ki yana da kyau don ka zauna da mutum tsakani da Allah kuma ka fada mashi gaskiya a idan yake da gyara ai shine kyau.
Muna a gurin muna zancen maryam ta shigo sun gaisa da mama ta juyo gare ni tana fadin ke uwar biyu zaki ko iya fita anty Salbiya ta neman mu fa yanzu mukai waya da ita.
Nace yau din nan banjin fita ta tace naga alama yadda kika zauna turus din dake kamar wanda ta kumsa cikin diya goma wallahi cikin nan kamar kada a bayana shi naga ya kara maki wani bunkasa yanzu.
Duk kin wani koma jagwal yanzu gaba daya nace ai ko biyu na haifa da a gidan zaki tare tace zancen kike so lokacin kika sani ko ina gidan nawa mijin nima ?
Nace Allah dai ya nuna muna ranan wanan auren da aka ta fata kuma ni banga ana da niyar yin shi ba a zahiri.
Ke wallahi ni yanzu tsoron maza nake yi anshani farko banji dadin su ba ina zan yarda su kara shana.
Dariya nayi ina mikewa nace aure kuma dole yarinya tayi ba don ko ba fashi a gare ta tace haka dai antyn ki ke ce min.
Daki na shiga sai dana watsa ruwa a jikina na shirya na fito mukai ma mama sallama muka nufi gidan anty Salbiya din.
Mun samu tana falo muka shiga ta tare mu da murna ta fadin khadija kin yi wuyan gani a garin nan komai yayi daidai ke nan dai da alama.
Zama nayi ina fadin wanan shu,umar ai halin ta sai ita anty yanzun haka ba su kasan nan daga ita har mijin sun na indiya sun kai yar su da bata da lafiya nan dai nake fada mata abindake faruwa.
Ta tausayawa yarinyar sosai tayi mata adduan samun lafiya tace dama irin masu bakar asirin nan ai haka ke faruwa dasu sosai amma sai kiga kamar ana bushe masu zuciya ne.
Yanzu dai ai ba zancen biye biye tana fama da yar ta nace Allah yasa ni tunda suka tafi wlh hakalina ba akwace yake ba da ita don da zaran na kwanta ita nake ganin taza min a wani irin yanayi da ba dadi fassarawa.
Nace yanzu ko sunan ta aka kira wlh gaba sai yai mugun faduwa tun rikicen gida da mukayi da yan uwanta anty Salbiya tace dani.
Kina ko ibadan ki yadda ya dace don kin san irin yanayin nan da kike ciki yana sa mace raggata yin ibada sosai sai kin kara jajircewa.
San nan yanzun haka kiran nan danayi maku an turo min da kaya da na ba da sako ne kasar mu ke ce farkon fado min a raina wlh barin dauko maki ku gani don Allah kada ki wasa da amfani dasu don tunda kike yawan wanan mafalkin da ita dole akwai abinda take shiryawa ne a kan ki.
Kema nasan kina da farfarun mabiyane dake sanar dake suke baki kariya daga sherin nata shiyasa kike ganin wasu abubuwan a cikin mafalki haka.
Mikewa tayi zuwa dakin nata sai gata dauke da wani katon jaka dake da rubutun arbiya a jikin shi tazo ta aje a gaban ta mudai muna kallon ta ta fara fitar wa daga cikin jakkar nata tare da fara muna bayanin shi.
Tamiko tana fadin wanan da kike gani aikin sa shine koda ace irin yadda mijin nan naki yake da mata da yawa ne idan kina matsa wanan din a jikin zai ji koda yaje gurin wata matar tai mai dandano na daban.
Hakama idan namiji yana da yawan neman mata insha Allah zai dogara gake matar shi ta gida da yardan Allah don duk inda yaje sai yaji dandanon bai gamshe shi ba sai ya dawo gurin ki.
Ta kara dauko wani tace wanan sabulune na hadi da akayi na gargajiya bake ba ko yaran da zaki haifa idan kika malaki wanan kuna amfani dashi zai maku aiki sosai matuka gaya.
Ko yau kika haifi yar ki ko yaron ki kina gudun irin wani abu na sihiri ya shafe shi zaki iya lakata dan kadan a wanke al,auran yaro dashi haka ma ke ma fa dan kadan zaki diba amma kada ki amfani da wanan a yanzu don yanayin cikin dake tare da ke baida wani chemical a cikin sa kayan gargajiyane masu karfi aka hada dashi.
