MIJIN BUZUWA complete Hausa Novels.txt

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   48 / 144

141K to 144K   out of 431K words

fadin khadija dama nasan halin ki ba karba zakiyi ba amma ita kaunar nan nawa da tasan dadi kashin kudi kinga ta karbe da sauri ai.
Duk muka sa dariya ya wuce ya barmu a gurin nan gardama ya kaure muna akan abinda zamuyi sai zainab tace ba fa wanan ba shi yayan mu yasan gidan shi zamuyi event din gobe ?
Maryam tace ai mashi magana mana aji ko zai bari indan bai bari ai da wurin yi da yawa bashi kadai ke da gida ba khadija baki san halin yayan mu bane da masifa.
Amma mu gwada kiran shi mu gani yanzu da sauri binta tace wa zaiyi magana idan mun kirashi din maryam tace a ba khadija tayi.
Kira Binta tayi ta miko min wayan kafin in magana kamar ba zai dauka ba sai can aka daga yace wake magana ?
Malam gidan ka muke son aro gobe zamu danyi get together ne da kawayen mu na engament din Zainab yace kuna da hankali kuwa ?
May zakuyi wa wasa ko kun manta matar shi mutuwa tayi kada ko fara gigin yin wanan abin na fada maku wai ma wake magana ne ya tambaya.
Nan sani ba nace na kashe wayan da sauri Binta tace ke zaki ja muna masifan shi ne baki san shi bane wallahi .
Maryam tace yanzu yaya ke nan don maganan yaya AA gaskiya ne fa tunda mutuwa matar shi tayi binta tace humm ummm wallahi sai munyi shekara nawa da mutuwar matan shi yanzu.
Zainab tace mommy zamu fadawa ita kadai ne zatace ayi ya yarda ayi don kun san hajiyan mu ba zatai magana ba don haka muje wurin ta kawai.
Da sauri nace wa nikan sai kun dawo maji yadda kukayi amma nikan gaskiya ban iya zuwa wurin mommy kan wanan magana.
A take Zainab ta nuna min bataji dadin haka ba don nine hope din ta yanzu kuma nace ban zuwa dole na yarda muje wurin mommy din .
Mun koma ciki na dan gyara jikina muka fito muka tunkari gidan nasu a dakin mommy muka yada zango bayan mun gama gaisawa da mutanen gidan sai dai bamu je aurin hajiya mama ba sai mun fito.
Ni da maryam a kasa muka zube muna gaida mommy cikin fara,a take amsa muna tare da tambayan mu munzo lafiya ?
Ta kalli maryam tace wanan ne kuka zo asibiti ranan tare ko nace itace mommy tace yarinyar nada kirki wallahi ku yi hakkuri da junan ku kun ji nace to mommy mun gode.
Binta ce ta fara mata bayanin abinda ke tafe damu mommy tace shiko dai abinda ba a gari daya ake ba may zai sa ya hanaku yin farin ciki ai wanan farin ciki ne ga kowa.
Ya barku kawai kuyi abin ku tunda ba wani abu can zakuyi ba dan taruwa ne kawai mommy ayi addu,a binta ta fada wani addua kuma binta abinda za a tara yan mata.
Kada ki kawo min wanan karyan naki yanzu dai ku bari zan ganshi in mashi magana kafin goben ya kyale ku kuyi abinku tunda shima yusuf din baiki ba.
Zamu daga mi bar dakin mommy tace khadija an kusa gama karatun ko nace mommy da dan saura kadan insha Allahu.
To ai mu mun matsu ki karasa ansan abinda ake ciki don na matsu in kai ga sarakuwa irin ki sai dai ki matsa da addu, a fa don Nafisa ba wasa.
Mun fito wurin mommy dakin hajiya mama muka nufa muka gaida ita da fara,a take fadin ikon Allah ashe Allah ya nufa ayi dake sai gashi kin zo garin.
Dan dariya nayi ciki ciki nace wallahi mama basu fada min ba zuwa kawai nayi duba ya Amina don na dade ban zo ba tace ina zakizo wanan karatun naku mai wuyan sha, ani Allah yasa dai a gama lafiya nace amin mama nagode.
Muka shige dakin su Binta suna ta faman buga ma abokan su waya kan event din mu dai muna gefe muna jin su.
