yar su gare ka don mun roki hakan gare su kuma sun yarda.
Ba don iyayyen ta suna fada taji ba na tabbatar da khadija zata iya sa mu dawo da kayan mu a jiyan da muka kai gidan su a yadda ta nuna muna.
Cikin ranshi yace zata iya fiye da hakan ai mommy baki santa bane da shegen girman kan tsiya kamar ba yar tallaka ba.
Ashe ana samun masu irin wanan ra,ayin acikin yayan tallakawa a yanzu shi me take so dashi ne bai dai taba hurta ma wata mace kallaman so ba sai dai alama ya nuna sukai ga aure don may yanzu zata tsiro da wani surfan su na mata wai sai ya nuna yana son ta zata yarda son ta yake yi.
Mommy ce ta katse shi da fadin kayi kokari ka nuna mata so kamar yadda take so ita kasan fa boko da wayewa yariga yayi karfi ga zuciyar yarinyar nan.
Wayenwan kanta ya hango mata haka wanda kuma gaskiya ta hango ma kanta don may zata cusa kanta a inda ba son ta akeyi ba yaushe zatayi tasiri a zuciyar ka.
Wanan shi take hangowa ta kasa tsayawa ta fahinci manufar mu wanan maganan ko yaya ba zan so taji shi ba don mu manufar auren mu gare ka ba munyi shi ba ne don gidan ka ya watse ko mu kara jefaka a cikin matsala a, a muna son auren nan ne a tsakanin ku don ganin dacewa ku da juna saboda kwadayin iri daga gare ta.
Mommy na fahince ki kuma zanyi kamar yarda kika ce ya fada a takaice cikin gajiya da sauraron maganan ta.
Sukai sallama yabi wayan da kallo tare da fadi a fili may deedar take nufi da somaywa akaina da tayi tana nufin har cikin ranta bata kauna ne ko may ?
May take son in nuna mata bayan wanan da nake nuna mata wace mace na bata lokacina haka a kanta a wurin neman ta.
So take na maida kaina karamin yaro in dinga binta ina fadin deedar ilove you such things like that ko may ?
Tsuki yaja tare da mikewa yaji kwanciyan ya isheshi a lokacin wanka yayi ya sauya kayan jikin shi ya fice daga gidan ba tare da yasan inda zai dosa ba.
Sai tafiya yake yana zaga garin kamar wani tababe sai da ya gaji ya samu wuri ya faka motar shi tare da fitowa yana shakan iskan da ke kadawa alokacin.
Sai tara na dare ya shigo gidan nashi shigowan shi yayi daidai da dawowan nafisa gidan don ganinta da yayi zaune falo yaran ta sun rufa ta da sauran mutanen gidan.
Bai tsaya ba kamar kullun don yawan mutanen dake gidan baida daman ya kebe da iyalin shi su gana saboda yawan yan uwan nafisa a gidan.
Har ya gama abinda yake ya kwanta bata shigo inda yake ba barci ya fara daukan shi tazo tana taba shi firgigit ya mike tare da cafke hannun ta yana fadin deedar.
Tsaye tayi tana mashi kallon mamaki don jin abinda ya furta mata kokari mikewa zaune yake yana tattaro natsuwan shi guri daya.
Samad waye dida kuma take tambayan shi cikin kura mai ido tare da tuhuman shi gabanta sai wani irin mugun bugawa yake yi.
Sai da ya zauna yace da ita ke bakiji abinda na fada bane da turanci a fili ta sauke ajiyan zuciyan ta tare da zama a bakin gadon tana fadin wallahi har nayi mutuwar wacingadi na dauka ko sunan watane didan da ka furta.
Ance kije makaranta kin ki zuwa ki samu ilimi ke kenan kullun a cikin tuhumar mutum ya fadi yana komawa saman gadon ya kwanta rairai yana kallon rufin dakin.
May zanyi da wani karatu yanzu banyi jaratin kasan mu ba zan zo nan in bata lokacina da karatun kasarku ni dake da samad inani ina wani karatu kuma ?
Yace hakanane amma nasan nan gaba rashin karatun nan zai zo ya damay ki tace a kan may lokacin da take hawowa gadon da kyau ta kwanta.
May ake so a duniya banda arziki kuma Allah ya hore ma mijina arzikin da zai dubeni ni da diyana da yan uwana don haka babu wani ilimin zaman duniya da zan nema.
