rike da Ihisan yana fadi gata nan wai zata zo wurin ki uwarta ta hanata.
Fauziya ne tace ikon Allah har yara ma a cikin kishi wanan mace dai Allah mana tsari da irin su wallahi faiza tace ai abinda mutum keyi sai yaga kamar shi kowa ke yi.
Fauziya ta fada maki abinda ta roka maku kun tatauna da ita kuwa wani irin kallo nayi mai ina mamakin shi wani irin mutum ne haka da baya boyon magana kai tsaye yake fadin abinsa.
Kallo na sukayi tare da mayar da kallo a gare shi tana fadin bata fada muna baz yayan mu khadija alheri ne ya samay mu komay ?
Zanyi magana Samira ta shigo dauke da baby a hannun ta tana fadin anty ance in kawo maki ita nan na mika hannu ita fadin mama na Allah sarki na karbi yarinyar.
Nadan dubata tare da nufar anty Fauziya da ita na mika mata yarinyar tana ganin katon kai tace subbahanallahi haka take nace eh abin tausayi ne yarinyar yana tsaye a dakin har lokacin yana ma yar gurin Faiza wasa.
Nace ki duba cikin ta inda akai mata aiki da wurin a bude yake tayi saurin bude cikin yarinyar ta gani ta mayar da sauri don har yanzu akwai wani roba a jikin ta.
Da ta dago kai tana kallon yayan nata dake tsaye tace yaya haka aka haifeta ashe yace wallahi abin akwai tausayi sosai saura suka mike zuwa ganin yarinyar.
Yake cewa su Ikilima dai basu damu da zuwa wurin mutane ba Faiza da ta sauke ajiyan zuciya tace yayan mu kasan su ai da nuna akidar wariya dakin su har yanzu haka muke dasu ba abinda ya canza.
Yaran dakin mommy ne can zaka ga an kawo su suce sun zo ziyara ne kwana bibiyu suna zuwa wallahi yace shiyasa nake so mommy halin matar nan yana min wallahi.
Motsin da yarinyar tayi ne ta miko min ita da sauri yana kallon mu nace barin goya ta ko zata dade tana barcin yace likita ya fada mata haka daga ita har yan uwan nata raggaye ne.
Ina goyan yarinya Binta dake zaune fuskanta wani iri tace ke da cikin ki hakan nan zaki goya wanan yarinya don Allah ki bada ta amaida mata da abinta.
Dariya nayi nace may kike tsoro kada a kara haifo maki haka ko may ai mutum baya kaucewa kadaran shi ko ina yake.
Baiyi magana ba sai dan girgiza kai yayi ya fice daga dakin Faiza tace ai gaskiya ne khadija ko ita sheri yasa tabayar akawo maki don tasan kina da ciki.
Allah dai ya sauwa ka idan mada wani manufa tabada tayi wa kanta ai, ai itama Allah ya bata yar hakana da take kin ta a kusa da ita.
Khadija fada muna abin alherin don Allah don a kage nake tun dazun inji don yace kece zaki fada muna mu baki goron albishir.
Nace ina ganin bana zaku sauke farali ne don sharan dana bashi yace ko gyaran daki ko wanan nace dashi duka dai baidai ban amsa ba har yanzu.
Don mun dade dayin maganan tunda ya tayar da zancen yanzo nasan akwai maganar tafiyan ku ke nan tace ko shi yasa Yusuf ya amshi passphot din mu kwanaki nace shine.
Murna suka fara yi ba basu jima ba sukace gidan hajiyar su zasu tafi nace yau naso shiga mugaisa kuma gashi ban samu fita ba ko da zuwa dare ne zan shiga.
Bayan sun fita ne nayi waya da maryam ina fada mata zancen dawowan Nafisa gidan tai ta kunduma mata ashar nace kai maryam baki da kyau wallahi.
Dakin shi na nufa wanda wanan ne karo na buyu dana taba shiga dakin sai da na tsaya na kare wa dakin kallo tare da mamakin yadda akwai mace a gida dakin miji yake a haka.
Naga kokarin shi da ya iya zama haka a wanan dakin sai dai abinda na kula dashi shine iyaka a dan gyara fadon da za a kwanta akai.
Ga goyon yarinya haka na zage na gyaro ko ina na dakin har ban daki ina yi ina sauraren numfashin yar da ke bayana data take yin shiba wahalce.