Hajiya mama ne ta kwala ma binta kira tafita tadan jima sai gata ta dawo tana fadin ga su yaya AA nan sun shigo yanzu kuzo ku gaida su.
Nace daga inda nake kwance ku tafi kawai ni ina nan ba inda zanje sai kun dawo su fita sai ga zainab wai mama tace muzo mu gaisa da yayan su.
Dole na fito muka gaida su na tsaya can baya daga kofa maryam ne ta dan fita fili sosai yace kinzo lafiya maryam ?
Ai ba ita daya tazo ba ga diyana nan a bayan ta ai ina kun san ta khadija itama jiya tazo daga Abujan kasan acen take karatun ta.
Mama wanan diyar taki mara kunya ce baki ga inda ta tsaya tana gaida mutane ba daga nesa gaisuwan ma sai da kika roka mana tazo.
A a ban yarda ba kai kadai naji ka fadi haka ga khadija amma khadija ai tana da tarbiya ko dan hararan shi nayi daga inda nake lokacin da yake maganan.
Mommy ce tashigo dakin inda shigowanta baisa mama ta fasa maganan ta ba tace kai ai kowa ba daidai yake ba saboda murdaden halin ka.
Mommy tace may kuma yayi yanzu da shigowan shi yaya tace haka kawai zai saka min diya a gaba daga gaida shi wai bata da kunya.
Ina shi kunyan ne gare shi yaya ki barsu kawai don sun fi kusa idan kika shiga maganan nan kunya zakiyi .
Au to haka zancen yake to Allah ya tabbatar muna da alheri da nafi kowa farin ciki da hakan kuwa da sauri nace mama ba haka zancen yake ba mugune shi kawai nama rasa may zance dasu a wurin.
Dariya mommy sukayi tace na fada maki barsu kawai su gama boye boyen su kyaji may ke nan watarana.
Mommy ai ba sai watarana ba gashi sun nuna a gaban ku ai yanzu kowa ya sani haka da kika gansu muke fama dasu wallahi ko maryam ?
Yana tambayan maryam din tace mama kyale su haka suke ko yaushe ba a shiga tsakanin su don ko an shiga zasu dawo su shirya ba a sani ba.
Ji nayi wurin bai dauka na da sauri na koma ciki ina jin wani bacin rai tare dani ban san yaya suka kwashe a falon ba na daiji binta ta shigo tana murna wai an mashi magana yace muyi.
Suna murnan su nikan raina a bace yake da maryam da yusuf har da mommy data biye masu din.
Sai da kyat na saita kaina na dan koma normal kada a fahince ni bamu bar gidan ba sai dare so sai muka koma gida tare da ya Amina da dawowan su ke nan daga gidan jere.
Wanka nayi na kwanta don raina a bace yake da kowa nayi dana sanin zuwan danayi kadunan a yau da nake ganin ana son kula min sheri wurin matan da nake jin nauyin su.
Shi kuma munafukin bai fada masu ba gaskiya bane dan ya kullamin sheri kawai a wurin su komay yake nufi oho zan gani idan ana kula abinda ba alaka ne a cikin sa.
Da safe tun safe su zainab suna gidan mu ana sha,anin buki a cikin gida mu muna shirin namu event din.
Unguwar yacika da baki nakusa dana nesa ko ina mutum ya duba motane na masu zuwa daurin aure a haka muka ratso tarun mazan har kafana yana hardewa.
Kamar ance in daga kai can na hangoshi tsakiyan mutane daga nesa muka watsa ma juna harara mun shiga ciki zakace a gidan ne ake buki don jama, a da suka cika gidan.
Nan na kara yarda ba karamin alaka ke tsakan gidajen biyu ba mun zauna ke nan massage ya shigo a wayana na dauka ina dubawa.
Kina da hankali kuwa da zaki ratso wanan taron maza haka da dan gyale karami.
Haushi naji har cikin raina na mayar mashi da amsa ina ruwan ka da ni ka fara tsare matan ka kafin ka fito sa ido waje.
Yarinyar dani kike wasa ida na kara ganin ki haka a garin nan sai na bata maki rai .
Kaji min mutum da sa idon tsiya kai waye da kake son saka min doka na rubata mashi.
Ya sake rubuto min barin shigo ciki in nuna maki ko ni waye a gaban su mommu da hajiyan mu yanzu.
