nashi kalan soyayyan ke nan a baude yake nuna maki halin babangida sai shi wallahi da farko danaji wanan zancen nafi kowa farin ciki da jin hakan.
Amma kuma sai ga magana yazo muna ta karkace wai kin ce ba komai a tsakanin ku shiyasa na taso da mommy ku muzo muji wanan magana da kan mu.
Khadija kamar yadda kika sani babangida yana bukatan taimako macen da tasan kanta don gyara halayan shi na wanda yake mai murdade ra,ayi wanda sai macen da yake zaune da ita jaruma ne zata kwato man shi daga tarkon wanan buzuwan da ya ke aure a gidan shi yanzu.
Kin dai san komai khadija basai na fada ba yanzu anan kin san komai dake faruwa dashi tunda kusan a tare muke da ke da yar uwar ki a unguwan nan.
Don haka don Allah khadija ina rokon alfarma a wurin ki da, , , da sauri na dago kaina alokacin har na fara hawaye a fuskana nace cikin karfin hali mama bazan iya don Allah ki yi hakkuri abinda kuke nufi bashi bane a tsakanin mu wallahi ko mama mommy ku fahince ni mana wallahi ba komai a tsakanina dashi.
Mommy ta gyara zama tana fadin nafahince ki khadija abin da mu kuma muke rokon ki shine ki yarda da bukatan mu akan shi don girman Allah ki tausayawa mahaifiyar shi tunda ta tako gare ki.
Yanzu kin san maganar ba karamin magana bace Ya Amina ce tasa muna baki don tunda aka fara maganan take jin wani iri a ranta ganin kamar suna son su tursasani abinda ban so ne abinka da dan uwa tace don Allah mama ku bar zancen nan a yanzu zan zauna da ita mu fahinci juna don yanzu bata a cikin hankalin ta zata iya rikice muna anan don khadija na da iska masu karfi yana iya tashi yanzu haka anan idan ranta ya baci.
Jin haka yasa suka kalli juna da mama sukai murmushi mama tace hakan na da kyau ba sai mun tsaya wani dogon magana ba yanzun ai kun fahince mu.
Ya Amina ta sake fadin mommy da anbar zancen nan don Allah ko don mutuncin dake tsakanina da Fati kada ta zargi wani abu akai.
Hajiya mama ne tayi magana tace ai wanan abin har fatin taimakon kanta ne idan ta gane balle Fati ba mai matsala bane don haka ku kawar da zancen Fati yanzu don zamu fahintar da ita komai ta gane.
In Allah yaso zanyi magana da ita zakuji in Allah ya yarda komai zai zo da sauki ta lalabasu don su tafi don ita ma kanta abin ya bata tsoro don bata dauka abin zai zo a haka ba.
Mikewa nayi nabarsu a falon maryam ma ta rufa min baya zuwa dakin ta samay ni na kifa kai a filo ina kuka a hankali zama tayi kusa dani ta dafani tare da fadin may ye kuma na kuka khadija ina sai kina yi za a yi wa zai saki auren dole a yanzu idan baki so ai ba mai maki dole.
For god sake maryam ya su mommy zasuyi min haka suzo su sani agaba mama tana rokona akan wanan miskilin dan nata yaya kike ganin zan iya musa mata bukatan ta a gareni.
Gashi ni kuma wallahi ba zan iya auren wanan dan nata ba mai mata har biyu yaushe yake da wani lokacin mutum a haka.
Yanzu dai ai ki barsu da yaya Amina don gata can falo suna maganan har yanzu gaskiya ni basu min adalci ba don may bazasu barni dashi ba sai su zo su saka bakin su a ciki kuma.
Zan iya cewa mama ko mommy a a ne tace ai kin fada ko dan naga karfin halin ki sosai da kika iya yin magana a gaban su.
Ba dole in magana ba tunda sun kasa fahinta na da gaskiyar maganan shikuma munafuki wai harda fada masu wai ni na yarda.
Kin san fa alama ya nuna suna matse da yayi aure ko za a kawo karshen buzuwa a gidan nan nace ai Allah kadai ya isa da hakan a tunanen su ni zan iya mata wani abin ne ko may ?
Dariya sosai maryam keyi tana kumshe baki kada su jiyo ta a falo tace wallahi don ansa baki da tsoro ne yasa suke son sakaki cikin maganan.