Kacar nagama na fito daidai yarinyar ta falka nakai wa uwar itadaga kofa na tsaya ban shiga daga ciki ba na tsaya daga kofa.
Na sallamay sallah ya shigo dakin yana gaida ni da aiki tare da fadin yanzu hajiyan mu ta kirani a waya wai taji abin alherin da ya samu yayan ta sun koma mata da murna.
Yaya ka biya masu din ne na tambaye shi sai da yace nifa ba yayan ki bane nace inawa su Zainab kara ne ai nima nasan ba yayana kake ba yanzu.
Yace yana zama sun tsorata da ganin yar nan ai don naji binta na maki magana nace ita dama ai matsoraciyace .
Yanzu na maida ita nazo in yi sallah ya mike yana fadin ki girka abinci da dan dama don ina ganin su chezer zaso gidan nan don muna da meeting yau.
Nace anty ya kamata ka fadawa don itace mai gidan don ni ba girki nake yi ba yace amma kin san yadda mukayi dake tun Abuja ko.
Sanan idan ma ba kece da girki ba may zai sa in fada mata tunda ba kunya zata iya fitar dani ba nasu banda kayan haushi.
Haba yaya AA kaima fa kana da laifi akan anty gaskiya bai dace kuna haka ba ga yara girma suke suna ganin abinda kuke yi kuma.
Baice dani komai ba sai fitan da yayi daga dakin ganin banda lokaci yasa na mike lokacin kyautan da abokan shi sukai min jiya .
Wardrobe na bude na fito da kudin sai da na ware ido daga inda nake zaune don ganin yawan kudin har zuciyana tana zargin wace irin sana,a sukeyi hakane wai.
Da wanan tunanen a raina na fito zuwa kitchen din wanda banyi tsamanin an dafa wani abu ba a cikin sa da rana laraba tana zaune dan lungun kitchen din kamar marainiya nace mama kun koyi abinci da rana gidan nan tace to shine nake nan ai a cikin damuwa.
Na tambayi hajiya tace wai na tambaye ki aike ce mai mashi girki ba ita ba nace kuma da sauri tace tau haka dai tace min da naje gurin ta dazun.
Allah ya kyauta nace ko wani gauta ja sai dai in bai sha rana ba yadda take so zan bita mu tafi a haka tunda itama alamarin ta ba baya bane.
Aiki muka hau yi gadan gadan sai gashi yafito yana fadin wai ba ai abinci bane da rana ko may ?
Shiru nayi ban tanka mai ba tana zaune a falo yake sake tambaya tace ba,ayi ba don na dauka khadija zatayi ne yace itace mai girki ?
Ita naga tanayi ai da kuka zo OK kawai yace ya kira yara shi suka fice daga gidan Samira ne tazo ta samay ni a kitchen din tana fadin anty yunwa tana taba cikin ta.
Nace bari dafa maki indomie kusan a tare mukai aiki da ita don bata koma dakin su ba again.
Sai yamma lis suka dawo gida da yaran nan suke fadin wurin hajiya mama suka tafi ashe kafin magariba na gama hada masu komai abinci ne tuwon alkama da miyar yauki sai jar miya da na dafa na cow tail ya dafu sosai sai dafa duka da yaji cabeji da kayan hadi nayi amfani da zaukaken nama daban soya ba sai kayan ganishin dana yi a sama.
Bayan nan kuma na hada masu zobo da yaji kayan kamshi da kayan hadin shi dadai sauran tarkace na motsa baki na aje masu sai da na gama jerawa na haye sama na bar gurin bayan na mutanen gidan dana saka daban na nuna ma laraba wanda ke so ya diba.
Ina shigewa Nafisa na fitowa ta nufi abincin zata diba Laraba ta fada mata abindanace tace ita wanan din nasu zasu diba din don nasan sherin da nayi a ciki yasa nace hakan komay ?
Kamar an fada min sai gashi na manta wayana a kitchen na sauko in dauka na samu zata bude mama ihisan kada ki taba wanan din .
Muryana taji daga bayan ya yasa ta juyo tana fadin akan may ba zan debi wanan din ba nace saboda maigidan da bakin shi na girka ba don ke ba.
