zuciyar shi a cunkushe.
Ban falkaba sai asuba karan agogon dakin ya ta dani duban lokaci nayi tare da saukowa saman gadon na nufi bathroom din daki.
Alwala nayi bayan tsarkin da nayi na fito na tayar da sallah ban kara kwantawa ba kitchen na fada don ina son in dan dafa wani abu in rika wanda zanci don jiya nasha wahala sosai a school din.
Saida na gama hada abincin ne na shiga wanka tare da zuba wanda zan dan karya dashi kafin in fita yau tafa na sa a jikina zani da riga da yake zamay min wahalan idan na daura amma haka nake koyon sabawa da daura zani yanzu.
Falon na dawo a cikin shirina na zauna cin abincin ban jima da zaunawa sai gashi ya shigo dakin dago kai nayi na kalle shi na kawar da kaina naci gaba da cin abincin da nakeci.
Sai da yazo gab dani na ce dashi ina kwana bai amsa ba sai da yakai zaune ya amsa da lafiya maimakon in ci gaba da cin abincin sai na koma wasa da cibin.
Amsan cibin yayi daga hannu ya debi abincin yakai bakin shi tambayan daya jeho min ne yasani dago kai in kalle shi.
Yanzun kika dafa abincin ko may da eh na bashi amsa kawai ina nawa abincin yake ya tambaya cikin tsure ni da ido .
Nace ban dauka zakaci ba nawa kawai na dafa na bashi amsa yace saboda may koni ba zanci abincin bane naji ya fada.
Nace na dauka a asibiti zakaci naka ai daga haka na mike na shige ciki na barshi a wurin bin bayana yayi da kallo yana murmushi.
Koda na fito a ciki shirina na samu ya cinye abincin gaba daya dana bari kujeran dake gefe na samu na zauna akai ba tare da nayi magana ba.
May yasa jiya kika fita baki kirani ba kuma waya sauke ki school din da kika tafi nace ban san amsan da zan bashi ba don haushi sai nayi shiru.
Yace tambayan ki nakeyi kin kyale nace yan uwan matarka da zasu fita na roka su sauke tare dasu muka fita yace OK da izzinin wa kuma kika bisu ?
Amma kasan ina karatun ko da ka aure ni ko yanzun ne kuma zaka ce baka san ina fita zuwa makaranta ba din.
To yau ki zauna babu inda zaki daga haka ya mike ya bar falon binshi nayi da kallon mamaki ban samu magana ba.
Kofa na mike na rufe bayan fitan shi na koma uwar daki na cire gyale tare da aje jakkana na haye gadona ina tunane a raina.
Ba komai nake tunane ba sai hanani fita da yayi don ban san ko may yake nufi da hakan da yai min din ba.
Waya na dauko na kira maryam kafin ta shiga class ina fada mata abinda ke faruwa tace dani kyale shi sa mai ido zanje department din ku in masu complain baki da lafiya .
Amma maryam saboda may zai hanani tsabgar gaba bayan yasan ina karatu ya aure na hakana tace kiyi hakkuri.
Gwada ki yakeyi ko zaki fita ko ba zaki fita ba din ya samu bakin magana idan kin fita kin ga gara da kika kyaleshi ya fita baki magana ba yasan wa yake aure.
Idan mun fito da yamma zan leko ki sai mukarasa maganan nace to nagode na kashe wayan.
Barci ne ya dauke ni a wurin da nake da tsakiyan tunanen sabon rayuwan da nake fuskan ta din a gidan.
Saida ya gama abinda zaiyi ya fito zuwa asibiti kallon part dina yayi ya ganshi a rufe ranshi ne ya baci ya nasa watau fita nayi da ya hana fitan.
Har yaje asibiti ya duba su da kwana nafisa sai korafi take mai yaki zuwa da sassafe ya dubata sai yanzu na barshi yazo ganin ta .
Yana zaune office rai bace yana tunanen iri hukuncin da zai yanke min ji yake kamar ya hana karatun gaba daya yaga tsiya ko bai hanani ba sai ya bata min rai kamar yadda na bata mai.
Zai nuna min a karkashinshi nake a yanzu ba karkashin wani ba yana wanan halin ne Yusuf ya shigo office din ya samay shi a haka.