Yana da kwai sosai matukar kina amfani dashi ko da kishi tana jifar ki da sihiri ne da yardan Allah bazai yi tasiri akan ki ba.
Ta kara dauko wani tace ga wanan kuma poweder ne kamar irin da ake fadar aljani ya shafe ka ko kuma wani sihiri haka zaki iya amfani da wanan din wurin karya shi musanman ke mai kishiyoyi hakan nan zaki iya amfani dashi ki shafa a hammatarki da wuya da sauran gurare na jikin ki haka da yardan Allah zaki ga na miji yana bin ki sau da kafa da sauran su.
Wanan kuma da kifi ake cin sa mallaka ne sosai sahihi idan kikai amfani dashi sau uku zaki raba shi zaki iya yin miyar kifi ko soyayyen ki ki dan barbada a sama wallahi yana da kyau da amfani sosai don mutum zai dinga jin shakkan ka da kuma baya iya ketera maganar ka ko diyan zaman nan ke gare ki zaki ya masu amfani dashi bazasu iya ketare maganar ki ba.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin ni ya su a raina yanzu dole aure ya koma sai da irin wanan abin idan kana son zaman lafiya da maigida ke nan.
Ta miko wani tana fadin wanan turaren wuta ne shi ake kira da turaren sakata zaki dan zuba a kaskon garwa shi kizo karkashin gadon da kuke kwana ki aje sai turaren yabi ko ina ya dauka.
Zaki cire abin hayakin a wurin hmmm idan kina amfani da wanan a hankali a hankali in Allah yayi duniya don manzon sa sai an wayi gari yaji ba wata mace a ransa saike.
Shiya bamu son ba mai kishiya wanan din amma ke ya zama dole mu baki shi don wanan shu,umar sai da hakan gare ki don ke ma baki san iya sherin da take maki ba ai.
Ta aje ta dauko wani tana fadin kinga wanan kuma shi muke kira da dan lalai idan zaki kumshi zaki dan zuba kadan a ciki ki kwaba ki kumsa idan kiyi yana jawo yawan alheri gun namiji sosai zuwa ga matar shi.
Wanan kuma turare ne ana kiran sa dan mara zaki shafa ga maranki da goshin ki yana da matukar amfani sosai yana saka dandanon jima,i sosai tsakanin miji da matar shi.
Wanan matan da suka san kan su sosai suke amfani dashi ko a kasan mu saboda yana da wuyar samu sosai kin ganshi nan.
Sai hummara da zan baki da turare da powder da kwali na fari jini both yan mata da matan aure zasu iya amfani dashi don saka kwarjini a idon jama, a so kinga idan har kin daure kinyi amfani da wanan zamu zubawa sarautar Allah ido mu gani Allah yasa mu dace ya kare mu daga miyagun kadarori.
Muka amsa da amin ta fada min kidin su naji shi a sawake don na tabbatar ita Nafisa Allah kadai yasan irin makuden kudin da take zubawa a kaina don dai kawai in bar gida.
Tace akwai addu,oi da zan baki wanda zaki tsare sosai ki dage a gurin yin su shi addua kin san shine gaba da komai wa yan nan munayin su don Allah yace tashi in taimake ka.
Idan gari ya waye kafin ki ci komai zaki komai kuma kafin ki magana da wani zaki dinga karanta li,ilafi kafa tara ko wace da bissimillah ki nayi kina tofa a tafin hannun ki.
Da kin kammala sai ki shafe jikin ki daga kai zuwa har tafin kafan ki da yarda Allah idan kika juri yin haka sai ubangiji ya fifita ki kan makiya ya kuma sanya masu tsoron ki a zukatan su.
Ina fatan kin yi karatun arabic sai maryam tace malamace wurin nan ai anty don na gani da mukaje garin su bukin ta abin har mamaki ya bani.
Tace to masha Allahu to lazimci karanta tabara kulun idan zaki kwanta don yana daga darajan mace a vikin kishiyoyin ta.
Komai aka nufike dashi zai koma akan maishi da yarda Allah ko a makaranta ko wurin aiki duk yana da amfani ga mutum ya dinga yin sa idan kika daure kina wanan abinda na fada maki dayardan Allah duk wani sheri zai koma kantane.
