yaushe kuma aka taba yin haka in bakai mai godiya ba ai sai ka kyalesu da wace aka ba din ko ?
Tace umma tace zatayi mashi magana ai idan ya shigo nace Allah yasa ma bai buga mai ba kamar yadda yace zai kirashi din.
Altine na kalla nace yace wai ki kirga mai mutanen da suka zo daga kaduna da minna ko mutum nawa ne suma yasan mutum nawa suka zo tace dan gidan momy ke nan ga dadi ga wuyan sha,ani.
Sai zuwa goma da wani abu ya sauko kasa koshi tare da Yusuf suka shigo part din su gaida mutane a can dakin dasu umma suke ne bayan ya gaida su tace babangida sai muke jin wani zance kuma mara dadi.
Idan baku samu karuwa ba kun ga wani ya kawo abin arzikin shi gidan nan a baya arzikin diyan ka ne ya jawo maku alheri don may zakace a mayar da kyautan motan da aka baku.
In ma kana ganin da wata manufa ya baka ai samun hanyar da zaka mayar mai dashi kaima zakayi ba wai a dauka kai tsaye ace amayar haka ba.
Kallon shi Yusuf yayi yana son karin bayani yace Umma ba wai hakana bane sun biyo ta wanan hanyar ne don suga sun bata min tsarina tace idan da haka ne ai ba zasu hada da matanka harda diya ba ko ?
Kayi hakkuri abinda ya wuce abarshi akan ya wuce sai a faki gaba kuma yace to shike nan umma ya wuce ai tunda kinyi magana.
Tace ta gode nan yace naji ance yau zaku koma wai munyi waya da Abba nace dashi gobe zan sallamo ku kudawo gida tace to shike nan Allah ya kaimu goben lafiya yau da gobe duk daya ne a gurin Allah ai.
Ya barin wurin su dakina ya shiga inda nake zaune da yan uwa suka gaisa dasu ya fada masu yana son su bar tafiyan su har gobe mama Tani tace bai zama dawainiya ba tunda angama abinda ya kawo mu.
Sai dai kuma dama muna son magana akan ita khadijan wai muna rokon ko za a bamu ita mu tafi da ita taje gida tasha ruwan zafi sai su dawo.
Dan murmushi yayi tare da fadin mama kuyi hakkuri a barta a dakin ta don mu gidan mu ba a hakana sai dai idan wata zata zo ta zauna da ita nan ne babu damuwa.
Mama Tani tace to shike nan zamuyi shawara mu gani abinda shawara ya yanke zakaji yace karatun ta ma sati biyu kawai suka bata leave.
Yana fita na turo baki nace ni gida zan koma gaskiya ban iya zama ni kadai anan inyi jego da yaran har biyu haka a gabana.
Yafi mu gaskiya mama Tani tace don kinga idan kinje gida yaya zakiyi da karatun ki kuma yace komawa gida ba aladan gidan su bane dole dai kiyi hakkuri sai a turo maki wace zata kula dake nan.
Ban so haka ba don ni na sama raina zuwa gida inyi wanka a can ban taba tunanen zai kawo min cikas ga zuwa gidan da na kwalfawa rai ba.
Wunin ranan dai haka nayi shi ba dadin rai sun shiga gari har yan kadunan yan tsiraru aka barmu dasu a gida da yamma ya dawo ya kirani falo na fita na samay shi zaune.
Yace wanan sallaman yan minna ne wanan kuma na yan kaduna ko akwai sauran wani abinda za a basu ne nace babu an gode.
Ina shirin mikewa yace min ya na ganki haka wani abin yana damun ki ne shiru nayi sai da ya kara maimaita maganar shi nace gida nake son zuwa in sha ruwan zafi.
Nan da kike ruwan sanyi kike sha kafin in magana sai fa Nafisa a gaban mu tace samad kasan yarinyar nan bata da girki tunda ta haihu ko ?
Yace wani abin kika ga munayi da ita anan tace ban yarda kana ke bewa da ita ba haka don hakkina ne yanzu.
Nace au hakane to tunda abin haka gobe zan karbi girki na a gidan nan ko ba za a ban ba inji tace wallahi baki isa ba don sai kinyi arbain.
Nace tunda ke ke iko dani sai mu gani idan ban insa ba din ko kin manta ke ma haka kikayi baki arbain din ba kika karbi girki ki ko kinfi wani ne a gidan nan.