Kyau ne da diri Allah ya ban da mijina ke alfahari dashi wanda nasan ba wata macen da zata gilma a gaban ka ka dubeta da sunan so don kafin ka dubi mace da wanan yanin sai idan na daina numfashi kai ko na daina ba zaka kalla ba don tunawa da zube na.
Murmushi yayi yana jin maganan wautan da take zuba mashi mai kama da almara a fili yace watau ke nan haka kike gani ke ?
Haka din ne na sani na kuma san matan ku na Nigeria yadda suke kaima din kuma kwadayin kirana ne ya jaka gareni ba wani abu ba don haka ba zanji kunya fada komai a gaban ka tunda bani gishiri in baka manda muke ni da kai.
Really tace yes ciki yin kwalkwal da idanuwanta kanana tana juya su wanda a da intayi haka abin na burgeshi sabanin yanzu da yake ganin ta mai kananan ido don yaga inda manyan ido madaidai ta suke ga mace.
Yau kwana biyu daddy bai sani a ido ba shima bai damu da yanemay ni ba ina ji fitar shi gidan ya na sallama da maman mu ya dan dade da fita gidan na fito daga dakin zuwa dakin mama.
Sallama nayi na shiga na samay ta zaune tana ninke kaya da aka wanke kai ta dago ta kalleni tare da mayar da hankali ga abinda takeyi.
Mama ina kwana ta amsa min da lafiya ba tare da ta kalleni ba wuri na samu na zauna na dan yi shiru sai can nace da ita.
Mama ke ma fushi kike danine yanzu na tambaya cikin kura mata ido ta dago kai ta kalle ni sau daya ta kawar da kanta tare da fadin.
Khadija don may ba zanyi fushi dake ba kin kasa hakuri da kaddaran ubangiji a kan ki har yanzu fushi fa naga kinayi da mahaifin ki baki fitowa ki gaida shi kamar yadda kuka saba.
So kike shi yaje ya gaida ke a dakin ki ko may mama ni ba fushi nake da ku ba wallahi kun dai kasa fahinta nane kusan may mutimin nan ke nufi dani.
Wallahi mama AA ba sona yake tsakani da Allah ba so yake yayi amfani daku don ya cuta min da sauri mama tace Allah ba zai basu ikon cuta maki ba khadija.
Nasan abinda kike ciki ba ban sani bane so nake kiyi biyayya kamar yadda shima yayi biyayya ga iyayyen shi.
Allah kadai yasan may wanan auren naku ke nufi da ya hada ki da wanan mutumin fatana gareki koma manene ubamgiji ya kara mayar dashi alheri ga kowa.
Hawaye ne ya zobo min a idona wanda na kasa controling din shi na barshi yana tsiyaya kamar yadda yake son zuba din shike nan yanzu itama mama ta yarda da wanan hafin ke nan.
Tace khadija da farko na dauka don kudin shi mahaifin ki ke son maki haka amma da Amina ta zauna ta fahintar dani sai na gane taimakon su kawai mahaifin ki ke son yayi dake bawai do abin hannun shi ba.
Ku diya mata Allah ya fara bamu a farkon haihuwan mu don haka na jajirce inga ke din kinyi karatu duk da mahaifin ku bai son hakan na samu da goyon bayan mijin Amina mukaci nasaran hakan.
Sai yanzu ne nake fahintar ba diya mace ne kadai keda matsala da rauni ba harda namijin da mata da yawa suke fatan samu farkon haihuwan su suke da matsala.
Wanda a zaman nin nan da namiji ya zama tankar innuwar giginya ne ga iyalin shi na nesa kasha innuwar shi ma,ana matan shi da wasu can daban zasu ci amfani shi ba iyayyen da suka reneshi suka gina shi ya zama wani abun ba.
Khadija akwai aiki ja a gaban ki wanda aka taru aka dora nauyin shi a gare ki yanzu da addua kadai zamu biki don taimakon ahalin wanan bawan Allah.
Cancantan kine ya ja maki haka bawai rashin son da kike tuhumar ba ai maki bane ko wani abin ko nine yau dana yake cikin wanan halin dole in nemi mafita a gare shi.
Matukar naga abinda zai fitar dashi din ga halaka kada kiga laifin kowa ga wanan abin abinda Allah ya kaddarane a kanki ya tabbata ubangiji yasa haka shine daidai.
