Allah komai nason kwanciyan hankali wallahi ji babangida kamar bashi bane ke wanan abin.
Altine tace gaskiya tsohon ku ya sauya gaba daya wallahi gashi yanzu har za a sake dashi ayi hira da komai dashi ya sauke wanan jin kan nashi na da can.
Momy tace yarinyar nan ai ba karamin kokari tayi a cikin ruwan sanyi take ganar dashi hanya ba a garaje ba indai mace zata iya bin namiji a saukake sannu sannu zasu kai ga manufan da ake nema.
Ya Amina tace yanzu idan mace na samun itin kulawan nan ga namiji mai zai dame ka kuma da zancen wani kishi can indai za a baka hakkin ka.
Hakkuri ai bai bar komai ba yanzu datayi hakkuri gashi Allah ya bata wa yan nan yara haka masu kyau dasu da sha,awan dauka.
Samira ne ta shigo dakin da sallama sai da nayi mamaki nace Samira ashe baki da lafiya ne ta zube a gabana tace anty wai kin haihu nazo in ga baby ne.
Yaron dake hannu na take dan tabawa tana mai wasa ta dago tace ance biyu kika haifa anty nace eh ga dayar can hannun maryam ta juya tana kallon ta daga inda take durkushe ta juyo tana fadin so cute .
Anty yaran nan nada masifan kyau sun fi baby Ami kyau sosai nace itama tana da nata kyau din ciwo daine ya mayar da ita hakana ai.
Tace hummm that mumu girl sai kuma ta bata fuska tana fadin zanci abinci anty nace tuwo ne fa kin ga kalar shi ta dan ya mutsa fuska sai can tace zanci a ban .
Nace baku dafa abinci bane tace wai Ami ta wuce da key din kitchen kin sai ance that madam ta fadi and she break her leg .
Allah sarki nace mata tana mikewa daga durkushen da take tace anty kina tausayin ta ne ke ni ban son ta muguwa ce sosai ita da Ami yau naji suna magana kan twins din nan fa zasu kashe su ni kuma ban yarda a kashe yaran nan masu kyau haka dasu su kashe momo din Amin dai amma ba wanan ba.
Bani ba duk wanda ke dakin sai da hankalin shi ya daga nace cikin karfin hali ke Samira kada ki masu shiri tace wallahi anty naji ne sai Amin mu ta kore ni dakin.
Nace ikon to Allah ya tsare laraba na kira nace a ba su abinci har da sauran dake part fin
Tin samira bata fita dakin ba Altine tace suyi a hankali don sun fara ganin kohin tagwaye a kan su tun yanzu in sunce sheri suka iya sun kai karshe ai.
Yarinyar dai ta kalle ta ta fita dauke da abincin da laraba ta mika mata momy tace wanan zancen ba na kyalewa bane fa babangida zanwa magana ya binkici yarinyar yaji komai wanan karon.
Don gaskiya ba maganan kyalewa bane wanan don mutum mugu ne tunda tayi niyar masu cuta tasan duk hanyar da zata bi ta cuta masu din
Nace anya ko an fada mai zai yarda don kirikiri yasha kamata da makamancin case din nan ni banga yana daukan wani mataki ba akanta sai ma abinda ya karu don agaban shi sai tayi ikirarin halaka mutum bai kuma daukan matakin komai wallahi.
Altine tace ko ba zai dauka ba wanan kan dole a fada mai komai don ya sani ya bincika yarinyar yaji da kunnen shi mana.
Momy tace kai abin ne da daure kai wallahi ya Amina tace momy kun san fa ba banza ta barshi ba wallahi aikin banza nayin haka ina sai dai asiri kan inji maryam.
Tare da Yusuf suka shigo part din falo na fito na samay su Yusuf yana min barka tare da yaba kyaun yaran sosai Altine ce tace dama kai muke jiran shigowan ka tun dazun.
Yace shi tace eh sai momy ta karbe tace dazun muke jin abin mamaki a gurin yar nan diyar Nafisa babban sai Altine tace yar agolan gidan ka dai.
Kai ya girgiza yace ke baki barin sheri dai momy ta kwashe abinda mukaji a wurin samira din ta fada masu bude bakin shi yace kai shine abin damuwa momy ?
Nafisa bata da hankali wallahi zafin kishin ta ne kawai amma may zata iya yiwa yaran nan don tasan ba kyale ta zanyi ba itama.
