murda min don haka na tashi na bude kofan.
Yana tsaye saye da farar jallabiya kamar yadda yake fitowa da safe guri na bashi ya shigo daga ciki.
Kallom fuskana yakeyi nace dashi ina kwana kafin ya amsa na sake cewa ya jikin yace da sauki tare da samun wuri ya zauna a falon.
Bayan kujera naje na tsaye tare da rankeafowa ina wasa da yatsun hannu na dan shiru ne ya biyo bayan sai can yace.
Deedar na fa gode abinda kikai min a daren jiya nace namay fa yace da baki biyewa wanan mahaukaciyar ba kukai min tashin hankali a gida.
Yaci gaba da fadin sai dai baki kyauta min ba da kika rufe min kofan dakin ki kika hanani shigowa inda kike.
Yau ina son fita gurin gyaran kai don kaina ya damay ni na sance ina son in je ai mun wani yace baki son zancen ke nan yasa kika kawar da maganan da zancen zuwa wurin gyaran kai.
May zan ce tunda kaji abinda tace kaga a barta ta maida kwana kin da take so tunda ba wani abin zama dama don haka afaki gaba.
Dago kai yayi ya kalle ni tare da idan naki ra,ayin ke nan haka a biye mata ni ba haka abin yake a wurina ba.
Bazan dauki wanan dokar ba don nike auren ku ba ita ba da zata kawo min wanan jahilin a gida wanda ra,ayin ta ne kawai yin hakan.
Wanan ni ba matsalana bane ku hakan ya shafa dakai da ita, don kun fi kusa kallona yayi ya dan harara ni tare da mikewa yana fadin idan kin shirya sai ki fada min in sa a kaiki.
Ya mike ya fita nabi bayan shi da kallo har ya bace min da ganina na sauke ajiyan zuciya tare da fadin Allah ya sauwa ka.
Maryam tazo bamu fita ba sai da ta karya a wurina muka shirya na kira shi ina sheda mai mun shirya yace drive na waje yana jirana.
An wanke mun kai da kitso tare da gyara min kafa sukai min zanen da maryam ta matsa sai aimin .
Ni kaina sai da gabana ya fadi yadda nagani na sauya a dan kankanin lokaci kamar bani bace bamu dawo gida ba direct sai da muka shiga wani plaza muka danyi sayayya wanda ni duk kayan kamshi ne na kwaso.
Mun shigo gidan Nafisa da yan uwanta ne zaune a falon sai shewa suke ban san abinda yayi masu dadi ba suke wanan jin dadin haka.
Mun yi sallama amma ban tsamanin wani daga cikin su ya karba muna muka shige su muka nufi part dina shirun da naji sunyi ne yasani gane mu suka bi da kallo.
Muna shiga daki maryam tace dani kai khadija wai kina nufin wa yan nan garadan maza da matan duk gidan nan suke gaba dayan su.
Murmushi nayi nace kema dai ke fada ni ma ban san iya adadin su ba don ban gama tantance su ba.
Shawarman da muka sawo muka baje a falo muna ci bayan munyi sallah la,asar wata ce daga cikin su ta fado mun dakin babu ko sallama sai da na kalle ta da kyau na gane bata ranan bace ma yau.
Kallon ta nayi cikin daka mata tsawa kafin ta fadi abinda ta shigo yi gurina din nace wai ku wasu irin mutane da baku iya sallama ku fado ma mutum daki kai tsaye babu sallah kamar kafirai.
Zatai magana na sake fadin idan ba zaki mun sallaman musulunci ba ki fice ki bar min shiya na fadi cikin fusata sai da ta juya ta fara tafiya ta juyo tana fadin dama maigidan ne tace in fada maki kije ki kwashe kayan da kika bari a shiyan maigidan.
Nace jeki ce ta barsu nan sai idan ta kara tsowo zan zo in kwashe amma yanzu tayi kadan.
Maryam ta kallo tana fadin wasu kaya sai lokacin nake ba maryam labarin abinda ya faru a daren jiyan kallon mamaki take min tace khadija anya matar nan tana da hankali kuwa ?
Nace in bata dashi ai zatayi bari muji may zatayi maryam tace khadija wallahi ban son tashin hankali a rayuwana.