Sun gaisa ne ya kalli yanayin shi yaga bai a cikin dadin rai yake tambayan shi ko jikin nafisa din ne ya tsanan ta haka.
Kai ya girgiza mai yana fadin taji sauki sosai dani da Deedar ne wanan karon ban san may yarinyar nan ta dauke ni ba .
Wani abu ya faru ne yace zai dai faru don zan saba mata sosai wallah har zance mata kada tayi abu tayi shi.
Yusuf yace ita khadija da kanta ko dai bata fahince ka bane don banyi tsamanin zatayi haka ba gaskiya yace OK karya ke nan nake maka.
Jiya na dawo na samu ta rufe kofa bata aje min abinci ba naje kofanta a rufe da safe kuma again wai bata girka dani ba ta dauka a asibiti zanci ina mata magana kuma tashige daki ta barni a zaune.
Sai gashi ta fito wai school zata nace ba zata tafi ba shine ina fita daga dakin ta fita bansan may yasa take son cudanya da maza suna daukan ta a mota ba ta san kuma ban son haka.
Hannu yusuf ya daga mashi yana fadin kai malam gyara zancen ka don Allah kada wani yaji ya dauka wani harkan banza take yi na daban.
Har wasu maza suka dauke ta ba dai driver gidan ka bane kokai kuma kana bada wanan go ahead din.
Kenan su ba maza bane ya tambayi yusuf din cikin bacin rai yace jiya kayi ta kanta ne ko ka bugo mata waya gaka nan tafe kakai ta daba zata bi wasu ba.
Yanzun ma da kake wanan magana ka tabbatar da bata gidan tana makaranta ko a gaban idon ka kags fitan ta yace dashi a hasale nasan fita tayi tunda na samu part din ta a rufe.
Waya Yusuf ya ciro daga aljihun shi ya kira layina a cikin barci naji kiran na dauka da sallama bayan mun gaisa ne yace .
Kanwata kina ina yanzu don Allah nace ina gida yayana yace yau ban fita school ban san may yake nufi da hakan ba gashi yanzu lokacin tsananin karatun mu yake.
Yace ok zan mashi magana ya barki kiji yanzu zai zo ya dauke ki nace No ka barshi kawai yayana na riga na makara yau.
Na kare da fadin wani abune ka kirani dama yace amma barshi kawai na dauka kin fitane in baki sako wurin maryam.
Dan murmushi nayi nace kai yayana kada ku sani tsaka fa ga sister inlaw kuma ga friend yaya kuke son in yi da raina yace haka shine karin zumunci ai na kashe waya ina dariya.
Kallon AA din yayi cikin zafin rai yana fadin kada ku cutawa yar mutane kai mata wasu suyi maka jiya a gaban ka yarinyar nan tabar karatunta taje gaida matar ka sukaci mata mutunci a gaban ka bakai komai ba.
Yanzu kuma ka nemo wani fitina kana kokarin haddasa fitina a tsakanin ku tun bata iya yiba kazo ka koya mata maka mussu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Darajan Allah da Annabinsa ya fi komai nauyi ga musulmi koda yaro karami ne yasan darajan wanan kallaman mai muhinmanci ga musulmi ko kafiri yasan daraja da nauyin wanan kalman.
Balle dan musulmi baligi ko baliga har yanzu ba zan gaji da daure ku agun Allah ba da wanan kalman don darajan Allah da annabinsa kada ki fitar min idan ma an fitar yar uwa musulma kada ki karan ta idan baki biya ba don darajan Allah da Annabisa musulman kwarai ce kadai zata fahinci hakan
Idan kuma kin nace da karanta hakkin wani Allah yasan tsakannin ki dashi akan haka don na sauke nayina na fada na kara fada don darajan Allah kada ki karanta hakkina idan baki biya.
Inagama daukan wayan Yusuf kiran ya Amina yana shigo min mun gaisa na tambayi yara ita ta tambaye ni muna lafiya dai?
Nace lafiya muke anty tace jiya ta shiga cikin
gidan su mommy ake fada mata cewa Nafisa bata da lafiya an kwakaina da ita asibiti.
Nace eh hakane anty an bata bedrest a asibiti yau
kwanan ta biyu a can tace da nace idan su mommy zasu zo zan biyo su inzo in gaida ita.