Ki natsu ki san abinda kikeyi kada ki sakacin da za a gane tako ki da sauri ki fara aiwatar da shirin ki tun yanzu wanda ba komai bane wanan shirin sai komawa ga mahalincin ki Allah ki mika alamuranki a gare shi tunda bakin alkalami ya riga da ya bushe mahaifin ku ya riga da ya bada ke garesu.
Kuka namike inayi nabar dakin da sauri zuwa dakin mu ban fito ba har tsawon wani lokaci sai da zanyi sallah azahar na fito na watsa ma jikina ruwa.
Biyar na yamma daddy ya shigo gidan ina jin shi na fito ina mashi sannu da zuwa ya amsa min ba yabo ba fallasa a fuskan shi.
Na juya zan wuce naji yace dama ina son magana dake sai na dawo na tsuguna a gaban shi tare da dukar da kaina kasa ina sauraren shi.
Yace khadija da na zaci zaki fahinci manufana amma yanzu tunda kina ganin zamuyi maki dole ne na janye kudirina ga maganan mutumin kaduna a kan ki ki fada ma wanan mahmud din da kike so ya turo wanan satin don ba zan janye lokacin dana sa akan ki ba yana fadin haka ya juya ya shige bandaki da buta a hannun shi ya barni a wurin tsugun ne.
Bayan kwana biyu sai ga mahmud ya amsa kiran daddy har falon daddy ya shigo nan daddy ya aika a kirani nida mama muka shigo falon.
Banyi tsananin ganin mahmud afalon ba kallo daya nayi mai naga duk ya rama bakin shi ya kara fitowa fili tausayin mu ya kara kamani.
Dan mun nasan muna cikin wani hali dani dashi a lokacin gefen kujera na samu na tsugun na bayan yan gaisuwan da akayine a tsakani daddy ya fara magana.
Yace mahmud mun aika kazo ne don maganan da ke tsakanin ka da yarinyar waje na khadija wanda nace ta fada ma ka turo magabatan ka yau kwana biyu naji shiru.
Don haka na kiraka gaka gata ga uwar ta lamari ne na aure ban son wani boye boye don lamarin aure ba wasa a cikin sa.
Ina kallo sai da mamud ya goge zufa a goshin shi ya fara magana da fadin a gaskiya daddy ina son khadija tsakani da Allah.
Sai dai matsalan da aka samu shine maganan yanzu yazo min a girshi banyi tsamani jin haka a yanzu don tun farko naso muyi aure a lokacin da nake bukatan karin aure sai ta nuna min sai ta gama karatun ta.
Yanzun kuma nasan idan na kara tunkaran iyayyena da zancen karin aure a wanan lokacin abune mai wuya iyayyena su yarda a yanzun din.
Zaici gaba da magana daddy yace dashi dakata haka mamud ya isa haka ma sai dai a gaskiya baka kyauta muna ba da kasan da hakan tun farko da ka bari son ka ya zurfafa a zuciyar diyar mu.
Yace daddy ba haka bane wallahi na dauka sai ta kare karatun ta ne za a fara maganan auren ba yanzu ba zuwa lokacin na shawo kan iyayyena da maganan.
Wallahi da gaskiya nazo ma khadija bada wasa ba don ina son khadija tsakani da Allah irin son da ban taba yiwa wata mace shi ba.
Daddy ya amsa da fadin wanan magana ai ya wuce mamud don gaskiya ba zan dauki diyana in bayar inda iyayyen miji da yan uwa basu son ta ba.
Don irin haka har jikokin da zata haifa masu sai kaga rashin kauna ya shigo tsakanin su da su don haka kayin hakkuri kabi umurnin iyayyen ka yadda suke so.
Ita kuma Allah ua bata wani mai albarka ta aura daddy yana fadin haka na mike nayi waje da gudu zuwa dakin mu ina kuka.
Ba wanda ya kara bi ta kaina har kwana biyu mama ta samay a dakina kwance ina faman tunane ta samu wuri ta zauna tana fuskanta na tace.
Yanzu may ya rage kuma banda kiba kanki hakkuri agaban ki dai akai komai ba a bayan ki ba kinji da bakin shi ya fada matsalan daga iyayyen shi ne.
Kina son ki fada gidan da ba a san muhinmancin ki bane da darajan ki abi yazo har ya shafi diyan da zaki haifa nan gaba kin fi kowa sanin halin nufawa ga abinda suke ki.
