MIJIN BUZUWA complete Hausa Novels.txt

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   3 / 144

6K to 9K   out of 431K words

Yaja numfashi tare da cewa wanan deal ne a tsakanin na dan wani lokaci banga abinda zai sa ki dauke shi kamar serious ba.
Nayi dariya tare da cewa wasa mai kamar wahala ba indan buzuwa ta sanda hakan akwai matsala babba ashe sai na kwashe da wanni irin dariya mai ban haushi dake wa yayi bai ce komai ba cikin kuluwa.
Yusuf ya fito da manyan jakkuna a hannun shi yana kokarin bude motar ta kofar baya ya saka jin dariya yasa shi cewa abin ya fara tafiya ke nan dai.
Ya dai kusa na bashi amsa a takaice kai a fasa wanan deal din nace a fasa gaskiya zai fi don wanan ba zai kai ko ina ba.
Zai kai mana yace yana rufe kofan motan ya zagaya ya shiga kallon Samad dake dafe da kan shi yayi muka kama hanya a lokacin hadari ya hadu sosai a garin ruwa na iya zuba a ko wani lokaci.
Mun iso Yusuf ya tsayar da motar yace khadija mun gode sai mun kara haduwa yanzun ba time hadari ya hade gari ta ko ina nace nagode kwarai.
Ka kula min da mijin buzuwa don Allah na bude motar zan fita yace ga kayan ki nan ki kwasa duka naki ne godiya na sake mai karo na biyu na fice daga motar.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUYanayin damana yanayi mai cike da albarka yayin da ban gare guda yake burge alumma ko babu komai yanayin da daminar kan haddasa jamma,a sha,awan ta saboda ire iren abunda damanan kanzo wa jamma,a dashi musanman musan nan abuja da ba noma suke ba amma yanayi yana kawatar da jamman cikin ta yayin da damanan ta fara mikewa zaka ga tsirrai iri daban daban dake kara kawata garin.
Wanan yanayin yakan saukar min da nishadi sosai musanman idan naga garin ya gaure da hadari kasan ba wuya ruwa ya sauko masu.
Yau ma na fito daga aji ke nan naga yanayin garin ya sauya nasan bamu nisa da samun ruwan sama ke nan kusan kwana shida ke nan ana zuga muna ruwa a irin wanan lokacin.
Tafe nake a hankali nake takawa daga cikin haraban makarantan zuwa hanyar da zai fitar dani daga cikin makarantan sai dai zuciyana cike yake da tunanen rashin kudin da ban samu fita zuwa turawa daddy ba har yau ko da zan fito hadari ko ruwa zai tare ni gashi ban son inyi missing din lecture da safe.
Abu biyu ne yake damu na yanzu yunwa da tunanen daddyn mu saboda banci komai ba tunda safe da na fito don yau na makara ban tsaya na karya ba.
Saboda nacin karatu da nake dashi a raina don koda dare haka nakan raba dare ina karatu ni kadai a daki sai na gaji zan dan taba barci asuban farko kuma in tashi in fara nafila ina kusanta kai na ga Allah idan na gama kuma karatu zan dan dasa a wurin sai zuwa haskawan gari zan tashi in wanka in karya in kama hanyan shiga cikin makaranta.
Yau sai aka samu akasi na makata ban tashi da wuri ba har rana ya fito hakan ne ya hanani tsaya in karya wanan tsarin dana dauka yana matukar wahal dani .
Amma ni ina aganin shine daidai don iyakacin abinda ya kawo ni kenan a garin indan ban yi ba may zanyi.
Domin karatu na bar gidan mu na bar dangina da kowa nawa a gida nazo nan idan ban mai da hankali ba mai zanyi sai shiririta ke nan kamar yadda naga sauran dalibai suna yi.
Don a ganina karatun shi yazama min dole dashi na dogara dashi nake saka ran samun ci gaban rayuwa na dana iyayyena nan gaba .
Buri na ne burin iyayye na da yan uwa na ya ta,allaka ne akan karatun don haka babu dalilin da zai sa in zauna ina wasa dashi.
Nikan zauna in dinga tunanen yadda nake ganin wasu dalibai suna wasa da daman su ta hanyar zibar da abin da ya kawo sai in rika mamakin su ina tausaya masu don nayi imani da cewa suna cutar da kansu ne sun kuma ha,inci iyayyen da suka turo su karatu .
