kulun.
Dakin a hautsane yake sai da na tsaya na kare ma dakin kallo sannan na fara takawa zuwa ciki na rasa ta ina zan fara da dakin.
A gadon na fara na yaye zanin gadon na kakabe gadon tare da share kasan dakin ina mamakin yadda yake rayuwa haka acin wanan dakin .
Ban ga takaici ba sai da na shiga bayin nan naja nayi tsaye ina mamaki duk gayen shi a haka yake rayuwa a tauye.
Kwal nayiwa ban dakin tare da wanke gajajerun wandunan shi da ya tara da singlet na bazasu a waje kasa don su bushe dawuri.
Na dawo na gyara ko ina na dakin tare da saka room fresh din da nagani a aje nagama na nado mai inner din shi nakai cikin wardroveb na jera mai wanda bai bushe ba na baza a bandakin.
Koda na dawo dakina na gaji don haka wuri na samu na kwanta don in huta sai barci mai nauyi ya dsukeni a gurin ban tashi ba sai uku da wani abu a gagauce na mike naje nayi alwala na dawo na tada sallah .
Koda ya dawo ya shiga part din shi abin ya bashi mamaki yadda dakin ya canza a lokaci guda ga kamshi da kyali yana tashi a dakin.
Har part dina ya shigo yana min godiyan canjin da yagani a dakin nashi ya samay ni a kwance falo ina karatu ina saye da wando da riga sun matse min jikina .
Yayi min kallon tsab idon shi ya sauka saman kirjina ya dago ido ya mayar a fuskana da yasha kwalliya.
Yace ce sannu da kokari na samu wuri na yau ya samu gyaran da ya dade bai samu ba sai yau a wurin ki.
Bai gama magana ba sai ga Nafisa ta fado muna dakin tana huci tare da zare ido.
May kazo yi dakin wanan ko ka manta da sauran lokacina har yanzu tunda magariba baiyi ba yace ke kada ki kuskura ki kara shigo mata shiya da sunan haukan kishin ki.
Wanan wani irin shashanci ne zaki fado ma mutane daki babu ko sallama tace nice shashan yau samad yace idan ba shashamci ba yanzu may kikayi haka.
Ya nuna mata kofan dakin da hannu yace ta fice tace ba inda zan tafi sai ka fito mun fita tare idan ba haka ba sai dai mukarasa lokaci mu anan.
Daga inda nake zaune ina kallon su ina rike da littafina da nake da nake bita ciki nace saukin abindai yau yake naki anjima nawa har zuwa gobe iwar haka sai ki kama.
Kin ga ke nan kin rage tunda har zaki iya sakar ma wata shi na wani dan lokaci koma in ce wasu dakike son haka may yasa bakije kin auri mijin ki ba.
Kika zo kika auri mijin wata watan ma har da kari kuma kika samu ai irin wanan ki aurin mijin ki na kan ki ba mijin mamu duka ba.
Zagi ta fara jefo min tana fadin sai taga bayana a gidan nan nan bada jimawa ba nace ta Allah bataki ba gani nan bari nan takalmin kaza.
Ya fice ta bishi ta tasa shi gaba tana zagi dariya nayi nace kun fi kusa ku karata can tare na samay ku ai.
Da dare na gama shirya komai a basket ina cikin wasu english wear na mata dogon rigane irin mai bin jikin nan ya fitar maka da sura sai dan gyalen da na dora a saman kaina nayi rolling din kaina dashi.
Bayan na gama jera mai abincin ne na nufi daki in gani ko yana ciki muyi maganan daya kawo ni wurin shi.
Kofan a bude take na tura tare da sallama na shiga zaune na hangoshi saman sofan din dakin ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki a cikin sa.
Ganin haka na juya zan koma naji yace yaya zaki koma kuma shigo mana ke da dakin mijin ki dazun fa naji kin ce ma Nafisa anjima ke dani.
Wani kallo nayi mashi nace idan ka gama abinci yana jiran ka a falo yace sannu da kokari sai na dan tsaya jin ya kara dagowa ya dubeni.
Ki zauna mana yace nace mmmh dama ba zama nazo yi ba nazone in tuna maka batun karatuna don yanzu sati ke nan da muka koma.
