raina ai gaskiya kika fada bai dace ba nima na san da hakan.
Watau khadija mutumin naki yana da matsala ne a gidan shi wallahi wana abin ya dade yana damun mu muma.
Ace mutum kamar wanan ba abinda ya nema ya rasa a duniya amma cin abincin gidan shi ya gagare shi sai na waje ?
Shiru nayi ina kallon shi yace ya zama dole mu samu mafita akan wanan matsala kada abin yazo yai yawa na yaushe kuma ?
Ko sau daya aka ganka a waje kana magidanci kana cin abincin sayarwa ai girma ya fadi ko a wurin mutane sai dai a gyara don gaba.
Yarinya kamar tsuhuwa wurin iya tsara magana haka ashe shiya take karatun lauya ya fada a ranshi.
Khadija ni na rasa samun mafita ka wanan matsalar wallahi don ko nafisa ba gyarawa zatayi ba tunda in ita batayi ba bata bari kuma ya dauko yar aiki irin namu na nan wace ta iya saidai yan uwan ta zasuyi.
Wanan kuma shi ya daukar mata don shi yaga zai iya zama a haka don may ba zai dawo da matar shi hala tsoron ta yake yi ?
Sai lokacin ya cire hannun shi da ke saman kanshi yace tsoro tsoron wa nace ka alamu nan sun nuna kuwa buzuwa ta shiga gaban ka.
Ke fa baki da kunya din kikan wuce limit din ki nayi saurin fadin wurin fadin gaskiya ba haka nan Ya Amina na ke fada min wai banda tsoron fadin magana ga kowa.
Ni kuma naga idan gaskiya tazo a fadeta komai dacin ta kuwa dayake baki da kunya ba zaki iya fadin maganan da wani bai iya fadi ai .
Ciki ciki nace a nan zaka zare idanu agida ko a zare maka idanu matsorancin banza kawai.
Ban yi aune ba na gan shi a gaba na waye matsoraci yace cikin zare min idanu Yusuf nace ni gaskiya na fada ai Yusuf ne yace daga fadin gaskiya sai leifi ?
Laifin ka ne mana kaima ka sani ai in ba tsoro ba ka dauki mataki mana a kan haka mugani nace aishi na gani walla, , ,
Hannu shi yake ya kamo bakina yana fafin wanan wanan baki sai nayi maganin shi wataran zai shiga hankalin shi.
Don Allah ka bari bana son namiji yana taba min jiki wallahi kin dauke ni dan iska ke nan ashe nace bai da kyau yin haka ka sani.
Yusuf yana dariya yace ina zuwa ya barmu a gurin zama yayi a kusa dani yana fadin bari ma yau in nuna maki dan iskan nake.
Tsoro ne ya kamani yadda ya zauna a kusa dani din nace may ye haka malam ?
Malama iskancin nake son nuna maki kalan tawa ki gani ya rankwafo inda fuskana yake har muna iya jin hucin numfashin juna a lokacin.
Cikin sanyi murya nace ka dai san hakan bai dace ba a addinance ai kin san ban san addini ba ni yace wanan ba gaskiya bane don gidan ku kaf hazifai ne kuna karatun addini tun kuna kanana .
Sai naga ya maida kanshi saman kujera yana zaune kamar yadda yake bai daga kusa dani ba yace khadija ina cikin matsala wallahi ina son in gyagyara wasu abubuwan da suka baci min a yanzu.
But i don't know how to make things easy ?
Tausayi ya bani nace ka yawai ta addua da sadaka ga dukan al,umurorin ka sai kaga Allah ya kawo maka mafita a ciki.
Sai ya mike daga hannun kujeran yana fadi n muje in mayar dake yamma ya fara yanzu saurin mike wa nayi ya kira yusuf a waya yana fadin mun tafi.
Yafito da sauri tare da fadin har kun gama hiran ta masoyana zaku tafi kai haba yayana firan masoya kuma a haka ?
Har ya fara tafiya shi muka mara mai baya yusuf ya bani hakkuri akan bai bani komai ba gashi na kawo mai ziyara.
Ba koma nace muka kama hanya na tsaye sai da yaga wucewar mune ya sauke murmushi tare da fadin ikon Allah komai yana da sanadin shi.