Da sauri nace No kada kizo ya Amina ban son kowa nawa yazo gaida wanan matar don gudun matsala.
Haba khadija daga gaisuwa kuma sai matsala ina laifin wanda yazo gaishe ka ai komai abinta ba zata ce sheri ya kawo ni ba ko ?
Naga yin haka kamar sayen mutuncin ki ne a gurin su ita da mijin ta nace ya Amina na fada maki kada kizo don Allah don ba irin wanan matar akewa haka ba gaskiya.
Idan ita bata gani ba ai
mijin ya san don shi aka zo ko nace harshi din anty halin su daya don ko a gaban shi sai ta ci maki mutunci ba abinda zai yi don haka kawai ki zauna.
Tace kina ganin hakan zaifi nace kwarai kuwa ina hawaye duk da ba ganina take yi ba amma zuciyar ta ya bata ban cikin dadin rai.
Khadija hakkuri zaki aure ya gaji haka don dan kalubali ne aure wata rana ka wayi gari a cikin dadin rai watarana akasin hakan.
Koda kuwa baka da kishi balle ke mai kishiyoyi da yawa don haka sai kin hada da hakkuri da addua kina yawaita kai kukan ki ga Allah.
Sai komai yazo maki da sauki a cikin alamuran ki don Allah yana tare da masu hakkuri da yaiwata ibada a gare shi.
Hawayen dake fuskana na goge tare fadin bakomai ya na gode kudin da na turo sun kare na sadaka ko in turo wasu tace da saura a hannu na sosai kullun ana maki sadaka dashi.
Maryam ta tambayeni nace yau bamu hadu ba don ban shiga school ba tace lafiya nan shiga ba nace banda lectures ne yau na tsaya in hutane.
Dan nasiha kamar kullun tai min tare da kara min karfin gwiwa a zaman takewan rayuwan aure nayi mata godiya tare da kashe wayan mukai sallama da juna.
Kwallan dake fuskana na share tare da gyara kwaciyana ina tunanen yanzu may ye matsalana ko laifina a hakan da yai min .
Ni da ya wullakanta akan matar shi ya manta dani banyi fushi ba sai shine mai daukan mataki a kaina wani abu sai ko aure yakai haka ga mutum.
Kayan jikina na tashi na sauya tunda ba fita zanyi ba kuma ni kadaice a gidan wando da yar riga armless sai kaina da na daure da ribon ko dan kwali ban aza a kan nawa ba.
Falo na dawo bayan nayi sallah azahar na dauko cake da drinks na aje a gabana na kunna tv ina kallo ina kora drinks din a hankali.
Motsin da naji kamar wani zai shigo part din yasani dago ido ina kallon kofan jin an kara murda kofan yasa na mike na nufi kofan tare da cire key a kofan .
Gardawan samarin nan ne buzayen gidan suke shigowa da kayan masarufi zuwa kitchen dina da sauri na koma daga kuryan dakin na zauna harsu bar part din.
Sai da naji na daina jin motsin su na fito na zauna a inda nake ba tare da na kara rufe kofan ba ban kuma je na duba abinda suka shigo dashi din ba.
Sai dai ina tunane a raina ina dadin wanan kayan da ake jibga min babu kwanciyar hankali a tare da zuciya na ko kadan.
Shi ya shigo da sallaman shi a dakin daidai lokacin da na dauki kwalin drinks ina korawa a bakina yana sabale da corth din shi a kafadan shi, sallaman na karba mai tare da kawar da kaina daga kallon shi.
Shima ni din ya tsurawa ido yana kokarin samun wuri yakai zaune don daga ganin shi a gajiye yake a lokacin muryan shi naji yana fadin dauko min drinks mai sanyi in kora.
Ba tare da nai magana ba na mike zuwa kitchen din anan na samu kayan da masu karfin nan suka shigo min dashi a tsakar kitchen din nawa.
Bin kayan nayi da kallo na wuce zuwa wurin fridge na dauko kwanlin five alive da kofi na nufo falon dashi a hannu na.
Gaban shi nazo na dire da zan dago na rusunna irin al,adan mutanen Niger din nan ko mai zakayiwa na gaba da kai sai ka dan bashi girman shi duk da addini ya rage wani abu da wayewan kai kuma.
Wanan dabi,an kowa ya san mutanen Niger da irin sa wurin ba na gaba girma da girmamawa ba su da wari a gurin nan .
