Jikina ne yayi sanyi da jin maganar shi ban iya furta komai ba na nufi kitchen din zuciya ta yana tunane itama zainab ke nan irin rayuwa na zata fada zama da kishiya.
Sai da na dora komai na haura sama inyi wanka na fito ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin ya fito daga gidan iyayyen shi.
Inda nake zaune a gaban mirrow ya nufo yana fadin daga wurin su hajiya nake tafe yanzu nayi mata maganan mai aikin ki tace zata diba ta gani idan za a samu kafin mu tafi.
Nace tare da su Affan nake son zuwa suyi min hutu a can tunda zan samu hutu in two weeks coming sai su dan debe min kewan zaman gida.
Yace kunyi magana da hajiya ne nace banyi na dai fadawa maman su wancen zuwan da mukayi yace ok bari zan mata magana muji sai dai kin san ni zuwan su zai takura min.
Nace wani takura kuma duk mutanen dake gidan ka basu takura maka sai wa yan nan yaran kananane zasu takura ma.
Baiyi magana ba sai hannun shi dayakai saman wuyana ya shafa na dan noke yace zan bar maki driver guda da zakuyi zirgazirga dashi don aike.
To nace tare da furta angode kada ki manta da yan uwan hajiyan mu fa na zaria a wurin rabo nace ni ina nasan su yaya, ?
Yace waye yayan naki ya tambaya yana matsowa inda nake again nace cikin dariya gaka kuwa ko zaka banbantani da su zainab da binta na tunda ka zama kifi yanzu, , , ,
Bakina ya kaima cafka ban samu karasa zance na ba ya ce shiyasa naman shi keda dadin don da yan uwansa ya girma.
Karni dai na bashi amsa bakina yana makure da hannun shi yace wanan bakin zanga ranan da tsiwan sa zai kare ?
Sai ranan da ka bar tsokana na zai daina tsiwa nace mai tare da fadin da su anty Fauziya da Anty faiza da antyn nan gidan ai zamu kasafa kayan yace kin yi daidai.
Ruguma ya kai min daidai ina mikewa zuwa wurin jakkan kayana ajyan zuciya na sauke da ban san yazo min ba tare da lumshe idona.
Yace you miss my hug ko two days nace na fada ma haka tunda na saba an hanani auren mara mata a inda zan samu kulawan mijin ko yaushe a kaina.
Murmushi yayi ya sake ni tare da fadin kin makaro yarinya sai dai diyan ki su samu kila au dazun hajiya take wani magana da ban gane kansa ba nace na may fa ?
Dauka kamar suke kina da ciki ko nace haka suks ce min nima basu san canjin yanayi bane kawai yai dariya ya fice dakin.
Nagama shirina na sauko kasa lokacin shima ya fito da shirin shi zasu wuce ke nan a falo inda na bar anty na samay ta zaune.
Na gaida ita tare da dan zama a gurin ta nace anty dama akwai kayan da muka zo dashi na rabon azumi da yace su anty Fauziya da anty Faiza zasu shigo sai a raba.
Tace wanan aikin ki ne ai khadija tunda bai taba yin haka ba na gani nace anty ai yin hakan yana da kyau may ne amfanin kana da baka yi wa yan uwanka abinda ya dace dasu.
Ko mutum nada hali ai yana son kari ko tace wanan kuma dai yanzu naki shawaran ke nan dai nace bai yi bane anty tace yana dakyau hakan ai.
Nace ko dacen sai nake ganin laifin ki ne da baki lurar dashi abinda ya dace yayi wa yan uwa da abokan arziki wai laifina kike nufi mutumin da baida lokacin kansa balle na wani .
Nace ko yanzun haka yake anty a haka dai zaki matsa ki ta saka shi a hanya daya dace tayi murmushi a gitsire a fuskan ta.
Kitchen na nufa wurin girkin miyan dana dora na bar ma laraba dafa shin kafa fara na samu komai yayi yadda nake so.
Wutan na kara ragewa na kara ruwa na barshi ya dahu da kyau daki na koma na kira binta take cewa gamu tafe munga yanzun mijin ki ya bar nan ai zai tafi zaria.
Nace ni ida ma kuzuwa bashi na kiraki ba tunda nasan zamana daku yanzu kiran ki nayi ki ban lamban anty Fauziya don Allah.