Nayi mata godiya sosai tare da bata kudi duk da nasan nadai bata sune ba wai kudin kayan bane don ma batayi niyar amsa ba sai da nace tasai wa yara abin sallah ta karba.
Maryam ne har mun daga tace wanan jirgin dankaro Allah yasa tai amfani da su ko tayi abinda kika ce din yanzu duk ta sukurkuce ga baki daya wallahi.
Nan Anty Salbiya tace haba kamar fa kina abakin kura ne da wanan kishiyar taki ko bakin rami ko ta turaki ko ki turata haka abin yake yanzu gidaje da yawa wallahi ko da baka da kishiya ma.
Wata tana waje tana maka hassada da bakin cikin zaman da kake yi da mijin ka akace ko kana da kyau ka kara da wanka.
Idan ita tana shirka tana kaucewa mahaliccin mu ke a saukake zaki kama mijin ki kuma kauce wa kai,din ta da yarda Allah don Allah ki kula ki yi amfani dashi kamar yadda nayi maki bayanin komai.
Ai yanzune daidai kiyi su don bata gidan kinga kafin ta dawo duk abin ya fara zama jikin ki insha Allahu.
Gidan anty hauwa naje na gaida ita don nasan da wuya in kara fitowa a yadda nakejin kai na kafin sallah kuma nan na samu sakon ya iso na kwaso wanda kayan yara ne sai nawa da na su mommy mamana da su ya Amina da hajiya dana saya masu.
Ko da na dawo gida sai naji zancen ta ya tsaya min a rai gama yadda ta hada ni da Allah in amfani da abinda ta ban yau din dama wa yan can na farkon.
Bayan nayi sallah na zauna in lakaci wancen in shafa in goga wanan na fito falo na samu laraba ta dora girki abinda zasuyi buda baki dashi.
Na fito zuwa kitchen din wurin ta a nan na tsaya muna hira da ita ina dan tayata gyara ganyen da naga ta fitar zatai amfani dashi.
Kusan a tare mukai aikin da ita muka gama na shiga sallah la,asar ne naji shigowan ihisan part din nan na fito na samay su da yan uwanta suna wasa nace ta kira min samira yar ta yarinyar ta fice da gudu zuwa kiran Samira din.
Sai gasu sun dawo a tare nan na bude kayan sallah su da na sayo masu amma fa da kudin miji na bawa ko wace nata har na su yanyala nace takai masu.
Abin mamaki bai karewa ina zaton ba zasu karba sai gasu har part dina sun zo min godiya nace ba komai suka fita anan suka bar samira da ihisan a wurina suna kara duba kayan su din.
Anty da maman mu tana garin nan ba zata bari mu karbi kayan nan ba ko su yanyala sun fada yanzu da na kai masu nasu sunce kada mu bari maman mu taji doin idan ta sani zatace a mayar da kayan ni kuma wallahi ina son abina don bazata saya muna irin wanan ba na sani.
Nace idan tace kada kusa sai ku dawo min da abina ina da wa yanda zabawa su saka tace nima ina son abina wallahi.
Abinci laraba ta debowa yaran zasu suci sai samira tace itama zataci nace haba samira babba dake baki koyon azumi har yanzu tace aiko su samiha basu azumi wai basu isa yi ba sai sun haihu biyar zasu fara azumi.
Abinda ko maman mu bata kanyi tace bata isa fara azumi ba sai ta yi haihuwa biyar ko fiya da haka zata fara.
Innalillahi nai ta maimaitawa har yarinyar ta rude tace ko sallah fa sai da malamin mu na islamiya ya koya mun ne nake koyawa maman mu dasu samiha suma basu sallah.
Gabana ne ya fadi a raina nace ashe dole abin yaiwa Nafisa yawa don babu kusanci tsakanin ta da Allah har yanzu.
Mamakin mijin mi ne ya kamani a raina nace yanzu yaya yake zama haka da mutanen da basu sallah a gida nai tsoron Allah ya tambaye shi wanan abin gobe kiya yaya irin macen nan zatayiwa yayan ka tarbiya mai kyau a haka ?
Ranan dai da wanan damuwan na kwana a raina har dare ina kara nanata maganan ga mama laraba tace ai haka suke har mazan su idan kinga namiji ya fara sallah wai sai ya aske gashin kansa nan na kitson su ya fita samar taka ke nan imani ya fara zuwa mai.
