Adaga ta wai tayi kariya a kafan ta daga faduwa fa a gaban gidan nan su momy suka mike suna fadin subbahanallahi yanzu tace gata can za a kwashe ta ai duk sun tada hankalin su a waje.
Gurin nace aniya mako miya wallahi kinga mugun abinda suka riko ne ya koma masu nan suka barmu zaune suka fita sai ya Amina ne bata fita ba dakin ta zauna dani a dakin da yara.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yadda naga maryam tana ta faman shirya ma sunan yasani tambayar ta wai har suwa zasu zo ne take wanan shirin haka ne ?
Tace idan ke baki da mutane yaran da mutanen su suka zo duniya don haka ki barni in shiryawa bakin su ke baki san abinda kika haifa ba ina gani.
Ga mijin ki shi sai faman shiri yake keko kin zauna sai kumshe kai a cikin daki gobe dai ki shirya mai sallon na tafe gidan nan suyi maki gyaran kai.
Murmushi nayi mata nace to maman biyu Allah ya kaimu goben lafiya saura kwana biyu suna babu zama don abubuwa sun yiwa kowa yawa don an gyara ko ina na gidan.
Yusuf ne ke gabatar da komai shikan AA nasa bayar da kudine kawai washegari yan kaduna suna isowa basu dade da zuwa ba mutanen minna suka iso mota daya doguwar motar maikatan lafiya nasu mama tani aka basu.
Duk gidan ya cika da jama,a hotel AA ya kama ma bakin namu mai kyau da tsada sai yabawa suke yi yara sunyi goshi inji momy tunda har hajiya umma tazo Abuja suna hajiya mama kawai aka bari a gida.
Naji mamakin rashin zuwan Anty Fati da batayi ba sai dai sakon da ta bayar a kawo min yaran dai sun zo da wasu yan uwanta mata biyu nasan su don suna zuwa gidan idan naje kaduna.
Duk wani abinda za a gabatar sune masu gabatar dshi su Fauziya basu samu zuwa ba don suna tsamanin kira binta da zainab dai sun zo sun hade da maryam da wasu kawayen mu biyu da muke zaman mutunci a hostel.
Baiyi shawaran komai dani ba da iyayyen shi da yan uwanshi yake shawaran shi nima kuma hakan bai damay ni ba.
Ban baku labarin sunan yar gurin Nafisa da sukai shagali ba bayan dawowan mu inda mata yan duniya suka barje gumin su ranan akai ta muna iya shege agida dasu haibaici da gori.
Sai ga Nafisa yanzu fitowa waje yana son ya gagareta don nuna tan da akeyi tana gani ana cin arzikin mijinta babu dama tai magana.
Muna nan da daren nan muka samu labarin hajjata mata an hanasu tafiya don a shekaran akai doka saudiya sai mace taje da muharamin ta zata shiga saudiya.
Wanan abu ya tayar muna da hankali sosai don muna ganin bazasu samu dagawa ba zuwa makka sai da yusuf ya shigo yana muna bayanin wai AA ya biyawa Ahmed shine zai tafi tare dasu da yar wurin umma daya su hudu ke nan.
Washe gari aka tashi da hidimar buki a gidan inda ake ta shigowa da kulolin abinci gida yana waje sai ganin Nafisa yayi ta fito da yaran ta da yan uwanta wai zasu bar gidan har taro ya watse yace babu inda zata tafi mai da yara inda zata tafi ita daya bai hanata ba.
Dole ta juya ciki dasu bata dade ba ta fito ita kadai ta fita ta barsu da yan uwan ta su Fatiya a gidan.
Sai abin arziki nake samu daga matan da ban sani ba wai matan abokan shi da yan gurin aikin su ne ke zuwa muna murna.
AA ya yanka ma yara raguna biyu na suna sai shanayen da aka yanka don aukin nama Umma da momy ne suka zo kiran su mama Tani su fito falo ga kayan suna za a gabatar masu.
Duk wanda yazo ina bashi kulawa da tallaka da mai arziki don abu daya ne ya tara su a gurin don haka nake ba kowa kulawan daya dace don kada wani yace na fifita wani.
Ihun dana a falo ne yass mu yin shiru ashe cikin kayan sunan ya saka min makulin motana sabuwa dal baka kal da ita wata jeep dirkekiya na mata new desgn.