Maimakon tayi magana sai kara ma anty Fauziya waya a kunne tayi naji tace hello khadija yanzun muke maganan ki da hajiyan mu ai.
Nace Allah sarki anty dama ina son ku shigone akan zancen kayan nan da muka zo dashi na azumi tace yar halas yanzun hajiyan mu ke min bayani gamu tafe gidan.
Sun ji dadin wanan abin don da farko har sun fara zance na suna fadin ni kuma da iyawa na shigo sai nice zan raba masu abu sai gashi na kirasu akan maganan.
Hajiyan mama tace baku da hakkuri akan abu wallahi ni nasan baza tai haka ba don yarinyace da zuciyar manya tasan ya kamata sosai ai.
Sun shigo gidan a lokacin kowan mu na dakin ta sai laraba dake gyaran wuri sama suka hau suka fara shiga wurin anty Fati daga nan suka shigo dakina.
Mun da jima muna hira suna fada min komai ya kammala na taron baki da suka tanada sai zuwan su ake dako yanzu.
Falo muka fito na tura laraba ta kira driver da zai shigo muna da kayan ciki ni da kaina na shiga dakin anty Fati na kira ta tana kwance nake fada mata ita ake jira ta sauko.
Tace muje a raba kawai dan jimm nayi tare da fadin anty ina fatan ba fushi kikayi ba akan haka idan ma kin dauka wani abu ne Allah yaga zuciyana wallahi.
Ban shigo cikin ku da zuciya biyu ba sai alheri tsakanina dake don baki min komai ba a rayuwana tarkan yayata na dauke ki a gurin na.
Don haka ina mai baki hakkuri idan ni na saba maki badon niba sai don Allah ki daure ki fito ki bada umurni a matsayin ki na uwar gidan nan.
Kada ki sakaci da daman da Allah ya baki a kan mu Allah ya gani ba zan taba shige maki gaba a kan hakkin ki ba a gidan nan da yardan Allah.
Murmushin nan irin nata tayi kamar dole tace khadija na gode na kuma fahince ki sai dai nima bana fadi haka da wani manufa bane gaskiya na fada maki ban son irin wanan abin ganin laifin ne.
Nace yaya zakiyi Allah ya baki wanan girman sai dai ina kara baki shawara badon nakai ba ko na cancanci na fada maki kina sakaci da daman ki don ko ke ce babba a cikin mu kamata yayi wani abin ke ce mai daurewa ki fada koda ba zai dauka ba a lokacin nasan zai duba daga baya yai amfani dashi.
Yanzun dai khadija na fahinci dole sai naje kasa ke nan ko nace haka nake so anty don ke ya kamata ki komai a matsayin ki na matar gidan nan .
Kinga yanzun ana ta shirin kawo kayan zainab alhalin hajiya mama ta kiraki baki kuma leka ba har yanzu.
Mikewa tayi daga kwancen da take tana fadin gaskiya ta fada min kamar kwana bakwai da ya wuce sai dai ban samu lekasu ba din.
Nace anty yin haka kamar kina sakaci ne da daman ki da Allah ya dora maki tunda ko banza wanan abin ai ya shafe ki amma ki gafarce ni idan na fadi ba daidai ba.
Tare muka fito da ita daga dakin zuwa kasa inda na samu su Anty Fauziya sun kulu da dadewan mu a ciki.
Nice na basu hakkuri nace na samu tana bayine na tsaya jiran ta anty Faiza tace na dai dauka tana halin nata ne data saba ai don dukkan su sun girmay ta ga shekaru.
List din nabawa anty Fati tun muna saukowa nayi mata bayanin komai ta karba ta zuwa kuma sai ta mikawa anty Faiza anan na fahinci halin ta irin mutanen nan dake da halin ko in kula akan abu.
Na suka shiga bin komai yadda ya kamata tun nan suka tayar da binta da driver aka fara mika na mutanen cikin gidan su kafin wani lokaci a kaiwa kowa wanda ya kamata anyi yadda ya dace.
Kitchen na koma na duba girkin yayi na shiga rabo tare da laraba tana mikawa a falon karshe na fito ma laraba da nata .