Ikon Allah ni kuma nan Allah ya kawo ni idan baka mutu ba baga gama ganin duniya ba ashe tsoron al,amarin naji a raina sosai ranan nayi nadaman kasancewa na da su a gida daya.
Bayan kwana biyu sallah saura kwana biyar muna zaune da dare falo sai ganin mutum mukayi kamar anjefo shi ina kwance a kasa a wurin da nayi sallah naga shigowar shi sai da naji gabana ya fadi.
Don ban sa zasu dawo a wanan lkacin ba tunda sunce an wa yarinyar aiki ne na dauka sai bayan sallah kamar da sati biyu zasu dawo sai gasu.
Addu,oin tsara naja daga inda nake kwance din ina mikewa zaune da kyat yara na mashi sannu da zuwa da laraba.
Har inda nake ya karaso ya zo ya tsugun na daidai saitin fuskana tare da fadin ya akayi ne nagan ki haka har yanzu kina azumin ke nan baki hutawa ko ?
Nace tafiya irin haka babu sanarwa kuma sai kuyiwa mutane girshi yace hakan nake tafiyana ba sai wani ya sani ba ko Yusuf yanzu na kirashi suzo su dauko mu a airport shima korafin da yake min ke nan.
Nace dole yai maka korafi ai sannun ku da zuwa ya hanya ya kuma mai jikin ina kallon fuskan shi inji may zai fada don a zatona ko yarinyar ta rasu ne ma.
Yace lafiya kalau take ta samu sauki sosai shima kan yana dan ragewa don sun bada maganin da za, a rika mata amfani dashi idan munzo nan sunce kan zai rage girma.
Ya mike tsaye yana fadin barin dan watsa ruwa ko zan rage jin wanan gajiyan dana debo na hanya mikewa nayi bayan fitar shi na mara mai baya.
Na samay shi a falon bai shiga part din nashi ba yana fadan don may aka kai mai kaya part din Nafisa a dauko mai kayan shi.
Nidai na wuce shi nan na nufi saman yana a rufe har lokacin na bude da key din wurina dakin yana a gyara sai kamshin turaren dana bude dakin dashi ke tashi ciki.
Bandakin na shiga na hada mai ruwan wanka na fito na samu suna shigo da kyan dake daure kamar na mahajjata yadda aka daure su.
Ga ruwa na na hada sai dai yau mama tuwo ta girka masu wai shi suke son ci mai za a dafa ma yanzu kaci ?
Yace tuwon ma ai is ok zanci ai in akwaishi don ya zama abin marmari a gare ni yanzu da wancan cimar nasu da na baro yanzu kai wanka kafin ka fito na hada ma abincin.
Na barshi ya fara cire kayan jikin shi na fita daga dakin zuwa hada mashi abinci lokacin an gama shigo da kayan ban ko kali inda kayan suke ba na fice.
Sai da na dan jima a part dina don mun tsaya hada mai da dan abu mara nauyi da zai sha muka gama na shiga na gyara kaina na nufi part din.
Ina shiga na rufo kofan na samay shi zaune da waya a hannun shi yanayi na jera komai a inda ya dace a jera din na samay shi ija fada mai na hada abincin ko.
Ina zaune gefen sai da ya gama baiyi magana ba har ya kare na hada kayan na samay shi a dakin guri na samu nakai kwance don tunda ya dawo amsa waya yake yi har lokacin.
Acikin wayan da yake yin din ne na fahinci dawowan baram baram sukayi da Nafisa din don yana fadin ace mutum baisan ciwon kansa ba kamar ba itace ta haifi yar da cikin ta take cikin wanan lalurar.
Bansan Nafisa tayi nisa haka ba sai wanan karon wai zaka yarda har gurin boka taje a india wai ya duba mata ya akayi ta haifi yar haka ?
Wani iri naji a raina daga inda nake kwance yace wallahi alamarin nafisa ya fara fita min rai don bata san Allah ba sam a rayuwan ta in dai taje boka ta iya bi ai tajiyo makanta matsala a can daya tada mata da hankali banji may wanda suke wayan ba yace sai dai shi danaji yace.
Ni ina zan yarda da wanan shirkan da shashanci iri nasu na mata wa take zargi yanzu tace ya hurhura