Ban bashi amsa ba don tsoro ya kamani kada bakina yaja min jin kuya sai hira muke a falon hajiya mama ban yi aune ba sai ganin mutum nayi ya shigo falon.
Da sauri na noke kaina kasa ina hajiyan mu ya tambaya cikin daure fuska take dakin yayi tsit kamar ba kowa a ciki lokacin.
Sai zainab ne tace mai yanzu ta shiga dauko abu a ciki sai gata ta fito yace a hada muna abinci akwai bakin da suka zo daga Abuja yanzu.
Kai babangida shine kaki fada da wuri a cire masu tun farko ai da ko matar ka sai kasa ta aje masu yace ni kaina wai bata aje min ba tace.
Kai wanan irin abu naku damay yayi kama ace ana buki a gidan ku bazaka aje ma mijin ka abinda zaici ba sai ya tambaya mama ta fada cikin bacin rai.
Nan ya fice daga falon na sauke ajiyan zuciya muna zaune kafin wani lokaci an hada masu aka kai ina jin mommy da mama suna ta fadan abinda banji dadin shi ba kan fatin.
Mun dage bukin mu sai washe gari don hidimar bukin da yayi yawa a gidan dole muka dage namu din sai washe gari four na yamma zamuyi inda nasa rai ya wuce a lokacin don Sunday ne dole ya koma aiki na manta akwai hutu Monday da za ayi.
Kamar yadda muka tsara zamuyi four mun gama shiri a cikin dogayen riguna bakake gaba dayan mu sai zainab ne tasaka fari kwal a cikin mu.
Mun gyara wurin dakyau kawaye na zuwa guda guda har wurin ya dan cika mu mata zalla ne a gurin muna gidan Fati ta dawo daga gidan su daukan abu.
Maryam ta zuba mata ido tana kallon ta ina gefe ni kuma ina kallon maryam din bata tsaya ba ta fice ta barmu a gidan .
A falon su ne zamuyi event din so ba wasu maza a gurin sai wanda zai muna dj da aka dauko bayan yan bayane aka fara gudanar da event din gwanin ban shaawa.
Mun sake sosai don mu kadai ne a gidan haka ya bamu daman sakewa yadda muke so a gidan kira ake guda guda mu fito mu taya zainab din murna a fili muna fitowa har akazo kaina na fito na fara takawa kamar ance in daga kai sama tsaye yake da waya a kunnen shi yana saukowa kasa.
Da sauri na rage rawan na fita fiilin suka sa ihun basu yarda ba don time din da ake ba kowa baiyi ba na fita.
Gyaran muryan da yayi daga bayan mu ne yasa kowa dake wurin ya natsu sai da ya fita muka koma abinda mukeyi din wayana naji yana kugi da sauri na ciro a jakkana ina dubawa fito nan waje yace dani.
Sai na basar da sakon naki fita wani sakon ne ya kara shigo min again ki fito ko inzo wuei in samay ki cikin bacin rai na fito cike da rashin mutuncin wanan takuran haka da yake min.
Ina fitowa na duba ban ganshi ba sai naji horn a gabana na gane yana cikin motar shi zaune wurin na nufa na samay shi zaune a motan.
Shigo yace min nace bazan shiga ba nan yayi min nace dashi kai tsaye yace ki shigo tun ban fito ba wallahi ban shiga nace kai tsaye yana fitowa na fara ja da baya baya har nakai jikin wani mota na tsaya.
Ashe karya rashin kunya kike yi may kika rubuto min jiya tsakanin mu bai wuce tako daya ba nace may ka gani ya tako kenan zuwa gare ni binta tafito daga ciki tana kwala min kira.
Da sauri ya ja baya na sauke ajiyan zuciya kirana ta kara yi ya juya a fusace yana cewa da ita stupid wanan kira haka fa kamar makauniya.
Ta juya simi simi zata wuce nace jirani muje Binta yace bace min da gani ta wuce ba ko waige ta shige ciki da sauri ya dawo da kallon shi gare ni da zuman nufo ni na zille da gudu na bar wurin.
Sai gab da magariba muka gama muka kwashe kayan lokacin har ishai yayi kai tsaye gidan ya Amina muka nufa ni da maryam.
Binta mamaki ne ya cika ta ta kasa sakin jikin ta na abinda ta gani yana aukuwa tsakanina da dan uwan nasu sai da sukaje gida ne take fada ma zainab abinda ta gani.