Yace ina sane amma na dauka hutun aure kikeyi ai yanzu wani kallo na aika mashi yace naga kamar zaman aure yafi maki wanan karatun da kikeyi yanzu.
Nace aini ba zaman aure nake yi ba don ban yi kama da masu aure ba a yanzu haka don Allah na fada ma monday nake son shiga.
Wani kallo yayi min na mamakin jin abinda na fadi nace kana mamaki ne aure aure fa na dauka sai wanda yaji yagani shine aure ba irin wanan nawa da nake zaman biyayya ga iyayye ba.
Murmushin karfin hali yayi sanan yace makaranta zaki koma idan kin gama hutun ki sai munje kaduna karshen satin nan mun gaida su idan mun dawo zanyi shawara in gani yaushe yakamata ki koma.
Shiru nayi tare da dan tsayawa sai na juya zan fita yana rufe laptop din nashi yake fadin ina kuma zaki zan tashi inzo ki bani abinci kuma zaki tafi aina dauka kin zo kwanan da kuke ma fada ke nan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ranan monday na fito daga wanka na samay shi zaune a dakina bina yayi da kallo kunya ne ya kamani na yadda ya riskeni.
Kamar zan koma bayin sai kuma na dake naje wurin wardrobe dina na bude na dauko zani na koma bayi na daura tare da yafo tawul dina saman jikina.
Yana zaune ya kallon abinda nakeyi zuwa nayi na zauna a saman dan stoll din mirrow ina sauraren shi.
Murmushin nan nashi ya sake mai kama da manufa idan yayi kallon shi nima nakeyi ba tare da nayi magana ba.
Yace dank kin gama boye boyen naki muyi maganan da ya kawo ni sai dana dan ja lokaci nace kai nake sauren ai.
Yace to ki shirya idan zan fita sai mu sauke ki a school din idan an tashi kuma ki min waya zan zo in dauke ki.
Nace naji kawai ya mike kamar zai fita a dakin sai kuma ya juyo zuwa gareni baya na fara ja har na hade da jikin mirrow .
Anan ya samay ya matse yana fadin muga wurin kudu yanzu kuma wai may kike dauka nane da kike wanan gudun kina boye min kan ki.
Cikin karfin hali nace dashi may zan ma gudu gare ka tunda kai ba dodo bane kawai dai ina kare mutuncina ne.
Ido ya kura min sai na kasa jimirin kallon sa ido cikin ido na kawar da kaina daga kallon da yake min din.
Ji nayi yana kokarin kama bakina ya hada da nashi nayi saurin zille mashi amma hakan bai yuyuba don ya riga da ya kamani ko ina kokarin zille mashi nan muka fara kokawa dashi har ya samu ya matse ni yadda yake so don karfin mu ba daya ba dashi.
Jin abinda yake so ya tabbatar yayi ya dako yana kallon fuskana tare da fadin wa kikewa karyan fashin sallah ?
Nace kamar ya karya dama nina fada ma ina fashin sallah ko gane ganen ka ya gano maka ni wallahi irin wanan abinda kake min ban son shi don kaga, , , ,
Jinayi ya kara hada bakin shi da nawa a ciki na karasa fadin magana na don bakin shi da ya hade da nawa a lokacin.
Don kanshi ya gaji ya sake ni tawul din dake jikina nasa ina goge bakina dashi ya wani waro idanuwa waje yana kallona da mamaki na abinda nakeyi din.
Kai ya girgiza min ya fita daga dakin ba tare da yayi magana ba shirin na fara yi don kada su tsaya jirana na gama na dawo falo na zauna ko karyawa banyi ba saboda zumudi.
Shi ya shigo a cikin shirin fita office yana saye da suit baka da wandon su sai farar riga daga cikin suit din daya fito fili da necktie.
Sai kamshi yake zubawa kallo daya nayi mashi tare da kawar da gaina gefe daya saida ya karewa shiga na kallo don babu ta inda zai kushe min shigar tawa don shiga na kamilanci da nayi ga mayafin dana yafa har saman kaina na dora shi.
Idan kin shirya mu tafi naji muryan shi yana fadin haka da sauri na mike don tafiyan tare da dauko handa bag dina nabi bayan shi.