Maryam ta shigo dakin da murnan ta tana rawa tace kin kai ga mota khady AA ya bada ki kyautar mota albarkacin su yan biyu.
Baki na tabe nace in dai don su zai ban mota ya bari ban so suka shiga min shakiyanci a gurin amma kasan raina nace may wanan mutumin ke nufi danine dama daya kasa saya min mota kullun yana min wake.
Nafisa ne suka shigo da kawayen ta gidan kallo ya koma wurin su don shigar su sun nuna hali da gadara sosai a jikin su.
Sai zuwa rana Anty hauwa ta danno da tawaganta sai motoci ake fakawa a gidan bata dade da zuwa ba hajiya laila SJJ ta iso itama wuri ya dauki manyan mata don su shidda ne ita ma .
Kyautar da suka kawo ne ya girgiza kowa a gurin motace Parado fara na mata mai kyau dashi sai da jikina ya mutu na kasa magana a gurin.
Tace yayan ku ne yace a kawo maki ita albarkamcin su yan biyu ki karba don Allah don yasan halin ki su momy da Umma aka kira don karban wanan kyautar sai manya.
Anty hauwa ta karba tace ai godiya wurin maigida su yan biyu sun gode nikan na rasa may zance don nasan akwai rigima gurin AA idan yaji.
Walima aka shirya zuwz hudu aka hallara babban falon gidan Nafisa suna ciki ana cacakan AA dani da yaran sai mugun baki suke muna.
Labarin kyautar wata motar ya kai gare su ranan da kyat su Badosa suka shawo kan nafisa ta haukace wai an nuna mata banbamci annuna mata ita ba yar kasa bace.
Da kyat aka samu ta fito wirin walima suka zauna sai wani sallo suke suna ganin su anty hauwa da mutanen ta sai kuma ga matar Sjj sun fito sunga karyan naira inda take aiki a gurin.
Sai suka koma kuskus ina na samu mutane ne haka irin kudin da ake ba malamar da gudun mawan da tace ana nema marayu wurin ya firgita Nafisa ta fara mikewa zuwa dakin sauran ma suka bita.
Malam ta gama sai Fatiya tace a dan bata lokaci akwai kiran da zatayi mata yan mintuna kadan don Allah.
Tunda ta karbi abin magana ta fara wurin yayi tsit inda tai nasiha kan hakkin yaya zuwa iyayyen su kafin su girma da inda illoli ke fitowa daga iyayye mata wurin tarbiyan yara yanzu.
Kowa ya yaba da hankalinta sosai kudin data samu tace a hada a bawa malaman batayi don karban komai ba sai ta rufe akan jin tsoron Allah a zukata saboda mata sun shagala da yawa.
Coure mate dina sunyi kokari sosai don ku san musulmai da Christian duk sun halarta harda wa yanda ba course din mu daya dasu ba sunzo.
Anci an sha araba jakkuna dake dauke da kayan buki a ciki mai hoton yaran su biyu taro dai ya watse lafiya ana sam barka.
Can kuwa kawai Nafisa ne ke kara zugata har yaushe na shigo gidan da zan bunkasa haka a cikin dan kankanin lokaci kai mutane akwai munafunci dasu.
Don neman fada ne a gurin mijin ki yasa suka tara mata wanan abin arzikin haka mai yawa wata tace ni ba shiba kun ko ga sarkan wuyan ta a wirin waliman nan zai tasan ma milayan kusan biyu ko uku fa.
Kai kai ina wanan yar talakawan ta gama min yakar kauna a gidan nan yaushe nasa sarka makamancin haka a wuyana wata tace kece baki so lokaci daya sai ya mallaka maki wanda ma yafi wanan kudi.
Banda abinda zancewa Anty hauwa da maryam sai godiya don itace ta hada kan sarkunan ta canzo min wanan a Dubai a matsayin kaddara ana gama taro ta rada min a kunne in adana sarkan nan don ya tsone ma kowa ido a gurin sosai.
Yara sunci suna don na Mijin an saka mai muhammadu Aminu-lah kanin Abban su daya rasu, sai mace da aka radawa sunan hajiyan su Aisha humaira tun haihuwan Ihisan yaso sawa tace bata yarda ba don ba wani ya haifa mata diyar ba.
Ko zuwa dare ban samu kaina ba duk da ciwon da kaina ke min don bakin kaduna dana Minna dake gidan zakace ba a watse ba.