Abin ya daure ma laraba kai sosai tace hajiya har dani sai kin biyo ni da nawa kason kuma nan ai da ki barshi a can in dauko.
Nace haba dai mama kina gaba dani zan bar maki abinci acan ki dauka karma ki koma irin maganan nan don Allah kije ki huta yau mun aikatu da yawa sai zuwa anjima a kai makarde shikafa da zamuyi sinasir dashi.
Ta karbi abincin tana godiya nace sai dai kada ki manta da markaden don ya dan samu rana ya tashi.
Tace yanzun kuwa dana gama zan mika insha Allah jinayi anty Faiza tace uhumm, ummm laraba yau ke ma dai kin ga canji a gidan ku ko.
Yanzun dai Fati dabara ya saura gare ki duk da baki son afadi matsalan ki ya zama dole ko mu fadi don ke din dole mu ce.
Yanzu dai ga abokiyar zama kin samu kamata yayi ku hade kan ku ko bazan kune yan kasa al,adan ku daya kabila daya kin ga komai zai zo maku da sauki idan kan ku yana hade.
Anty Fauziya ta karbe da fadin naji dadi danaji yayan mu na fadin da yaran Khadija zata tafi suje can suyi hutu a gurin ta haka ya nuna ita mai son muce mai kuma kaunar mu.
Don ance wanda duk yaso yayan ka ya gama son ka a duniya koda kuwa ya nuna kai bai kaunar ka balle gashi yanzu mun gani rabon kayan nan ki duba fa bata yarda an taba komai ba sai da taje ta kira ki dakin ki kizo aka fara.
Sanan kuma muma gare mu abin farin ciki ne ace yau gamu gamu gidan dan uwan mu muna raba abin arzikin da ya fito a hannun shi may yafi wanan farin cikin a ran mu sauran sukace babu wallahi.
Mu dai fatan mu yanzu ku hada kai sosai ku jawo muna hankalin dan uwan mu ya dawo jikin shi ko kwata muna shi daga kaidin wanan shedaniyar matar tashi.
Anty Fati tai wani murmushi tace kayyah anty wanan wazai iya da ita a cikin mu kike gani kun fasan duk ta girmay muna a shekaru ba kusa ba.
Zainab tace bari fadin haka mana Anty Fati ita tayi kamar Allah ne ga Allah duk damu daku za,a dukufa wurin kai kuka mu ga Allah.
Ai tunda har khadija takai haka a gidan nan tare da Nafisa alama ya nuna hakan Allah yana karban adduan mu.
Yanzu dai mu hadin kan ku muke fatan don kada kuma kawunan ku ku yazo bai hadu ba abin yafi nan lalacewa kuma.
Nan dai sukai ta magana wanda yawan maganan duk akan anty fati yafi yawa don inda take da sakaci duk basu boye mata ba a gurin ranan.
Karfe uku daidai suka bar gidan zuwa cikin gidan su nace zamu shigo da anty Fati idan mun shirya da ga baya.
Fitan su gidan yai daidai da dawowan su AA da Yusuf bayan mun tare su ne na shige daki na shirya ban fito ba sai da nayi sallah la,asar na fito na samay su a falon har lokacin bata shirya ba.
Nace anty lokaci yana gabatowa fa shima Yusuf din mikewa yayi yana fadin zai je ya shirya motan da zasuyi amfani dashi ya bar gidan .
Falon ya rage daga ni sai shi a zaune ina jiran ta tashiga yace dani zo nan Deedar hanya hawa saman na kalla inda tabi sai na mike na isa gurin shi din.
Jawo ni yayi zuwa jikin shi tare da fadin wanan kwalliyan yai maki kyau sosai na gode nace ina kokarin dagawa saman jikin shi din.
Ji nayi ya kara riko ni da kyau ya kokarin kai min kiss nace kaima Allah ya AA ka bari kada anty ta fito ta samay mu a haka kasan ranta ba zaiyi dadi ba fa.
Yace and so what idan ta samay mu a haka budurwa taga na rungumay ko farkana nace koma dai may don Allah ka daina don ba dadi irin hakan aiwa mutum sake ni yayi yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin yau dai kin san ke ce da girki ko ?
Da sauri nace dashi girkin may kuma ana zaune kalau may zai sa in yi girki anan bayan ba lokacin mu bane kada ki kawo min wanan zancen anan don ba a kanki aka fara haka ba.
