yau kada kiji nauyi ko kunya na duk abinda ya shige maki a duhu ba sai kin kira gida kin tada masu da hankali ba ki tuntube ni nan kinji na fada maki ko.
Kai na gyada mata tace akwai abubuwan da nima zan hada maki a nan da zakije kiyi amfani dasu idan ya dawo zata sha mamakin ki da yardan Allah.
Don irin su nasan yanzu ta shirya sosai ma dawowan shi ai irin mazan ku mace bata shiga gidan su haka kai tsaye yanzu sai an shirya ta kima godema Allah don kila kina da tsari ne a jikin ki da har kike iya tsayawa ki mayar mata da amsa kai tsaye.
Wallahi da watace ai wane ke dasu madam fa take hurda a kasan nan wanan kungiyar tasu ko mutum da ransa akace zasu iya birnewa ba abin mamaki bane gare su don tsafin su.
In Allah ya yarda tama zasu barki mu zuba dani da shegu ai sun sani na san su ba yau ba ko wani kallon gani gani tayi maki kada kiji nauyi ko kunya kirani ki fada min karta san kar dani dasu.
Jin ta kawai nakeyi ban iya yin magana ba don mamaki nake na yadda mata a wanan zamanin suka dauki yin asiri kamar wani ibada can gare su.
Kamar tasan abinda nake tunane a raina tace yanzu idan kina son zaman dakin auren ki sai da yan dabaru wallahi don da kinyi sake yanzu wace ta iya zata zo ta kwace maki maji kina ji kina gani ba yadda za,kiyi babban abin ke dai kawai ki dage da addu,a sosai da zan baki da kuma yawaita sadaka ga mabukata da dai sauran aiyukan Allah da zasu iya tsare ki daga duk wani abin ki.
Nasan abune mai wuya ki iya yin su anan to zaki iya bada kudi gida ga wanda kika yadda dashi a dinga maki wa yan nan abubuwan a saukake.
Na gode naji bakina yana furta mata tare da dan marairaice da zama a gaban manya tana mikewa take fadin bari ma in tashi don kila ba lalai bane ku dawo ta nan din don naji kunce gurin gyaran jiki zaku tafi.
Wardrobe din kayan ta ta bude tayi tone tone a ciki tare da fito da wani jakka ta dawo ta zauna tana fadin ba fa a wanan kadai zaki dogara ba khadija.
Ya zama dole yanzu ki nuna ma mijin ku kin fi kowa damuwa da damuwan shi kallon ta nayi don son karin bayani tace eh na farko shine ki kula da kulawan shi kin dai san abinda maza suka fiso gun matan su.
To kiyi kokari ki fahinci may ye weak din ita wanan matar a gurin shi sai kiyi kokari ke kuma ki toshe girin da halin ki na gari da zai sa yaji ba wata sai ke a gare shi.
Ko akwai asirin wani lokaci har da sakacin mu na mata hakan ke yawan faruwa ga mace cin shi shan shi fitar shi da uwa uba kwanciyan ku ya kasance ke naki sallon yazo a daban gare shi.
Maryam da tai kasake tana sauraren mu tace Allah yasa tayi kin ganta nan anty ba abinda ban lurar da ita ba akai.
Anty tace rufa min baki ai duk kun ne kema ba a garin sakacin ki kika bari bayaleraba ta kwace maki mijin da tun kuna yara kuke tare ba.
Kinji khadija don Allah badon niba kiyi kokari ki gyara auren ki idan ya dawo inji wayan alheri bana na kasa anty ba don wallahi bani shiri da macen da ke da sanyi ga mijin ta .
Dariya nayi lokacin da take magana ina jin wani irin nadama na shiga raina yanzun kan na shirya yaki akan mijina ta kowani hali yazo min.
Ba wasu abubuwa ne masu yawa ba sai dai ta fada min abinda ta ban shu,umai ne a gurin aiki da kariya ga jikin mutum.
Dan haka nayi mata godiya sosai tare da fadin insha Allahu anty zanyi duk yadda kika umurce ni dayi din zan kuma zo maki da kyakyawan labari in Allah ya yarda.
Tace sai kin jajirce sosai don akwai yaki babba a gare ki idan buzuwa nan ta fahinci mijin ki ya mayar da hankali a gare ki yanzu don haka banda sakaci da addu,a ko yaushe.