Don haka nima zan karba kamar yadda kika karba kina nufin dani zaki takara a gidan nan nace da abin kwarai kikeyi da nayi koyi dashi sosai kuwa amma girki a gidan nan gobe kamar nayi shi na gama ne.
Ina fadin haka na dauki kudin tare da kiran laraba ta shigo min da kayan na barsu a gurin suna fafatawa da ita na shige ciki ban san yadda suka karata ba.
Nasha alwashin dama sai na rama hakan a raina idan ita tayi a kuraren lokaci wancan karon ni da wuri zan mata nawa iya shegen nima tunda da gangan take yin tsiyar ta don ta nuna tafi wani iya iskanci.
Momy na kira na danka ma kayan su na yan kaduna mutanen minna kuma na ba mama Tani nasu a hannun ta.
Washe gari baki sun watse sai su momy da Altine sai ya Amina muka saura a part din maryam ne ta shigo zuwa yamma muka shige daki muna hira damu uku.
Anan nake fada masu yadda mukayi da Nafisa da jiya maryam tace kwarai kuwa gwama da kika ce hakan ko ba zaki dakin shi ba nuna mata kowa ya iya iya shegen ai.
Girki nasa Altine su shirya dashi zuwa biyar ya shigo gidan ya dan jima zaune a falo gurin su kafin ya shigo wurina ciki.
Ganin shi maryam ta fita ya samu wuri ya zauna yace ya batun girkin naki yau nace yana nan kamar yadda nace yace cikin marairaicewa bazaki bari yaran nan su kara kwari ba.
Nace cewa nayi zasu hanani yin girki din dama haka zanyi tunda tace bata san nasiha ba muje zuwa ga haka.
Ya ga dai da gaske nake magana ba wasa a cikin harkan don ashe ita ce ta tayar mashi da hankali ya mike jiki ba karfi ya fice dakin.
Can ta samay shi ranan dai sunyi bala,i sosai yace ai ita ta fara tunda nace zan rama sai ta kyale ni da ta kyaleni bata fito da cin mutunci ba yasan da ban karbi girki a yanzu ba.
Dare yayi da kaina nakai mai abincin shi na zauna sai da ya gama na kwashe kayan yace ina yaran suna daki na bashi amsa fuska a daure murmushi kawai yayi yace a can zasu kwana ne ?
Nace tare da wa nima ai ba anan din zan kwana rashin mutunci tai min nima na rama in nuna mata ba tsoron ta ake ji ba nasan da gangan ta take iskancin ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: An buga ma yan uwa da abokan arziki zancen haihuwana na kusa da na nesa sai kiran waya nake faman karbawa na mutane.
Sallama akayi a kofan falon za a shigo duk muka maryam da hankalin mu wurin mai shigowa da sallama da murya a natsune haka.
Wata bakuwar fuskane daga cikin buzayen mai sallaman tana gaba rike da hannun Ihisah sai wata daya dake bayan ta sai daga bana ya fadi don ganin kamar su da Nafisa da yaiwa take na daure fuskana don ganin su.
Bani kadai naga wanan kamar ba duk wanda ke falon ya san Nafisa yaga kamarsu da wanan buzuwan wani sallaman ta kara muna a karo na biyu muka sake karba masu.
Ihisan ce ta shiko gurina ganina rugumay da baby a hannuna tana fadin anty baby babyan mu ne nace eh Ihisan banganki ba tun da kuka dawo sai yau.
Wuri momy ta basu suka zauna mai kama da Nafisan bata zauna ba saida tayi bissimillah a tsigar kamala takai zaune.
Tare da fara gaida mutane da ta samu a gurin tace dani kece maijegon nace eh tace tubarkallah masha Allah Allah ya raya muna su akan tafarkin addinin musulinci.
Allah ya tsare mina suna daga duk wani aikin shedan daga mutun ko aljan da duk wani abinki masheranci muna fadin Amin.
Tace munzo mun samay ku lafiya don muna zuwa washe gari sai mukaji haihuwa nace bari mu barki ki huta sai mu shigo mugaida ke.
Nace na gode dan shiru ne ya biyo falon sai ihisan dake zuba surutu wai a bata baby ta dauka nace ina Samira sai matar tace tana kwance gajiyan hanya ya saukar mata da zazzabi jiya.