Banko muna kofa mukaji anyi nace wani dan iskan ne haka ba sallama ya turo min kofa ido waje take kallo na mikewa nayi tsaye don jin damay tazo min.
Ke wa kike da suna don ni ban ko sa sunan ki a raina ba nace amma kin sani a ranki dai zaki iya kirana da kishiyar ki ko sunan bai maki ba na tambaya cikin kureta da ido.
Nafiki iskan ci don ni banda wata kishiya a gidan nan nace gani ko kina gani inba kishiyar ki nake ba yaushe zaki barni na zauna a gidan.
Banga kishiya ba don banga mutum a gidan ba nace nine nan mai shirin zama maki ciwon ido ki fadi abinda ya kawo ki, ki barmin shiya na don ba hurumin ki ba ne nan kuma saurara kiji iskancin ki ya tsaya iya mijin ki kada ya kawo kaina.
Zagi da ashar babu wanda bata aika min ba ga maryam ta hanani magana Allah da ikonshi AA ya shigo gidan tun da ya doso falon yake jin hayaniyar nafisa da mamaki ya karaso part.
Abinda ya fara zuwa mai a baki shine Nafisa may ya kawo kinan haukan naki har yakai ki shigo part din ta da fitinar ki.
Kan shi ta juya da masifan tana fadin ya dauko karuwa tazo tana mata iya shege a cikin gida yace gidab ki ko nawa ni na dauko ta ko ke.
Turata ya fara yi ganin da gaske idan ta tsaya zai iya jibganta yasa ta fice daga part din maryam ne ta kalleni tace gara da kika kyale ta yanzu kin ga ya gani da idon shi.
Ban san yaya suka karata ba bayan tafiyan maryam ne na gyasra part dina na shiga nayi wanka na zauna na feshe jikina da turararuka dakin shi na nufa.
Yana ciki zaune ga laptop ya tasa a gaban shi amma ya kasa aiwata komai a ciki shigowana yasa shi dago kai ya dan kalleni gaidashi na fara yi na samu wuri na zauna.
Haka yasa ya dawo da hankalin shi gareni nace dama nazo ne in maka tunin monday in Allah ya kaimu nike son fara shiga school.
Nan take ya bata ranshi tare da fadin kai nifa wanan karatun ba dole bane sai kinyi shi kuma ko kin gama ba aiki zan bari kiyi ba.
Nace amma kasan ba haka kukayi da iyayyena ba tun farko ai kasan ina karatu ka auro ni a hakan ka kawo wanan gida naka na fitina.
Sanan kuma a hostel zan zauna don yafi min sauki ko ka sama min wani gida na daban in zauna don ban iya fitinar wanan matar taka haka .
Wanan shine ra,ayina don zama na anan ina takura maku kai da matar ka yace wanan kuma maganar kine don haka ba ra,ayina bane kinji na fada maki.
Wasu hawayene suka zubo min a fuskana kamar zanyi magaba sai kuma na juya na fita daga dakin batare da nayi magana ba.
Bina yayi da kallo har na fice daga dakin ban san may yagani ba sai gashi a dakin ya biyo ni, sai da yasamu wuri ya zauna ya fara magana.
Khadija may yasa kike son kema ki daga min hankali ina kokari in ga na shawo kan nafisa a gidan nan abubuwa su koma daidai.
Ke kuma zaki zo min da wanan magana yanzu ina sane da zancen karatun wanan nasan dashi amma zancen in canza maki gida bai taso ba.
Nace fitinar matar kace bazan iya ba tun yanzu ta fara kawo min takakka a daki na ba don maryam dake gidan ba da yaya kake son in yi.
Ni kadai kagana ganin zan iya sune ko sai sun min yadda sukai maka sanan zakaji dadi ance sarki yawa yafi sarkin karfi.
Ki bani lokaci akwai abinda nake shiryawa komai zai zo da sauki da yardan Allah amma yanzu indan munyi haka ai kamar taci galaban ki ke nan kece fa ake fadin zaki iya da ita amma gashi tun yanzu kin fara sarewa da ita.
Ba tsoron matar ka nake ji ba fitinar tane nake son kaucewa sai ta lafa yace aiba lafawa take bukata ba barin gidan take bukata gare ki.
Wanan mai sauki ni idan nice ba sai tayi fitina dakai ba yace aina san da hakan ba sai kin fada ba a fili amma nayi mamakin saurin kariyan ki tun yanzu ko wasan ba,a fara ba.