Tace kin dai san sherin da kikayi a cikin sa don haka sai na diba din sai dai ki mutu idan na diba na karasa wurin ina fadi bazaki diba ba tunda iri dayane da wancan dana aje din .
Kai may ye Nafisa wai kina da hankali kuwa tace sai ka koya min na gaji da wanan rashin hankalin da kake kira min a gidan ka ka wanan yarinyar.
Na kira maki don ko baki da alaman shi da baki tsaya kina wanan abin kunyar da kikeyi a gidan nan ba.
Bar wurin nan yanzu kafin ranki yakai ga baci anty Fati dake tsaye tana sauraro tace ikon Allah a ranta ashe Allah zai gwada min faduwan buzuwanan haka ingani da idona.
Samad an wanke an baka kasha diyar matsafa ta gama dakai ka fita hayacin ka baka cikin hankalin ka baka ganin kowa a gaban ka sai ita yanzu.
Yace ashe kema da don ban ganin kowa a gaba kikewa mutane yadda ranki yaso ke nan to yanzu itace a gaban nawa kamar yadda kika ce din.
Sunyi tsiya sosai dashi duk da haka na dauka bazata debi abincin ba sai gata tana diba abinci ta haye sama dashi tana sababi ita kadai don shi har ya shige ko ya barta a gurin.
Idan dane na tabbatar da sai anyi dayan biyu ko ta kifar da abincin ko kuma ta diba tunda tace shi din dai zata diba din.
Abin duniya ya taru yai mata yawa a rai gashi ganin da tayi muna mu biyu tsaye a falon ya kara tayar mata da hankali sosai wai ace duk biyun nan da Samad suke kai ina ba zai yuyu ba wallahi.
Bakin shi sunzo sai da ya fada ma kowa yana tare da abokan shi a falo sai dai bai leka wufin Nafisa don kofan ta a rufe yake.
Suna tsaka da tataunawa ne sai ganinta yayi gaban su bata damu da duk wanda ke gurin ba bata kuma gaida su ba sai jin ta kira sunan shi gatsal sukayi.
Tace Samad ina son ka sawo min magani yanzu kakuma sayo ma yarinyar nan permpers tare da magani itama don mura take yi.
Yace baki da hankali ne baki gani tare da mutane bane ko baki da hankali ne tace idan na ganka da duniya ne ni may ya damay ni dasu tunda wurin ka nazo.
Nafisa wai baki da hankali ne komay Yusuf dake rubutu ya dakatar yana fadin haka yace kin fi saura yan uwan ki ne da suka natsa kansu a dakunan su komai.
Dayan ya kalle ta yace ai dama tare kuka zo ne ashe yana tambayan AA din da yakai iya wuya da abinda tayi mashi din.
Bai bashi amsa ba sai mikewan da yayi ya nufi hanyar sama tabishi tana maganganu itama bai tsaya ba sai dakin ta.
Tana shigowa yakai hannun zai wanka mata mari ta gwauce mai tace akan dan wanan maganan da naje ma dashi zaka mare ni ?
Baki da hankali ne ko baki ganni da baki bane da ba zaki iya jirana su wuce ba ko sai kin zubar min da kims ta a ko ina zaki ji dadi ?
Daga yau idan ina da baki a gidan nan kada ki kara zuwa inda suke idan bani na bukaci kizo ba ke wata irin mace ce da baki da tunanen abinda ya kamata haka ?
Ai basai kai mun haka ba zan san ka auro diyar matsafa ta canza ma tsari da ai naga ko bakin may baka shayin in fito a gaban su.
Sai yanzu ne zaka tsiro min da wanan dokar naka mara amfani ko haka ta tsara maka yanzu kuma a gidan.
Yace eh haka ta tsara min don ta fiki hankali da tunane abinda ya kamata ne ga addini na ta tsara min hakan.
Wani dariya tayi tace wai abin mamaki bai karewa a duniya haushi yake ji cikin ranshi kamar ya shaketa yake ji a ransa.
Don bakin da ke gidan ne ya juya yafice daga dakin baice mata komai ya zauna gurin su rai bace dashi.
Yana zama dayan yace sai kai mijin buzaye wanan matar taka ashe halinta na nan yadda yake ada bata canza ba har yanzu.