Yusuf ne yace a, a AA wanan ba karamin magana bane ya zama dole wanan karon ka nuna mata an fasan abinda take yi kafa san halin Nafisa sosai wallahi don may zaka tsaya yin gardama kan abinda ka sani kuma.
Shiru yayi yana sauraren maganan kowa yanzun zan bikici yarinyar inji komai kafin in mata magana sai lokacin na sauke ajiyan zuciya jin zai dauki mataki akan zancen.
Abinci aka fita masu dashi yaci sai da ya sallami Yusuf yazo ya kira Samira cikin dabara ya fito mata da zancen ya shiga jin har abinda bai tsamani ba daga gurin yaran yana recoding a wayar shi.
Ta dawo yawon gantalin ta a falo ta zube karfe takwas da wani abu tun safe da ta fita abin ya faru da madam suna can wurin jinyar ta.
Ya sauko daga sama fuskan shi a daure yace ina kika fito a wanan lokacin tace amma dai kasan abinda ya faru da madam gidan ko ?
Na sani sherin ku ne da kuka dauko ya fara fada maku ai tace ban gane sherin mu ba yace Fatiha ina son ku saurara kuji ya kuna oudio daya dauka na hiran shi da yaran ta.
Ba Nafisa ba har yan uwanta da yanyala kanwar uwarta sai da suka kadu dajin komai tiryan tiryan yadda ya fara tambayan yaran yace kuga sabbin kannin ku ko yaran suka ce mun gani Abbi har biyu suna ta shirmay su yana dariya.
Yace ai za a sace maku sune Ihisan tace in kashe wanda zai sace su in yanka shi sai Samira tace ko Ami ban yarda ta kashe su yace takashe su kuma samira tace eh Abbi naji suna magana da Madam din nan ai ta kwashe komai ta fada mai.
Oudio na karewa ya dago kai yace may zakice kan wanan yar uwarta ta hawaye yazo ma tace amma ke kan halin ki ya fita daban a cikin mu.
Ban san may kika dauki duniyan nan ba wallahi shiyasa nace wurin bakar bidan asirin ki kika dauko yar nan dakika tsana.
Tace Fatiya kada ki fada min maganan banza don bake ke min zaman aure ba zan shigo kasar su ina bare su kyale ni ne ?
Don wanan hiran yara da ya dauka har zaki dauka gaskiya ne in shirya masu akayi suce haka kafin a dauka fa baki tunanen haka ke ?
AA ya kaleta yace nine zan shirya maki sheri ko may yace bari kiji wanan recoding din zai kashe ga hukuma ne yanzu don su sani ko ciwon kai daya daga cikin diya na yayi wallahi ke ce.
Lokacin da kuke kulin sherin ku idon ki ya rufe da bakin kishi kin manta da yaran suna kusa dake bakin san abinda kike fadi ba.
Su yarane suna nan suna koyi daduk abinda kike yi a gaban su don haka ba zan lamunci wanan ba ga diya na ita Samira yar kice komai zaki koya mata banki ba don yarkice nai maki kara kuma a kanta.
Fatiya tace yanzu dai wanan kadai ai ya isheki ishara don babu abin kunyan dayafi wanan idan mutanen nan suji wanan zancen fa.
Yace yaushe kuma shiyasa suka hana mata yara an mayar dake mujiya maciya abin tsoro don sherin ki ta harzuka tace suji mana suma ba sherin suke min ba.
Ko ban san abinda take aikatawa a gare ni bane har canza min diya a ciki da tayi na sani amma baka dauki mataki ba sai wanan zancen yaran zakazo ka tsure ni da zancen banza haka.
Yace an cen za maki ya kamar yaya cikin tsure ta da idanuwan shi yace kowa yaga yaran nan ansan ba nata bane wallahi diya nane ta sa aka sauya mata zuwa nata.
Kana dauka zan yarda da hakane ko may yace Nafisa anya baki da tabin hankali kuwa kin san ko abinda kike fada nan dai kanwar tayi mata kaca kaca tace gobe zata koma Niger ina zata da wanan abin kunyar haka ?
Azo ana nuna su a tare kishi haukane ko may kin samu gidan da zaki huta mu huta rashin hankali ya hana ki kwantar da hankalin ki.