Nace ashe akwai sauran wasa a baya yace ai ba a ko fara ba don yanzu somin tabi ne tunda bataga kin fara rungumana ba kina goya ni.
Hararab shi nayi baka so hakan ba don baka biyo ta hanyan da za ai hakan ba yace saboda ban maki may ba ?
Ya kasheni da idanuwan shi da ba zan jure kallon shi ido cikin ido ba ya mike tare da fadin ki sawa kan ki hakkuri komai zai wuce da yardan Allah .
Har yakai kofa ya juyo yana fadin wai yaushe ne zaki kare wanan abin naki nace wani abu cikin watsa mashi harara yace barin zo in gani don ina ganin kamar ya dauke ni kike kwara.
Ya nufoni gadan gadan nai saurin mikewa na shige bayi tare da turo kofa ina saka key yace matsoraciyar banza kawai ai ba sai kin gudu ba.
Jin ya fita daga dakin nafito na nufi falo na rufo kofana na dawo na kashe wutan dakin na kwanta tare da tunane a raina.
AA mutum ne mai saukin kai a yadda na fahince shi sai dai matane bai samu ba ji yadda yazo yana min magana cikin tsigar lalashi.
.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Sai da ya gaji da ya mutsani don kan shi ya sakeni idanuwa na lumshe ina mai jin takaicin hakan a raina yana koma gefe ya mirgina yana mai da nunfashi a wahalce .
Bakajin komai a dakin sai shiru sai ko karan na,uran dakin dake aiki a lokacin kasa kasa naji muryan shi yana fadin.
I am sorry Deedar kada ki dauke hakan don haka nayi na bane hakkinane na fara bi a gurin ki daga inda nake kwance bai iya tabuka komai sai hawaye dake fitamin daga idona wanda da taimakon haka nake jin dan relief a zuciyana.
Can ya mike zaune yana fadin ki tashi ki yi breakfast mushiga mu gaida su Abba a cikin gida don sun ji muna garin nan tun jiya da dare and ba aladana bane inzo ban shiga wurin su ba a duk lokacin dana iso.
Kinga sai su dauka naki sallon ne haka na hana ni shiga in gaida su sai lokacin nayi karfin halin yin magana nace tunda ka iya keta zaka sa su dauke a hankan ai don ka bata min suna.
Murmushi yayi ya mikewa tare da fadin ba ga laifin ki ba da kike karatun low don shine daidai da wanan bakin naki mai surutun tsiya.
Yakai kofa nace mugu kawai wanda bai san tausayi ba ya juyo yadan kalle ni yana fadin ke aikin sani tunda kin iya.
Bayan fitan shi dakin nan iya dagawa a yadda ya banni ba a gurin nake kwance yayin da wayana yayi kara na dauka Ya Amina ce take fada min gata nan zuwa.
Nace ki bari sai anjima don yace wai cikin gidan su zamu shiga yanzu idan mun karya tace to shike nan hakan yana da kyau ai.
Kirana yayi da waya in fito mu karya mu fita nafito falon zaune na samay su shi da Yusuf suna magana Yusuf din na dan rankwafa ina gayarwa ya amsa min da kanwata ya gajiyan hanya Alhamdullahi na bashi amsa kawai.
Zagayawa nayi ban yarda na bi ta faman su ba na samu wuri dan nesa dasu na zauna fuskan shi na akaina sai dai na kasa daga ido in kalle shi ni.
Labara ta fito ta nufi dining din gidan ta fara jera abinci a sama sai cewa yayi kawo muna nan zafi don baku gyara wurin nan mutum nacin abinci zuciyar shi na tashi.
Sai lokacin na dago ido na kalle su gira ya daga min nayi saurin kawar da kaina gefe kamar ban gan shi ba zama sukayi kasa don su karya iba zaune ban motsa ba.
Kefa yaya ne bazaki karya bane yace min ba yanzun zan karya ba sai an jima na bashi amsa koma da zan karya a tare da abokin shine zan zauna ina budan baki.
Yana bude kula naji ya ja tsuki yana fadin idan zaka iya ci Yusuf kaci ni ruwan tea din kawai zan kora Yusuf yace kaci mana ko kadan ne yace wanan abin haka kokai nasan ba zaka ci ba.
