MIJIN BUZUWA complete Hausa Novels.txt

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   73 / 144

216K to 219K   out of 431K words

su ba.
Da sauri tace zan dai je in gaida ita din ko shi don yaudara zan tafi kuma don kin ce inyi haka amma aini banki yar iska ta mutu ba ma.
Nan dai sukai ta kitsa sherin su har suka gaji suka watse a gurin rai bace basu cin ma manufa don maigidan yace ta barmai gidan ita da yan uwan ta baison kowa a gidan nashi.

Mun isa asibitin likita mace ce muka gani doctor Rahama itace ta dubani yan tambayoyi taimin ina bata amsa ta fahinci matsala don dagani sai itace a office din su suna waje.
Magunguna da allurai ta rubuta min ta bashi yaje ya sawo basu dade ba suka dawo d taimin alluran da kanta tare da fada min abinda zanyi in kara samun lafiya tace wasu mata da yawa hakan na faruwa dasu don rashin sabo da abinda farga ba.
Ba laifi na dan fara jin sauki tun a hanyan Yusuf ne ke min zaune daga inda yake yana jan motar murmushi naji shi ya sauke tare da dan juyo gare ni yana fadin.
Wanan kaunar taka fa da alama raguwa za ayi anan mace haka sai bakin raki ina ga in zata haihu wayasan irin rakin da zataiwa mutane.
Dan lumshi idona nayi cikin yanayin ciwo na dan harareshi cikin yana yin ciwo ina gyara zama na daga inda nake zaune.
Babu je gida ba sai da suka tsaya wani shago Yusuf din ne ya fita ya shiga shagon ko kaina ban iya dagawa ba a lokacin don yadda bake jin kaina.
Hannun shi yakai ya jawo ni zuwa jikin shi yana fadin mai baki dama bai iya raki ba daga dan tabaki kadan sai ki fadi ciwo haka kina ma mutane makyarkyata.
Yana magana yana kokarin rungume ni a jikin shi cikin karfin hali na furta don Allah ka bari jikin nan nawa kamar gyabo nake jin shi yau.
Na karasa fadi cikin wani irin kasalalen murya mai tatare da rauni a gare ni yace da sanu zaki saba da hakan kuma har da rakin banza da son jiki irin naki.
Naji nace ina mai da kaina saman kujeran motar tare da lumshe idona a hankali muryan shi naji yana fadin kodai na zama shape shorter ne har na aika sakona na ya shiga.
Kasalalen murmushi na sauke tare da damtse baki na a hankali ina tunane a cikin raina Yusuf ne ya fito daga shagon ya bude mota ya aje lodojin da ya fito dasu daga shagon.
Sai da ya zauna yake fadin kana nan kana damar min yar kaunata da zolaya ko bayan kasan ka mata laifi yau.
Wani irin nauyi da kunya ne suka rufe ni a lokacin don ban zaci Yusuf ya fahinci abinda ke damu na ba a lokacin.
Mun shigo gidan babu kowa a falo sai Samiha tana ganin mu ta fara min sannu ni dai ban iya amsawa ba don wurin kwaci nake bida a lokacin.
Shima ciki ciki naji ya amsa mata gaisuwan da taimin din muka shige part dina tare dashi Yusuf ya shigo da ledojin har cikin part din nawa yana kara yi min sannu da jiki.
A falo na kwanta saman dogon kujeran falon tare da lumshe idanuwa na a hankali zama yayi yana kokatin bare min maganin da zan sha a lokacin.
Sai jin sallama Nafisa mukayi a falon su shigo ita da Yanyala ban bude idona ga yadda nake ba sai dai ina sauraren abinda ya kawo ta dakin a lokacin .
Ji nayi tace ya mai jikin yadda ya amsa mata ba abin mamaki bane don yanayin bacin rai da suke ciki ita dashi.
Tace ummmh wanan ya jikin fa Allah ya sauwaka ya kawo sauki maryam ne ta amsa masu da amin shiko yana kokarin dago ni ya bani maganin a baki.
Juyawa sukayi suka bar dakin ranta a bace yake na abinda ta gani wai yau samad din ta ne ke faman rungumar wata mace a gaban ta bata iya yin komai ba.
Ta na fita dakin ta shiga wani irin huci tana fadin wanan akwai makirar yanrinya ji yadda take wani narkewa a gaban shi ita a dole ga mara lafiya miji na jinyan ta a haukace.
Iya abinda zai iya mata ke nan dai lalashi amma badai yakai a gareta ba yar iska wanan ba don ta samay ni a tsaye ba da ba karamin yar iska za ayi ba.
Ya dade zaune a dakin yana rarashina inci wani abu dan fresh milk din daya zuba min a cup ban iya shan koda rabin cup din ba ina batun aje cup din ya karba daga hannu yana fadin.
Miko min in sha tubarlakin ki tunda nima jiyan ake a tare dani ai ya karbi cup din yana shan milk din yana wani irin lumshe idanuwan shi.
Girgiza kai nayi ina kokarin komawa in kwanta yace a a bafa kwanci zakiyi ba zama zakiyi muci naman nan tare ko ba haka ba Yusuf.
Don Allah malam ka tashi mu fita kada ka damar min da kanwa ta hutu take so yanzu haba nima ku tausaya min mana.
