MIJIN BUZUWA complete Hausa Novels.txt

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   40 / 144

117K to 120K   out of 431K words

May yasa kike magana kamar wata bagidajiya ne khadija samu yafi iyawa aida samu din ai yadda zakiyi dashi ba abu bane mai wahala.
To bazan roka din ba period sai kuma may a take ta bata ranta a wuri banza nayi da ita na mike ina dauko kayana da zan goge itama batayi min magana ba.

Yana zaune a falon shi kiran Fati ya shigo mai a waya bayan sun gaisa dashi dan shiru ne ya biyo baya sai can ta kau da nata miskilancin tace naga dubu dari biyar ga account dina dazun.
Shima cikin magana kamar yana gune dayin maganan ya bata amsa da cewa eh kudin da kika bukatane nace a tura maki har wanda zaki wanin abin.
Angode tace mashi zata kashe wayan yace ke baki taba kiran mutum sai idan wani lalurar kudi ko wani abin ya taso maki zaki kira.
Bazaki kira kiji halin da mutum yake ciki ba anan tace yanzun kiran nawa inyi godiya ya zama laifi ne kuma ?
Tsuki yaja tare da kashe wayan ya lumshe idon shi yana jin takaicin wanan baki halin na fati a kulun ita bata taba wayewa tana nan a yadda ya san ta a baya.
Karan takalma daji ne yasa shi bude idanuwan shi ya sauke a gare ta ba laifi idan zata fita tana kwalliya na kure a daka.
Sai dai a gidane baka taba samun ta a cikin shiri yadda ya kamata gashi shi mutum ne mai son yaga mace ko yaushe a cikin kwalliya hakan nayi mashi dadi sosai.
Karasowa tayi gare shi tana fadin zan fita don kasan yau saura yan kwanaki kadan bukin namu zan leka inga may ake shiryawa a gidan kareemay din.
Yanzu wa kike fadawa da zaki fita kin nemi izzinina kan zaki fita din kallon shi tayi tana dariya tace wata sabuwa ke nan ?
Yanzu fitan ma da zanyi nan cikin gari sai na nemi izinin ka ko may bafa gari zan bari ba wanan wani magana kake nema kuma ?
No ba sai kin nemi izzini ba tunda haka kika daukar wa kanki amma ki sani komai daren dadewa watarana wace zata nemi izzini na a gidan nan tana tafe.
Da sauri ta gimtse fuskan tace bako a gidan nan ba idan ma mafalki kake ka falka ba wata shegiyar mace da zata sake shiga rayuwan ka kuma muddin ina raye kai koma ban raye na fada maka haka.
Kina zancen ki dai yanzu don kin ga ban tashi ba cikin daure fuska tace don Allah mu bar wanan zancen zan fita lafiya kana son bata min rai na.
Ta juya ta fita ba tare da tayi mai sallama ba don ranta ya gama baci sosai dashi a lokacin nan ta fita ta barshi zaune a falon .
Zaman falon yaji ya ishe shi daga inda yake zaune yake jin kukan yar shi na zuwa mashi haka yasa ya mike yabi inda kukan nata yake zuwa.
A dakin Yanyala ne kukan ke fitowa ya tsaya daga kofa yana kwakwasawa ba a karba ba yasa kai dakin ya samu yarinyar ta tashi daga barci tana zaune tana kuka ita kadai a dakin.
Dauko ta yayi zuwa sama yayi mata wanka ya bata abinci har ya shirya ta ya fito gidan ba wanda ya nemay ta cikin gari ya fita da ita yawo.
Gidan Yusuf ya nufa ya samu zai fito sai suka fita tare da yusuf din Yusuf ne ya kalle shi yace ina mukayi yanzu ga yarinya ka dauko kuma ?
Yace dashi kaini gun khadija please batare da ya kalle shi ba murmushi Yusuf din yayi yace yau ranka a bace yake halan ?
