yadda na gyara shi komai tas sai walkiya gurin keyi.
Sai da muka gama jera komai a inda ya dace na koma daki don in watsa ma jikina ruwa in shirya na fito daga wanka har na saka ma jikina tufafi sai gashi a dakin nawa gaida shi na yi sai dai fuskan shi duk da ya tashi daga barci ne babu walwala a cikin fiskan shi.
Daga inda yake tsaye yace ki shirya zamu koma Abuja yau din nan dago kai nayi da sauri ina kallon shi.
Yace kinji may nace ai ko nace ni da zaka barni in badon karatuna ba sai in ce kabarni nan kaduna don Allah don wallahi nafi jin dadin zama a nan.
Wani kallo yayi min sai baiyi magana ba bayan fitan shine na fara shirin kaya duk da ba wasu kaya mai yawa nazo dasu.
Bayan na gama shiryawa ne na sauko kasa ban samu anty a falo ba don haka na nufi dakin ta don in fada mata zamu tafi yau inji maigidan.
A kofa na tsaya ina sallama ta amsa min daga ciki na sakai na shiga har wanan lokacin tana kwance jikin ta ba riga batayi wanka ba.
Gaida ita da kwana na fara yi tare da tambayan yaran ta tayi murmushi tace yanzu na kora su zuwa islamiya don yau basu shiga boko.
Abinda na lura dashi shine maganan diyan ta yana sakata farin ciki shi kawai zakai mata kaga farin ciki a fuskan ta.
Daga inda nake tsaye nace anty Fati ya fada maki yau zamu koma wai don nima yanzu ya shiga yana sheda min batun tafiya.
Gashi kuma su Affan basu nan zamu tafi kila don Allah anty zanso idan an masu hutu suzo Abuja wurin mu suyi hutu tare da mu.
Zaune ta mike tana fadin a, a Amarya ban maki wanan alkawarin ba gaskiya yaran da ko wanda ya haife su ba wani damuwa yayi da al,amarun su ba ina zan tura su zuwa can suje su zama abin tausayi.
Muna tare dasu ma yaya aka kare ballantana sun tafi su kaida tare ta nayi da fadin haba anty ban son ki fadi hakan karki manta gidan uban su zasu tafi hutun fa ba wani gida ba.
Daga inda take take gyara zama tare da gyara daurin zanin jikinta a gaba da kyau tana fadin Amarya ke nan wallahi zan iya tura maki yara na ko zuwa ina ne don na yarda dake sosai dan kwana biyun da mukayi tare.
Bayan haka kuma ina da labarin halinki da komai naki gurin su mommy da su Bintu sai dai matsala daya ne daba zan turo maki yara zuwa Abuja ba gaskiya matsalan kuma kin sani itace Nafisa.
Na dago kai na kalle ta nace Nafisa kuma anty tace kwarai kuwa don na fiki sanin waye Nafisa ke yanzun kika shigo kila baki fara sanin halinta ba ko wani abu nata.
Halin ki kawai khadija yasa na aminta da dake da diya na wanda idan Nafisa ce ko na minti daya bz zan aminta da ita da hakan.
Kiyi hakkuri nace da ita kawai don taban tausayi a yadda take maganan nata
Amarya matar da bata kauna na da diyana ko na second daya taki jinin ta bude ido tagamun tare da mahaifin su a gidan nan.
Idan itace fa tazo yadda kukazo da mijin nan ban isa in saka shi a ido ba yanzun ma ne da abin ya danyi sauki har zai iya dan kwana a dakin mu da zara gari ya waye kuma bazan kara ganin shi ba sai wani jikon.
Sannan zan tura yarana inda take ai duk abinda tayi masu a can nina ja don ni nayi sake suka tafi.
Nace anty ai ba wurin ta suka zo ba gurina suka zo kuma gida gidan uban su ne ba wanda zai hanna su abinda suke son yi da zakiyi hakkuri ki turo min su ko kuzo muna hutu tare dasu ki gani babu abinda zai faru wallahi.
Tace ummh,ummmh amarya bazan je ba suma ba zasu zo ba barsu dai nan inda nake shiya fi ni wallahi na gode da abinda kikai min don ko yanzu kin nuna min ke mai kaunar mu ce.