Allah sarki gaskiya dai banganta ba tace eh ai tana yawan ban labarin ki sosai tace kina basu abinci mai dadi kina dai kyautata masu sosai.
Yarinyar dake hannun maryam ne ta danyi kuka kamar irin mafalkin nan da yara kanyi tace idan sunyi haka ku karanta masu kalman sha hada a kunnen su kunnen hagu kuma ai masu auzu billahi mina shetanin rajjim.
Ki dinga shafa masu man zaitun sai da dare idan zaku kwanta ki shafa masu man habba da safe ma hakane don kariya daga duk wani abin sherin daga gare su.
Nagode nace tace ba damuwa Allah ya raya ya inganta cikin hausan su na ayan Niger take magana mai kama da kananci ko sakwatanci.
Mikewa tayi tana fadin mun gaishe ku dama nace bari mu shigo mu gaisa muyi barka kuma to na gode sai dai ban sanki ba gaskiya.
Tace tana dariya wanan ne karona na farko da nazo Nigeria a Niger nake aure mijina ya rasu shekara biyu ke nan yanzi na dan zo ganin ku ne in koma kwana biyu.
Nace munko gode wallahi tace ba komai nace baki dauki yaran ba don naji nauyin matar sosai ganin kamalanta ya cika min ido tace a, a barsu har gaba ai muna nan daku kwana biyu.
Dayan matar tace wa Ihisan tazo suje tace ki barta mana tana wurin uwarta ne ai sai dayan tayi yare sai ita ta juya da hausa tana fadin.
Za a rabata da yan uwanta ne wanan ai duk shirmay ne don sune dai nata din kinga don Allah mu tafi maryam tace baki dai fada muna sunan ki ba har yanzu.
Tace hakane sunana Fatiha wanan kuma Zakiya ita ubane muka hada da ita amma uwarta ta rasu ita ta kare karatun ta ne batayi aure ba niko nayi aure har ina da yara biyu sai dai basu tare dani suna gurin mahaifiyar uban su can Cameron don acan nayi aure.
Da fatan zamuji dadin kasancewa daku na dan lokaci a gidan nan nace insha Allahu mun gode kwarai tace sai mun kara shigowa ke nan.
Suka fice tare da rufo muna kofan a yadda yake kowa gulma ya cishi a falon marym ta fara magana tana fadin ikon Allah ashe akwai na Allah haka a cikin su ?
Momy tace haba maryam akwaisu ma sosai kuwa ai irin masu shigowan nan jahilan su ne da talauci yaiwa katutu suke shigowa nan.
Ko a cikin sun kuma akwai na kwarai sosai laraba tace itace mai ibandan nan dana fada maku ko yaushe ka wuce su suna sallah ko karatun kur,ani a falo suke zama abinsu har dare.
Ikon Allah gashi kuma abu daya suke da Nafisa ita ta fito daban inji ya Amina sai momy tace haka abin yake ai wani lokaci.
Mun kai wani lokaci muna hira a kansu kafin in mike zuwa cikin dakin in kewaya koda na fito ban koma falon ba wurin su na zauna a daki.
Ya Amina ne ta shigo dakin tana fadin in hada maki tea ki shane ko kunun zaki sha nace bani kunun don yai min dadi sosai.
Tace Adam ya bugo waya kin kewaya nace sai yanzun zai kirani ai nayi fushi wallahi tace ke ko ai ya kirani jiya da muka iso mana.
Muna zancen shi ne wanan matar SJJ ta fado min a rai nayi salati nace kinga na manta da matar mutumin nan tazo nan kafin in haihu kwanaki har taban layin ta tace idan na haihu in sheda mata kinga na manta ban fada mata ba ko.
Tace tazo gidan nan fa nace wallahi tazo har da kudi maigidan ya bayar a bani sai dai ban karbi kudin su ba nace don yaya Adam ne nayi masu hanya.
Tace amma dai Khadija nan don may baki karba ba su wayan nan ai ko nawa ne baki ragesu ba wallahi bacin ribar ma da sukaci dake ai da kin karbi abin ki wallahi.
Nace haba dai ya Amina sai kace ba training din ki ba da su daddy don may zan karbi kudin su haba dai tace kirata don Allah ko don in santa ma don ban santa ba Allah yasa tana kasan ma indai itace bata faye zama nan ba sosai kullun tana waje.
