haka kuke son gani na dama kuka lakaka min aure binta ne ta amshe auren bagaki kin sake ba kin zama wata basaraka dake.
Baki na tabe yace kyale ta binta kinji tana matar last done haka takewa mutane korafi yanzun zaki koma ko kina nan zanje gidan hajiya in dauko yara ne dama sun maysa a dauko su suzo wurin ki tunda sukaji kina gari.
Nace ina nan har dare tare daku yace barin je in dawo mu sha hira ashe iya matar manya duk kin wani canza ga baki daya wallahi.
Nan dai na wuce ya na barshi ya shiga mota yana min sheri muna shiga na samu anty tana gyara falo su tana ganin mu ta washe baki tace mutanen Abuja.
Wallahi yanzu na gama magana yau idan azahar tayi ban ganki ba zanje gidan naku in ganki nace ai gani nazo yanzu.
Muna waje da mijin ki yana min sherin shi da ya saba ina ganin sai munyi fada dashi zai daina yanzu ma fa dariya ya dinga yimin a waje.
Binta ne ta gaida ita yasa bata bani amsa ba suka tsaya gaisawa ta tambaye ta mutanen gida tace suna lafiya bata tsaya ba ta mike tana fadin madam ni zan tafi sai kin dawo ke nan.
Nace madam kan ai tana abuja suna bushasha wata kawar buzuwa ce uwar dakin su suke kira madam tace ko wata garmakar mace haka karfafa nace ita ashe kin santa ma ?
Tace na santa mana lokacin da mukaje sunan ihisan sukayi muna tsiya suka kulle abinci Allah yasa da mommy na gidan ta saka aka kawo muna a wani gida.
Dariya nayi nace kai Nafisa ai ta tsula tsiya gidan nan kuma har yanzu akan yi take don ku jiya sai da muka kwasa da ita ai bayan fitar ku.
Kai khadija wallahi kina kokari mun dawo gida muna maganan ki da hajiyan mu take cewa ai tunda batayi galaba a kan ki ba yanzu bazata taba yi ba da yardan Allah.
Ke dai adai yi sha,ani wai ancuci na kauye ni abin nata gani shi nake kamar mai motsi akai tace babu motsi wallahi inji ya Amina haukan kishine irin nasu kawai su haka suke kishin su a haukace.
Nan gaba idan taga abin ma bai mata ba taga ba ci kokari zatayi ta wawashe mijin naku ta gudu kasar su bai kuma samun labarin ta.
To Allah ya kyauta nace ina dora kafana saman kujeran da nake zaune akai Binta tace wai khadija wallahi ba don na sanki ba da sai in ce baki taka kasa wallahi.
Duk kin canza gaba daya komai naki yayi fresh nace tafi yar sheri wanki da ko mota ya kasa sai min don tsoron buzuwa wani kasa zakice ban takawa kuma.
In dai mota ne tafe yake ai ki dai haihu ki gani har abinda yafi mota zamu saya maki nace oh haka kuke ashe kowa yaci ladan kuturu yasha dungu ko ?
Ta fice tana dariya ya Amina ta zauna gefe na tana fadin abindai da sauki yanzu ko na mede baki nace wani sauki dukkan su biyu fa anty ba wani sauki don ko anty fati ba baya ba ashe.
Tace ita fatin nace dama mana nidai kawai ban bin ta nasu ne don kawai a zauna lafiya amma ko ita ba kanwar lasa bace.
Tace zata iya indai Fatice don ba wanda ke jin dadin ta a gidan nan ko kwanaki na iske suna rikici da na shiga wai motar ta ya baci ta sayar bata fada ma kowa ba kuma an nemay kudin an rasa su.
Wai to Ya Amina may take da kudine sai naga tayi dariya tace ke ma ai ba sai kin tambaya ba ni dai abinda nake so dake khady shine.
Kada ki yarda da cewa wani zai iya maki wani abu ki yarda da Allah shine maiyin komai a rayuwa ki idan rokon Allah ne ki tashi da kan ki Allah maji rokon bawan sa ne.
Ki dai dage da gyaran jikin ki kina kara ma kanki daraja a furin mijin ki wanan kan ban hanaki yin sa don yana taimaka wa mace a rayuwan auren ta.
Amma bin boka ko malam kin san ba dabiar gidan mu bane kullun da wanan zancen nake kwana ina tashi ina kuma maki rokon Allah kema kada kiga suna yi kice zaki kauce ma hanya yanzu da abinda yan uwan Fati suke mata korafi ke nan.