Yana shigowa get din gidan idon shi akan motar da aka kawo min kyauta ya yaba da motar sai dai ya dauka mai shi na cikin gidan ne tazo buki.
Yana shiga Nafisa dake dakon shigowan shi tana mara mai baya kusan a tare suka shiga dakin lokacin.
Ganin yanayin ta yasan tana da magana a bakin ta don haka ya sashi daure fuska jin muryan ta yayi tana fadin macuci azzalumi ya juyo da zauri
yana kallon ta tare da fadin may nayi maki kuma daga shigowa na yanzu.
Tace azzalumi zakace baka san cutar da kaimin ba wai kai zaka nuna ma duniya niba kowa bace yace to wa kike nafisa shugaban kasa kike ko matar shugaban kasan ?
Tace ban ko daya yace to ki tsaya a matsayin ki na matar Abdulsamad yafi maki cutan da kike cewa nayi sai ki fada min inda na cuce ki kuma ?
Tace wani cuta ne bakai min ba kuma na taba haihuwa ka sai min sarkan gwal ko na taba haihuwane ka bani mota a matsayin kyautar haihuwa.
Kai ya girgiza yace lalai Nafisa ke butuluce ta karshe sarka wani irin ne ban sawo maki ba duk naje turai shine tsaraban ki kina amfani dashi a gidan nan ne idan na saya maki ban ganin shi.
Mota kuma shigowan ki gidan nan mota uku na saya maki kina kadarwa wanan ma yanzu da kike shiga nawa ne kika dauka a matsayin dannan kirjin ki bayan kudi da kika saka in baki na fati ko ita khadijan ?
Tun suna fada su biyu a dakin har yakai sun fito falo a bainan jamma,a suna yi umma ta fito tare da gwagwanin shi suka kada kan shi ya fice ya barta.
Yace umma wanan matar kashe ni take son yi haihuwan nan da tana da halin murde yaran nan da uwar su da tuni ta murde su sun mutu kowa ya huta.
Akan ki ne kishiya ta fara haihu a zauna lafiya may wanan matar take nufi da nine kamar itace ta haife ni ko ta ajeni a gidan nan haka ?
Fitan su bai sa ta yi shiru sai tonawa kanta asiri da miji take a gurin yan uwan shi kowa na tirda halin ta.
Ban samu kebewa dashi ba sai washe gari don fada mai zancen motar tunda nayi wanka na shirya cikin wasu atamfan exclusive na sillace jiki zuwa wurin shi.
Yana kwance har lokacin sai dai ba barci yake yiba kuma yana kwance rai rai kamar wanda ke tunane a lokacin sallama nane yasa shi dan dagowa gare ni.
Tun ban kai zaune ba nace yaya lafiya ko ina zama a kusa dashi ya dan gyara min na zauna da kyau yace matsalan kune da baya kare wa nake tunane.
Nace mun kuma da mamaki ina kallon shi kafin in kara fadin, wani abin mukai maka kuma yace zaku fasa ne gaba dayan ku na rasa gane inda kuka dosa da rayuwana.
Allah ya kyauta nace don ban san may mukai mashi ba yai wanan jam,in haka gare mu nace godiya nazo in wa su yan biyu akan kokarin da akai muna mun gode Allah ya kara rufa asiri yasa a fi nan karfi.
Kamar ba zai karba min ba sai can yace amin ke kin iya godiya idan an maki alheri nace kowa ma ai ya iya tunda bamune muke nema ma arzikin naka ba sai yadan yi murmushin yake.
Yace ina yaran suke nace ana masu wanka sai dai naji umma na fadin kamar yau zasu koma fa yace yau din nan nace haka naji ta fadi jiya dai don wai Abba yace kada su wuce yau idan sun zo.
Komawan su ba zaiyi yau ba sai dai gobe har yan Minna din nace harsu yace eh haka nake so idan sin dan huta sai kowa ya kama hanya kisa Altine ta kirga min ko su nawa ne daga minna haka ma yan kaduna.
Nace nabarka lafiya har na daga na dawo nace ai na manta kaga bakuwar mota a waje gidan nan ko ?
Yace eh to akwai dai motoci a gurin gaskiya nace wata parado fara yace ok da wani flawer kamar gift ko nace eh ita yace naganta tun jiya a packer gurin.