Ya fada yana mikewa tare da fadin amarya zan dan raka wanan sarkin nacin ya tafi ya bamu wuri nazo muyi jinyar a tare.
Maryam don Allah idan ya fita ki rufe muna kofa please so yake sai wanan matar tashi ta dawo ta karanta muna haukan ta kuma ina fama da kaina.
Haba ai yau bazatayi halin nata ba ba yanzu tazo ta gaidake ba anan ai ta saduda yanzu da alama.
Yusuf yace kaiya wanan duk ladabin shegune da wata dai a kasa Nafisa ce zata shigo don Allah wai gaida khadija.
Fita sukayi sai da suka fitane yake koro ma Yusuf abinda ke faru a gidan tsakanin shi da Nafisa din inda yake fada mashi ya basu kwana daya su kwashe nasu i nasu subar mashi gidan shi.
Bai son ya sake ganin su a gidan don suna yawan takura ma rayuwan shi yanzu kuma ga khadija duk da batai magana ba yasan zaman nasu a gidan a takure take dasu.
Yusuf yace tun farko ban so ka aje khadija a wanan gidan ba amma wanan makiran matar taka ta kawo sallon yaudar ta tace dole sai a nan zaka aje khadija din don kawai su takura ma rayuwan ta ita da yan uwanta.
Dakin mu maryam ne ta lalaba don in watsa ruwan dumi ko jikin nawa zai kara sake min inji dadin barci da dare.
Ban ki ta taba bayan ta hada ne tazo tana fada min in tashi in je in watsa ruwan yana bayi ta shirya min.
Naji dadin wankan da nayi din alokacin don nakara jin jikina ya sake min sosai ina fitowa dsshi na fara arba zaune a bakin gado yana jirana a lokacin .
Kin fito yace min ciki ciki na karba mai tare da fadin eh kawai na nufi wurin mirrow ina bude mai na lakato zan shafa ma jiki.
Hannu na naji ya rike tare da karban man ya fara murza min a jikina a hankali ina runtse idanuwa na don yanayin na shigana sosai duk da halin da nake ciki .
Cikin dauriya murya makale nace dashi don Allah ka bari mana jikina ciwo yake min wallahi zai daina yace min ki bari in karasa sai ki kwanta.
Dole na kyale shi ya karasa shafa min man tare da dauko nightgown ya saka min da kashi sai da yaga na kwanta na dunkule a wuri daya ina runtse idanuwana.
Ji nayi ya zauna a kusa dani tare da fadin sannu ko Allah ya sauwaka, daga dan murzan ki saudaya wanan irin ciwon haka kuma.
Don Allah ka fits matar ka tana jiran ka please yace in fita inje ina anan zan kwana jiyan amarya na zanyi yau.
Bude ido nayi ina fadin yaya Abdulsamad don Allah ka fita kafa san haka ba kyau don shiga hakine hakan tunda ba lokaci na bane yanzu ka sani.
Ido ya kura min sai na dukar da kaina kasa don ban iya hada ido dashi yinin yau wani irin kunyan shi nake ji can naji yace
Korata kike ko may na kara dan marairaicewa ina fadin ba wai koranka nake ba kasan fa hakan da kake yana iya kawo rashin zaman lafiya a gidan nan don zata dauka wani abu muke kullawa.
Yace kodai fushi kike dani ne Deedar kiyi hakkuri don Allah dama dole ne zaman aure sai ancin ma wanan ranan.
Shiru yayi yana kallon yanayin da nake maganan in serious ya dan jima a zaune baiyi magana ba sai dan wani lokaci naji ya mike yana fadin take care zan tafi Allah ya sauka.
Ciki ciki nace amin ya fita ajiyan zuciya na sauke ina gyara kwanciya na dakyau tare da lumshe idanuwa na ina jin wani iri a raina.
Barci na son daukana naji muryan maryam a kaina tana fadin ki tashi khadi ki dan sha tea ko zakiji nauyi a cikin ki don Allah.
Idona na bude ina bata fuska tare da fadin maryam wallahi baki nane ba dadi ban jin zan iya cin wani abu a yanzu.
Kafana taja dake saman gadon tana fadin don't be a lazy tun yanzu mijin ku mai karfi ne in kin ce haka zaki dinga yi aikuwa aiki ya samay ki khadi don ko gobe ma karawa zaiyi ba fashi.
Da sauri na dago ina kallon ta tare da watsa mata harara ina fadin tunda gani jaka ko may ni wallahi yanzu ko muryan shi naji tsoro nake ji daurewa kawai nake yi.
Dariya ta dinga yi tare da fadin kajiki inda ana jin tsoron maza haka ai da ba a haife mu ba yanzu haka nace wasu suna tausayawa ai ba irin nashin nan ba gaskiya.
Tace ke don Allah kin faye raki wallahi dama masu bakin nan haka kuke da shegen raki ai wallahi kada ki bari ya gano kina da rauni a wurin nan don dai buxuwa tafiki fada a gurin shi kan dan wanan abin da kika raina.
Miko min tea din tayi ta kafe ni da ido dole na daure na sha fiye da rabi na miko mata cup din na dan zauna don ya fada min kafin in kwanta mun dade muna hira a gurin kafin mu kwanta.