Ban saki da yawan raki ba haka don naga yanzu kina son ki sare akan buzuwa kawar ki ko kishiyar ki zan ce ban sani ba.
Ke dai kika sani suje can su karata badani ba shiga sharo ba shanu ba abinda ya shille ne da zancen gidan su shi da ya jajibo ta yaje can ya karata da ita su suka sani.
Mama na shigowa falon ta ta zauna tare da jawo wayan ta tana dadannawa takira dan uwanta kawu salihu a waya.
Kira biyu ya daga wayan yana karbawa yace salamu alaikum Aisha kun wuni lafiya ta amsa lafiya yaya dama akan maganan yaron ka ne na kiraka.
Tabsa yarinyar da malam ya fada ta bayyana sai dai tazo da akasin da shi malam din ya fada za a samu sai dai muna bakin kokarin mu don ganin ta yarda da maganan .
Aisha kin san dama malam ya fada muna za a samu jayayya akan haka don haka abunda nake so dake yanzu abi komai a hankali har mu cin ma manufar mu.
Allah ya gani alheri muke hadawa ba wani abu ba akasin hakan mudin hakan zai muna kwanciyan hankalin mi zamubi ta ko ina muka wanan abin ya tabbata idan haka din ne mafita gare shi damu duka baki daya.
Don haka yau da dare zan koma wurin malam in mashi bayanin komai ko akwai wani karin haske akan haka.
Idan da hali sai yayi muna istihara agani ko itace zabin Allah akan shi idan da alheri sai muci gaba da rokon Allah a kanta.
Tau yaya na gode tace Allah ya bar zumunci yace ba komai Allah dai yasa a dace Allah yasa muga bayan wanan abin tace amin sukai sallama ta kashe waya .
A gidan ya Amina sai hada kayana nake ina fadin da safe zamu koma Abuja don gujewa wannan abin da ya kunno kai.
Sallaman su Binta da zainan ne a falon ya Amina bayan su gaisa suke tambayana tace ina ciki ina shiri gobe zan koma Binta tace ba tace sati daya ko kwana goma zatayi ba yanzu kuma tace komawa zatayi.
Ta mike tana fadin barin ganta zainab ma ta biyo ta zuwa cikin dakin inda muke maryam na zaune da earpiece a kunen ta tana sauraron waka nikuma ina tsaye ina nike kayan mu ina sakawa a jakka suka shigo dakin.
Kallona Binta tayi tana fadin wai zaki koma gobe zainan ta samu guri ta zauna a kusa da maryam take zaune tana kallona.
A raina nace shegeya mai kama da dan uwan ta wurin miskilanci nace da Binta gobe zan koma nan iya fitinan da su yusuf suka fito min dashi.
Wai akan wanan magana kike son komawa ai ko kin koma baki tsira ba don gara ki tsaya ayi ta takare anan kowa yasan matsayin shi.
Don nima wallahi ban goyi bayan wanan maganan ba gaskiya ina zaki iya da wanan yar iskan matar tashi mai bakin kishin tsiya kamar kafira.
Ke Nafisa fa bata sallah sai taga dama ki fada min in akwai imani a gurin mutumin da bai cika sallah shi.
Zainab tace ni inda take ban tsoro shine idan fa yaya zaizo weekend da sai ta biyo shi garin nan tazo kawai don ta takura ma anty fati da yaran ta.
Tana daki da miji sai Fati ne zata girka masu abinda zasuci har ya koma wai kuma sunan anzo wurin ta ita dake nan zaune .
Amma haka zai koma bata mijin ba sai dai ta hango su suna mu,amulan su a gidan da abokan sherin ta sai da su mama suka taka ma haka burki.
Yasa yanzu ta daina biyo shi don mama tace idan sun zo anty fati ne kadai zasuyi girki har su koma haka yasa da taga da gaske mama keyi ta daina zuwa ki idan zamu zauna baki labarin nafisa da shu,umancin ta sai mun kai safe anan.
Nace shine kuma su mommy ke son ni sakani a cikin bala,i sun san yadda take, Binta tace ni nama shina gani wallahi zainab ne ta katse ta da fadin ke Binta kin kai su hankaline da wayo ko haka kawai zasu ce suna son wanan abin.
