ba.
Amma duk wani nawa sai da Yusuf yasa ya Amina ta kwatanta mashi suka sani sun nuna masu nine na bada bakin su nemay su.
Sam nan san da hakan ba don ba wanda ya kirani ya fada min ya Aminace tace su kyale ni don ban son zancen aure yanzu.
Su kuma suka dauki maganan ta suka zauna akai ba wanda ya taba nuna min hakan da sukayi sai da muka samu hutu da yake mai dan tsawo ne na yanke shawaran zuwa gida in dan kwana biyu sai inzo kadauna in karasa hutu na can.
Sai da naje gidan su maryam na kwana biyu kamar yadda nayi mata alkawari na wuce zuwa minna tafiyan dare nayi na iso ba wanda ya sani sai da safe aka ganni a garin.
Tunda na dawo ban fita ba ina ta ramuwar barci don karatun da mukasha na jerabawa ranan ina kwance dakina mama ta shigo dakin wurina.
Kusa dani tazo ta zauna haka yasani dagowa daga kwancen da nake tace magana nazo muyi dake khadija.
Da sauri na dago kai ina kallon ta yanayin ta ya nuna min magana ne mai muhinmanci tazo muyi a dakin da ita.
Nace mama wani abune da baki kirani ba kika zo da kan ki tace nan din ma ai bai baci na gyara zama na dakyau ina sauraren ta.
Tace shin khadija tunda kika dawo daddyn ku ya taba maki maganan mutumin dayazo neman auren ki ?
Dago kaina nayi da sauri tare da fadin wani mutumi kuma mama na tambaye ta cikin kura mata ido da son jin wanda yazo bidan aure na ban sani ba.
Tace wani mutum ne daga Abuja ko mutumin kaduna ne ban sani ba ya dai zo nan har can suke gurin kakanin ki ya zagaya.
Da sauri nace mama ni ban turo kowa ba wallahi tace baki turosu ba yaya zasu zo gidan nan in ba ke kika basu baki ba ?
Wallahi mama ban turo kowa ba da maganan aure tace to sunzo sun kuma gana da mahaifin ku akan maganar auren ki dashi.
Lokaci daya zuciyana naji yai min nauyi waye wanan yazo zai mun sheri a gurin iyayyena nake tambayan kai.
A take naji hawaye na fita a idona wani na bin wani nace mama wallahi ni ban turo kowa ba gare ku sheri dai maishi ke so yi min.
Tace ba maganan sheri a cikin aure mudfin kina so shi ni abinda ban so kizo baki son shi ayi maki dole dashi.
Nace wallahi mama ban san kowaye ba yanzu haka ki hawaye wani nabin wani yaki tsaya min a idona.
Tace na fada maki ne don naga kin zo har kinyi kwana ki baki mana maganan ba kuma shi mahaifin ku bai tambayi kan maganan ba.
Don naji tsoron irin abin arzikin da ya shigo muna gidan nan dashi da sunaan sunzo neman izini suna son a basu dama su nemay ki.
Mama wallahi bani na turo su ba tace na sani kuma na fahince yanzu sai ki bari mahaifin ku ya dawo zan tayar da zancen muji shawaran da ya yanke akai tana kaiwa nan ta mike ta fita daga dakin.
Nan ta barni zaune ciki da tunane a raina na wanda yazo gidan mu bada sani na ba koma waye zaiga rashin mutunci a wurina wallahi nace a fili.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Mun shirya tsab don zuwa gidan hajiyan mijin ya Amina idan yaran ta suke zan diba su kafin in koma Abuja ban fada ma anty gidan da zamu tafi ba sai da muka shirya mun fito nake sheda mata inda zamu tafi din.
Taji dadin jin hakan dama tasan ina matukar son yaran nata sosai har cikin raina don ban yarda idan ina nan wani abu ya taba su.
Muna fitowa bakin get din gida ya Amina muka samu motar da zai kai mu har unguwar su hajiyan baban su yasir din.
Sai da muka fito maryam tana ba mai taxi din kudi Yusuf ya faka motar shi a gaban mu kallon mamaki nayi mai don bamu san lokacin da ya biyo bayan mu ba.
Kina mamaki ne yace lokacin da ya karasa fitowa daga cikin motar shi sai alokacin na tuna da zancen dake cina a zuciya.