Wanan karamar yarinya kuma Allah ya jefo a rayuwan Abdulsamad mutumin da magana da mace a wurin shi aiki
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Gidan ya nufa kai tsaye tare da sayayyan da yayiwa bakin shi na abubuwan bukatun su ya nufi part din fati dashi.
Babu kowa a falon sai yake mamaki yau ina mutanen gidan su shiga haka duk da basu ciki hakan bai hana falon nashi jin tashin yanayin da jikin su ke dashi ba a falon.
Hakana har ya isa gurin su mommy zuciyar shi cike da tambaya da tunane ya samay su a zaune suna hira yarinyar da suka zo da ita tana cin abinci.
Sai da ya aje kayan a gaban mommy ya zauna lokacin ya fara gaida su suna kara mashi yaya sula samay su yace mummy lafiya sai hamdala.
Nan dai ya zauna dasu suka dan taba hira har wani lokaci sai ga Nafisa ta biyu shi har dakin dags kofa ta tsaya ta kira sunan shi.
Bayan ya amsa kamar ba zai tashi ba sai kuma ya mike ya tafi sude su mommy kala basu ce ba suna kallon ikon Allah kawai.
Ya fito ya samay ta zaune falo tana ganin shi ta mike da kyat ta fara fadin muje sama ina da magana dakai ne ta juya ta fara tafiya yana biye da ita a bayan shi.
Ko da suka hau sama bai tsaya bin ta nata ba don har ta juyo da nufin tayi mai abinda ta kulla a ranta sai hango shi tayi yana bude kofan dakin shi kai tsaye.
Ido ta bishi dashi tana fadin samad maganar nakira ka muyi zaka shige kuma yace baki san dakina bane ko a kan hanya kike son maganan da ni ?
Sai lokacin ta dan juya ta dubu wurin da suke tsaye din sai kuma tayi shiru don ita bata ga komai a nan ba don sunyi magana ai gidan su ne.
Dakin ta samay shi tsaye yana rage kaya a jikin shi ta fado dakin babu ko sallama ya dan juyo ta kalle ta ya kawar da kanshi gefe yaci gaba da abinda yake yi.
Bayan shi ta tsaya tana kama baya tare da fadin Samad wai may wanan mutane suka zo yi ne a gidan nan ?
Yaushe zasu koma don ban son sa ido da takura a gida na sai da ya gama cire kayan ya rage daga shi sai boxes a jikin shi yace cikin duban ta ina fatan wa yan nan mutanen da nace su bar min gida na yau sun bari ?
Tsaye tayi sororo tans kallon shi ta shige ban daki ya barta a wuri tsaye tana mamakin yau wai itace samad ke ba amsa haka daidai da nata tambayan.
Da dane da yanzu ya fara matairaice mata yana bata hakkuri akan zuwan su mommy din itako tana cika tana batsewa tare da kafa mashi sharudda dole ya bi ya juye mata makudden kudi yana lalashin ta.
Yanzu ko da yake kokarin kwato kanshi daga sherin ta sai take ganin wasu ne suke kokarin bata mata aikin ta ta baya.
Tunda ya shiga bayin taja kafanta ta zuwa bakin gadon dakin ta zauna tare da tin tagumi don ta fahinci ba maganar da zatai sanyi bane dashi sai da yanzu cikas din ta shine cikin da ke jikin ta don bai bari tayi yadda take so sam.
Da mamaki samun ta wurin yake kallon ta da ya fito daga ban dakin don yayi zaton tuni ta tafi dakin ta ta kwanta sai ganin ta yayi zaune cikin damuwa.
Samad wai may kake nufi danine yanzu da ke tsiro da wasu halaiya na daban da ban san ka da su ba a da don may zakace sai na sallami yan uwa na gidan nan ?
Yace saboda ba gidan yar uwasu bace su bari idan kin kaiga naki gidan sai su kwaso gaba dayan su su dawo inda kike ba dai nan gida na ba.
Da bakin ka kake fada min haka Samad yaushe ka tashi ga samad din da na sani mai so na da tausayina da son duk wani abinda nake so a rayuwa na.
Da ke nan Nafisa a lokacin da ban fahinci koke wacece ba amma yanzu da na fahinta yasa kike ganin sauyi daga gare ni haka .