Kunun da ta zuba min nasha sai na dauko wayana na danna kiranta watace ta dauki wayan mun gaisa nake fadin nice sister din matar Adam.
Tace ok wacce muka zo gidan ta da anty ko nace eh anty na kuss ki fada mata na haihu jiya tace masha Allahu anty ko tayi tafiya amma zan kira ta in fada mata insha Allahu.
Mukai sallama bayan tayi min barka muka kashe wayan Altine ta shigo dauke da kwanan abinci ta dire min a gabana sai da naji gaba ya fadi sauko ki ci kada huce nace anty ba yanzu ba yanzun nan nagama shan kunu kinga kofin nan.
Tana kokarin bude kulan ta zuba min abincin tuwon farar shikafa da miyan shuwaka sukayi naga tazuba da yawa na bata raina nace haba anty ina zankai wanan abincin haka.
AA ne ya shigo dakin fuskan dana bata yake kallo Altine na fadin duka zaki cinye shi fa yace bazataci abincin bane ko may naga ta bata fuska ?
Nace haba yaya ya zanyi in cinye wanan abincin data zuba min yace haka kuwa zaki cinyesa duka sai kun kula don bata cin abinci sai kayan kwadai.
Cikin marairaicewa da yanayin shagwaba nace ni dai wallahi ana takura min mafarin a saka mutum yin babban tunbi ke nan.
Yace tunbi kan ai tunda diya biyu suka fito a cikin ki sai kin yi shi in zakici abinci ki sauka ki ci Altine tace kaima baban jegon in dauko ma filet ne a zuba ma yace Altine kamar kin san tun safe ban karya ba wallahi.
Tace kana may haka har wanan lokacin tsohon su bakaci abinci ba ina momy taji dan ta bai karya ba wai har wanan lokacin.
Yace wallahi muna can wurin kai wanan matar asibiti ne ashe a cinya ta kare fa da kuma kafa abindai ba a magana wallahi.
Nace wai garin ya ta fadi ne tayi wanan kariyan haka yace abinne ikon Allah tace wai taga kamar abu ya gitta a gaban ta sai taga duhu bata san lokacin da ta fadi ba.
Altine tace mugun abin su ne ya koma masu balle tagwaye da kofi yace nima dai abinda nayi tunane yanzu ke nan wallahi don yanzun na dawo security ke ban wani abu wai a jikin ta ya fado lokacin da za a dauke ta.
Altine tace kaga abinda nake fada ma jifa muna tsaye dakai kasan kamar an kifa ta a kasa ne yadda ta fadi kofin yaran ne ta gani ba wani abu ba.
A nan zakaci tare da matar ka ko a hada ma naka akawo ma karkuma buzuwan matar ka tace an mata shishigi yace indan ma tace bani zatayi yaushe ma ta zauna gidan balle ta dafa.
Tana can suna zancen wanan matar na barsu can nayi masu abinda zan masu tunda a gidana ta fadi na barsu can.
Yusuf yana tafe yanzu ya dawo zai karaso sai muci daga falo momy ta shigo dauke da yaron yafi fitina sosai tace khadija sai fa kin karawa yaron nan nono yasha don tun dazun yaki shiru.
Na tabe fuska nace momy a bashi ruwa don Allah yace saboda may za a bashi ruwa ko nono sayarwa zakiyi ne ?
Karban yaron yayi daga hannun momy ya dora min a cinya na yana fadin gyara ki bashi ya sha kinji.
Raina bata sosai ya Amina daga inda take zaune tun shigowan shi dakin batai magana ba tace dole sai kin daure kafin su saba don ita kamun nan take jiwa zafi.
Dukawa yayi bai damu da suna dakin ba yana kokarin bude min riga nayi saurin budewa shi ya gyarawa yaron kai ya tallabo shi ya sa mai nonon a baki yadda zai iya kamawa.
Shi kuwa yaron ya cabe ya kama ja ban san lokacin da nace wayyo Allah na ba don zafi cikin tsigar lalashi yace min daure zafin zai bari na dan lokaci ne kawai yana rike da kan yaron ya duka yana kallon yadda yaron ke shan nonon.
Ya samu ya zuka sosai ina faman runtse idanuwa na don zafi da nake ji har cikin raina yana ganin yaron ya kama da kyau ya mike tare da fadin barin dan shiga ciki in fito idan Yusuf ya karaso.
Ya fice daga dakin momy tayi murmushi tace ikon