Bayan mun gaisa ne nake cewa yayana dama ina son ganin ka wallahi yace wani abin ne kanwa ta nace i am sorry to say wallahi ban taba sanin matar ka rasuwa tayi ba sai yanzu dana ji.
Fuska ya dan daure yace wallahi haka ne khadija Aisha ta rasu ta barni da kewan ta a wurin haihuwa Allah ya karbi ranta babban bakin cikina shine ban samu ganawa da Aisha ba tunda na kaita gida haihuwa sai labarin mutuwan ta da ya riske mu lokacin ina waje dani da AA bamu kasan.
Allah yayi mata rahama ya gafarta mata Allah yasa ta huta yayi masu rahama maryam ma takarba da Allah ya jikanta da rahama mukace amin yace ya gode.
Sai dan shiru yabiyo baya sai da ya hade wani miyaun bakin ciki yace dama nima ina son ganin ki shine na biyo ki nan yanzu.
Nace gani ai yayana lafiya dai ko ya gyara tsayuwan shi tare da jingina bayan shi a motar shi yace well maryam ga khadija gaki ina son muyi magana ne na fahinta amma kuma naga kamar ku zo wani wuri ne ko ya tambaya ?
Nace cikin hausa da yake gauraye shiba na gwari ba bana nufawa ba ba kuma hausan yan kaduna ba sai dai idan nayi zaka san may muke nufi don hausa daya ce sai dai daga kara harshe ko tausa shi.
Ba matsala ai kana iya yin maganan ka gidan iyayyen mijin anty na nazo gaida su don yaran ta na nan dukan su a gidan kada na koma ban gansu ba.
Yace ok aiko kin kyauta shiyasa nake son ki wallahi don kin san abinda ya kamata sosai nadan yi murmushin jin yabon da yayi min.
Yace akan maganan ki ne da AA yau da safen nan hajiya mama da mommy sun kirani kan maganan sai dai ban san ra,ayinki ba ke don haka nace su ban lokaci zan ganki kafin in yake maku hukunci akai.
Da sauri nace akwai wani abu a tsakanin mu ne dama daban sani ba murmushi ya dan sake a fuskan shi yace haba haba kanwa kada muyi haka mana dake ke ma kin san akwai shi ai.
No,no kada muyi haka dakai ya Yusuf kai ma kasan babu komai a tsakanin mu sai mutunci don haka don Allah abar zancen nan gaskiya banji dadin, yadda sukai ma zancen wani fahinta ba na daban dan kai ma kasan ba wani abu a tsakani na dashi tun farko har zuwa yanzu sai mutunci.
Kai naga ya girgiza min yace kada ki fadi haka khadija don kowa a nan yasan akwai soyayya a tsakanin ku da AA din daga ni har maryam da kuke tare don may kuma yanzu ana son akai karshen magana zaki fadi haka ?
Ya Yusuf ka taba jin Ya AA ya furta kalman so a gare ni tunda muka hadu ba zanyi deceive din kai na ba ba abinda bashi bane gaskiya ka fada masu ba wanan a tsakani na dashi.
Khadija ya fadin in serious voice na kalle shi yace ke ma kin san AA da shegen girman kan tsiya ba zai taba hurta ma mace wanan kalman ba gaskiya.
Da sauri nace ban mace ya furta ba ya rike abinshi don nima bai min ba bani fatan in auri na miji irin wanan mutum da baisan darajan mace ba sam.
Ya yusuf may yasa kake son in decieven din kaina na kada kaina ina fadin ban taba jin son shi ba wallahi a raina don haka ku daina maganan nan na fada tare da hade hannaye guri daya ina rokon shi.
Kai ya girgiza yace amma idan kin ce haka baki kyauta muna ba khadija don ke ce hope din kowa a yanzu ga AA nace kunyi kuskuren fahintar hakan.
Don ba wanan kun sani a tsakanin mu so ka fitar dasu daga abinda suke tunane na gode yayana a lokacin na fara tafiya bai tsayar dani ba sai cewa da yayi zaku dade anan din ne ko in jiraku na mayar daku gida.
Haba dai katafi kawai abinka don bamu san lokacin da zamu fito ba na bashi amsa haka na ci gaba da tafiya nan na barsu da maryam a gurin tsaye.
Sai dana jirata tazo muka shiga tare da ita ciki da kanin Abban su yasir muka fara haduwa yana ganin mu yace a, a, a yau yau baki muke dasu haka a gidan nan ?