May kagani kace haka yace naji kace in kai gun khadija abinda na dade banji ba a gare ka shiyasa nasan an bata maka rai ke nan.
Ya furzo iska daga bakin shi tare da kara rungumay yarinyar a jikin shi yace ban san irin rayuwan Nafisa ba Yusuf yau da yake ranan hutu ga kowa daya kamata in zauna gida in huta da iyalina.
Sai gashi ta kirkiro fita wanin unguwar da baida dalilin komai wai kawar kawarta ne zata buki shine suka fita gin shirye shiryen bukin.
Aka bar wanan yarinyar tana kuka ita kadai a dakin da sauri Yusuf yace subbahanallahi ina masu kula da yarinyar suka tafi kuma ?
Yaja tsaki yace itama ta iya fita tabarta don may zasu tsaya kula mata da ya suma sun tafi nasu mana.
Kai Allah ya sauwaka da halin bariki wallahi ba don nasan ka tun farko ba Abdulsamad da sai ince auren bariki kukayi da nafisa.
Yanzun dai ni kaga ina jin kunyan Khadija wallahi na dade ban kirata ba kuma ban nemay ta ba tasan kuma muna garin .
Ranan yakai three weeks mun hadu da ita da Nafisa a shago nakaita taiwa Bannan sayayya sai gasu ita da maryam har dan rikincin kayan shafa yaso hada su a gurin.
Kasan halin nafisa da rashin hakkuri nan dai suka rikece ya bashi labarin komai da ya faru a wurin a tsakanin mu.
Dariya Yusuf yayi sosai yace dakyau khadija baki daukan ta kwana ko kadan AA yace shine matsala ta da ita wallahi.
A bakin hostels din mu suka tsaya aikawa sukayi a kirani bayan an tabbatar masu da ina ciki wata Annah ce tazo ta fada min ina da baki a waje.
Ban tsaya wani gyara ba nasa kai na fita ganin kowaye yake nemana din tun daga nesa na hangoshi yana ma yarinyar wasa a mota.
Har na iso inda suke fuska daure bai dago kai ba hannkalin shi naga yarinyar muryana yaji ina gaida Yusuf.
Ya dago ya dan kalle ni bance dashi komai ba lafiya dai na gan ku a wanan lokacin na tambayi Yusuf din cikin daure fuskana.
Haba kaunata kin daure fuska haka kamar ba gobe ai kya gaida dayan yayan naki ko tunda kin gan mu tare dashi nace ai ba wuri na yazo ba.
Ka taba ganin mai arziki mijin hamshakiya yazo wurin diyar matsiyata wace bata kai matsayin a tsaya da ita ba ?
Haba khadija ina wanan maganan ya fito haka kuma nace gashi nan ai ka tambaye shi idan nakai matsayin yazo inda nake sai ya fada ma .
Murmushi AA din yayi yace da zaki shigo daga ciki zaifi don wanan zafin ranan zai iya maki illa anan har lokacin bai daina wasa da yarinyar ba.
Ido na waro waje nace mota ai sai ku da matan ku yar matsiyata da bata gaji shiga mota ba ina zan taba motar ku in sha maku talauci a ciki.
Motan ku na gama shigar ta tun ranan na dogara ga yadda Allah yayi mu ni da mahaifa bamu kai kan mu inda Allah bai kai mu ba.
Ido ya runtse yana jin maganan da nake fadi har cikin ranshi Yusuf yace dakata kauna na nasan abinda yasa kike wanan maganan yanzu ma shi yace muzo mu duba ki don tun ranan bai samu lokacin zuwa nan ba.
Ga kuma yar ki nan ya kawo maki ita ki ganta mun san Nafisa bata kyauta a yadda kukayi din nan ina ganin shine dalilin ramshin zuwan shi gurin ki don yasan dama a jirace kike dashi gashi kuma ashe har yanzu baki huce ba ke ?