Maryam taceai shi na gani nifa banga wani abin jin tsoron a wurin wanan nafisan ba tunda kinga har suna ra,ayi a kan ki akwai abinda suka hanga a hakan ne.
Kai na girgiza nace nidai badani ba wallahi kwatakwata ban ra,ayin auren mai mata a rayuwana shine kawai magana ta amma ni wata nafisa bata gabana yanzu.
Nasan bata gaban ki ya kamata ki jaye wanan ra, ayin naki na baki son mai mata don ke nasan kuna daidai da ita.
Ban iya magana ba don abinda nake ji a raina a lokacin nan binta taci gaba da fada muna halin nafisa ciki da bai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kuka zanyi ko ihun takaici zan sake a lokaci daya don tunane na ya karkata akan mamud ne yayi min hakan don a haukan shi na yarda zan aure shi yake zato.
Jiran dawowan daddy gida nakeyi duk da nasan zai dauki lokaci bai shigo ba yana kasuwa wurin neman kudin shi.
Ina son tashi in kira wayan maryam nauyin da jikina yayi ya hanani tashi zaune ko ya bari inyi wani abu sai zuciyana ne kawai ke aiki ajikina a lokacin.
In kulla wancan in sance haka har yamma yayi na mike da kyar ta fito na samu ruwa na watsa ma jikina.
Ban jima da fitowa ba ina zaune ina saka kaya naji shigowan dadddy gidan haka kawai naji gaba na na faduwa dashi sai dai na daure na fito ina mashi sannu da zuwa.
Yace ah khadija ya gida ya kuka wuni na amsa da daddy lafiya fridge din gidan mu na nufa na daulo mai ledan pure water na sa a plate na kai mai.
Sai da ya zuke ruwan ya sauke ajiyan zuciya yace dani Allah yayi maki albarka da fara,a a fuskana na amsa mai da amin daddy.
Mikewa yayi ya nufi inda muke zama muyi alwala ya dauki buta ya fara alwala ina tsaye rakube a kofan dakin mu har ya gama ya dago yaba fadin khadija lafiya kike kuwa ?
Daddy lafiya na kalau ina dai , , , ki bari yaje sallah kada ya makara kin san su basu tsayar da sallah da sun tayar suke haraman tada sallah.
May ke faruwa ne ya tambaya cike da son jin abinda yake tambaya yana kallon fuska na nace daddy ba komai bane mama tace idan kadawo sai kuyi maganan yace yana da kyau hakan.
Ya fice mama ta kalle ni tace kije kiyi sallah kafin ya dawo ta na fadin haka ta dauki buta zuwa ban daki ta kewa yawa.
Bayan na idar da sallah na zauna a gurin ina addua tare da mika kuka na ga Allah akan ya kuburar dani daga sherin masu sheri da fatan cikawa da imanin a zuciyar mu.
Sai da akai sallah isha,i daddy ya dawo gidan inda mama ta gabatar mai da abincin shi na dare gaban shi.
Sai da na tabbatar da ya kare abinda yake na shiga wiri shi da sallama yana zaune a kasa saman jan carpet din dake shimfide a falon ga kayan abincin aje a gefen shi yana kallon labaran NTA minna da akeyi .
Na samu gefe na zauna kasa nima na kara gaida daddy da wuni daidai nan mama ta shigo falon itama dauke da kayan abincin ta da zata ci.
Sai data samu wuri ta zauna ta kalle ni tana cewa ga khadija nan dazun da rana na samay ta da maganan mutanen da suka zo neman ta take nuna min bata san da maganan ba.
Sai lokavin daddy ya cire idon shi ga kallon da yake yi tare da fadin idan ita bata sanda maganan ba ai mu mun sani don itace ta fara kawo muna su a gidan nan.
Da sauri na dago kaina ina fadin daddy ni ban kawo kowa a gidan nan ba daddy kaima kasani da zan kawo wani nice zan sanar dakai zuwan nasu ai.
Khadija a gaskiya naso ace sai kingama karatun ki zamuyi wanan maganan amma kuma daga baya naga rashin dacewan hakan gare ki yanzu.
A gaskiya bazan iya barin ki haka har ki gama karatun ki babu aure gare ki ba don ko yanzu hakkuri nayi aka kai hakan idan kinyi duba ga irin yadda tan uwan ki sukai aure da wuri a baya.
