dawo ki zauna.
Kallon shi nayi da mamaki sai naci gaba da tafiya ban tsaya ba ya sake fadin bakiji bane Deeadar nace ban san dani kake magana ba ai.
Dawowa nayi na samu wuri na zauna dan wani lokaci baiyi magana ba sai can yace wanan itace first wife din Fati nasan kin santa tun baya.
Ya ce ke kuma wanan itace khadija wace na aura kwanan nan a garin minna da fatan zaku zauna lafiya a tsakanin ku ban son inji wani fitina ya fito a gidan nan.
Da fatan kun fahinci abinda nake nufi shiru ya biyo maganan shi yace ina kuna jina tace a gyatsire munji Allah ya bamu hakkurin zama.
Nace Amin sai na dan yun kura nace zan iya tafiya yanzu yace is Ok ba tare da ya juyo inda nake ba haka yasa namike nabar masu falon na koma dakin da aka bani din.
Ban tsaya yin wani abuba na samu guri na kwanta da niyar barcin da nake ji sai dai barcin yaki zuwa min a lokacin sai tunanen yanayin zaman shi da matar shi har diyan su nakeyi.
Can barci ya fara dan fisga na naji an turo kofan dakin da nake kwance da sauri na bude idanuwa na na sauke su akan shi.
Yana tsaye daga kofa ya rike hanayen shi saman kirjin shi yace bakiyi barci ba ashe wutan dakin nagani a kunne na shigo.
Nace tsoro nake ji yasa ban kashe wutan ba tsoro ya tambaya cikin mamaki nace tsoron wanan gida mai girma haka nake ji na karasa fadi cikin kara rufe jikina da bargo.
Yace kenan izo in tayaki kwana ke nan kada dodon gida ya kama ki a gidan nace Allah zai tsare ni ba sai ka zo ba.
Allah da gaske nake gunda naga kina jin tsoro yana magana yake nufo inda nake kwancen da sauri na mike zaune nace rufa min asiri kada matar ka ta dauke ni macuciya.
Da can kaike tayani kwana da nake jin tsoro ni haka nake idan zan kwana inda ban taba zuwa ba.
Don na kwana wurin amarya na sai ta daukeki macuciya ai tasan abinda ke tsakanin amarya da angon ta ko ?
May ke tsakanin amarya da ango na tambaye shi ina hararan shi yace a tambaye ki ai kaidai zata a tambaya don kai kasan wanan.
Don Allah malam kafita don kada ta dauka wani abin ne ban son bata wa mutum rai a sanadina sai da safe.
Dariya ya soma yi ya fita daga dakin yana tunane a ran shi karfa maganan Yusuf ya zama gaskiya don yau jin kan shi yake kamar bashi ba ga wani feeling da yake ji a kaina wanda bai taba jin shi ba tunda na shigo gidan.
Deedar da yake so yake kauna a baya yanzu gata a gidan shi a matsayin matar sunnan shi ya kasa tabuka komai a ranshi yadda yake so .
Wani akasi yazo ya muna hijjabi a tsakanin mu wanda bai san ko may nene ke damun shi ba a halin yanzu.
Sai dai yanayi yau jin shi yake wasai ba faduwan gaba ko jin wani kasala da ke saka shi jin sanyin da yake ji yan kwana kin nan.
Yanzun tun deedar bata fahinci halin da nake ciki ba da ita har tazo ta gane abindake faruwa dani ai sai ta dauke ni mayaudari .
Ko ya zata fassara abin ya zama dole inyi nisa da ita har lokacin da abin zai zo mashi karshe.
Da wanan tunane kala kala ya shiga dakin shi ya kwanta inda ba a dauki lokaci ba Fati tashigo dakin ta samay shi.
Da safe ko dana tashi da zancen yaran dake so ya kaisu makaranta na tashi a raina sai dai bansan a halin da yake yanzu ba gashi kuma ina son tuna mashi.
Na rasa yadda zanyi fitowa nayi falon na samu laraba na faman shirya yaran nace barin taimaka maki mama kije ki karasa hada masu abincin.
Sun gama shiryawa na rasa yadda zanyi don haka na tura mai text har biyu a jere da juna laraba na fadin su fito su wuce kada su makara nace tadan dakata ta gyara ma karamin rigan sa don dai aja lokaci.