Suna zaune a falo sai hayaniya sukeyi karan takalmana ne ya dawo da hankalin su daga part dina suka kura ma wurin ido.
Yana gaba ina bin shi a baya har muka iso daidai inda zamu dan gwauta su muryan nafisace ke fadin yaya kuma haka naga ka fito da ita zaku fita tare .
Wurin da suke na dan kalla tare da wurga masu harara naci gaba da tafiyana hankali kwance shima din naga bai tsaya bata amsa ba don haka ta mike ta biyo bayan mu.
Driver yana ganin fitowan mu ya bude kofar motar yana jiran isowan mu bude mata other side din yace ma driven sai ya zagaya ya bude min na shiga.
Ina zama shima ya zauna sai ga Nafisa ta iso gurin daga ita sai rigar barci a jikin ta wanda ta kwana dashi ta dora zani a sama kanta babu dan kwali.
Kofar motar ta rike tana fadin sai ka fada min inda zaka da ita munafuki macuci azallaumi dan cin amana nidai ina zaune ina kallon su kalman dai dayace da yake yawan fada mata ko yaushe.
Nafisa zan saba maki idan baki shiga hankalin ki ba wallahi ban san dalilin da maganar yake kashe mata jiki ba sai inga ta yi laushi idan ya fada mata hakana.
Yanzun ma daya fada mata sai ta sake kofan motan taci gaba da surfa mai zagi har motocin suka daga suka bar gurin bata daina ba kuma bata shiga ciki ba.
Hannun shi daya yasa ya dafe goshin shi dashi sai faman tsuki yake ja motar na tafiya ban juyo na kalleshi ba sai kallon inda muke wucewa nakeyi.
Har cikin school din ya shiga inda ake aje motoci suka sauke ni zan fita naji ya rikoni juyowa nayi na kalle shi sai kuma na sauke ido na don banda jimirin jure kallon nan nashi.
Jinayi yace behaviors self kin ji ko kai kawai na gyada mashi nace naji a fili zan kara fita naji ya jawo hand bag dina ya cusa min wani abu a ciki.
Ban duba ba sai dai na fita ina gyara gyale na saman kaina na fara tafiya a hankali zuwa department din mu.
Tun farkon haduwa da wa yanda na sani suke min murnan auren da nayi ina fadin na gode kawai.
Ko dana isa na samu an fara lectures saukin abin wanaan malamin dake ciki baida tsanani sosai ina shiga idon kowa a kaina caaaa har abin ya ban mamaki.
Wurina samu can baya na zauna ina noke kaina don kunya Allah, Allah wasu keyi ya fita su fara min sheri don bani ba harsu course mate dina ba wanda ya dauka zanyi aure a yanzu din.
Bayan an gama lectures ne suka fara fadin amarya amarya nan ma wanda basu san nayi aure ba suka sani.
Ranan dai nasha sheri a gurin su shiru nayi sai fadi suke wai aure ya mai dani silent na koma wata shiru shiru dani yanzu.
Bayan mun raraagene na fito na samu maryam tana ganina ta saka ihun murna muka rungumay juna zuwa hostel muna shiga dakina na bude ban san lokacin da wasu hawaye suka zubo min ba.
Maryam ta shigo dakin tana bina da ido tare da fadin barin kawo maki abinci ki dan ci kai na girgiza mata tace nasan fa baki karya ba murna zuwa makaranta ba zai barki ba.
Nace kamar kin sani wallahi ban son in ciye maki abincin hostel ne tace ko dai baki son warin shi yanzu tana kokarin kai hannun ta saman ciki na tana shafawa.
Saurin buge mata hannun nayi ina hararan ta tace ba ssni ko har kwallo ya shiga raga ko kike min wanan sabon surfi haka.
Dukka na kai mata tana kaucewa tana dariya tace wallahi bawan Allah nan ya iya kiwo ji yadda kika koma cikin kwana biyun nan da ban ganki ba.
Ni ina nan ina tausaya maki ashe ke kina can kina sheke ayan ki a gidan mijin ki tashi tayi ta dauko min wani leda tace antyn ta ce tace ta kawo min shine gudun mawarta gare ni tunda anyi aure bata nan.
Nafi yaba dogon rigar dake cikin kayan da mayafin shi sauran kuma maganin mata na zamani bayan na gama duba rigar na koma ga maganin ina kallo ina tabe baki.
