ma,ana mukeyi idon matan nan da suka shigo su uku ya dawo a kan mu suna kallon mu gashi jikina na kusa da nashi kamar dai mata da miji.
Mommy ke fadin yaji sauki sosai yau gashi ma yana cin ayaba har mun ga idon shi ai jiya abin ba dama wallahi.
Basu tsaya ba suka yi ma mommy sallama tare da fatan Allah ya kawo sauki suka fita muma bamu dade ba mukace zamu tafi Yusuf ya taso yana fadin barin je in sauke ku ko ?
Sallama mukai masu muka baro asibitin Yusuf ya fito ya sauke mu tare da yi muna godiya nace ba komai ai Allah dai ya bashi lafiya.
Fitan matan kenan daga daki suna shiga motar su dayan tace nikan yau naga abu wallahi wai waye wanan yarinyar danagani tare da mijin Nafisa.
Dayan tace aini yau imani ya kashe ni anan anya Nafisa batai sakaci ba kuwa ta yaya zata zaune gida ta bada damar wata na mata jinyar mijin ta don tsaban son jiki da sakaci irin nata.
Wanan may ta sani banda karyan arziki da nuna son miji a baki kawai waya ta daga ta kiranta tana labarta mata abinda suka gani.
Bata jira ta gama bayani ba ta kashe wayan tare da fitowa waje a sukwane tana zunduma ashar tare da fadin su Yanyala su biyu ta.
A hanya take fada masu abinda ke faruwa a asibiti da mijin ta da wata sai dai kafin su zo mommy tasha ita da Yusuf da mijun nata uwa uba yarinyar da bata san ko wacece ba .
A fusace ta turo kofan mummy dake zaune tana lazimi ta dago kai tana kallon ta da shigowan ta tace ina yar iskan yarinyar da tazo tana bare ma Ayaba ina karuwan yarinyar ta tafi ?
Wacece ita wa ya bata dama tazo kusa da miji na haka tana magana tana zaran ido ta kalli mummy ta kalli Abdul di dake kwance yana kamllon ta.
Nafisa you're very stupid zaki shigo ma mutane daki ba sallama kizo kina fadin rubish haka wakika ba ajiyan yarinyar da kike tambaya ?
Mommy tace wace yarinya wai take magana ne wani kallon wullakanci tayi ma mommy din tace ko wace yarinya ce ai kun sani ni za a munafunta kuma ?
Dama na sani ai abinda ake kulla min ke nan ba yau ba wallahi anyi kadan aga baya na a gidan nan balle aje a dauko wata karuwa tazo tana bare ma ayaba tana baka a baki.
Subbahanallahi wani munafuki ya fada maki haka mommy barta an bare min ayaban an bani a baki may zakiyi ?
Au ashe ma kasan karuwan ka tazo har ta baka ke nan karuwa kema kin san nafi karfin karuwa don yar kwarai ce ba irin ki ba da tashigo duniya tabar iyayyen ta.
Babangida kubar maganan nan don Allah tunda kai kasan gaskiya tace dole kice haka mommy tunda dake ake hada bakin yin haka.
Samad akan karuwa kake zagi na har kake min gori na baro iyayyena gida nazo nan ni kadai.
Ba karuwa bane yadda na aure ki haka itama zan aure ta in kawo gida ta zauna dani tafiki komai da kike tunanen kina dashi.
Ido ta waro waje kafin tai magana security din asibitin suka shigo suna kokarin jan ta waje suna fadin ba ai masu hayaniya anan kuma ba lokacin zuwa duban marasa lafiya bane yanzu.
Samad aure kake fada min da bakin ka zakayi aure fa kace suka tura ta waje tana masifa tana zagi mommy mamaki ne ya cika ta da jin kalamin da ya furta.
Bayan fitar ta tace Babangida dama kuna tare da khadija ne ko dai ka fada mata hakane don ka bata mata rai.
Mommy bar yar iskan matar nan da bata da hankali zanyi maganin ta nan bada dadewa ba.
Lamarin Nafisa ne sai hakkuri kabar biye mata kuna sai da hali haka haka ba tarbiyan ka bane wallahi.
Bai iya mata magana ba don ranshi a bace yake da abinda nafisa tazo tayi masu yanzu sai mommy tace wai ma a ina taji wanan abin ?