Nayi dan dariya tare da fadin uncle hamza ina kwana yana dariya ya amsa min tare da fadin dan dai yaran ki na gidan nan ne yasa muka ganki da sai ki wuce bamu san kinzo ba.
Murmushi nayi nace kai uncle hamza kana dai son hada mu da hajiya ne amma ai tasan nakan zo gaida ita idan na shigo garin.
Daidai muna zama a falon hajiyan ta fito daga ciki tana magana da nana yar karamar jinkanta yar wurin ya Amina din da ta yaye.
Tana ganin mu tace lale marhabin yau khadija ce a gidan namu kunya ya kamani nace hajiya ai nakanzo wanan karon dai ne na dade ban shigo kaduna bane.
Kin san hali karatun mu ban zuwa kaduna yanzu kamar da can baya ta kai zaune muna gaisawa da ita sai ga yaran sun fito suna gani na sukayo kaina da gudu da murnan su akan ganina.
Maryam dai na zaune gefe tana kallon mu cikin sha, awan mu nan na manta da kowa a falon muna hira da yaran suna zuba min surutu su na yara.
Abin sha irin na sauka ke ta kawo muna kunun aya da zobo mai sayi a ka aje a gaban mu mun dan taba na mike ina fadin barin gyara maki wuri hajiya kafin mu tafi dama nazo gaida kune.
Nan dai maryam ma ta mike muka shiga gyara mata gida dama idan naje gidan haka nake mata don halin girma yanzu hajiyan bata samun gyara wuri yadda ya dace.
Har abincin rana mun hada mata tuwo shikafa da miyar wake sai busashe kifi da mukai amfani dashi wurin hadawa.
Hajiyan ta yaba kwarai da girkin namu tace idan an ganku wa zai dauka kun iya girki haka sai a dauka gayun kawai kuka iya kadai.
Nace hajiya a gida idan naje hutu nike hada ma maman mu abinci har in dawo a gidan muka wuni sai yamma zamu koma after four nan yaran suka lake min zasu bini nima dama ina son zuwa dasu hajiya tace ai dama nasan haka zai faru.
Tunda sun ganki bazasu zauna ba kuma nan dai ta shirya masu kayan su mukai mata sallama muka tafi.
Kafin mu iso gida nana tayi barci a jikina a rugumay da ita na shigo gidan mun samu Abbasu yasir ya dawo ranan a hankali da sallama muka shigo gidan.
Mun gaida shi na nufi kujera na shimfede nana akai fada ya Amina ta fara min wai may yasa na dawo da yaran ranan bata gama hutawa ba.
Dariya daddy su yayi yace kema kin san ba zasu zauna ba can sun ga khadija wuri na samu sai da nakai zaune nace mata ai ba ke zaki kula su ba tunda ina nan.
Tace har kwana nawa zakiyi dazaki ce haka ni wallahi dakin barsu a gurin hajiya da yafi min sauki ban yi magana ba sai kallon maryam da nayi nace akawo maki ruwa ne ki sha ?
Yaya Adam mijin Ya Amina ya kalle ni yace lalle bazan gane khadija ba a hanya wanan irin canzawa a lokaci daya fa kin koma wani classic lady a lokaci daya haka ?
Dan kallon shi nayi cikin zolaya nace Ya Adam har dakai cikin fadan haka don Allah abinda wasu ke fada min yau kaima ka fada min haka ?
Yace wallahi khadija kin canza min ne gabadaya a lokaci daya yana min shakiyanci da zolaya na ya jima zaune muna hira dashi wanda hiran duk na karatun mu ne.
Kafin yace zai shiga gari ya sayo abu yana fita ya Amina tabi bayan shi nida maryam muka kalli juna mukai dariya saboda yadda suke kula junan su gwanin ban sha, awa dasu.
Nace shine kuke son hadani da wani mai tarin iyali haka mutum ko marmari babu wallahi ni bai taba burge ni ba Allah don namiji ba marmari haka ai ba mijin aure bane kema kin sani.
Maryam tace min an fada maki har a gida haka yake da iyalin shi ba marmari waje daine yake haka a gimtse kulun.
Amma ai namiji bai gimtsewa iyalin shi ko yau she ke dai sai dai idan baki son zama da kishiya nace ba kuma zan zauna da ita ba don uwata da yayyi na duk ba mai kishiya cikin su.