Yana kwance cikin barci yaji text na shigo mashi har biyu jere ga juna a wayan shi hannu yasa ya laluba wayan tare da duba text din.
Ka taimaka ka kai yaran ka makaranta tunda sun sa rai tun jiya muna falo muna jiran fitowan ka mamaki yayi sai ya ja tsuki ya koma barcin shi.
Ko may ya tuna kuma sai ya mike tare da zura rigan shi ya sauko kasa zuwa kai yaran makaranta.
Can ko sai gashi ya sauko da alaman daga barci ya tashi ina ganin shi na yi ajiyan zuciya ya sauko yana fadin idan kun shirya muje in sauke ko.
Da murnan su suka fita gidan na koma dakina bayan sun wuce don in yi wanka in gyara jikina don na saba da wanka tunda safe idan gari ya waye.
Na fito na zaina na shirya tsab dani don nasan da zancen shiga wurin iyayyen shi da zamu yi yau wanda yau shigan nawa wurin su a wani matsayi na daban ne.
Ina son indan mun fito in roke shi ya sauke ni gidan ya Aminan mu dan zan fi sake jiki a can idan ina tare da ita.
Kwance na koma nayi kwanciyar rigingine ina kallon rufin dakin sai aikin tunane nakeyi ban san barci ya daukeni ba a gurin sai wani lokaci naji ana taba min marana.
Firgigit na tashi daga yadda nake shine tsaye a kaina yana kallona kokarin tashi nayi zaune yace wanan kwamciyan da kikayi wuyan ki bazai maki ciwo bane haka.
Zaiyi na dan kwanta ne ashe barci ya dauke ni ban sani ba nace ina kwana ya amsa min da lafiya .
Deedar kina son kawo min wani sabon tsari a gidan nan da sauri na dago kaina nace har yaushe na shigo gidan da zan fara tsara wani rayi na dabsn can.
Don may zaki kwadai ta wa yaran nan abinda kika san ba zan iya yi masu shi ba nace zaka iya mana tunda kai ka haifi abin ka.
Wanan shine wani sabon tsari na dauka wani abin ne can na daban don uba yakai diyan shi makaranta kai ba abin alfahari bane a ganka da diyan ka kun fita.
Wani nacen yana nema Allah bai bashi ba kai ka samu kake sakaci da baiwan da Allah yayi ma saboda wani ra,agin ka na daban.
Bakina ya cafke yana fadin idan ina magana kinayi zanyi maganin wanan bakin mai katsalandan watarana .
Kokarin kaucewa nakeyi shikuma yana kokarin kama bakin nawa har ya hada jikin shi da nawa da sauri nake kokarin dago shi daga sama na amma na kasa.
Cikin karfin hali nake fadin may kakeyi hakane wai don Allah kadagamin mana kada wani ya shigo yagan mu a haka ya zarge mu.
Wanda ya shigo shi ya kawo kansa ai don ansan nan dakin ma,aurata ne nace wani aure masu aure dai suna inda suke yace barin gwada maki inda suke din.
Banyi aune ba naji ya laluba bakina yana kokarin hadawa da nashi cikin karfin hali da wani yanayi dake ziyarta na nayi kokarin daga shi gareni.
Sai naji na kasa sai faman motsu motsu nake ya kasa barin baki na can na samu na kwace bakina daga nashi ina gogewa yace baki natsuba ke nan.
Sake kokarin kamoni yayi zuwa jikin shi na gwauce ina fadin don Allah ka bari kada wani ya shigo ya samay mu a hakan.?
Idan suka samay ai tare da matata suka ganni ko ba zina nake aikatawa ba dai kayi hakkuri don Allah nace don nauyin shi akaina ya fara isata.
ZAINAB IDIRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bai kara bi ta kaina ba tun wanan ranan da ya kusa kawai gareni ban san may ya tsayar dashi ba ni dai naga ya koma baya yana sauke numfashi da karfi.
Bayan na gama sauke nawa numfashin ne na lalaba na gudu dakina na barshi nan sai da safe ya shigo min ido yayi mai zurun zurun kamar wanda yayi jinya kwana da kwanaki.
Zaune naki a gaban mirrow ina shirin fita school ya samay ni dago kai nayi na kalleshi na sauke kaina kasa da saurin don kunyan abinda yai min jiya nake ji.