Har take aibanta yarinyar mutane haka khadija ne take kira da karuwa wanan bata da tarbiya wallahi.
Har ta kare bai mata magana ba tace Allah ya kyauta taja bakin ta tayi shiru zuciyar tab da sake sake a cikin shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zaman da maryam yana min dadi sosai don itama bata da wasa da karatun ta gashi musan mutuncin junar mu kamar mun dade da haduwa da ita.
Ita ta tilasta min fara amfani da kayan da Yusuf ya saya min tace may ye amfanin ajesu da nakeyi gara dai a fara gani a jikina zai fi.
Ban sake bi takan su Yusuf din ba na mayar da hankalina ga abinda ya kawo ni garin sosai sai dai muna waya da kowanin su har yanzu wanda wayana da Samad duk ya kira fada ne da zolayan junan mu har ai fada a kai ga kashe wayan.
Munyi jerabawan karshen zango na farko inda muna gap da gamawa Yusuf ya kirani nake ce mai sati mai zuwa zan tafi minna don ba zan leka kaduna ba wanan hutun saboda hutun ba mai yawa bane .
Nan yake ce min suna tafe gurina kafin in wuce gida don suma zasu shiga kaduna don Samad ya dade bai je gida yana kokari yaga ya shawo kan shi su tafi.
Nace ka barni dashi in gwada in gani idan zamuyi sa, a da nawa dabaran yace ya gode muka kashe wayan suna zaune tare aiki suke a wani file.
Yusuf yayi mamakin jin ya tambaye shi khadija yace tana nan lafiya kasan jerabawa suke yi kwanan nan wayan shi ne yai kara baiyi saurin dubawa sai da ya gama abinda yake ya dago wayan.
Kallon Yusuf yayi da mamaki tare da fadin Yusuf yarinyar nan ko mutum ce jifa itace ke kirana yanzu muna maganan ta.
Yusuf ya kalle shi yace mutum ce mana kamar kowa kaima kana ranta kamar yadda take a ranka ke nan .
Ya dauka ciki daure fuska kafin in magana ya fara fadin lafiyan kirana ina aikina nace lafiyan ya kawo haka ai .
Ya sake kiran suna na a zuce da karfi yace matsala na amsa mai da cewa may ye ne haka zaka fasa min kunne da kira haka kamar makaho.
Kai na tsani wanan yarinya ya fada a hasale na amsa mai da nima haka wallahi cikin yanayin na bashi amsa.
Nace dama abinda yasa na kiraka don in fada ma ya kamata kaje gida ka duba tsofin ka don gudun su da kakeyi ba shine mafita ba gare ka.
Yace what da karfi don bai yi tsammanin jin wanan magana haka ba a baki na
Duk wani da mai neman albarkan iyayyen shi yana tare da su a kullun suna saka mai albarka da fatan gamawa da duniya lafiya don samun haske a gare shi.
Kai kana ganin kudi da girman kai da suke rudin ka zasu iya sama ma farin ciki haka ne a gare su, sunyi ciwo sun yi rashi amma bakai tunanen zuwa ka duba su ba har yau.
Who dear you are da zaki fada min abinda zanyi akan iyayyena, nace ni bakowa bace sai mai neman albarka iyayyena don haka kai ma na tunar da kai akan hakan.
Kuma kada ka manta da su Affan don sun fi kowa bukatan ka a wanan lokacin don nasan zaka iya zuwa masu hannu sake kai ba abin kunya bane a wurin ka.
Don haka oga aje a duba su kada a shagala da yawa wataran sune masu duba mu you are stupid kece zaki tunatar dani komai kike nufi wai ke wacece wai waya baki wanan right din da zaki min wanan magana haka.
Nace gani kamar kowa na tsoron fada maka gaskiya don suna ganin kana da kudi niko kudin ka ba damuna sukayi ba wallahi gaskiya komai dacin ta dole ne in fada ma mutum shi.
Amma gani nayi buzuwan ka kamar kanta kawai ta sani sai yan uwanta ai don haka nima dan uwa na na sani a yanzu.
Kit na kashe wayan ina dariyan keta shima Yusuf dake zaune yana jin yadda mukayi dashi sai murmushi yake yi yana huci yabi wayan da kallo.
You see abinda nake fada maka kenan gashi yarinyar nan har ta hango tunda kaji ta fadi haka akwai abinda taji ya faru a gida may be.