Akan may zanyi fushi da abinda ta fada ai gaskiya ta fada ba karya ba ni yar tallakace bamu da ko keke a gidan mu ita kuma da ya mayar yar masu arziki ba rawa taiwa Allah ba ya bata shi.
Sai dai ta sani daren baiyi ko balle gari ya waye tajira taga zuwan daren tukun kafin ta wullakanta mutum.
Yarinyar ne tasa rikici don haka hankalin mu ya koma gare ta yana dan jijiganta ta kallon inda nake tsaye a side din Yusuf tana mika hannun ta.
Yusuf yace kin ga Banan tana ba mamanta hakkuri on behave of her father murmushi nayi ina kallon yarinyar nace fine girl wanan bai shafe ki ba ko ?
Daga inda nake na mika hannu sai yarinyar ta zillo zuwa gurina banyi gigin karban ta a wurin shi ba sai cewa nayi ku kaita gida mana.
Taga kuna kama da uwar ta ne take dauka ko ita ne nace Allah dai ya tsare min kama da wanan matar yarinyar bata bar kukan ba haka yasa naji har cikin raina na mika hannu ya miko min ita in dauke ta.
Da sauri ko tazo wurina karban yarinyar nayi ina dan jijiga ta a hankali tare da shafa mata bayan ta sai tai shiru tana ajiyan zuciya a jikina.
Ikon Allah banan kin san ta ne Yusuf ke fadan haka yana dariya AA yace daga inda yake zaune dauka ta ko maman ta ne don ta ganta fara.
Farin mu ba daya da ita na na fadi a tsiwace shi dai murmushi yayi kawai bai yi dogon magana ba sai Yusuf ne yace dani wai yanzu na fahinci gori motar nan ya bata maki rai sosai fa.
Wallahi ko daya raina bai baci ba don nasan rashin ilimi ne yasa ta fadi haka ba wai tasan ni ko wacece bane don ita halinta ne wanan.
Khadija kina son mota da sauri na dago kai ina kallon shi kamar bashi yayi maganan ba sai kuma na mayar da hankali na gurin yarinyar dake kokarin yayemin gyale dana yafa a kaina.
Yusuf yace ana tambayan ki wai kina son mota ne kai na girgiza nace ina yar tallaka dani ina zanje da mota ita mota ya dama a yanzu har take fankama da hakan.
Kiran sallah azahar aka fara yi Yusuf yace tau ashe har lokaci ya jane haka ban an kara ba zamu tafi da fatan kanwana ta huce ko ?
Murmushi nayi don ban son jan zance ina son fara aiwatar da shiri na akan buzuwa yanzu ina kokarin mika yarinyar gare su tare da fadin .
Sai ko yarinyar ta make a jikina taki zuwa karshe da na matsa da mikata sai tasa muna kuka tana lafewa a jikina.
Yusuf ya juya ya kalle shi tare da fadin yaya ke nan za ayi yace mutafi kawai anjima zan dawo in dauke ta in mai da ita gida.
Bazatai kuka na na tambaya da sauri yace ba gashi kin gani da idon ki ba taki zuwa wurin mu ku shiga da ita don ba gida zan tafi ba dama.
Haka suka ja motar su suka tafi yarinyar kuma bata damu da tafiyan su ba din muka shiga ciki da ita maryam bata nan sai da ta dawo ta samu ina bata indomie dana dafa mata tana ci.
Tambaya na tayi ina na samo yarinya haka diyar AA ne na bata amsa kai tsaye ido waje take kallona da mamaki a ina kika samota kuma ?
Shiya kawo ta na bata amsa in bata wanan in bata wancan har barci ya dauki yarinyar .
Ina da wasu set din ribon a jiye kana na a hankali na kama kan ta ina mata kitso tana barci .
Har na gama bata tashi ba na daura mata ribon din a kowani tukuwa yarinyar ba tashi don yadda nake kama mata kan a hankali.