Karasawa gaban mirrow din yayi ya dan jigina jikinshi saman mirrow din yana fuskanta na ina kwana nace dashi ina kokarin ci gaba da shafa mai a jikina.
Kin tashi lafiya yace tare da kai hannun shi ga man ya lakato ya fara murzawa ga hannayen shi a hankali.
Ban san may zaiyi da man ba sai da naga ya fara shafa min a bayana a hankali har zuwa mazauna na da sauri nace dashi nace ma ba zan iya bane ?
Basai kin fada ba don nasan bazaki iya mulke wurin nan ba ina tsaye to kafita mana tunda mun gaisa sai in karasa.
Fitana da rashin fitana baida wani amfani a gare ki yanzu don na gama ganin inda baki son in gani a jikin ki saura wuri daya yarage min in kai.
Wanda kema kin san dashi yanzu magana yake kamar mai yin rada kada wani yaji shi a dakin baki na turo gaba ina fadin .
Wanan ai shiga hakki ne yaya zaka kama kalle min jiki kamar wata yar , , , , , ji nayiya dagoni daga zaunen da nake yana kokarin mikar dani tsaye tare da fadin Deeder nima nasan ina shiga hakkin ki da yawa kuma kina hakkuri dani sosai a hakan.
Sai dai ki sani ba laifi na bane yin haka don Allah ki kara hakkuri ki kuma tayani da addua a bisa hakan dake faruwa damu ko yaushe.
Hakkuri hakkuri fa kace sai ya kashe ni da ido yana jiran jin abinda zan furta nace hakkuri akan may kuma bayan haka dama kake so kuma an kawo ni gidan naka kana yadda kaga dama dani.
Ajiyan zuciya ya sauke do bai tsamani amsar da zan bashi ba ke nan sai yaji ina maganan shirmay kuma.
Nan ma bai barni ba sai da ya hade goshin shi da nawa yana fadin yau zanyi tafiya zuwa waje nima tafiyan yazo min unexpected ne ban kwana da zancen tafiyan ba na tashi dashi.
Ya sake ni yana fadin bansan yaya zamuyi da zuwa school din ki ba sai dai zanwa musa driver magana ya dinga kaiki ua dauko ki idan kin gama.
Don Allah ki natsu Deedar ki kara kama min kanki duk da nasan kina iya kokarin ki but sai dai in ce ki kara don kada wani abu ya samay ki.
Kaima kasan rawan kai ba aikina bane mursmushi yayi yace na san baki da matsala ga hakan saidai yanayin zaman gidan nan dake da wa yan nan mutanen nake ji mawa.
Ka bari in koma hostel da zama har lokacin da zaku daidaita da matar kanace mai kai yana girgiza kai yake fadin haka wai kina haukane ke da wanan hostel din yanzu ai sai dai ziyara kawai.
Ina fa da gidajen da zan iya kai ki ki zauna a cikin garin nan ban kaiki can ba sai wani hostel gidan kowa da kowa ko da yake naga maza basu shiga amma dai ai wurin ba safe.
Ya juya ya nufi gadona ya dan kai kishingide yana fadin maryam zan wa magana tazo ku zauna da ita idan na dawo kuma sai ki sa a kawo maki wata wace zaku zauna a tare tana debe maki kyawa don gudun hakan don ni mutum ne mai yawan tafiye tafiye a rayuwa na.
Wardrobe dina na bude na fito da wani buje da riga na atamfa tare da hijjab don suna fitar min da shape dina idan na saka su da gyale.
Kallon kayan yayi sai ya tabe baki yana fadin sorry fa nikan manta da zancen hado lefen ki da hajiya mu ta tuna min .
Dama ka bar abinka don ni banda bukatan su yace saboda may ko sai kin haihu zan hado maki gaba daya.
Wani kallo na watsa mai idon shi na akaina nayi saurin kawar da idanuwa na shima shiru yayi yana tunanen da ban san may yakewa ba.
Bandaki na shiga na shirya ganin ba zai fita min a dakin ba ina shiri ina tunane a raina har na gama na fito yana a yadda na barshi a wurin.
Kallo na yayi tare da mikewa yana fadin idan kin gama muje in sauke ki zanga maryam in mata magana daga can.
Na maryam mai sauki ne ai don ko ni nayi mata magana zata zo sai dai wa yan nan kardawan da zaka barni da sune abin dubawa don mazan ma tsoro shigan su ke bani.