May yarinyar nan ta dauki kanta ne wai zanyi fa maganin ta a garin nan Yusuf da sauri Yusuf din yace kunfi kusa ai ni dan kallo ne a tsakanin ku sai dai ya kamata ka bincika idan ba wani taji bai da lafiya a gidan ba.
Tsaki yaja yana rufe file din da suke aiki akai alaman rashi ya baci sosai ya dafe kai da hannun shi daya tunane ya shiga yi yaya akayi yayi sake rainin da bai taba shiga tsakanin shi da kowa ba har shiga tsakanin mu haka wai abinda nake mai zakace ko mu din cousin ne.
Kan shi yana dafe da hannu shi daya Yusuf yace muci gaba mana yace kana iya tafiya yanzu makarasa next yanzu matsala ya shiga .
Dariya yayi yana mikewa yace matsalan khadija ke nan ko hararan shi yayi da idanuwan shi da sukai mashi ja shidai ya fice bai yi magana ba.
Ya dade zaune a gurin a karshe ya jawo wayan shi yana neman layin mommy don ita kadai ce zai tsaya yayi magana na fahinta da ita ya gane komay ke guda.
Kira biyu ta dauki wayan da sallama a bakin ta ya amsa mata tare da fadin mommy kowa na lafiya ko kwana biyu ban kira waya ba.
Tace lafiya kalau muke sai dai Alhaji ne jikin nasa ba dadi wallahi wanan matsalar tashi dai ta kwanaki ke damu shi kuma sai kuma Affan da suka kwanta asibiti amma dai yaji sauki sosai yanzu.
Wanan yarinyar takai shu,uma wallahi mommu tace wace yarinyar ke nan kuma yace da sauri No magana mukeyi a nan bayan ya gama waya da mommy sai ya kira hajiya mama.
Sun gaisa ta fara mai korafin rashin kula da kyautatawan da bai yi take mai fadan ga mahaifin shi nan ba lafiya yan uwan shi na kai da komo akan sa amma ace shi yayi biris dasu badon suraj da yazo ya kai shi asibiti ba may yake son mutane su fada a kan shi.
Hakkuri ya fara bata yana fadin in Allah ya yarda jumma,an nan mai zuwa zai shigo ya tabayi jikin Affan sai bata bashi amsa ba.
Bayan sun gama waya ya dade zaune a wurin kafin ya mike ya nufi hanyar fita office din ya rasa abinda ke yawan shagaltar dashi yanzu gamay da iyayyen shi haka.
Zuciyar shi ne tayi mashi zafi don haka ya nufi gidan shi dan ya dan sarara batare da ya sanar da kowa ba ya fice a ma,aikatar nasu sai gida.
Tun a kofa yake jin suruntun yana shiga Nafisa tana zaune a tsakiyan falon tana shan bakin shayi a dan karamin cup tana lumshe idanuwanta.
Ganin shi a wanan lokacin tayi mamakin dawowan shi gida yanzu rigar da ya barta dashi na barci ne saye a jikin ta har wanan lokacin ga su hadiye na busa shisha duk falon ya gauraye ta ko ina kamar ba falon da ya narka ma makudan kudi ba haka.
Batare da yabi ta kansu ba ya haye sama zuwa part din shi har ya kama hanyan da zai kaishi dakin shi sai kuma ya juys ya shige dakin hutun shi ya rufo kofan.
Sai da ta gama shan attayen ta ta mike zuwa wurin mijin nata ba tare da damuwa da irin shigar dake jikin ta ba bata samay shi a dakin ba don haka tasan yana dayan dakin da yakan kebe kan shi wani lokaci.
Can ta nufa duk da tasan ba lalle bane ta samu kofan a bude sai dai tayi mamakin da ta tura taji kofan a bude ta sa kai ta shiga yana kwance yayi rub da ciki a saman gado ta iso gare shi tana fadin.
Samad yau lafiya ka dawo irin wanan lokacin tana kokarin hawa saman gadon ta zauna a kusa dashi juyowa yayi yana fuskantar ta wani irin karni da bashi kanta da jikin ta ke sakewa da kyat ya daure yace banjin dadi jikina ne tace oho ba sannu ba Allah sauwaka.
Samad dama ina son in fada maka satin nan akwai bukin da zamu maradi sai kuma wayan nan kannen nawa maza da suka zo zasu koma gida.