Ban taba yarda da halin ki ba sai yau Nafisa da har mahaifa na zasu zo gida na ki tsare ni kina tambaya na wai yaushe ne zasu koma ?
Alhalin ke ga yan uwan ki nan a gidan sun hana ni shakat dani da gida na ba daman in huta in samu natsuwa a ciki ga dan banzan kazanta da kuka bata min gida dashi ya koma wani iri.
Samad mune kazamai dani da yan uwana kake nufi ko may yanzu ne kasan da kazantan mu din ko may yace da na dauka idan idon ki ya bude zaki daina Nafisa ashe abin ba haka yake ba a gun ki.
Komai ai zaka iya fada a kaina tunda kaga yanzu banda moriya a gareka yadda kake so a da, da kake yawan naci a kaina da banda komai.
Wanan ne tunanen ki ashe kike min yadda kikaga dama bakin ce in dauki matakin da zan dauka ki gani ba ranan to matakin ne yanzu na fara daukar wa kaina.
Su mommy kuma da kika gani nan sun zo gidan nan ke nan harsai kin haihu kinyi arbain zasu koma gida.
Ido ta zaro waje tace ina zasu zauna din yace a inda kika gan su and bari kiji idan naji wani rashin mutunci ya fito daga gare ki zan baki mamaki sosai a gidan nan.
Mamaki ne ko rudewa ya kamata a wanan daren na Abdulsamad wanda take gani karfin haline irin nashi daya iya fada mata wanan magana haka babu ko dar a idon shi.
Bai kara kulata ba ya shiga gyaran jikin shi ya barta zaune a gurin cike da mamakin shi fita yayi ya duba ko an rufe gidan ya samu ko ba a rufe ba shi da kansa yaja kofa ya rufe yasa mashi key.
Washegari mommy da wanan yarinyar da suka zo mai suna Aisha bayan sunyi sallah basu kara kwantawa ba suka fito falon gidan suka gyara tas ta saka turaren wuta dana tsunke a ko ina na gidan.
Take gidan ya dauki kamshi da sanyin Ac kitchen suka koma sai da gaban mommy ya fadi ganin yadda kitchen din yake kamar ba mata ke amfani dashi ba.
Nan kuma suka shiga aiki a kitchen din gyara can gyara nan take kitchen din ya koma na macen da tasan kan ta girki suka dora na abinda zasu ci a gidan.
Sai da suka kusa gamawa ne matan dake gidan jin kamshin girki yasa suka fara fitowa daga dakunan kwanan su daya bayan daya.
Suna lekawa kitchen din suna masu ina kwana don tsaron mutuncin su ga maigidan.
Bayan sun gama girki mommy ta zuba masu nasu taba Aisha nasu ta shige masu dashi ciki tabar saura da mutanen dake gidan zasu ci.
Yanyala ce ta shiga dakin Nafisa take kwarmata mata abinda ke faruwa a gidan da fushi Nafisa ta sauko kasa zuwa kitchen din don taga abinda ke wakana mata a gida.
Komai na gidan neat yake yau ya samu gyaran da ya dace daga bakin su ta shiga kitchen din taga yadda suka gyara komai suka jera shi a inda ya dace.
Fita tayi zuwa sama ta samu Abdulsamad ya gama shirin fita tsab ta fado dakin da fushi tana fadin ban san may kuke nufi ba kaida wa yanda kake fadi wai iyayyen ka ne ?
Ya juyo yana fafin kamar ya fa tace don may zasu zo min gida suna min abinda suka ga dama a ciki suna matsayin baki a gare ni.
May sukai maki ya tambaya cikin bata lokacin shi yana sauraren amsa daga bakin ta tace a hasale yanzu ya dace ace sun shiga kitchen sunyi abinda suke so haka ?
Sai da ya dubeta dakyau yace kada ki manta gidan dan su suka zo suna da ikon yin komai da suke so a gidan nan.
Dansu ko dan ta da sauri ya kalleta yace may kike nufi da wanan maganan naki tace dashi gani nayi itama arziki tazo ci kawai a gidan nan do ba itace ta haife ka ba.
Au dama wanan ne tunanen ki ke nan dama raba daya biyu a gida to bari kiji mommy tankar hajiya mu take gare ni don matar mahaifina ne ita ma kamar hajiyan mu don haka nake daukan su daya.