Ire iren su gasu nan da yawa sai yadda suke so sukeyi a cikin makaranta kwata kwata basu damu da karatun ba sai idan jerabawa yazo ne ido ya rena fata duk dadai wasun su ne suke damuwa da hakan.
Wasu ko iyayyen su ko samarin su suna masu hanya su haye ire iren tunanen da nake yi ke nan ina tafiya saman dogon titin da zai sada ni da gidajen da muke ciki.
Ido na zubawa wata dankareriyar motar jeep dake nufo inda nake a hankali ba ka gane wanda ke cikin motar dan glassen motar da ya kasance masu duhu baka gane na cikin motar balle ma wana sani ni anan.
Ta gefen ido nake kallon motar har zuwa lokacin da motar tayi gaba kadan dani ta tsaya a gaba na ban dauki komai a raina ba don a gani na wani abin maishi ya tsaya yi.
Nazo zan wuce motar ne naji muryan kamar wanda na sani yana cewa yar garin mu yanzu nake tunanen ki da hanya ya biyo dani ta wurin ku.
Don sheda muryan maishi da nayi yasa ni sakin dan murmushi kadan nace kaine kuma yau a wurin namu yace wallahi aiki ya biyo dani tanan din kuma ashe da rabon ganin ki.
Murmushi nayi na fara gaida shi ya amsa yana fadin ummm Khadija ko nace eh ashe baka manta da sunan yar garin naku ba dai.
Murmushi yayi yace ina zan manta da yar mama baki tambaye ni mijin bazuwa ba yau murmushi na kara yi nace kace dai miskilin mijin buzuwa.
Yace kin kara masa inkiya ke nan nace shine daidai dashi ai suna lafiya ko ya labarin gida koda yake muna waya dasu Binta ma nasan suna lafiya koda yake tace an ma mama rasuwa zariya ta tafi can tun jiya zata kwana uku a can.
Yace kai haba bata ko fada muna ba wallahi wa ya rasu a can zariya din sai kuma yace kada in tsare ki a hanya don naga kamar bakin son hakan ke.
Murmushi nayi nace idan hakan ya dauro yaya zanyi sai yace shigo mana in karasa dake idan ba damuwa nace lah ai ba wani nisa don na kusa karasawa ai.
Sai dai don Allah ina zaka bi don ina son sauka a bakin, banki in tura kudi yace to shigo mana in sauke ki ai ke din kanwar mu ce na zagaya gefen ina fadin na gode.
Mun dan fara tafiya wayar shi tayi tsuwa ya daga yaya akayi ne mijin buzuwa banji may yace ba don karan kira,an dake tashi a motar murya malam Ahmed sulaiman kano ne.
Yace wallahi gani nan dawowa sai dai kuma uzuri ya tare ni din na hadu da yar garin mu a hanya na rage mata hanya zamu banki da ita.
Wake nan ya tambaya a cikin wayan yace khadija wama surname din ki Adamu nace mai a takaice yace khadija a dabu kawar tafiyan ka na ranan.
What Yusuf sai da ka kara nemo yarinyar nan don Allah yarinyar nan bata da kunya fa ganin Yusuf nata dariya yasa ni wafce wayan ina karawa a kunne na naji yana fadin wanan yarinyar matsalace wallahi sam bata ganin girman babba.
Nace nakai matar kane rashin ganin girman dan adam kai har kana da bakin fadar haka yace baki da kunya ko nace aikai kana dashi kada ka kara kirana da mara kunya wallahi.
Yusuf ne ya karbi wayan a hamnu na yana dariya yace kadai ji abinda tace kada ka kara kiran ta da mara kunya ehheh.
Yusuf abin naka ya girmay sani na yanzu tunda har ka iya mika mata waya ta zage ni yace bata fa zage ka ba man ina jin yadda kukayi da ita sarai.
Mun iso ya tsaya na fita ina mai godiya yace shiga ki fito ina nan ina jiran ki har ki gama kin ga akwai hadari a garin sosai komawa zai maki wuya kuma.
Nagode nace dashi ina fita yace ara min wayan ki kafin ki dawo dan jimm nayi kamar ba zan bashi sai kuna mika mashi wayan na fice daga motar sai da na gama abinda nakeyi na tabbatar da kudin sun shiga na fito lokacin har an fara yayafi kadan kadan a gari yana zaune yana duban wayan shi na dawo na samay shi ina shiga yace har kin gama eh nace mai ina rufo kofar motar waya na ya miko min na karba ina fadin ka gama dubawa ne yace dama waazi neke dubawa a ciki murmushi na danyi kasan baki na.