Baki ta tabe min tace sai akace maki abin na gado ne kema bazaki zauna da ita ba ko ai suma dace sukayi baki san gaba mai zai faru dasu ba.
Ya Amina na shigowa nace au fatan da kike masu ke nan ya Amina kin ji wai ya Adam zai kara mata wata rana da saurin maryam.tace kada ki mun sheri wurin anty fa.
Nan ta koro mata kan maganan tayi dariya tana zama ta kalle ni tace dama ina son magana dake ai dazu bayan fitan ku har gidan nan mommy take akan zancen ki da Abdulsamad .
Da sauri nace wani zance kuma nifa ins ganin gobe zan bar garin nan ma don ban son abinda zai kawo wani fitina a tsakanin ku ana zaune kalau.
Ta sauke ajiyan zuciya tace nima abinda na fada ma mommy ke nan wallahi ga matar shi Fati muna mutunci da ita za a dauko wanan maganan kuma yanzu don Allah a bar zancen ga mutunci da kikace kawai.
Ya Amina ni abin na ban mamaki fa mutumin dax bai taba cewa yana sona ba bakina da nashi shine za a kawo wanan zancen idan hakane ko mutuncin abari ma shiya fi.
Kafin tayi magana wayan ta yai kara jin sunan mommy data ambata yasa ni kallon ta da sauri naji tana fadin eh ta dawo gamu zaune a tare ma.
Naga ta duban waya ta aje batace dani komai ba nima ban tambaye ta may tace ba mukaci gaba da maganan mu maryam dai tana zaune tana sauraren mu.
Bamu jima ba mukaji sallaman mummy a kofa ta shigowa duk na rude a lokaci daya ashe ba ita kadai bane tare suke da hajiya mama suka shigo da sallaman su muka karba masu.
Mikewa nayi zan shige ciki bayan mun gama gaidasu tun kan su zauna ina kuma zaki dawo ki zaune ai gurin ki muka zo inji mommy.
Simi simi na dawo na zauna a kasa wanan karon tare da dukar da kaina kasan ina sauraren su mommy taci gaba da magana .
Khadija ta ambaci sunana hakan baisa na iya dago kai na kalle ta ba sai dan amsan wan danayi ciki ciki tace may ke faruwa ne tsakanin ki da yayan ku mukaji amsa sabanin wanda muke tsamani da farko ?
Shiru nayi sai kara dukar da kaina kasa danayi tace khadija iddan wani abune kada kiji nauyi ko kunya ki fada muna ra,ayin ki tunda kikaga mun taso mun zo da kan mu kin san ba maganan wasa muka zo dashi ba nan .
Kaina na kasa nauyi da kunya ya rufe ni a lokacin ban san yadda zan daga kaina basu amsa ba muryan hajiya mama naji tana fadin ki saki jiki kiyi magana ni a matsayin yar ciki na nake daukan ki khadija magana ce ta fahinta don shi mun kasa gane inda ya dosa ga maganar shi.
Kakakarakaka ga wurin fadin magana sai dai babu hali a gare ni mommy tace shi ya nuna muna da muka tuntube shi kamar kun gama tsaida magana a tsakanin ku dashi wanda dama haka mu muke fatan muji.
Yau yafito da kan shi ya nuna ga abinda yake so a ranshi kin san babangida mutum ne mai murdaden hali da ba a gane kan shi a lokaci daya idan bai ra,ayin abu bai ma abin kallon muhinmaci sai yaga dama.
Muna farin ciki ga abinda muke ji sai ga Yusuf dazu yazo muna da wani magana wanda bamu fahinci may yake nufi da amsar ki ba don haka muke son ji daga bakin ki.
Don idan kin tafi yanzu bamu san lokacin da zaki dawo nan ba maza don yanzu baki faye shigowa garin ba kai tsaye kamar a da da a nan kike yawan hutunki.
A hankali na dago kai na sai na dukar nace mommy ni ba soyayya muke da yaya Abdulsamad ba don bai taba cewa yana sona ba nima haka ban taba jin son shi ba sune dai suke fahintar haka a tsakanin mu.
Ashe khadija muryan hajiya mama ta katse ni tace soyayya kuma wanda yusuf ya fada muna a tsakanin ku idan yafi haka ai ya baci .
Shi