Yanzu ke baki jin kunya baki tashi kin tare su da abin karyawa ba sun tashi sunyiwa kansu har kike fadan akan haka don baki da kunya ?
Tace ba zan yarda da wanan wuce wurin ba irin nata dama na dade da sanin halin ta tun shigowa na cikin ku do haka kayi saurin taka mata burki a hakan.
You're very stupid ya fada da karfi sai data razana yace kada ki fara kice zaki saka masu ido a gidan nan ko bayan fitana ne don zan saba maki sosai kuwa.
Fita yayi daga dakin ya barta cike da mamaki tana ganin wankin hula zai kai ta dare wai itace samad din ta keyi wa abubuwa haka yanzu.
Lalai duniya na shirin juya mata baya idan batayi da gaske ba tin yanzu dakin ta ta koma ta jawo wayan ta cikin tashin hankali take fada wa madam abinda ke faru da ita.
Sai da ta gama sauraron ta tace Nafisa sai kin hada da hakkuri fa yanzu don ni a gani na akwai ida aiki ki ya samu matsala ko kuma don cikin dake jikin ki ne asiri ya daina kama mijin ki yanzu.
Ina cikin wani hali walahi haka na nufin yan uwan samad zasu dawo gare shi suyi yadda suke so gidan nan ke nan wanda ba zan taba yarda ba sai dai duk abinda zai faru sai dai ta faru.
Madam tace Nafisa kibi sannu fa ba kullun ne ya zama dole mutum yayi nasara ga abinda yake so ba kowa kika gani sai yanayi yana hadawa da hakkuri da kuma kissa bawai ga magani kawai muka dogara ba.
Madam ni abin ne yazo min a bazata wallahi tace yanzun dai ki kwantar da hankalin ki mubi komai a sannu.
Tace na ji amma duk da haka zan nuna masu gidana suka zo ba zan bari suyi min abu gaba gadi ba haka tace kiyi a sannu dai na fada maki.
Shiko yana fita tun a falo ya fara ganin sauyin da gidan nashi ya samu da zuwan su mommy din ga gida ya koma neat a lokaci daya a falo ya hango su hadiye suna kuskus a cikin yare suna ganin shi suka shiga gaida shi.
Fuska a daure take amsa masu ya wuce part din su mommy din wanda anan fati da take zaune da yaran ta ganin haka yasa ya tuna da abubuwa da dama na rayuwan su a baya a gidan.
Kagin zuwa yanzu da komai ya hargitse mashi haka wanda kan shi yanzu ya dorawa laifin kasancewar haka kamar yadda na fada mai.
Ya samu su mommy sun yi wanka suna karyawa a cikin tsanaki ya shigo da sallama ya gaidasu tare da masu ya gajiyan hanya.
Mommy tace gajiya ai yabi lafiya don mun zama yan gari yanzu ko yace mommy duk ku kukai wanan gyaran haka a gidan nan ?
Tace ba dole ba babangida gida ya koma kamar ba mata a cikin sa kasan mu mun saba mijin mu baya son ganin kazanta ko kadan.
Iya bawa tace mai ni ina mamaki gida da mata haka ace bai samun gyaran da yadace mace ta yi a gidan ta wanan matar taka akwai bakin son jiki ne da ita.
Ciki ai bai hana ka gyara muhalin ka sai dai dama idan gyaran bai damay ka ba can amma yaushe ne mace kirki zata bar gidan ta haka ?
Mommy tace ga abin kari can a kitchen idan ta fito sai ta raba maku ka karya kafin ka fita yace mommy zuba min zanci anan gurin ku don bata fito ba ko ina sauri ne.
Anan ya zauna ya karya tare dasu yana mai jin dadi a ranshi yaushe rabon da ya karya a gidan shi haka cikin dadin rai.
Bayan ya gama yayi masu sallama tare da tambayan ko akwai wani abinda suke bukata a gidan ya sayo masu idan ya fita.
Mommy tace sai kayan kitchen din da taga sun soma lalacewa saboda rashin amfani dasu da ba a yi akai akai yanzu dole a sayo wasu yaje matar shi tai mashi lissafi don gudun su shiga mata hakkin ta.
Bai koma takan Nafisa ba ya fice gidan inda ya samu Sani driver yana jiran shi a waje suka dauki hanyar zuwa