Ko ba komai ki nuna min so tunda kin so diya na ni kin gama yi min komai wallahi shiru nayi sai can nace amma ya kamata ace kuna zuwa hutu Abuja duk lokacin da yaran suka samu hutu sai kuzo sai nake ganin kamar haka zai kara kawo masu shakuwa da mahaifin su.
Tace hakane kuma amma gaskiya ba zan iya zuwa ba ke dai kawai abar maganan nan zaifi sauki.
Nace idan ke ba, , , , , shine ya shigo dakin ya samay mu a ciki yana muna kallo mai kama da zargi ganin mu a tare muna magana.
Saidai ganin shin bai hanani karasa maganar da zan fada ba din nace in ba zaki zo ba sai ki barsu su suzo suyi min hutu a can.
Tayi dan dariyan nan nata a gyatsire tace zasu zo wata rana ai tunda kin kwadaita masu zuwan zasu shiga damu na ne don dama suna son zuwa.
Nace to yayi anty sai na gansu ke nan idan ma basu zo ba ni zan zo nan in masu hutun ba shike nan ba na juya zan bar daki yana tsaye yana duba wayan shi bai muna magana ba.
Nan na barshi na fita zuwa dakina ina bugawa Ya Amina waya cewa wai yau zamu koma Abuja inji shi.
Tace yau kuma Khadi gashi baki ko shigo wurina munyi magana ba nace ai haka kuka zaba min a tauyeni a hanani dama na.
Dariya tayi min tace aure ne khadi aure kuma yakin mata ne kin sani nasan dai idan zaku wuce zaku ratso nan ai shi ya shigo yana fadin in fito mu tafi in kule dakin in bar key din a wurina shine dakina a gidan.
Ya sa hannu ya dauki dan trolley din da na aje a tsakar dakin yayi waje dashi mikewa nayi na dauki hand bag dina na yima dakin kallo na rufo na sauko kasa.
Anty Fati tana kasan anan na samay ta tana jiran saukowana na taka zuwa inda take ina gyara mayafin da ke a kaina tare da fadin anty zamu tafi.
Ta dan kakaro murmushi tace khadija na gode sai kuma wata rana ke nan nace ai zanzowa su Affan hutu tunda su basu zuwa shiko yana tsaye yayi kicin kicin da fuskan shi bai annuri.
A waje muka samu Yusuf da sauran drivers din suna magana suna diban dayan motar ya fito yana fadin da matsalane Yusuf ?
Yusuf din ya juyo yana fadin iska kawai zai kara mata idan mun fita yanzu kafin mu fara hanya rai bace ya ce ma drivern motar kasan ban son irin haka shiyasa nake cewa kowa ya duba motar shi kafin muyi tafiya.
Yallabai ban san yau zamu koma ba da tun jiya nazo na dauke ta na kai an kara mata iskan.
A family house din su muka tsaya sai da muka tsaya muke gaisawa da Yusuf din don suna ta fada da driver.
Niko sai kallon su nake ina cewa a raina samun duniya ma wani wahala ne ji yadda yake ma dattijon nan fada don Allah ?
Mun shiga ciki muka gaisa da mutanen gidan dakin hajiya mama kamar kullun muka shiga karshe.
Gaisawa da ita nayi na mike na shiga wurin su Binta nayi haka ne don in barshi ya gana da mahaifiyar shi din.
Hira mukayi sosai ina jadda ma Binta zancen zuwan da tace zatayi wurin mu tayi IT zainab tace dani don kinji tana fadi kawai wa zai barta tazo .
Fitowa mukayi falon don tafiya yana zaune har yanzu a gaban hajiyar su daidai lokacin da take fadin kasan dole sai ka mata lefen ts kamar kowa don iyayyen ta sun dubi korafin mu sun aura maka ita a haka bashi zai sa ka dauki lokaci ba wurin bata hakkin ta.
Tsam mukaja muka tsaya sai kuma nayi niyar komawa dakin da muka fito din tace dawo ki zauna ai ba wani magana bane magana muke akan zancen lefen ki da bai maki ba har yanzu tunda anyi auren ba wani shiri a duka bangaren biyu.
Kaina na sada kasa don kunya kan ai iyayyena sun gama sayae min da daraja na a idon kowa sai dai biyayya ya rage min don ni ban ma ko tuna da zancen wani lefe ba can.