Lokacin aka fara ruwa mai yawa duk da ban ganin hanyan da kyau amma na gane ba hanyar da muka fito bane muka bi yanzu.
Dan kallon shi nayi yace kada ki damu zan dauki mutumi ko ne ya gama mintin driver kuma wai yakai Nafisa Nasarawa bai dawo ba.
Banji dadin jin hakan ba sai dai ba yadda ja iya kuma a wani ma, aikata muka shiga ya tsayar da motar da sauri ya fito ya shiga motar ni kuma na koma baya.
Kamar ban cikin motar don banyi magana ba sai fada yakewa Yusuf wai ya dade baizo ya dauke shi ba yace kan wani aikin da kasa kanka can .
Ya haba taimako ne fa nayi kasan ace a taimaki mata ai a duk sanda suke ga bukatan taimako cikin tsawa yace ya ishe ka hakana Yusuf enough ta fada da karfi yana dafe kan shi da hannun shi daya.
Nan zan sauka nace a daidai lokacin da yake dafa kkan nashi da alama bai san dani a cikin motan ba ma sai a lokacin dan juyowa yayi yana kallo na da mamaki a fuskan shi ya sai kuma ya juya yana kallon Yusuf din.
Na sake fadin a nan zan sauka nace fa nace ma Yusuf ya juyo yace acikin ruwan nan zaki sauka haka a ina zaki samu abin hawa nace kada ka damu ai zan samu idan na fita.
Yace to bari in dan karasa dake inda zakiyi saurin samun abin hawa ya fadi shima fuska a dake da alama yaji haushin abinda yayi mashi a lokacin.
Karasa da ita ka ajeta yace ba tare da ya kalli kowan mu ba yai magana dama ba sauke ta zanyi ba ai sai na kaita inda na dauko ta.
Ba wanda ya sake magana a motan har bakin gidan ya tsaya da mota lokacin an dan rage ruwa sosai amma anadan yi kadan kadan yace ashe hajiya an mata rasuwa ne.
Ina fita naji yana fada mai hakana na gode yaya Yusuf agai da gida da mutanen gidan Allah ya kara rufa asiri na fice daga cikin motan abina.
Ban tsaya ba don ruwan sama bai bani lafiya idan ya buge ni sai dai ban tsira ina fita ruwan ya sake saukowa da karfi da gudu na karasa cikin .
Sun kama hanya ya dubu Yusuf din yana fadin wata hajiya akaima rasuwa nace yace hajiya mama mana hajiya mama nawa kake nufi ita yanzu wanan yarinyar ke fada min .
Shiru yayi bai sake magana ba sai zuwa can yace wata ce ma yarasu a zariya din kana son sani kake daure fuska haka tsuki yayi sai can yace barin kira hajiya din in ji.
Har ya dauko wayan ya fara duba lanban mama din sai kuma ya dago kai yace kana da nomban wanan yarinyar kaba in kira ta.
May zakayi da layin ta kuma yarinyar da bata da tarbiya yace malam idan zaka bani ka bani kawai ba dogon zance nake so ba kyale shi yayi kamar bada shi yake magana ba.
Sai zuwa can yace ana son ai maka gata kana wani jiji dakai wanan jida kai din ba zai kaika ko ina ba a harzuke yace nomba nace kabani kada ka fada min wani magana da zai kara bata min rai bayan wanan.
Har saida yakai shi hara ban gidan shi ya ajeshi zai fita ya miko mai wayan shi yana fadin ga nomban nan kamar ba zai karba ba sai kuma ya daure ya karbi wayan ya kwashe nomban.
Ya mika mai wayan ya shige ko sai anjima baice dashi ba shiko murmushi yayi yadan bugi sitiyaein mota shi ya juya ya fice gidan.
Nafisa buzuwa ce suke tafe da kawar ta nan cikin garin Abuja sun fito nasawa state ganin wani malamin su a can da tai ma mijin karya zasu duba wata aminiyar ta ne .
Bai hanata zuwa duk inda take so shiyasa tale samun yin yadda take so a gidan don shi kwata kwata bai dauke ta da irin wanan halin ba na matan dake shige shige.
A hankali suke magana yadda sani driver ba zai fance su ba shiko a idan yake tuki ya mayar da hankalin shi ga hannya ne amma kunnuwan shi yana gare su.