Dariya yayi yana mikewa tare da fadin ba mutane bane kamarki su da zasu baki tsoro ai baki da matsala da mazan sai matan da ke cikin gida tare da ke.
Ko matan banda matsala dasu don ba a kaina suke zaune ba ba kuma ruwa na dasu don ba zaman su nake a gidan ba.
Tare muka fito dashi na kulle wurin nawa yana gaba ina bayan shi muka fice a gidan lokacin babu kowa a falon suna cikin dakunan kwanan su.
Tafiya yake kamar baiso har muka kai kusa da school din ya juyo yana fadin kira maryam kafin mu isa ta fito ta samay mu a waje.
Banki ba na daga waya na kira maryam din tace gata nan fitowa tana hostel bata karaso ba tukun hostel din ya nufa muna isowa tana fitowa.
Da fara,a afuskanta ta tare mu tana fadin Mr & Mrs AA sannun ku da zuwa yau yallabai da kanshi ya jawo motar wani abu sai amarya wallahi.
Waye amaryan nace mata ina hararan ta tare da kokarin saukowa a motar yace zauna itama shiga zatayi in sauke ku baya ya bude mata ta shiga ya ta da motar.
Ya dan hau titin da zai sada mu da cikin makaranta yake fadin maryam an tashi lafiya tace sorry ganin ku haka wallahi ya rudani sai nake ganin abin kamar a falki wallahi.
Nace mafalki kike koma ki kwanta kan shi ya girgiza tare da murmusawa yace ke kowa baki bari ba ashe ?
Maryam tace ai kana fama wallahi da wanan mai kama da goyon kakan bakin nan ba komai sai bakar magana a cikin sa.
Yace maryam ina yi yaya na iya ga abinda nake so nace gulma ke nan wani abinda kake so sallon yaudara dai naka maryam kin ga ba wanan ba yace.
Alfarama nazo nema a gurin ki da fatan zaki min shi tace Allah yasa wanda zan iyane insha Allahu zan maka yallabai.
Ni mamakin yawan girman da maryam ke bashi nakeyi don ni har yanzu haukana bai barni na san ko shi waye ba alakarmu dashi kawai nake duba.
Tafiya zanyi yau nake son ki dan zauna min da madam na kwana biyu a gidan dafatan ban takura maki ba ga hakan.
Lah don wanan ai babu komai wallahi zan zauna da ita har zuwa lokacin da zaka dawo kada kaji komai yallabai tace.
Nace ai kyazo ki hadu da buzayen gidan shi tun a kofa zasu tare ki da halin shi tace ba komai tunda basu maki komai ba nima ba zasuyi min ba nasani.
Haushi ta bani don naso tace bata samun zuwa ya yarda in zauna dakina na hostel har zuwa lokacin da zai dawo daga tafiyan shi.
Godiya yai mata tare da rokon ta kada mu shiga harkan kowa a gidan matukar ba sun takale mu bane ya kare da cewa zanso kuyi hakkuri da duk abinda zasu yi maku don zasuyi da gayya ganin ban kasan.
Tace insha Allahu zamu kiyayye kada ya damu komai ba zai faru ba bayan mun tsaya ya dakatar da ita tare da debo kudi ya bata tafita tana mai godiya.
Wasu ya dibo ya miko min kai na kada mai tare da fadin ka barshi cikin basarwa nace ina da kudi a hannu na yace nasani ai baki zama dani ki zauna ba kudi a hannun ki ki rike wanan din ko wani abu ka taso bayana sai ki lalura dashi.
Nagode nace ina saka kudin a cikin jakka ta na zuge zif din na rufe ina kokarin fita a motar ba tare da nayi magana ba.
Zan fita ya riko ni yana fadin haka zakiyi sallama da maigida idan zaiyi tafiya Allah ya kai lafiya nace ina kokarin fita daga motar naji ya sake rikoni ta baya na sake juyowa .
Saida ya lumshe idanuwan shi yace min I gone miss you deedar give me a hug please jikina na ne naji yayi sanyi nace cikin daurewa sai kace ba zaka dawo ba kana wani kashe min ido sallon yaudara kuma.
Murmushi ya danyi cikin ciki yace cikin daurewan fuska please bazaki min ba ya wani