Sai dai kuma dole ne yasa Fatin yin haka don tana ganin shine kawai mafita a gareta ta manta da Allah shine mai yin komai.
Nace anty ni jiya na kara yarda da halin ta da ake fadi ai wai fa kin yin girki tayi don kawai na taimaka nayi mata girkin sallah ranan danaga suna rikici da miji.
Ashe ta kulle ni a rai ta aje shine jiya taki girkawa da yai magana tace wai ai nice mai girka mai may yasa ba zai tambaye ni ba.
Tace ai da kin sani ki kyale su a zauna hakana mana ba ita zata sha wuya ba ita dake da yara ke haka fa take bata dadi da kowa bata shiga mutane ta waye.
Ai mijin nan naku yana da mata wallahi ga mutum har mutum amma bai samu abokan rayuwa a gidan shi ba shiyasa yake kara yin abu a dabbale wallahi.
Don mace na kara gyara namiji ta hanyoyi daban daban sai idan ba ai dace ba zaki namiji bai kullawa yan uwan shi komai.
Nan nake fada mata hiran mu da hajiya tace matar tana a cikin damuwa ne khadija yau ba maison ace nashi baida kirki ai.
Mijin ku fa yadda nake ji ba karamin mai kudi ba ne a garin nan shi ma rigima ne dai kawai da baida shi amma kinga yan uwa sai korafi sukeyi akansa.
Waini ya Amina yanzun haka zan zauna ban leka mama ba idan shi Daddy bai son ganinna ita mama fa da ya tauye mu da ganin juna.
Tace kin manta haka halin daddy yake ne ko suwaiba dake cikin gari ai dai kinga yadda suke kwashe wa dashi idan ta jera sati uku tsakani tazo gida.
Halin su ne na filani ya dauko yake wanan akidar haka ko kuma tsabar izzala ce ta haushi haka ban sani ba kiyi hakkuri kwana nawa ya rage idan kin haihu zaki gan su.
Ya Amina har wanan lokacin ban je gida ba gaskiya nikan da mun koma din nan zan matsa mashi zani gida ne don banzama har wanan lokacin ban leka su ba.
Shigowan yaran da ihun sune ya dakatar damu da hiran sukayo kaina na rungumay su a jikina Allah ya dora min son yara a rayuwana tun kan yayan ya Amina din.
Karamar da bata saba dani bane taki zuwa wurina dole na yunkura ina fadin zo nan yar bura uba mai shege kiuya kawai wai ita nan bata san ni ba.
Uwar tace ke ko ina zata sanki tunda aka haifeta ba zuwa kike sosai ba kuma datai wayon na kinyi aure ba zuwa kike yi ba tana ganin ki.
Mijin tane ya shigo gida yana fadin matar manya ke nan gani na dawo nace wata matar manya can kodai matar wahala may ke gidan ban da tarin fitina kullun safe da kalar da za a tashi dashi.
Yace mijin ki fa last done ne wurin kudi khadija bazaki fadi haka ba ai mana nace ya Adam kudi ai basune farin ciki ba ko ?
Yace hakanane kuma kin fini gaskiya tanan har ina cewa zan kawo wani ogana da ya dade yana neman fili a wurin shi yasa mashi hannu yaki ki muna hanya asa.
Tsuki naja nace wanan idan yaki abu ai ya kishi ne sai dai mu gwada mu gani idan zamu ci sa, a kawai amma bansa zai yi ba wallahi.
Yace kai dako kin kyauta muna wallahi khadija bashi ba harni nan da na warke idan wanan abin ya yuyu ai aje aki gaba daya zanyi in fara business.
Nace kai yaya Adam wanan wani irin abune da zaisa harka aje aikin ka kanshi kuwa yace wallahi khadija muddin muka samu ya sa ma takardan nan hannu mur warke har abada.
Ina fada maki AA ba karamin mutum bane fa sa hannun shine kawai ya gagara wata kila kuma da rabon mune har abin ya biyo ta wurin mu yanzu.
Ogana wani dan jalingo amma lagos yake zaune yayi ritaya shine ke ta binshi shekara da shekaru yaki saka mai hannu a takardan nan.
Shiru nayi ina tunane har banjin may yake fadi sai can naji yana fadin ai kinsan da ina da sister wace ta rasu din nan a lagos farkon auren mu da yayan ki nace eh yace to ai mijin tane nake maki zance nace in Allah yaso zan masa magana sai dai nasan zamu kwasa dashi koda zai yarda din ma.