Nace ni sai ciki ni da wanan abubuwan akeyi kuma basu da amfani a gare ni dariya tayi tace da saura ki kenan ashe.
Wai kina nufin har yanzu baki mallaka ma wanan bawan Allah kan ki ba komai kike nufi ne wai shima AA din har da laifin shi daya kyale ki yana kallon ki haka.
Nace idan bai kalleni ba mai zai min kike so tace kema ai kin sani don baki fi karfin shi ba kyalle ki dai yake yi kwance nakai ina fadin kanki ake ji ni barin huta ina kaiwa kwance wayana yana kara na dauka.
Ganin sunan shi yasa na kalli maryam ina fadin mutumin ki ne ban san may zai fada min ba daya kirani.
Har wayan ya kusa katsewa na daga tare da sallama a bakina bayan ya amsa min ne yake fadi har yanzun baku tashi bane daga lectures din.
Mun tashi yanzu gani nan na shigo hostel wurin maryam zan dan dauki wani abune yace da izzinin wa sai nayi shiru.
Kashe wayan yayi na kalli maryam ina fadin jimin wanan mutumin fa kamar bashi bane buzuwar matar shi kewa yadda take so a gida .
Ina ruwan ki khadi ramin ta daban naki daban kowa ya gyara nasa kada ki daka ta tata don ba tarbiyan ku daya ba.
Bani daka ta ai maryam nasan abinda nake yi don haka ne nake dan daga mashi kafa kada mu zama daya da ita Allah maryam yanzu har tausayi yake bani idan tana mashi wani abin.
Gwamma da kika fadi da kan ki yanzun lokaci yayi da zaki fara bashi salama ya samu saukin wanan tsiwan a gurin ki.
Nace Allah maryam ko nayi niya sai inji na kasa don irin abinda nake gani matar sa na mashi a gaban idona kuma bai daukan mataki ga hakan.
Wallahi khadija sanyin hali kega AA din nan naki bawai ya kasa daukan mataki ba shu,uman mata iri su Nafisa wuyan sha,ani ke gare su sai an bi abin a sannu .
Don girman Allah ki sauke wanan halin hakana khadija ki rungumi mijin ki ku ba mara da kunya dan kin san yana son ki yanzu dai.
Dama nasan da hakkan maryam amma zuciya ta ce ta kasa natsuwa dashi ban san may yasa hakan ba nima naso ace ko ba don komai ba nayi wa iyayyena biyayya don samun haske na gobe kiyama.
Addu,a zaki dage dayi da sadaka da sai kiga komai ya zo maki a cikin sauki ina nan ina kokartawa maryam ki dai tayani da addua.
Ko nayi niyar kyau tata mashi idan ina kallon abinda wanan matar ke mashi sai inji komai ya fita raina.
Baki tunane ba khadija aiki ne fa ja a gaban ki yanzu don Allah idan kin mutu a wanan irin yanayin fa may zaki je ki fadawa Allah zaki ce akan wata buzuwa ne kika kasa cika naki ibadan.
Kafin in wani magana ya sake kirana karo na biyu na dauka yace fito mu tafi gani a waje kallon maryam nayi nace kinji wai gashi waje.
Tace da sauri mike mike don Allah kada yaga kin dade kuma kiyi laifi a wuri shi ni dariya ma ta bani don har ta rigani mikewa tana fadin kada ki manta da abin nan da Anty ta baki tace in fada maki kiyi amfani dashi yadda ya dace.
Naji nace kice mata na gode sai nazo in Allah ya yarda tace don Allah maryam ki natsu ki yi tunane akan maganan nan.
Mun fito mun samay shi a mota wanan karon shine mai jan motar ba driver ba kuma mota daya ba kamar yadda muka zo ba.
Sannu da zuwa taimai ya amsa mata fuska a sake tace dashi ya aiki lafiya kawai yace da ita ya bude min kofan dirkekiyar jeep da yake ciki zaune na juya wurin maryam ina mata sallama.
Mun fara hanya ya juyo yana fadin waya baki izinin zuwa nan da kika zo shiru nayi mashi ina kallon window motar ya sake fadin badake nake magana bane ?
Na fada ma daukan wani takarda