Wayan shi ne Nafisa ta kira a gigice wai basu ga Banan ba a gida yace kamar ya ba a ganta ba may kike nufi.
Nan ta rikece mashi tana koro mashi bayanin yadda yanyala ta kirata daga gidan buki tana fada mata basu ga yar su ba wai.
Yace maganan banza ke nan duk inda suka kai min yarinya na su fito min da ita kafin in dawo gida ko rayuka ku su baci ya kashe wayan cikin hasala.
Ranan dai nafisa ta kirashi a waya yafi a kirga bai dauka ba kuma bai koma gidan ba kamar yadda suke jiran shi ya dawo duk ta fita hayacin ta yar ta ta bata a gidan.

Yanzu baiji kunyan idon ki ba khadija ya dauko yar shi ya kawo maki yar matar da tayi maki zagin wulakanci a saman hanya.
Wallahi da nice ba zan ko kalli inda yarinyar nan take ba balle ya bar min ita da sunan lalashi duk wanan abin fa sallon ba da hakkuri ne irin na maza.
Shi a dole matar shi ta saba maki ya wani dauko yarta ya kawo maki nan don ya nuna maki ya isa da gidan shi ko may ?
Dariya nayi nace ke ma kin san in dai wanan mutumin ne ba zai taba bani hakkuri ba bakina da nashi ba kuma kawo min yarinyar yayi ba nan .
Sun zo da itane tagani ta lakemin taki yarda su tafi da ita shine yabar ta har anjima zai zo wai ya dauke ta yace .
Tace bakin ji ba may ye na kawo maki ya kina makaranta kina fama da karatun ki ni dai nasan akwai wani abu a bayan wanan abin.
Tashin da yarinyar tayi ne tana kuka hankali na ya tashi na rarashe ta tea na hada mata tare da bata cup cake sai tayi shiru taci gaba da wasan ta.
Sai bayan magariba ya dawo daukan yarinyar ya bugo layina yana fadin gashi ya dawo in fito da yarinyar ya mayar da ita gida.
Tun daga nesa ya kura muna ido yana kallon mu cikin mamaki yadda yarinyar batai min kiuya ba har muka iso gurin tana ganin shi ta washe baki tana dariya.
Sai dai yana tara hannu tazo ta make tare da lafewa saman kafaduna ban san lokacin da murmushi ya subce min ba yace Banan yau fushi kike damu ne a gidan haka ?
Nace kasan yaro kamar kyanwa yake yana son a kyautata mashi ko da yaushe indai zai samu jiki gurin mutum .
Wanan ne kuma bata samu a gurin mu daga ni har uwar ba mazauna gida bane dukkan mu nace kuna daukan alhakin ta gashi babu ruwan ta wallahi.
Dan shafan ta da nakeyi daga tsaye yasa ta koma barci nace kaga tayi barci yanzu lalaba ka maida ita wurin uwar ta tun kan ta tashi tasa rikici.
Banji yace komai ba haka yasa na dago ido ina kallon shi sai naga yana wani lumshe ido yana kallon mu.
Da sauri na kawar da kai daga kallon shi kamar bangan shi ba muryan shi naji yana fadin .
Kun dace da Banan kamar kece uwar ta kenan goyo zai maki kyau sosai fa nace don Allah kakai yarinyar nan gida tun bata tashi tasa rikici ba.
Yace af koran mu kike yi don na fadi gaskiya gaskiya kuma da kama da ita kamar kece mahaifiyar ta fa.
Nace kaidai ka sani da jan magana a bayan idon uwar ta zaka iya fadin komai yanzu .
Tsoron idon uwarta nake ashe nace ai naga zahiri ne ranan don Allah ka karbe don hannuna ya fara tsami da daukan ta.
Miko jikin shi yayi don ya dauki yarinyar numfashin mu ne ya hade a guri daya nayi saurin ja da baya jikina yana rawa rigumay ta yayi a jikin shi yana fadin Thanks for today Banan da baban ta sun gode.
Yana kallon kan yarinyar da ya sha kitso fuskanta ya fito shar da goshin ta saboda kitson da akai mata din yace wayayi mata wanan kitso haka nace gun wa ka kawo ta.
Matsala na dake kenan tambaya a cikin tambaya halin ku na yan Africa leda na miko mai ciki da kayan ciye ciye nace a rika mata wanan idan ta tashi yai min godiya muka rabu yana cikin farin ciki da ya kasa boye wa.
Sai da ya wuce a zuciyana nace ko yaya akayi yazo da wanan yarinyar nan yanzu kuma may zai koma ya fada mata kai halin maza sai su wallahi maganan maryam ne ya dawo min a raina.

Ya na isa gida suna waje bakin get cirko cirko dasu sai da ya gama seta kan sa ya fito da yarinyar a kafadan shi.
Gaba daya suka nufo inda yake nafisa ta mika hannu zata karbi yarinyar ya gwauce ya wuce ta ba tare da yayi mata magana ba.
Sai da ya kwantar da yarinyar dake barci a saman gado ya juyo zai wuce ta tace ashe kaine kafita da yarinyar nan baka fada muna ba.
Ke ki fita min a ido banson maganan banza har kina da bakin tambaya na haka da kikasa kafa kikabar ta agidan tana kuka iidan wani abu ya samay ta fa.
Wallahi kasan su Yanyala na barwa ita amma sai suka bugo min waya suna fada min wai basu ganta ba.
Yace bari kiji akan yarinyar nan zan iya bata muku rai baki daya a gidan nan duk sanda kuka bari haka ya kara faruwa.
Kitson dake kan yarinyar dake barci saman gado take kallo muryan ta ne take tambayan shi a wurin mace kakai ta ke nan wani kallo yayi mata sai lokacin ya tuna da zata iya tambayan shi haka.
Kallon yarinyar yayi da take a kwance shar kamar zaiyi magana sai kuma yaja kafar shi ya wuce zuwa dakin shi.

40 / 144

Chapters