a gadarance.
Yusuf ne ya fara gaida mama sai shi ya juya wurina yace khadija yaya jikin naki ni bisu da ido tare da kawar da kaina gefe ina son kwantawa.
Mama tace barin hada mata tea maryam biyo ni ki kawo mata tea din ta dan sha maryam ma tabi bayan ta.
Kara tambayana jikin sukayi daga inda suke tsaye akaina ban basu amsa ba sai kukan dana sake a lokaci daya shiru sukayi dukan su suna kallo na.
Ya Amina ne tare da maryam suka shigo dakin kukan nan bazai kare maki bane har yanzu kina son ki jawa kanki wani matsalane kuma ?
Ya Amina ta juya wurin su tana fadin ashe kun samu ganin daddy din yanzu yake fadin sai nan da kwana uku za, a kaita suka ce Allah ya kai mu sautin kuka na kara sakewa a lokacin.
Shi ya fara barin dakin don bai iya jimirin sauraren kukan da nakeyi wanda yake jinshi kamar ana diga mai garwashin wutane a zuciyar shi.
Wai shine mace kewa kuka haka hartana neman halaka kanta saboda rashin kauna yanzu ya tabbatar da khadija ta wuce sanin shi.
Sallama yusuf yayi mata akan zasu wuce yajuyo gurin da nake ta gurzan kuka yace khadija kiyi hakkuri ba munyi haka bane don mu saba maki hannu na dago mai daga inda nake yasa yayi shiru da bakin shi ya fita.
AA
Tunda suka kama hanya baiyi magana ba yana dafe da goshin shi da hannu daya Yusuf ne ya kalle shi yace dashi wai ya nagan ka haka ne kayi weak dakai.
Ba a mijin mata biyu ko uku ko hudu haka fa wan halin mijin mai mata daya ne kakeyi ya kamata ka jajirce ma duk wani kalubalin da zaka gani daga matan ka yanzu don kasan mata da kishi suke.
Zaka samu kalubali masu yawa har ta inda baka zata ba amma idan ka zama masu namijin duniya sai kaga komai ya lafa an zauna lafiya.
Ajiyan zuciya ya sauke tare da lumshe idon shi yace ban jin komai a yanzu duk wani haukan da Nafisa ko Fati zasuyi ban dauke shi a komai ba illa mamakin da nake wai ni Abdulsamad yau mace ke nuna ma kiyayya haka ?
Why khadija why ashe har abinya kai haka a zuciyar ta ban sani ba ina dauka halin su na mata ne take nuna min kai ina bazan zauna da macen da bata sona haka ba a gidana.
Yusuf dake kallon shi yana murmushi yana gurgiza kanshi yace duk laifin na waye AA kai ka jawo abin nan yakai haka nina sani nafi kowa sani halin ka do haka nasan kana son khadija har cikin ranka.
Sai dai girman kai da izza ya hana ka nuna mata son da kake mata din wanda ita kuma tai amfani da haka wurin daukan kaima ba son ta kake ba illa tilasta kan da iyayye sukayi ne a kanka ka yarda ka aure ta.
For god sake ya kuke son in nuna mata so ne bayan wanda na nuna mata din for how long take son in nuna mata ina son ta ne kuma ta yaya.
Yace just say to her a words of love shi irin wanan matan ke so ba tarin dukiya ko wani kyau da nasaban ka ba duk basu a gaban irin khadija akwai mata da yawa haka Allah ke yi su .
Kamar yadda ko cikin mazan ma akwaisu zan iya cewa kana daya daga cikin su yanzu haka don baka san may ye so ba sai an nuna maka don haka dakai da ita jirgi daya ya dauko ke nan.
Ya Sallam ya furta yana kara dafe goshin shi da hannun shi daya so so so may zance mata tasan ina son ta yace kalman nan da kuka kasa furta ma junan ku da dadewa shi zaka furta mata yanzu dubara ya rage naka.
Bazan so khadija ta shiga gidan ka a haka ba har matan ka su gane abinda ke tsakanin kai da ita gara ka gyara maysalan tun wuri nima zan tayaka gyara in Allah ya yarda.
Tunda ya dafe kai baiyi magana ba sai da suka tsaya a kofan gidan shi ya bude idanuwan shi da suka kada sukai mai jawur dasu ya dago kai yana kallon Yusuf din.
Yace bissimillah kadai shiga da addu,a a bakin ka don nasan rikici na ciki yana jiran ka yau yace tare zamu shiga ma Yusuf yace tsoro kake kenan ?
Tsoron may haukan nan nata ne ban iya dauka sai in mata illan daban tashi yi mata ba don fitinar Nafisa yayi yawa.
Bude motar Yusuf yayi yana fadin bissimillah mu shiga kadai tina da addua na fada maka ba abinda