A,A yana shiga part din shi ya rufo kofan dakin shi da key ruwa ya shiga ya watsa ma jikin shi ya fito
Nafisa tana kula da shi tana ganin ya fito tayi saurin komawa ta shirya zuwa dakin nashi don ta shirya bashi hakkuri acin daren nan.
Kofan ta tura taji yai mashi ke ta shiga dan bubuga kofan a hankali yana daga inda yake tsaye yake tambayan waye ?
Tace nice bude min mana tsuki ya ja mata ya kyale ta a wurin yaci gaba da shirin kwanciya da yakeyi ta kara buga kofan bai sa ya je ya bude mata ba.
Sai ma hauwa gadon da yayi yana kashe wutan dakin don ya kwanta anan ya fita batun ta tare da shigewa bargo don ya huta.
Barci yake son yi sai dai tunanen duniya ya hana shi a lokacin alamarin Nafisa ne ke damun shi a rai duk abinda yake wanan damuwar na mashi yawo a zuciyar shi daurewa kawai yake yi abin yana damun shi sosai a rayuwan shi.
Duk yadda ake son mutum da hakkuri da iyalin shi yana iyakar hakkuri da Nafisa amma ita bata ganin hakan da yake mata.
Sai kokarin daukan shi macuci mayaudari da takeyi shi baiga wani abinda yai mata ba in ma cutarwa ne Fati da khadija yake cuta .
Don tana da motar shigs amma Fati tun zuwan da yayi bukin kannen ta motar ta ya samu matsala bai sa an gyara mata ba kuma yana sane da hakan.
Ga wanan yarinyar shiga da ficen da Nafisa keyi a cikin dukiyar shi bai taba tsone mata ido tai mashi gori a kan hakan ba.
Kafin barci ya dauke shi yayi tunane kala kala a wurin kafin barci ya sace shi ya manta da komai da ya faru a wanan wunin.