Ta juyo kaina tana fadin khadija bamu da abinda zamu saka maki dashi dake da iyayyen ki sai addu,a don mahaifan kin sun nuna muna harcin da ba kowa ne zai maka shi ba a wanan zamanin.
Don Allah kada naji wani abin assha ya fito daga bangaren ki ko kadan yadda mukayi hadin nan a cikin aminci muna fatan zaku ba marada kunya dukkan ku biyun.
Mommy ne ta shigo dakin da wani leda mai ruwa blue mai dan girma a hannun ta tana fadin masu tafiyan nan babu sallama ga dai dan abinda kika samu ayi hakkuri dashi na rubuta duk bayani a cikin ko wani idan kin duba.
Godiya nayi na karbi ledan daga hannun ta na kara sada kaina kasa ina jin kamar hawaye zai zubo min tace to babangida gadai amanar diyana nan muna kara danka maka muna maku fatan alheri ke kuma ki bi mijin ki amana yi nayi bari na bari.
Muryan shi naji cikin rashin tsammani yana fadin mommu ku dai kara ja mata kunne ta fita harkan Nafisa don Nafisa takala ita kuma tace sai ta mayar da martani.
A , a tun yanzu har sun fara ne inji hajiya mama yace mama ai kin san halin Nafisa akan kishi zuwan nan da mukayi ba irin kirana da batayi tana zagina ba.
Nasan in min koma akwai tsiya shiyasa nake son a ja mata kunne don Allah kada ta dinga biye ma haukan ta.
Ina zaki tsaya bin ta kan wanan da bata san ida ke mata ciwo ba mommy tace kada ki soma inji haka na faruwa dake khadija.
Ba zata taba son ki ba haka sukayi da Fati a baya yanzun kuma ta dawo gare ki hajiya mama tace bazaku zo daya ba khadija don ke mai ilimi ce kiyi amfani da ilimin ki ku saman ma yaron nan kwanciyan hankali don Allah wayan shi yai kara ya mike ya fice daga dakin.
Hajiya mama tace khadija nace a sanyaye na,am mama tace don Allah ku sama ma mijin nan na ku lafiya ya natsu ya dawo kan hanya.
Idan kin duba da halin da ake ciki shi kan shi yanzu bai san abinda yake yi ba kin ga ko wanan maganan na tana zagin shi da yafada yanzu abin ne ya ishe shi har mukaji.
Mun sa ayi auren nan naku ne don muna fatan samun sauyi daga gare ki a gidan don ke din mai ilimice da ko wani gida ake sin samun irin ta.
Kin ga mu nan idan kika shigo kika gan mu a haka sai ki dauka ba wani kishi a tsakanin mu amma akwai shi.
Kaina na dago na kalle ta tace kwarai akwashi mana a tsakanin mu sai dai muna kishin mu da ilimi ne bamu wanda za ai Allah waddai damu.
Don haka ki natsu ki karanci waye Nafisa ki san ta inda zaki bulloma haukan ta don ban dauke ta cikin mutanen kirki ba ni kina da ilimin ki na boko dana addini ki dinga kai kukan ki ga Allah kina neman kariya daga sherin ta in Allah ya yarda bata komai dake da yardan Allah.
Nan dai sukai tamin fada ya aiko daga falon Abba in fito mu tafi muka fito da su mommy banda hajiya mama da tai muna Allah ya kiyaye daga dakin don kawaici.
A falon Abban muka samay su dukan su ya dan taba muna nasiha mukai mashi sallama muka fito muka dauki hanya sai Abuja.
Tunda muka dauki hanya na lunshe idona har barci ya dauke ni a hakana mun shigo Abuja da dan sauran rana kai tsaye gidan muka nufa.
Nikan ina fitowa kai tsaye na nufi cikin gidan da addua dauke a bakina basu falon don haka na samu na shige ciki kai tsaye na bude part dina na shiga.
Sai da na shiga na dakatar da addu,an dake bakina ban zauna ba ina aje handbag dina ban daki na fada don a matse nake a lokacin pad din dake jikina ya damay ni.
Wanka nayi na canza wani pad kafin in fito koda na fito na samu an shigo min da kayana dankin nawa na gama kintsawa na zo na kawar da kayan inda ya dace.