Zainab tace nima naso in fahinci hakan tun ranan da taje waje tayi mai magana a hostel din su amma koma may ye zan binkici yaya yusuf inji ko akwai wani abu a tsakanin na su.
Wai har khadija taban tausayi wallahi ina zata iya da Nafisa anty Fati da take babba yaya ta iya da ita balle khadija da take karama ?
Zainab tace ai abin badaga nan yake ba in fada maki sai ko kiga khadija ta iya zama da ita tsab balle khadija da take da baki.
Magana may naji kuna yi haka baku kwanta ba muryan hajiya mama ne a dakin nasu take tambayan su zainab tace a a magana mukeyi kawai.
Binta tace mama wani abin mamaki na gani yau wallahi yayan mu tare da khadija nagani sun ban mamaki don akwai wani abu a tsakani su nake gani.
Koma may ye a tsakanin su Allah ya tabbatar muna da alheri shi muke fata ga kowan ku yanzu ta fice ta bar masu dakin cikin sanyin jiki.
Kodai dama hajiyan mu tasan da wani abu a tsakanin su ne ga yadda tayi magana yanzu kamar tana da masaniya akan abinda nagani.
Kokarin rungumay khadijan fa naga yanayi sai dai ita khadijan kamar a tsorace take a lokacin kai Binta banda sheri fa.
Au kin dauka karya nake yi ai koma may gobe zan tambayi khadija din don nasan ba zata boye muna komai ba inji Binta.
Zainab tace yau zan tambayi yaya Yusuf idan ya kira ni inji don shi zai san komai akan haka ?
Washegari Mun sha barcin gajiya don haka bamu tashi da wuri ba gashi ina son zuwa hidan kakanin yaran Ya Amina in duba yaran dake can.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zaune nake a gaban ya Amina da maigidan ta sai maryam da muke zaune saman kujera daya mijin ya Amina ne ke magana bayan ta gama kora mashi halin da ake ciki dani da gidan su AA har nace zan koma gobe.
Magana yake min ta fahinta yadda zan fahinci komai a tsanake ina sauraren shi sai dai hankali na yana kan maganan da mukayi da su binta da zainab a dakin mu dazun.
Abinda naji ya fada ne ya dawo dani daga abunda nake tunane din yace a gaskiya khadija naso ace sai kin gama karatun ki zakiyi aure.
Amma yanzu yadda wanan zancen ya fara bullowa nasan abune mai wuya ki samu ki gama karatun ki ba tare da aure ba.
Yace mun sha waya da daddy yana min complain din kiyi aure haka na don yan uwan ki ba wanda ya yi karatun gaba da secondary acikin ku sai ke kadai.
Hawaye ne ke fita min daga fuskana da ban san lokacin da suka silalo min ba yace abu ne mai wuya idan daddy yaji zancen nan ya barki har ki kare karatun ki babu aure.
Don haka nake baki shawara ki lalaba wanan mutumin ya dakatar da maganan nan sai idan kin gama kin ga zuwa lokacin idan Allah ya kawo maki wani sai ku shirya kuyi auren ku dashi idan kuma wanan din ne to sai dai muce Allah yasa albarka don dai gaskiya Abdulsamad mijin aure ne ga ko wace mace.
Da sauri nace yaya Adam don Allah ka bar zancen shi ni ba soyayya muke dashi ba wallahi kuma shima nasan ba sona yake ba har cikin ran shi.
Kawai dai don yaga iyayyen shi sun nuna suna so ne ya nuna masu shima yana so na karasa da fadin ni may zanyi da mai mata har biyu a gida.
Yace ba a auren mai mata ne ya tambaye ni yana dariya nace ga wanda ke so tanayi amma nikan harga Allah ban da wanan raayin a raina.
Wanan ma ya Adam banda fitina mai ke akwai a cikin auren shi duk macen da ta shiga gidan shi ai tasan abinda ta takane.
Ni dai don Allah ku basu hakkuri su bar wanan zancen please ya Adam yayi saurin fadin a, a khadija ai mi bamu shiga maganan aure ke dai ce da kan ki zaki nuna mashi hakan.
Yanzu idan mun hana Allah yazo yayi auren ku da wani ido kike

48 / 144

Chapters