Gashi kuma ina son ka canza min mato don wanan naje dashi har sau biyu an sani dashi sai kuma su hadiye da nake son inyi wa sayayya kafin mu tafi dakuma, , , ,
Ke enough ya ishe ni don Allah duk wanan abin a cikin sati daya kike son inyishi ko kay wai may yasa ke baki da tunane ne wai ?
Tsayawa tayi tana kallon shi galala tana mamaki yadda a dan lokaci yake son juya mata baya haka a lokaci guda tace Samad ni kake dakawa tsawa haka.
Kallon ta yayi yace an daka maki ke baki da aiki sai na abaki dai a naki ai ma yan uwanki kaza ai masu kaza sam baki damu da na wa yan uwan ba da damuwar su.
Tace amma kasan ina da yan uwa da ka aure ni ko yace wa kika fi yan uwa da bukatu ni nawa yan uwan basu son ai masu ne komay.
Tace wanan kai ya shafa matsalar kace kuma ni dai nawa yan uwan na sani kuma dole kai masu don dani sula dagora.
Mamaki da karfin halinta yaji yadda take fadin magana son ranta kai tsaye ta nuna mashi nata kawai ta sani shi yaji da nashi.
Queen matsala kinyi gaskiya yace a ranshi ya ta tunar dani wani abu mai nauyi da na manta a rayuwana shiru yayi taci gaba da masifan ta akan shi bai iya furta komai ba a lokacin.
Tashi yayi ya fada bathroom ya rufo kofan da karfi ruwa ya watsa a jikin shi yai wanka tare da yin alwala don yayi sallah la,asar don har lokaci ya dan gwauta da mintoci.
Har ya fito tana zaune a wirin inda ya barta ya dauki room fresh ya fesa a dakin don bashin da dakin ya dauka ganin zai ta da sallah ya sa ta fita daga dakin ta barshi.
Gyaran kai da jiki mukayi na zuwa gida don haka agajiye muka shigo hostel din mu maryam ta zauna dafa muna abinci ni wanka nashiga don zafi nake ji jikina ina ganin yayi min dauda.
Tsab na fito nayi sallah a wirin na jawo ledan ice cream din da maryam ta sayo muna na fara sha a hankali maryam tace wallahi ji jake kamar kada ai hutun nan da za ayi.
Da sauri na juyo ina ce mata saboda may maryam kika fadi haka tace ban son rabuwar mu wallahi yanzu ko ja koma gida banda wata abokiyar hira a kusa dani don anty na ba zama takeyi ba tana da yawan tafiye tafiye kullon don ita business woman ce .
Nace ko dai ai koya nene kyayi kewan gida mana ni banki ba yanzun haka in bude ido in gani a cikin garin minna ma.
Tace kin ji dadin ki wallahi khadija na yarda ba jin dadi bane farin ciki don ko dashi ne da bazan fadi haka ba farin ciki yana ga inda kake da sukunin aiwatar da komai.
Kafin in magana wayana yayi kara na dauka kina ina nace maynene yace ki ban amsa kada ki min halin ku na yan African don Allah .
Katambayi mutum ya mayar ma da tambaya shi kuma nace ina hostel mana yace ok kawai ya kashe wayan shi dip bin wayan nayi da kallo nace miskilin banza kawai.
Maryam ta gama abinci wanda indomei da kwai ta dafa muna wanda yaji danyen attarudu mai yaji a ciki zubawa tayi a plate guda ta dauko muna lemon kwali a cikin fridge din ta wanda muke ajewa yanzu a ciki ida mun samu.
Na fara cin abincin ke nan cibi biyu kawai nayi wayana yayi ringing na duba yaya Samad nagani a layin kamar kada in dauka dai na dauka kuma gani a kofan ku ya fada kawai.
Kofan mu na maimaita da mamaki nace may kazo yi a nan kuma ban sani ba yace idan zaki fito ki fito sai ya kashe wayan kawai.
Tsaki nayi na wurgar da wayan tare da fadin dan wahala kawai maryam dake zaune ta tsura min ido tana kallo na murmushi tayi tace.
Uhm wani lucky guy din ne yazo haka ake ja mashi aji kuma abinda wasu ke nema ido rufe a zo gurin su anzo kike wanan masifa haka ?
Nace sister kin faye bin kwakwafi wanan fa ba masoyi na bane zuwa kawai