Cikin kuka nace mama nidai naga kamar nice daddy baya so yanzu in bashi ba mai zai sa ya matsa sai nayi aure yanzu bayan yasan karatu nake yi.
Daddy yasan ba wasu maza nake kulawa ba nafi ba karatuna muhinmanci a yanzu bisa ga komai da nakeyi amma zai bijiro da zancen wani aure yanzu a kaina da rana tsaka.
Ke ki shiga hankalin ki ki natsu kisan abinda kikeyi aure ne kin san ba fashi kuma mahaifin ki ya baki daman ki kawo duk wanda kike so a yanzu ba sai wanan din daya fito ba.
Nace cikin kuka mama daddy ya kara bani dama in fito da wani bayan wanan don ni gaskiya ba zan auri wanan AA din ba.
Yanzu ai dabara ya saura gare ki tunda ke baki daukan shawara ki yarda da kaddara ta mike zata bar dakin nace mama don Allah kada ki fushi dani don ke kadai nake da ita wace ke tausayina a yanzu.
Kamar zata wuce sai kuma taja ta tsaya tana cewa dole un fushi dake khadija idan kowa zai cuce ki banyi tsamanin ni da mahaifin ki zakiyi tsamanin zamu cuce ki ba.
Sanan ki sani mahaifinki ya na nan ga bakan shi na aure zai maki bada dadewan nan ba sai dai ki karasa karatun ki a gidan mijin ki can .
Mama duka duka nawa nake yanzu da daddy ya matsa da maganan aure a kaina kodon nayi saurin shiga makaranta kuma anyi fushing dina don kokarina kuke ganin na girma da yawa a waje.
Tace sai ki tambayi mahaifin ku do shi keda amsan hakan bani ba daga haka ta fice dakin ta barni da tunane a raina.
Kamar daga sama zuwa rana sai ga maryam gidan mu naji ana taron ta da sauri nafito waje don in gaskanta abinda nake ji ita dince tana tsugune gaban mama suna gaisawa.
Da murna na isa wurin ta ina fadin ke kuma sai ki fadowa mutane haka ba sanarwa tace cikin jefo min harara ke tun yaushe ana neman ki a waya va a samu ki ba dole in biyo ki ba wana shiru haka.
Bayan taci abinci muna zaune dakina muna hira nake koro mata abinda ke faruwa dani sai da ta gama saurare na tace min.
Tace haba khadija kin so ki tayar da hankalin ki ne amma ni dama na sani duk cikin masu neman ki kun fi dacewa da AA don hadi ku daga Allah abin yake hankali na yafi kwantawa dashi gaskiya .
Don shi yafi dacewa dake tsakani da Allah kece dai baki gane hakan saboda wani dalili naki can.
To ai ke ma mace ce zaki iya auren shi tunda ya fi kwanta maki a rai don ba haram bane idan kin aure shi ai don naga halin ku kusan daya dashi don haka kunfi dacewa dashi.
So don haka kada ki kara min maganan wani AA can don Allah don ni bashine a gaba na ba yanzu mafita nake nema na yadda zan shawo kan daddyn mu.
Wani irin kallo take min can tace may yai zafi haka khadija daga fadan gaskiya sai ki fada min bakar magana kuma ke dai yagani yace yana so bani ba.
To ba zan aure shi final sai yaje can ya samu daidai dashi bani khadija ba dariya take min bata kara bi ta kaina ba kuma ba mu fada yayi nisa don haka ba a dauki lokaci ba muka shirya da ita.
Kwanan ta biyu da zuwa wanda naji dadin hakan don na manta da halin da muke ciki da iyayyena.
Sai dai maryam takan zolaye da wasan ga amarya ba ango tsayayye nakan ce da ita ke ki ganta can.
Zuwan Ya Amina yasa nasha jinin jikina don yanzu ina ganin zuwan ta ba alheri bane gare ni sai dai danaji tace tare da mijinta suke yazo wani aiki nan ne yasa hankalina ya kwanta.
Sai dare ya shigo gidan suka gaisa da iyayyen mu sun dade suna magana da daddy a falon mu kafin ya fito ya bar gidan tare da matar shi nan tabar muna yara a wurina.
Na dade ina barci da safe ban tashi ba ko da na tashi ina tambayan maryam mama tace min wai ta fita nayi mamaki wa ta sani a garin kuma ina taje wanka nayi don na samu mama ta gyara yaran ya Amina koda na tashi.