Nace insha Allahu anty na gode na saka abubuwan a jakkana mukai sallama da ita muka fito zuwa wurin gyaran jikin.
Daga kaina jikina har zuwa kafafuwana sai da suka koma sol don gyaran da suka samu maryam da yan saloon din sai faman wasani suke yi.
Mun gama muka dawo gida da yamma lis tun a waje muka sayo abinda zamu ci mu kwanta don ma Friday duk kan mu ba mu shiga school ranan.
Ba wani magana kai tsaye wurin na muka nufa yatin da wa yanda muka sama a folon suka biyo mu da ido caaa a kan mu.
Maryam ne ke rada min cewa suma shegu sunga canji yau gare ki dama ko yaushe haka kike wanan gyaran jikin kina dada ruda yar iskan buzuwan nan da bata iya gyara ba kullun cikin shadda doga ga zani.
Na shiga bayan na bude part din ina fadin ke maryam banda kishi wallahi kin san haka shigarsu take shada suka ba amana a kasan su sosai.
Tace yanzu wake ta shada komai kwalliyan shi ke nifa bakiga haushin da kika bani ba dakice masa baki son lefen da zai maki baki san irin hasaran da kika tabka ba wallahi.
Nace shima baida niyar yi don kada ran matar shi ya baci ne kinji rabu da dan rainin wayo kawai tace dani Allah khadi kin ki bada hadin kai ne da ba karamin abu zaki tara a wurin shi ba.
Tsuki naja nace mata ke wanan ya dama don ni abinshi baya gaba na rokona Allah shine ya barni in aiki in more ma kararuna don naji ya fara fadin ko nayi karatun ba aiki zai barni nayi ba.
Aa ya dai fada ne kawai amma aikin ku ai yana da kyau sosai wallahi karatun ne naku kawai da wahala kamar na likita.
Can falo kuma gulma aka kaiwa Nafisa na yadda na gyara jikina kwal dani ta tabe baki tana fadin duk ga banza don iya karta da miji sai gani sai hange.
Don ba karamin shiri nayi masu ba wanan karon in batai hankali ba gidan ma gaba daya sai ta barshi shegiya taurin tsiyace gare ta inayi kamar bana yi a kan ta.
Sai naga zancin ma nasara sai inga abu ya juye sun koma daran da miji kamar mai iraizai akai yanyala tace wanan wa yasani ko tana dasu ne don kyaunta itama yayi yawa wallahi.
Wani kallo ta watsa ma yanyala din don taki jinin taji wani ya furta wai nima ina da kyau a gaban ta ita abinda ta dauko sune kawai kyawawan mata a duniya.
Da sauri yanyala ta gyara zancenta don ganin ran uwargijiyar tasu ya baci ga maganan ta tace komai kyaunta ai a gaban ki mumuna take don kin dara ta ga komai wallahi ina ma za a hada tsarin ku da ita.
Bata ganni ba taso ta gannin din taga abinda su yanyala ke ta yabo a gurina tace yanzu shigiya na san ta hau akan zancen cikin nan dake jikina.
Da nayi wauta don na tashi zubar da shege ne don ban yarda in tsufa yanzu kan haihuwa madam ce ta kawo shawaran na barshi ko don amaryan nan na samu makami a kanta.
Waahe gari karfe shidda na safiyan jumma,a ya iso gidan lokacin muna kwance don ba zamu shiga school ba a ranan.
Mun sakata muna barcin mu tun bayan da muka tashi mukai sallah muka koma gado ni a kasa ma nake kwance a inda na idar da sallah.
Bugun kofan da akeyi ne ya sani tashi a gigice ina kallon lokaci tare da mamaki a iya sani na ko zamu kai wata daya bamu bude dakin ba ba mai buga muna shi a wanan lokacin.
Jin dukan kofan yayi yawa na mike ina saye a cikin bakar doguwan rigar da na saka jiya zuwa sallon da a suba da zanyi sallah na dauko shi na kara sakawa a jikina don nasan baida matsalar komai.
Fuska a daure na bude kofan cikin hasala tare da shirin taron abinda akazo min dashi tunda farar safiyan nan haka.
Shine a tsaye a bakin kofa yana saye da rigar sanyi a jikin shi tare da zura hannayen shi a aljihun wandon shi yana min wani irin kallo daga inda yake dan diriricewa nayi don banyi expectig din ganin shi a wanan lokacin ba.