Ya Amina tace ki daibi a hankali kada wanan maganan ya hada ku nace insha Allahu ko maryam kawana ta taba min korafin nan yaki saka ma mijin yayan ta hannu.
Ya Amina tace ashe haka yake dai sai mijin ta yace aikin nasu ne akwai hatsari a cikin sa da yanzu yana saka hannu barkatai da sun yi waje dashi tuntuni.
Ko jiya da dare naga matasan masu kudi garin nan sun parke motocin su a kofar gidan shi nasan wani harkan business sukeyi kinsan shi fa dan kasuwa ne kuma yana wasanni da dama ta idan kudi ke zo mai ke nan ai sai dai akwashi da boyon kurwa ne sosai wallahi.
Ina gidan tare dasu har dare anan na wuni sai baya magariba ne ya kirani yace wai kina inane nace gidan yaya na amma yanzu mijin ta zai sauke ni gida idan ya dawo sallah.
Yace No ki jirani in zo akwai inda nake son muje daga nan nace dashi sai kazo ya kashe wayan yaran ya Amina na rabawa goron sallah.
Kudi ns girka masu yawa na aje mata a gefen inda take zaune tare da kara kirga wani na sake aje mata nace naki ne da yaya Adam kuyi hakkuri dashi baida yawa.
Ita ya Suwaiba nace ta bude account taki har yanzu kuma tana raina sosai don nasan irin wahalan da suke ciki idan ta bude ai kinga zan dan rika tura mata da wani abu lokaci lokaci.
Tace zan ma daddy magana a bude mata din kin san halinta nako in kula da abu ai gaskiya kan tana bukatan taimako nace aishine kullun zaka bata abu sai ta hannun daddy dole shi kuma ya dinga fada da mutum wai kana rikon mijin ka kudine.
Ni kuma wallahi anty ban iya cewa ya bani kudi idan bashi ya dauka karan kanshi ya bani ba tunda muna samu a gurin girki idan zakayi dubu goman nan sai ya zube ma shi kafin ya fita.
Tace yanzu wanan din da kika bamu baiyi yawa ba khadija nace idan ban baku ba wazan ba anty tunda kune dole na.
Bandai ba dangin shi kudi kai tsaye sai dai in saya masu wani abu in basu gudun yawan magana da zargi tace haka shine daidai ai.
Don wallahi zargin ki zasuyi akan yana sakar maki kudi su bai basu ba tace kina da dabara da yanzu an fara kusun kusun kin san gidan yawa.
Wayana ne yayi kara na duba shine a layin ina dauka yace fito mu tafi nace a, a bazaka shigo ku gaisa ba ke nan kuma sai naji ya kashe wayan.
Tare da yaya Adam suka shigo gidan har cikin falon ta suka shigo suka shiga gaisawa tana mai barka da sallah.
Yaran suka zo suka rusunna suna gaida shi ina ganin yaji dadin hakane naga ya shafa kan yar karamar yana tambayan ta sunan ta.
Kudi ya debo ya basu tare da ajewa ya Amina nata a gefe ya mike yana fadin zai mu tafi zamu unguwar dosa ne.
Yaya Adam sai wani haba haba yake mai abin ni sai mamaki nakeyi na mike ina cewa ya Amina sai na kara shigowa tace yaushe zaku koma ne nace muna nan tukun ba rana.
Tace tafiyan ku ai kamar na filani ne idan ya tashi ko ba shiri ranan tafiya zakuyi nace to ya muka iya sai bi har wajen dirkekiyar motar shi suka raka mu ita da yara mijin ta yana tsaye dashi a waje nayi masu sallama na shiga muka tafi.
Yace yau kin kawo mata dawainiya ko nace wani dawainiya kuma mutum da dan uwan shi ina dawainiya ina zamune wai haka ban ko zata ba.
Yace baki da shiri ne mu koma nace ban ce ba ina dai tsoron ka saida nine kawai dariya ya dan sake yace dasun sai mai baki kan.
Gidan gwagona zani kanwar Abba tayi ciwo ance tana ta magana na ko yaushe can nake son muje mu gaishe ta don yau nake da lokacin zuwa.
Allah sarki ashe dai daddy yana da yan uwane da yawa haka yace sosai kuwa suna da yawa fa sosai don ma wasun su sun rasu ko .