Washe gari bayan yai sallah asuba bai kwanta ba yana zaune yana addua a gurin don neman mafita ga Allah akan damuwar shi.
Sai da rana ya dan haska ne ya daga ya sauko daga sama zuwa part din mu don ya duba jikin nawa ya samu kofan mu yana a rufe ba,a bude ba yai nocking yaji shiru haka ya sa ya gane muna barci har lokacin don da mun bude mai.
Part din shi ya koma ya shiga wanka ya kimtsa cikin kananan kaya kamar kullun yana shirin fitane yaji an turo kofan daki.
Ba sai ya juya ba don yanzu ya fara banbance yanayin shigowan mu dakin don zai fahinci wasu abu ga yanayin kowacen mu.
Samad ina kwana tace mai daga inda take tsaye ta kasa karasowa inda yake lafiya ya amsa mata fuska daure.
Don Allah na zo ne dama in baka hakkuri ga abinda ya faru jiya kuskuren fahinta ne wallahi.
Idona ya rufe ina ganin kamar wani abu ya faru ne a tsakanin ku a lokacin ashe ba haka abin yake ba don Allah kayi, , , , ,
Katse ta yayi da fadin idan ma wani abu ya faru a tsakanin zaki hanane ba mata na bane ita kamar yadda kema kike matana.
Ko ansa min dokan cewa dake kadai zan zauna in dinga mu,amula in bar sauran nagaji da wanan halin naki Nafisa ba zan iya daukan shi ba kuma.
Daya ke shiri take so a lokacin sai ta kwantar dakai tana bashi hakkuri don dai kawai ya kyale su ita da yan uwanta a gidan.
Duk fadan da yayi ranan bata bashi kwararar amsa ba don gudun abinda zai yi jawo mata fita yayi karshe daga dakin duk da bai taba ganin ns damarta irin haka ba amma baisa ya nuna mata ya hakura da bukatan ta ba.
A falo ya samay mu ina kwance maryam tana hada tea a kofi shigowan shi part din maryam ta rude ta shiga gaida shi.
Daga inda nake zaune na gaida tare da fadin ina kwana yace lafiya ya jikin naki nace da sauki cikin lumshe ido.
Kinsha magani ya tambaya yana mai kura min idanuwan shi yanzu zan sha idan na karya nazo dazun baku bude kofa ba.
Bamu dade da tashi ba na bashi amsa ya karaso gap dani yana taba jikin nawa tare da fadin zazzabin ya wuce ke nan ko ?
Kai na gyada mashi alaman eh don magana ma nauyin yin sa nake yi a lokacin yace raguwa kawai zan so inga ranan haihuwan ki.
Ban bashi amsa ba don maryam dake falon ta gama hada min tana miko min kofin zata shige yace maryam da zan dan samu ruwan zafin nan yanzu da nasha kafin in fita tace to barin hada maka.
Sai lokacin nayi kwakwaran magana nace haba maryam kada fa yin haka ya jawo muna matsala kuma kin dai san halin matar shi da kishi.
Zama yayi a kusa dani yana fadin ke baki kishin nawa ne komay don nagani a idon ki yanzun haka.
Dariya maryam tayi ta shige kitchen ta barmu a wurin kokarin taba ni yake ina kaucewa tare da fadin yaya samad ka bari don Allah.
Da sauri yace what kema zaki bi jahilcin Nafisa ne kina kira na da Samad bayan kin san ma,anan sunan .
Is better idan zaki fara kirana da wani sunan na daban ba wanan ba don kin san mai sunan haukanta ne yasa take kirana da hakan nasha warning din ta da tabari takine.
Maryam ne ta fito kitchen din rike da ture a hannun ta wanda ta shiryo mashi kayan karyawa a ciki ta aje a gaban mu.
Yun kurawa nayi na mike don in hada mashi yace zauna abin ki na hutar dake na yau zan hada da kaina.
Kallon yadda yake hadawa nakeyi har ya gama ya fara kurbawa a hankali ya dago ya kalleni yana fadin bazaki sha naki ba sai yayi sanyi .
Dauka nayi na fara kurbawa naji yana fadin wani irin mota kike so a rayuwan ki don zan sa a duba maku.
Nace wanda kaga ya dace dani ko wani iri ne na gode Allah saka da alheri yace ba godiya a tsakanin mu don ba zan iya biyan ku ba sai Allah.
Bai dade a zaune ba ya kube tea din ya mike kudi ya miko min na dago kai ina tambayan shi na may nene yace ki karba tukun nasa hannu biyu na karba ina sauraren shi.
Kudin ce fane ne da zaki da na sauran abubuwan da baki dashi a part din ki a shirya min abinci mai dadi don Allah.
Nace amma sai naga ai wanan kudin sunyi yawa ga cefane kawai da kara biyu don ni ina da komai a nan kallona yake daga inda yake tsaye yana fadin.
No haka dabia na yake mai girki zan bata kudi da zai

73 / 144

Chapters