Ban huta ba na shiga gyaran part din don dan kwana biyun da nayi naga wurin ya dan min kura ina cikin gyara ne ya shigo ya samay ni ina gyaran dakin.
Yace ke baki huta ba wani aiki kika daukowa kan ki na fada maki fa akwai may wanan aikin a gidan nan bakiji ba.
Sai lokacin na dago nace dashi in don dan wanan aikin ne zan iyayi wa kaina sannan kuma a gaban ka fa kaji tace in samo nawa yan aikin da zasuyi min ba yan uwan ta ba.
Ni kuma ko banza banga dalilin da zai sa in saka yan uwanta su gyara min daki ba da raina da lafiya na bai bani amsa ba sai cewan da yayi may zakici zan fita yanzu in sayo muna abinda zamuci ne.
Ban jin cin komai na bashi amsa tare da mayar da hankalina ga abinda nake yi da farko kallona ya dan yi yaga yadda fuskana yake daure tun fitowan mu daga gidan su.
Ni kuma haushin shi nake ji wanda ina ganin zancen lefen da naji hajiya mama tana mashine a kaina na kudiri koda ya kawo lefen ma bazan karba ba insha Allahu.
Bai dawo ba sai wani lokaci sai gashi dauke da ledoji a hannun shi ya shigo ina inner room ya samay ni a zaune ina nayi shiru na sadda kaina kasa ina tunane.
Yace may ke faruwa na gane ki a hakan dagowa na yi na kalle shi tare da kawar da kaina daga kallon shi nace ba komai yace ga abinci nan ki ci idan kin gama tunanen ki ya sa kai ya fice na bishi da kallon haushi.
Ban bude ledan ba sai bayan magariba dayake ina fashin sallah na gama addu,a na na jawo ledan na dara budewa.
Fredrice da barin kaza sai wani leda mai gasasa kaza a ciki dayan kuma kayan sanyi ne acikin sa cikin kwalaye.
Abincin na dan taba kadan na raja,a a cin kazan wayana yai kara na dauko na duba maryam ne a layin take kirana.
Na dauka da fadin yaya akayi ne yan mata tace ahhaye matan aure ke nan wai ke watau kin samu miji kina kokarin watsar da karatun ki ko ?
Nace to may akayi da maza inji dan daudu ina nada miji yanzu may zanyi da wani karatu kuma ?
Ke khadija ban son sheri wallahi muyi maganar gaskiya nace ke nake saurare tace yaushe wai zaku dawo kaduna ance fa monday kuna da test department din ku dazu na hadu da Ruth take fada min.
Nikan ina kaduna muna holewar mu inani ina wani test yanzu wallahi ki dawo khadija ki covering din abinda kika rasa nace sai wani sati maryam ihu tayi tace what ?
Nace da gaske tace wallahi kada kijawa kan ki caryover nace yau she kuma ni ban ma san ta inda zan fara ba wallahi ki dai dawo a cikin satin nan don Allah nace in Allah ya yarda ma na dawo don ni yanzun haka ina cikin garin Abuja ko.
Tace wai da gaske kike khadija nace da dawasa zan fada maki haka wallahi ina abuja nace mata tayi ajiyan zuciya tare da fadin da safe ki dubi hanya na zan shigo.
Nace ki barshi ba sai kinzo kin damay ni ba ina hutawa da mijina taja tsuki tana fadin Allah yasa da gaske kikeyi ba cika baki bane.
Nace ba abinda kuka kowo ni kenan in yi mai ba mai zaisa in cika baki kuma tace shegiya mai dadin bakin tsiya Allah sa da gaske kikeyi dai nace sai kin zo zaki gani.
Ina dago kai nagan shi a tsaye daga kofan yana saurena fuska na daure kamar ba ni nayi magana yanzu ba.
Maryam ce a layin naji ya tambaya nace dole sai kasan da wanda nake waya ne don bai cikin dokokin da aka fada min da zan shigo nan.
Matsala ta dake kenan baki san maganar arziki ba ke sai kin wa mutum wanan tsiwar taki nace ban mashi magana ba sai wasa da naman dana rike nakeyi a hannu na.
Kici abincin ki ni fita zan yi nazo yi maki saida safe ne don nagaji ina son in huta yanzu ban ce dashi komai ya juya zai bar dakin sai kuma ya