Kanshi a sama dage ya furta thanks tare da sauke kanshi hannu na naji ya kamo zuwa baya na fada a jikin shi.
Kokaein kwacewa nake ga jikin nasa yaki bari na kurce mai ji nayi yace kamar mai rada fushi kike dani don na hanaki fita yau ko mai ?
Akan may zan yi fushi tunda a karkashin ka nake kace ba zan fita ba ai dole in zauna fushi na may zanyi tunda nasan yau baka ra,ayin fitan nawa ne.
Kaina ya tallabo ya hada da goshin yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin kin dai huce daga fushin naki.
Kokarin mikewa nakeyi tare da fadin wani yace dakai ina fushi dakai dama ni dai naga hakan don ko abin sha sai dana roka yanzu a wurin ki.
Dama ina da niyar dauko maka idan ka bukata kuma ka bukata na dauko ma salin alim shine kuma abin fushi din.
Yanzun dai ba wanan ba zowa nayi inji idan akwai wani abin amfani da ba,a sawo maki ba wanan watan sai ki fada min a sayo yanzu.
Komai akwai na gode nace yaushe kika duba kayan da kike min godiya a kan su nace ko ban duba ba nasan zaka sayo muna komai na bukata ai.
Kwalin juice din ya dauka tare da balle marfin kwalin ya kafa a bakin shi ya fara sha hakana bada cup ba sai da yasha kusan rabi ya aje kwalin ya mike tsaye yana fadin zan koma asibiti in duba su idan na bar nan kafin in isa office Allah ya sauwaka nace ina kokarin dauke kayan da suke falon.
Zuwan maryam ranan yasa na basar da komai dake raina don hiran mu da ita yasa na manta da duk wani damuwa na.
Tana gidan har sai da tayi sallah isha,i ta bar gidan nayi nayi ta kwana tace zamu dai hadu gobe insha Allahu.
Bai dawo gidan ba sai sha daya Nafisa ta barshi ya dawo gida lokacin har nayi barci a dakina don banji motsin shi ba na dauka a can yake kwana.
Wayana ya kira sai da yai min call biyu na falka daga barcin da nayi nisa ga yin shi bude min kofa ya fada bayan na dauki wayan.
Nataso da sauran barci a idona na bude mai kofan dakin ya shigo shima da ganin shi a gajiye yake a lokacin.
Sai dai yayi wanka don alama ya nuna hakan saboda ya sauya kayan jikin shi zuwa dogon riga sabanin yadda ya fita gida da rana.
Abinci fa ko baki aje min ba kitchen din na nufa na dauko mai abincin nakawo tare da fadin sama zan kai ma ko nan zakaci ?
Aje min in ci nan ya bani amsa hankalin shi yana ga wayan shi saida na gama jera mai komai nace na hada ya dago yana kallo na tare da fadin kin rufe kofan nan ?
Kallon shi nayi da mamaki nace na dauka yanzun zaka fita yace yana nuna kofan rufe kawai na tashi ina mamaki a raina tare da rufo kofan.
Mikewa yayi ya nufi dan table din mai kujeran mutum biya ya zauna zuwa nayi na fara zuba mai abincin nagama nakoma dayan kujeran na zauna tare da harde hannaye na ina kallon shi.
Abincin har lokacin da zafin shi sosai tuwo na tuka mashi na farar shimkafa da miyar kuka da naman rago nayi amfani da kayan yaji sai man shanu dana zuba a sama.
Tunda ya fara cin abincin baiyi magana ba har ya kare na mike ina tattara kayan don idona cike yake da barci a lokacin.
Bayan na kawar da kayan ne na dawo falo da zumar zama naga ya mike ya shiga kuryan dakin kashe wutan ko ina nayi falon na shiga dakin .
Na samu yana cire rigar shi daga kofa inda nake nake fadi amma baka fada min a nan zaka kwana ba yau ban gyara wurin yadda ya kamata ba.
Baiyi magana ba sai da ya zauna a gadon yake fadin may ye laufin shi a hakan ai a gyare yake yana fadi ya haye gado ya kwanta.
Juyawa nayi zuwa falon bakomai nake yi ba sai dai na dauki lokaci ban dawo cikin dakin ba sai can na shigo.