Nac to ita ma wasu yan biyu aka kawo wa kyautan ta mikewa yayi da sauri yace wa ya kawo masu kyautar mota haka nace wanan dai matar mutumin nan dan uwan yaya Adam dakaiwa alheri sune suka zo dashi.
Nan dai na fada mai yadda akayi tun kawo kudin su da bankarba da kuma zuwan su jiya da mota da har anty hauwa ta karba.
Abinda nayi tsamani ne ya faru don lokaci daya idon shi ya canza min ya hauni da fada khadija jin ya ambaci sunana na asali yasa na fahinci maganan takai magana gurin shi.
Ban fada maki rayuwana ba haka yake ba cin hanci ke nan suka kawo maki komay yau idan badon nasan halin ki nasan ko ke waye ba da ba abinda zai hana in saba maki a gidan nan.
Nace yaya kada kaga laifina a hakan nayi duk iya kokari na in kaucewa hakan don gudun bacin ranka sai suka biyo min ta wanan tsigar kuma.
Banda yadda zanyi a cikin mutane ga maganan da ta fadi wai kanwa nake gare shi do haka su yan biyu yabawa mota bani ba yace ni zai gwada wa mota komay ?
Ko gidana bai gannin da motoci bane da zai dauko wanan motar ya kawo maki motar nawa na saya maki da kikaji nafisa na fada akan shi jiya.
Ke bari kiji idan kin shigo rayuwanane ki lalata min suna wallahi baki isa ba duk fadan da yake yi kaina na kasa ban san lokacin da hawaye yazo min ba cikin wani irin murya mai sanyi nace.
Ni yaya Abdulsamad nice na shigo rayuwan ka don in bata ma suna ni khadija Adamu danladi dini sai na mike hannun na naji ya riko min ta baya.
Na koma na zauna a inda nake yace ki fahince ni Deedar wanan ba rayuwana bane cin hanci da rashawa da ina wanan halin da yanzu nafi haka a garin nan.
Cikin kuka nace na sani yaya amma ni may ye laifina a ciki yanzu tunda ba rokon sa nayi ba sun nuna min wanda ya rigaka kwana ya rigaka tashi ne da ban karbi kudin su ba sai suka biyo min ta nan kuma.
Amma idan kaga laifina a cikin wanan maganan har kake ganin za a hada kai dani a cuce ka kayi hakkuri zan kirasu suzo su dauki abinsu tunda ni ban san gidan su ba ma.
Ki barni dashi zan kirashi inji dalilin yin haka a gareni don banga dalilin saka mata na ga maganar business din mu dashi ba.
Shiru nayi hawaye yana zuba min sai can danaji ya tsagaita fadan na mike na fice a dakin ina share hawayen fuskana da bayan hannu na.
Bayana yabi da kallo har na fice daga dakin ya sauke a jiyan zuciya tare da jan guntun tsuki ya mike a inda yake yaka ya shiga yanayi yana tunane abinda ya faru tsakan mu yanzu har na bar dakin.
Sai yaga rashin kyauta min da kalamin shi don a gaskiya bai ga laifina a cikin zancen ba don ko gidan su ma bawai na sani bane kamar yadda nace mai.
Ina shiga daki na samu a nata hada hadan wanka da shirya abin karyawa wa baki na samu ya Amina tayi wa su Affan wanka tana shirya su na shigo tace ga diyan ki nan wai ba zasu tafi ba yau suka ce.
Nace ina ganin ba yau bane tafiyan su duka ai ganin yanayi na yasa ta fadin wani abin ne ya faru kuma ?
Ina kuka nake fada mata abinda ya faru tace ikon Allah wanan mijin naku halin shi sai shi may ye a cikin haka ba karuwa ya samu aka kawo gudun mawa ba.
Ina share hawaye gajiye ta fado dakin itama tsayawa tayi tana tamnaya ya Amina tace uhmmm ita da mijin su ne akan motar da aka bata jiya ne suke jidali nan dai ta fada mata komai.
Tace shikan wanan shiya kwaso mai sunan nashi da komai wallahi to ba za a mayar ba wa ya taba wanan halin don Allah dai shifa wani irin bahagon mutum ne shiyasa yai daidai da kalar matan shi ai.
Fita tayi kafin wani lokaci sai fa momy ta shigo dakin tana fadin yanzu nake jin wani magana gurin Altine ya Amina ne ta fada mata komai.
Tace haba babangida