Mikewa nayi don barin falon lokacin da suka fara karyawan naga Yusuf ya gutsuri doyan ya mayar a cikin plate din daya diba.
Ko ruwan tea din dana zo sha ba wani kamshi ko dandano a cikin sa sai kona baki yakeyi amma haka na daure na shanye duka na aje cup din.
Sai gaya ya shigo yana fadin mutafi ko idan na gama na dankara gyara fuskana nafito har daki nabi anty Fati ina fada mata inda zamu tace mu dawo lafiya na fito muka dauki hanyan shiga cikin gidan su.
A kofan gidan nasu Yusuf ya tsayar da motar sai da suka fara fita kafin ni in fito suna gaba ina bayan su muka shigo gidan wanan karon bai barni nayi yadda na saba ba idan na shiga gidan.
Dole duk inda yasa kafa yacire in dora nawa nima tare da mika gaisuwa na gare su.
Watau duk yadda akayi wanan kishin sai an samay shi a tsakani mata kaji ana cewa su wance kai gidan su lafiya lau wallahi .
Akwai zaman lafiya da fahinta da yar uwar ta ko abokiyar yazaman ta idan kinji wanan zancen a gida ba sai kin tona ba.
Daya ce ta kwanta daya a sama ko kuma daya ta iya hakkuri da duk wanin abinda za ai mata bata nunawa.
Yanayin zaman sarakaina yasa nayi wanan magana don anty Amarya amaryan su mommy tana da wani hali mai wuyan fahinta don kokai waye ka shigo gidan su kana sallama zata karba amma idon ta yana kasan zanin ka ko a jikin ka ta karance yanayin shigan ka a lokaci daya.
Yauma hakane ya faru damu da muka shigo part din ta don mu gaida ita ina sallama gaba daya idon ta a kaina yake baifi second ba ta kare min kallo.
Sai naji banji dadin abinda tayi min ba na duka har kasa na gaida ita da gida tana tambayana yaya amarci kaina na noke kawai ina dan murmushi muna fita tabini da harara wanda ban san abinda nayi mata ba nayi kamar ban ganta ba.
Ummi ma da muka shiga wurin ta ta tare mu ba yabo ba fallasa cikin mutunci da girmamawa muka gaida ita tana ta saka muna albarka har muka bar dakin sai dakin mommy daga nan zamu shiga na hajiya mama hajiyar su AA din.
Mommy kasa boye farin cikin ta tayi da ganin mu tana ta faman yi muna sannu da zuwa tana washe baki don ta kasa boye farin cikin ta ita kuma haka Allah yayi rayuwan ta da rashin kyashin duk wani wanda ta sani har mutanen gidan sukan ji haushin ta wani lokaci.
Mun dan gaisa da ita yake fadin bari muje mu gaisa da hajiya do a nan zan barta ta wuni maku zan tafi wani wuri ne daga nan tace gaskiya mun ji dadin wanan abin sosai wallahi.
Surajo ma ya kawo muna yarinyar da zai aura shekaran jiya anan ta wuni muna sai wani lokaci ta wuce.
Hajiya mama na zaune a falon ta muka shiga da sallaman mu bantaba ganin farin cikin ta ba irin yau din da muka shiga gaida ita.
Akusa da kafanta na zauna suna gefe dashi da Yusuf zaune guri daya muka fara gaida ita sune suke gaisawa da ita amma hankalin mama na wuri na.
Sai da suka gama gaida ita na fara gaida ita cikin ladabi tace naji dadin hakan dana ganku Khadija ki kwantar da hankalin ki kuyi zaman lafiya da mijin ki da abokan zaman ki aure shi zaman hakkuri ya gada.
Zo mu zauna zo mu saba haka abin yake ba ko yaushe ake zama dadi da miji ba musanman ma idan mijin yana da mata da yawa kamar irin na mu dana ku yanayi.
Sai an kai zuciya nesa ga komai da zaka gani kagani kaki gani Allah yayi albarka ya baku zuria masu albarka.
Suka amsa mata da amin mama mun gode yace gata nan a nan zan barta zamu dan je wani wuri sai zuwa anjima zamu dawo in Allah ya yarda.
Sai mun dawo zamu gaisa da Abba don ance yau yayi sammako ya fita zuwa unguwa bamu