Ke har kin samu kin dibi karatun jamia wanda mijin yar uwar ki ya sakaki yi a gurin su nauyin shi da kunya yasa har na barki kikai haka.
Shiru mukayi falon babu mai magana a cikin mu muna sauraren daddy din dake magana don haka idan har kince bake kika turo mutumin nan ba yanzu sai ki turo muna wanda ke kike so a ranki ko waye zan aura maki shi insha Allahu.
Mama ne tayi magana bayan daddy ya gama magana tace gaskiya batin auren nan yanzu ya kamata ka jaye shi tunda har ta kusa gama karatun ta.
Da sauri daddy ya katse mama din da fadin haba Aisha ra,ayi zamu bi ko maganan Allah kada ki kawo wanan maganan yanzu.
Khadija kiyi hakkuri kiyi yadda nake so ki fitar da miji kin san gidan mu gidan malamai ne hankali baya kwanci ganin ki a haka da nakeyi kullun kuna gwada sa,a da uwar ki a cikin gida ina ranan wanan abin .
Yanzu ne kike a damarki na fida manemin kwarai daga cikin manemanki tun basu gudu daga baya ba ki koma kina neman su su watse su barki dana banza.
To aini gani nayi yanzun karatun nata baifi saura shekara daya ba ko watanin ta gama dadduly yace ta karasa shiba gidan mijin ta yafi mutunci hakan.
Don ba ido na zan saka mata ba tana abinda taga dama ke kuma kina biye mata tana abinda taga dama don haka ke nake saurare ki turo wanda kike so din yazo mu gana dashi.
Daddy na gamawa namike nabar falon idona taf da hawaye da na kasa controling din su nafice daga falon zuwa dakina.
Kuka nayi sosai dana koma dakina ina tunanen may yasa daddy ya sauya min acikin dan lokacin nan ya damu da maganan aure na bayan yasa abinda ke gabana yanzu.
Zai bijiro min da wani zancen aure may yasa kowa ya maryar da hankalin shi yanzu a kaina haka ne wai ?
Kaduna banji dadin abinda su Yusuf suka kula min ba nayi gudun zuwa can yanzu kuma na dawo gida na samu wanan matsalan a wurin daddy again.
Mamace tashigo dakin zuwa dare lokacin goma na dare ya gwauta sosai tashigo ta samay ni kwance ina faman tunane dake ci na.
Ki tashi kici abinci don kin san maganan daddyn ku idan ya fada ba fasawa zaiyi ba don haka yayi ma yan uwan ki a baya.
Ke ma kinyi arziki har yadan barki kin taba karatu yan uwan ki ko kwatan kwacin hakan basu samu ba a gurin shi.
Na dago fuskana dake tsiyayan hawaye nace mama bansan may nayi wa daddy yanzu ya tsane ni haka ba karatun nan fa in nayi shi karuwan mu ne duka bani kadai ba.
Yasan hakan kin ji ai abinda ya fadi abin kunya ne a gurin su yarinya ta dade haka batai aure ba don haka kiyi shawara ki tsayar da daya daga cikin maneman ki ya turo sai a wuce wurin.
Mama ni wa zan turo yanzu ban fa da wani tsayayen mutum a zuciya na su dukan basu kwanta min a rai ba zaune mama takai daga tsayen da take tace min.
Ya zama dole a cikin maneman ki ki tsayar da mutum daya a matsayin wanda zaki aure san nan ki sani shi rayuwan aure abune wanda ya shafi rayuwan mutum.
Saboda haka ki natsu kiyi zabin daya dace da rayuwan ki kada kiyi zabin tumun dare da za a dawo ana da an sani daga baya.
Don daddy ku ba fasa abinda ya furta zaiyi ba yanzu shiru nayi nace mama ni ban son su dukan su gaskiya da dai za a dan daga min kafa abani lokaci sai in fitar da wani daga baya amma ba cikin wa yan nan ba.
Mikewa tsaye tayi tace yanzu dubara ya saura naki ai, wai maye matsalan su masu neman naki ne da sauri nace mama suna da mata fa nan dai na bata labarin kowa a cikin su.
Sai naga hankalin mama ya tashi sosai dajin abinda na fada mata sai da ta nisa tace min ni ina ganin wanan ba matsala bane don suna da mata.
Gidan da ake tashin hankali ne kawai baida dadin shiga don gujewa matsala da saura su ki koma a wurin