Ganin kallon mamakin da nake mashi ya dan sake murmushi bansan lokacin da nace mashi sannu da zuwa ba.
Tsaye yake har lokacin yadda yake yana kallona tare da fadin irin taron da zaki min ke nan a kunyace nace wani irin taro kake so kuma hannayen shi ya ware min tare da fadin come on my friend give a hug cikin wani tako na kai gare shi tare da shigewa jikin shi ya mayar da hannayen shi ya dora a jikina yana maida numfashi.
Wani irin abune ya ziyarci jikina kamar shock a lokacin nima numfashin nake saukewa jinayi yana rada min kiyi a hankali fa kin san amare tsotsayi gare ku.
Nace amare ai suna inda suke dashi zaka fara kuma ko ya kara matse ni a jikin shi yace au daga fadin gaskiya kuma kokarin jayewa nayi daga jikin shi amma sai naji ya kara matse ni gam a jikin shi a hankali na ce mai kafa san maryam tana nan.
And so what idan tana nan zata hanani rungumar matana ne komai maryam kuma ba ruwan ta kin sani to nidai sake ni tarbon ya isa hakana nace tare da kara kokarin zare jikina daga nashi.
Khadija kina da tausayi kuwa kwana nawa ban ji kamshin ki ba yanzu kuma shine zaki min rowar shakar abina halin maza dai wa ya sani ko kana can da wace tafi mu kamshin bamu sani ba
Murmushin nan nashi naji yayi tare da sakeni yana fadin wanan kin san ba halina bane don da akan ki zan fara tunda ke kika fara koya min soyayya.
Baya naja na fara tafiya tare da fadin wani sabon magana ni din nan har yaushe na shiga rayuwan ka da zaka fadi haka yace tun a ranan da na fara ganin ki falon hajiyan mu ai kika so ki bata ni.
Dariya abin yaso bani sai dai na kumay dariyan a cikin raina falo muka iso ya zauna saman kujare da kyat yana fadin kiramin maryam mu gaisa nace barci takeyi yanzu nima shi nake ka tasheni.
Yau baku shiga school din ne ya tambaya cikin kafe da idanuwan shi nace yau muna up dukan mu sai dai gobe ita ta dan shiga.
Zama nayi tare da fadin kun dawo lafiya yaya hanya yaya jamma,an can yace suna gaida da ku cikin wani irin kasalalen murya tare da fadin ina son in watsa ruwa in samu abinda naci tun two na ranan jiya rabon da in saka wani abu a cikina.
May zakaci yanzu na tambaye shi yace duk abinda ya sauwaka zanci don yunwa nake ji bansan wanda zai bani abinci ba a cikin ku.
Shiru nayi ina kallon shi tare da fadin kada nayi ma wani abu yanzu ya zama laifi a gare ni kuma don abin laifi bai wuya a gidan nan.
Don kin tare ni da abinci kuma sai ya zama laifi tunda ba bani za ayi ba idan baki ba madin sai dai in zauna da yunwar hakana.
Nace to bani yan mintina kafin kafito wanka in hada maka amma sai dai in a nan zakaci don banson abinda zai iya kawo rigima daga dawowan ka yace ba matsala indan har zan samu barin je in watso ruwa in fito kafin nan kila maryam ta tashi.
Fita yayi da mamakin sauyin da ya gani a fuskana a tunanen shi baiyi zaton samun taro haka a wurina ba.
Sai gashi yaga sauyin da bai tsamana ba ya samu a tare dani a dan lokaci kadan yaga gaba daya na sauya mashi ga komai .
Wanda ganin nawa ya kara sashi a wani hali da nauyina da kunya kuma na yadda ya kasa cika min alkawarin aure a kaina.
Yasan ya rageni da abubuwa da dama da suka shafi aure wanda daga cikin babban abin da yafi daga mai hankali shine raya sunna ma,aiki da ya kasa yi min.
Kuma ban taba nuna bacin raina ga hakan da ya kasa aiwatar min ba bai taba ganin wani akasin kan hakan ba kodai yarinyar nan ta gane halin da nake ciki ne da ita.
Dakina shiga inda na samu maryam a zaune tana ganina tace sai naji kamar muryan mijin ki khadija nace ba tare dana kalle ta ba shine ya dawo.