Nafisa ke fadin kin san Allah wanan sakawa zanyi yai min aikin da ko uwar shi ba zai iya daga ido ya kalla ba balle wata mace don naga alaman wanan arnen yada aiki sosai.
Don su malam kasan mu ko ka basu aiki irin wanan sai sun kawo maka Allah kusa kafin su duba maka kukan ka.
Suwaiba kawar ta ya mutsa baki tace ke ma kikan so damun kanki nafisa mijin da ko a yanzu a hannun ki yake wanda kika sa ya kore uwar yayan shi kuma ka zauna lafiya may kuma yanzu zai wani daga maki hankali.
Bai fa kallon mace sau biyu a yanzu hakan ba anan matsalan yake ba suwaiba wanan abokin nasa da suke kamar tagwayen sheri dan iska mara zuciya nayi kora da hali nayi na fili amma ya na lake kamar kaska dashi.
Kina ganin ko baiyi niyar yi ba shi bai iya dauko ko mace ya kawo mai ke komai tsiyan su fa baki taba gane sirin su dashi dashi.
To ai yanzu ba tashi zakiyi ba tunda shi kin riga da kin samay shi a hannu ko sai yadda keki so dashi yanzu akan wanan abokin nasa zaki koma ki san yadda kika raba su.
Gaban Sani driver ne ya fadi har yana batun kauce hanya dama yana zargin gidan da yakai su din ga zargin shi ya zama gaskiya har ana batun raba ogan nasu da aminin shi.
Wanda yasa in tayi nasaran yin hakan ta gama da ogon nasu ke nan gaba daya tunda shi kadai ne dama ya saura yana sashi a hanya yanzu.
Muryan ta yaji ta daka mai tsawa ya kula da tukin da yake yi ya dubi hanya mana yace hajiya rami na kaucewa shi ya kawo hakan.
Suwaiba tayi mata rada su bar maganan harsu sauka kada yaji abinda suke kullawa sai suka dauko wani sabon hira.
Sai kuma tace malam sani ke nan dama ina son magana ta siri dakai sai dai maganace ta taimakon juna dani dakai.
Yace hajiya wani taimako kike sona dashi tace siri ne kuma amana a tsakanin mu dakai amatsayi na matar ogan ka kuma wanda yasan wasu abubu nawa.
Idan kuma kaga bazaka iya taimaka min ta wanan hanyan ba to zamu hada deal dakai in dinga biyan ka akan aikin ka.
Dan juyowa yayi yadan kalle su zuciyar shi ya tabbatar mashi da cewa wani abu mai muhinmanci zata saka shi yai mata da ya shafe ogan nasa.
A fili yace hajiya fadi bukatan ki a shirye nake da in aiwatar maki matukar bai fi karfin iyawa na ba murmushi tayi tace ai ba wani abu mai wuya bane zan saka ka yi.
Ogan ka nake son ka sama ido don Allah duk wata mace da kaga yana hurda da ita a bayana har sun shaku a tsakanin su banda gaisu ka sanar dani ni kuma nayi maka alkawarin duk wata zan baka dubu biyar bayan wanda mai gida ke baka.
Yai dan dariya yana shafar kanshi yace hajiya idon wanan ne kar kiji komai aran ki nayi maki alkawarin ko gaisawa da wata naga yayi wace bata gamshe ni ba zan fada maki.
Suwaiba tace dakyau dan gari dama ai na fada maki babu abinda kudi bai bayar wa ke bude bakin jakkan ki ga aiki da cikawa kawai.
Da sunan zuciyar Sani driver da basu furta komai a gaban shi ba don nasiha hajiya mama kullun suka je kaduna ya shiga gaida ita shine don Allah ga amanan yaro na baka Sani ko ba komai yanzu mun zama daya dakai tunda ana wuri daya.

Duk da kasalan dake damu na a lokacin bai hanani tashi in girkawa kaina abinda zanci ba lokacin bayan na gama ne na fitar da kayan da nayi aiki na wanka na shiga bayi na watsa ruwa masu zafi don ruwan sama bai bani amana ajikina.
Ina fitowa daga bayi ne mukai kicibis da zarah da ta shigo dakin nawa a lokacin wanda alama ya nuna yanzu ta dawo daga cikin gari sabada ledan da take dauke dashi a hannun ta.
Nasan key din dakin ta tazo dauka tana saye da wasu kaya da ya matse mata jiki sosai kin dawo nace mata eh kin gani sai yanzu na dawo wallahi.

3 / 144

Chapters