Cikin murje ido taciwa yar uwar nata mutunci tace ta tafi mana an tsare ta ne nan dama bata isa ta nuna mata ga abinda za tayi ba.
Don ba ita ke mata zaman auren ta ba ya mike yace zanyi maganin ki don haka ki shirya ki koma kasar ku don ba zan zauna da wace bata tsoron Allah ba a gidana.
Nan dai su fatiya suka shiga bani hakkuri da ban baki suka farar mata dole tayi shiru ya fice gidan gaba daya.
Duk abinda ya faru akan idon laraba itace ta shigo tana bada labari hankalin shi ya tashi sosai har yaji auren nafisan gaba daya ya fice mashi a rai.
Mun ci gaba da hada hadan shirin suna wanda maryam bata da hutu itace ke zirga zirga ka karatu AA da kan shi yace ya daukar min excuse a school inda suka ban sati biyu.
Yana jin dadin yadda yake shigowa gidan ya samu ana ta harkan arxiki da raha da dariya sai yake ganin gidan tankar ba nasa ba.
Part din nawa yayi masi karami don haka Altine ta mayar masu da zama can babban falon gidan inda gidan baya tsinkewa da kafar yan barka.
Abokan karatuna sun zo min barka lokaci daya suka hada kafa akazo don akwai hadin kai sosai a tsakanin mu lokacin Nafisa suna zaune a falon su ma.
Har falon gidan daya sha gyara kwana biyu da haihuwa an canza har labulayan falon da kujeru duk da ba a dade da suraj yasa aka gyara ba amma AA yace dole su sake wasu don bakin da ke shigowa barka.
Bayan sun ga yaran na fito muka gaisa dasu suna min barka da ba,a suna kirana da maman twin's.
Maryam ta dauko drinks ta kawo masu da zasu tafi suka bada gift din da suka zo min dashi matan sunce sai sun dawo suna su nace ko wanan ma na gode.
Tana zaune daga barin part din ta da yan uwan ta ganin yadda muke harkan da course mate dina ta tabe baki har suka fice ana wasa da dariya bayan sun dauki babies din.
Nan na dan tsaya muna hira da Altine sai naji tace idan da mutum bai haihu bane zai ga takaici saukin abin dai nabaya aka samu.
Murmushi nayi na girgiza kaina tare da fadin banda lokacin ki don ba finane yanzu a gabana ba abin arzikine a gabana.
Nasani ai tunda kin shiga kin fita kinyi musaya diyan da ba naki bane kowa ya duba ya sani ban san lokacin da Altine ta shigo ba tace kai amma ke katuwar jahilan inace haka.
Ke a tarihi kin taba jin wanan zancen naki na masu tabin hankali kinje gun tsafe tsafen kin sun fada maki karya tunda yaran ki ne ta juya zuwa nata sai kiyi yadda zakiyi ga yaran nan a gabanki ai.
Ke wai wa kike ne a cikin wanan zancen yar kalan dangi kawai na fada ko kun dauka bamu san komai bane tace a,a kin sani don naga alama tai mata alaman mara hankali da hannu.
Wasa wasa fadan su da nafisa yayi tsawo ranan Nafisa taga tujara taga zari agurin Altine yar duniyar mata don da wanda tayi da kazafi duk ta hada mata sai ga Nafisa na kuka da hawayen ta wai yan uwan Samad basu kaunar ta basu kaunar diyan ta.
Tunda ga Altine ta sheganta mata yaran da ta haifa dashi yau ya dawo ya fada mata matsayin ta a gidan dana diyan ta.
Da kyat dai su momy da yan uwanta suka samu suka rabasu ni dai har na gaji na shige ciki na bar gurin don ban iya tsayawa sauraren su.
AA ya dawo ya samu sun lafa Nafisa ta same shi yace ke ki barni da wanan haukan inji da abinda ya samay ina fama da abinda ke gaba.
Yana ce ta fice mai daki bai son kananan magana diya dai diyanane ba na wani ba tace ai baka damu da yaran ba wa yan da ka damu da zuwan su gashi kana rawan kafa an haifa ma yan gwal.
Ke may yasa baki haifa min ba in rawa kafa kan su kamar wa yan nan din yace ya kara hasalata nayi rawan kafa don an haifa min abinda ke kika kasa samar min a gidana.
May na kasa samu kana nufin namiji ai duk rawan kan da kuke nasan don shi ne kukeyi haka yace yan gwal din dai da kikace an haifa min.