Tafiyan dare sukayi ke nan ta fada nace lalai kan tunda kika ganshi yanzu ai kema kin sani yazo min wai yana jin yunwa ne in sama mashi abinda yaci tin jiya rabon shi da abinci.
Tace yi maza ki sama mashi barin tashi mu shiga kitchen din don kiyi sauri ta fada tana mikewa daga inda take zaune a saman gadon.
Kitchen muka nufa a tare muna shiga nace mata ni wallahi ban ma san abinda zan girka mai ba a yanzu don yace tun two na ranan jiya rabin da yaci wani abu.
A, a dole zakiyi mai wani abu mai dan ruwa da zai kama mai ciki don yanzu ba zai iya cin abu mai nauyi ba ke nan nace may zanyi to ?
Tace ki dama orth sai ferfesun mai dan kamshin kayan yaji don cikin shi ya bude ina ga zai ji dadin hakan ai.
Nace ni ban ma san abinda yafi so da safe ba irin haka bari dai muyi din ko zai so shi nan muka shiga kiciniyar hada abinda mukai niyar yi mashi din.
Kafin wani lokaci mun hada tace jeki wanka sai in karasa kafin nan kin shirya taron sa kada ya dawo ya kara samun ki ba shiri.
Na dan dauki lokaci a bandakin na fito ina shafa mai saiga maryam din ta shigo tana fadin ta kammala komai in gama in kai mai nace ai a nan zaici don gudun fitinan wanan matar tashi.
Tace a,a ita batayi ba kuma anyi mai tace zatayi fitina a ka ida ma idan bakece zaki karbi girki ba yau ki kwana dashi to yazama dole kece dashi har zuwa yamma.
Nace su ka,ida suke bi kedai kawai ayi shani maryam wai an cuci na kauye duk da hakan mudin ta gashi nasan akwai rigima wallahi.
Tace wani rigima zatayi kuma ga yadda abu yake don nasan da wuya ta bar maki shi ya kwana a wurin ki gaskiya yana da wuya nace mata.
Na sake cewa ai barta kin kawo min point idan zatai masifan ta ga wanan maganan naki zan dogara don wallahi yanzu kika fahintar dani na tuna haka din ne.
Shiryawa nayi cikin wasu lace brown dinkin buje da riga kayan sun matukar karban jikina sosai maryam tana gefe tana kara gyara min inda baiyi ba tace barin je in wanka in je gida in karbo maki abinda anty tace zata ba da sai dai kafin in je barin dan tuntube ta a waya muji ta kirata tana fada mata dawowan shi tare da tambayanta ko abinda tace din ya samu tace tazo ta karba jiya da dare aka kawo mata abin.
Har maryam ta fito ta shirya zata fita a lokacin ya shigo part din saye da wandon jeans baki da rigar t-shirts ja mai guntun hannu fuskan shi dauke da annuri askin da yayi a can ya fitar mai da kurciyar shi a fili.
Ganin maryan yasa ya dan sake murmushi tare da fadin a maryam kin tashi ashe mun samay ku lafiya itama yi mashi sannu da zuwa tayi.
Bayan sun gaisa na ya fara mata godiya tace ba komai wallahi tace dani tana zuwa zata fita yace maryam ina kuma zaki tace zan dan karbo abune nan in dawo yanzu.
Adawo lafiya yai mata tare da mayar da hankalin shi a kaina yana fadin masha Allah gaskiya nafi kowa more mata a garin nan irin wanan kwalliyan haka duk ni akaiwa shi.
Dan harara shi nayi nace zaka fara zolayan ka ke nan ni a kaina nayiwa ba kai ba don kasan dama ni haka nake a cikin kwalliyana ko yaushe.
Zaiyi magana nace malam yunwa fa kace kana ji kuma ka tsaya fadin abinda ba a tambaye ka ba.
Yace za a hanani kallon matana ne ko may nace matan ka dai suna inda suke ni kan ai yar kanwar kace kaima ka sani.
Zama yayi a saman dan dining table din dake falon na shiga kitchen cikin wani tako na fara fito mai da abincin na jera a gaban shi har lokacin bai kara magana ba ya soma ci.
Annurirn fuskan shi dai naga ya sauya ya zauna yaci abincin sosai sai da ya kusa kammalawa sai ga Nafisa a part din babu sallama