Mun isa gidan da ganin gidan ya dauki shekaru don ba wani gida bane can irin dai gidan tallakawan ne kamar mu.
Da haba haba dattijuwar ta karbe mu tana fadin maraba da babana yau kaine a gidan ashe da rabon zamu kara haduwa dakai yace yana shiga dakin gwago kiyi hakkuri wallahi ban faye zama kasan bane muka shiga dakin tana kokarin kawar da tsumakaran saman kuje ta gyara mai wuri tana fadin zauna zauna baba ubangiji yai maku albarka da ka tuna dani yau.
Ina tsaye daga kofa ta kawar da kayan saman gadon gefe tare da fadin karaso kinji yar albarka tana nuna min inda zan zauna.
Na kai kasa saman carpet din sallah ta tare da fadin babba nan ma yayi mun ai aka shiga gaisawa tana ta tambayan shi mutanen gidan su da iyalin shi.
Ta juyo tana kallo na nayi murmushi ina gaida ita ce itace buzuwar ko sabuwar ce ta garin nufawa yace sabuwar ce gwago.
Ta kamo min hannu tana fadin sannu kinji yar albarka ki rike min ubana da kyau kinji kinsa mata suke gyara gida ina murmushi nace to babba .
Nan sarakanta da yara ta suka fara shigowa gaida shi suna mashi sheri bai iya wasan tobashi ba sai kamay kamay yake masu yadda na lura dashi.
Matar tana da kirki a yadda na kula ga addini magana kadan ta kawo Allah tana nuni da rikon zumunci a gare su.
Yace Ahmed fa yana inane yanzu sai da ta dan bata rai tace yana nan gida kasan shanin aikin su na Nepa ashe basu da tabbas.
Yana cikin wa yanda aka kora daga aiki kwana ki ga iyali ya tara kamar ka shima mata uku gare shi sai dai yadara ka don yanzu diyan shi goma ga ba aikin yi kuma.
Yace wai ikon Allah yanzu Ahmed din ke da diya goma gwago tace ga na shadaya nan a ciki ana maganan shi sai gashi ya shigo tace kaga dan halas nan ya shigo.
Kallon juna sukayi sai suka dara yace wai mama yau kodai dan naki yayi batan kaine yau baban ku ne a gidan ki gaskiya ranan yau ta dabance.
Sun dade rike da hannun juna suna shammatar junan su sai daga karshe yake fadin yanzu nake ji wurin gwago abinda ya samay ka.
Yace wallahi ya za ayi da sha,anin kasarnan tamu sai hakkuri yace haba Ahmed shi ne baka leka ni ba yace kasan ganin irin ku idan baku kuka nemi mutum ba abu mai wuyane sosai.
Yanzu ai cikin hukuncin Allah gashi kai ka nemay mu ka kwashe ladan dazun naji Altine na maganan su hada kafa suje gaida kawu da sallah nace mata mu mun je tunda aka sauko idi.
AA yace haba ya bamu hadu ba daku yace wallahi ana saukowa mukaje muka gaida shi kasan mu bamu wasa da kawun mu yace ai na ga alama.
Gwagon tace Alhaji banda kamar Alhaji ga yan uwa duka kaf har gobe Alhaji duk da girma ga iyali yana tsaye ga alamarina garin nan sai ta fashe da kuka.
Wani iri naji a raina dukar da kaina nayi kasa ina kokarin maida hawayen da yazo min a lokacin gwago kiyi hakkuri haka rayuwa yake AA yace mata ya ciro kudi ya aje mata tare da fadin gwago mu zamu tafi zan maida wanan gida don yanzun bata dogon hira ta fara tsufa.
Hararan shi nayi sai lokacin Ahmed din ya juyo gare ni yace amaryan ne ko buzuwar yace amaryan ce yace ikon Allah aiko ita buxuwan ce sak.
Yana washe baki ya mike tare da fadin muje waje muyi magana ina Altine ne tazo in bata goron sallah kada ta cini da bakin nan nata gwago zakiji yadda zamuyi da Ahmed din insha Allah.
Sai lokacin na mike tare da fito da kudi cikin jakkana na mika mata nima tana ta saka muna albarka muka bar gidan.
Sun dan dade da Ahmed din a waje suna magana ni kuma muna tsaye da wace aka kira da Altine din da sauran yan uwanta muna hira sukace zasu shigo kafin mu koma Abuja sai kunzo nace na shiga mota suna