Sai daya yace cool down my friend mun saba da halin irin matan nan na ketare ko salis gashi nan haka yasha wuya da nasa kafin ta yaye shi tayi gaba Allah yasa yana da karfi arziki da yanzu ta gama dashi yanzu kai muke jiwa dan uwa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zan iya cewa Alhamdullahi a zaman mu na dan wanan lokacin a kaduna don zaman ya kara haska min hanya sosai a gidan AA na fahinci wasu abubuwa daga halaiyyan mutan gidan daga mijin har matansa da ma yan uwan uwashi.
Yanzu na gama tanadar abinda nake son fahinta daga gare su sai dai wanda ya kara boye halin shi bai fitar a fili na gani ba kan shine ban samu nazarin sa ba.
Na fahinci zaman akwai rikici na son mallakan miji ta ko wani hanya musanman daga wirin buzuwa.
Ida ita kuma fati ta kasa daukan girman ta ne a gidan sabado abuwa kamar biyu zuwa uku dana fahinta.
Na farko akwaita da son jiki don ko kanta bata iya yiwa komai balle danta ko mijin ta amma kuma a hakan take son jin girman ta.
Sai abu na biyu dana fahinta gare ta shine tana da kishi irin na matan da da basu iya boye kishinsu a zuciya sai sun bari abokiyar zama ta fahinci hakan gare su.
Na uku tanada fadar magana kamar wace taci kashi bata tsayawa ta auna magana ga ko waye zata fada mai kai tsaye cikin halin ko in kula yai ma dadi ko kada yayi tadai fadi zuciyar ta.
Ga bason mutane a kusa da ita don zaka iya zama da ita wuri daya idan bataga dama ba taima magana sai ku wuni a hakana da ita atakaice akwai ta da nakasa ga kowa.
Irin matan nan ne da ba,a gane samun su don ko yaushe jiya i yau ce gare su bawani canji tare da ita haka yasa mutane ma basu damu da ita ba sosai don har yau da ake bukin sallah banga wani bako kodaga gidan su yazo.
Ita kuma buzuwa gaba daya har mijin na fahinci ba dadi a tsakanin su burin ta kawai ta ba kowa iko kowa iko a gidan mu koma sai bi sai yarda tayi da kowa.
Ba ta kaunar taga wata ta rabi shi ko magana yayi da wata anjima kadan zakaji su sun rikeci dashi suna jidali kan hakan.
Ga rashin yarda da kowa kowa ta dauke shi mai tsafi idan kayi sallama sai ta tura aga mai ka shigo gidan dashi idan kuma ba gurin ta kazo ba bata taba amsa ba sallama balle su gaisa da mutum.
Kai abindai gashi nan sai gyaran Allah bana mutum ba don haka ne idan nayi sallah nakan roki Allah ya haudani kan su ga baki daya don shine kawai mafita yanzu gare ni.
Tun dana fahinci gaba dayan su suna adawa dani na fara kama kaina ga kowa a gidan.
Yau ma da aka wayi gari haka yasa ban fito ba tun safe ina daki na don Fati ce tayi girki don haka na zauna daki.
Banji motsin kowan su ba haka kuma baisa na fito ba dana gaji da kwanci na gyara daki nayi wanka bayan na shirya na haye gado na jawo waya ina kiran yan uwa na muna gaisawa dasu.
Karshe maryam ce na kira tana min korafin na tafi na barta don su abuja sukayi sallah tace ba inda ta fita tana jin garin ba dadi.
Nace mu kan muna nan don banga ya saka ranan dawowa ba gare mu kamar da abinda yakeyi ne a garin don bai faye zama a gida ba kuma kullun cikin meeting suke.
Jin an turo kofa dakin yasa nakai kallo na ga kofan inda naga shine ya shigo dakin ido na zuba mai har lokacin da ya karaso inda nake kwance din.
Ina kwana na tare shi dashi ya amsa min yana zama tare da fadin lafiya kike kuwa nace lafiya ta kalau may ka gani halan ?
Ajiyan zuciya ya sauke tare da bin dakin da kallo yana fadin naga baki fita bane har yanzu ko yau baku abin karyawa ne a gidan ?
Bani ce da girki ba ai ko ka manta ne na bashi amsa yace ok yana mikewa maryam na gaida kai nace mashi yace a itace ta bugo waya nace eh tana min korafin yaushe zamu dawo na barta can ita