Kinga rashin kyau gori ba abinda baki fada ma yarinyar nan ba a gidan nan kan haihuwa tana hakkuri da Allah ya tashi nuna maki abunki sai gashi ya bata biyu a lokaci daya kuma kyawawa har sun saki hauka.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: As usual na tashi tun da safe nayi wanka na shirya tsab dani kafin in fito laraba ta shigo min da abin karyawa ta aje sai dana gama shiri na zauna don shan kunun kanwar da yanzu na saba sha don nafi son shi da tea.
Altine ne ta shigo dakin zata dauki kayan yara ta kaiwa momy da tai masu wanka take fada min ga yar uwar Nafisa a falo tana magana dani.
Nace tace ta shigo daga ciki can sao gata ta shigo da sallaman ta fuskanta dauke da fara,a tace maijego sai kunun kanwa ina aje cup din nace Anty Fatiha kece ashe tace eh.
Ban samu shigowa ba ranan da aka kai muna kayan buki don jama,a sunyi yawa a lokacin nace kai haba ba komai ai muka gaisa ta tambayi yara nace ana masu wanka ne a dayan dakin.
Tace to idan sun fito ki shafa min kansu Allah yai masu albarka nace amin na gode sai naga ta gyara tsayu nace bissimila zauna mana tace ba sai na zauna sai dai magana nake son muyi dake dama.
Nace to ai gani tace don Allah ina fatan zaki fahince ni ki fahinci zuciyana kuma nace insha Allahu.
Tace kin san zama da mai ilimi da wanda baida sai anyi hakuri don zaka ga wanda bai da ilimi yana abu wani lokaci kamar zararre nace gaskiya.
Tace kiwa Allah kiyi hakkuri da yar uwata uwar mu daya uban mu daya amma mu kan mu mun sani abinda take bata yin sa a kan gaskiya.
Duk wanda ya yarda da Allah kuma yai imani dashi ina tabbatar maki baya taba tabewa a duniya Dija nasan kina da ilimin zamani dana addini gwargwado kima bazamu ce duk ba don kowa dan koyo ne.
Nace gaskiya ne tace a gaskiya ga abinda dan zama na ya hango min a gidan nan dan zuwan danayi na zauna daku din nan.
Na fahinci dukkan ku kuna da rauni sosai kina sani fa ba mai iya maka wani abu a rayuwan ka bayan Allah in ma har wani abu ya samay ka tabbatar wanan abin kaddararene a gare ka dama kuma bamu iya kauce wa kaddaran mu.
Zaman gidan nan yana bukatan gyara daga gare ku ko in ce daga gareki ki tuna abinda ya kawo yar uwana gidan nan shiya kawo ki ke ma ta yaya zaku zauna kuna kona kanku saboda son zuciyar mutum daya tak.
Ta girgiza kai tace gaba dayan ku gidan kuna tsoron ta har mijin naku an san akwai asiri tabbas yaci annabawa Allah balle mu da ba kowan Allah ba face bayin sa.
Kina da makami a tare dake kin iya karanta shi don may ba zaki bi dare kibi rana ba wurin kwatoku har ita daga halaka.
Ki dage ki bata duk wani lokacin ki kina da dama yanzu ba sai kin dauki Alkur,ani maigirma ba a hannun ki yanzun ne lokacin da kike hutawa ki dinga aikwa ubangini kina fada mashi matsalolin ku sai ki ga sauki ta inda baki zata ba.
Amma duk kun biye mata ana wai asiri asiri da ita dake zuwa da wanda ke mata wakeyi in ba Allah ba ba wani abinda zata iya maki muddin kin koma ga Allah .
Ita kanta wallahi tasan kinfi karfin ta ga komai yanzu don ta fada na sani kuma haka ne mutumin da kullun kake binshi da sheri munana yana tsalkewa ai kasan yafi karfin ka.
Kada kiji ina wanan magana ki fassara min magana da wani manufa ina yin shi a matsayin ku na yan uwana musulmai har maigidan na zauna dashi jiya na fada mai inda yake da kuskure da rauni ya kuma fahince ni .
Da fatan ke ma zaki fahince ni na barki da saura a zuciyar ki sai ki nemo mafita amma ku gyara gidan ku don Allah inda kake fa shine wurin ka ba nawani