Nace ni kaina na sani ai abinda banso kuma bazan ma wani ba bai kara kulani ba tunda na fadi haka sai ya share ni ya mike zuwa sallah.
Fitowa tayi muka fice daga gidan mun samu yan uwan haihuwan su kaf sun zo a lokacin muna shiga suka hau yi wa fati sheri kamar yadda dangin miji kanyi wa uwar gida wani lokaci.
Part din hajiya Umma aka gyara don taron bakin masu kawo kaya muna dakin mommy zaune na mukaji shigowan su gidan .
Ba bada wani yawa suka zo ba su shidda ne kawai an tare su a cikin mutunci suka gabatar da kayan ga manya akai masu godiya suka bada kudin dinki dubu dari biyu tare da fadin suna so jin lokacin buki.
Daga inda nake nayi murmushi naji hajiya Umma tace wanan maganar maza ne idan an shirya za a sanar dasu lokacin nan dai aka gabatar masu da drinks da su snack da kajin da aka soya don su tare da basu tukwaicin alherin da suka zo dashi aka rabu lafiya da kowa a wurin.
Yan gida suka shiga duba kayan suna yaba kyaushi da yawan shi suna sa albarka tare da fadin abu yayi kyau wallahi.
Dakin hajiya mama na shige na samu zainab ita kadai na fara mata guda akai tare da fadin amaryam mu na gobe ta dan hararane tare da samun wuri na zauna a kusa da ita.
Ta kalle ni tace ai amaren suna da yawa khadija don ya ce ba ni kadai zai aura ba wai kina nufin wanan maganan da yake da gaske har ke ya fadama shi.
Tace a kasale cikin wani murya haka yake fada min wai kuma ke kin san ko wace matar kuma kin san halinta don haka in kwantar da hankalina.
Gabana ne ya fadi nace a fili ni ni din nan nasanta yace maki tace kwarai kuwa da sauri nace wallahi haram idan bashi bane da sai ince yai min sheri don ya hada ni dake yace hakan.
Murmushi tayi tace indon nice fa khadija kada ki damu da wanan don nima kamarki ce auren biyayya mukeyi wanda muke fatan muga riban hakan.
Don haka wallahi kadama ki damu khadija kin san dai ni ba zan taba fadawa wani wanan maganan ba idan bashi ya fadi ba akaji.
Jikina ne yayi sanyi don ta kawar da hiran sai ce min tayi kinga ni yanzu ba wanan ba wani shiri kika tsara akan bukin kafin lokaci yayi.
Ajiyan zuciya na sauke nace Allah dai ya kaimu lokacin lafiya don shine mai wuya tace ai shine fa shigowan Binta dakin yasa mukai shiru a lokacin don ta shigo tana yaba kyau kayan da aka kawo.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENAB
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Sai daga baya ne bayan mun dawo gida na lura da AA yana fushi dani kan maganar da mukayi na girki ina gama cin abincin da na girka na shige daki tare da kargamay kofana.
Da safe shiya tayar dani daga barci wai a ranan zamu koma Abuja bance komai ba illa gaida shi da nayi da kwana har yakai kofa nace ina son shiga gun yaya Amina kafin mu tafi.
A,a yace min ya fita kawai dakin wani irin bakin ciki naji a raina kan hananin da yayi dole sai a waya na kirata mukai maganan da zamuyi.
Muna a falon hajiya mama zaune a gaban ta yana gurin Abbasu suna magana dashi mama tace dani ya kuma banga kun fito da yaran ba nace ban san may ya hana ashirya su ba.
Ta dauki waya takira anty fati tare da fada mata cewa ta shiryo yara yanzun da laraba ta turo su gidan ta ina son ganin laraba yanzu.
Labara suka shigo tare da yaran tace ina ita fatin take binta maza kira min ita ai maganan ya shafe ta yanzu.
Fatin suka shigo tare da Binta suka gaisa tace dani ashe baku tafi ba har yanzu nace eh yana tare da Abba ne.
Hajiya mama tace dama kiran ki nayi in fada maki cewa yaran nan yanzu dasu khadija zata wuce suje can suyi mata hutu a can idan hutu ya kare su dawo.