Fati bata fito ba mune kaidai ke ta bidirin mu a ciki.
Baifi awa biyu ba Nafisa da tawaganta suka iso suma sunyi daidai mun gama abincin da nasa a girka aka diba aka kai masu.
Nan gidan ya kici may da hayaniya na riga na fada ma Laraba ta saka ido akan yarana kafin yan uwa na da zasu zo su kara kulamin da diya na don haka ne na hutar da ita ko wani aiki sai kula da yaran kawai.
Munyi sallah na shirya su zasu shiga cikin gida da laraba su gaisa da su momy da Abba inda zasu rika kai dare a can badon komai nayi haka ba don sherin kishiyoyina nayi wanan gudu nai wanan dabaran.
Kamar zuwa na su Fauziya ke jira inda muka fara tsara abinda zamuyi kan bukin sai can ga Fati ta shigo wai ita daga barci ta tashi.
Fauziya ce tace ai da ki bari sai gobe kwa gaisa wanan halin dai naki baiyi ba wallahi ace mutum kullun alamarin sa sai kara lalacewa yake.
Ni dai gaisuwa mutumci mukayi da ita sai da zata fita ne take tambayan yaran nace sun fita kawai.
Daga haka ta fice a dakin kodai ba komai na dan rage jin zafin ta da nake ji a raina din tunda ta tambayi yara ai.
Amma duk da haka batayi wani dadani ba zainab ce ba kunya ta kawar min da tunane na tana tambayana kan kayan da aka saya mata waya na dauko na fara nuna mata inda sauran duk suka rufu muna kallon kayan ina masu bayini.
Binta tace har biyu nace daya a Abuja za a aje mata gidan ta nacan sai dayan azo nan dashi kai amma yayan mu ya fidda zainab inji binta.
Anty Faiza tace har da ita mai bayanin ai badon khadijan ba kina tunanen akwai wanda zai takwasa shi kan haka tunda yaba Abba kudin yin komai.
Ko yanzu Allah kadai yasan irin kai ruwa ranan da sukayi dashi kafin hakan nace wallahi ko anty kamar kin sani harda su kukana sai da nasha da gaba.
Tace ai na san halin mazan nan yanzu sosai don haka muke fama muma dasu ai gara ke ma mun samu yana sauraren shawaran ki ni nawa idan nai mashi zancen sai mun kwashe kwanaki ba shiri tsakanin mu ga ganin laifina da suke duk abinda suka ganin dashi sai suce dan uwan su ne ya saya min shi.
Ban san lokacin da nace dangin miji ai sai a slow ba sai dai idan ka iya zama dasu ne akwai dadi wallahi matsala kaidai kada abinka ya rufe maka ido.
Binta tace watau mu ke nan ko duk aka kwashe da dariya a dakin nace kuka ai yan uwa nane ba dagin miji ba yanzu.
Faiza tace lalai kam don khadija haihuwan tane kawai hajiya mu batayi ba yadda take son ki ma yanzu dukkan mu babu mai fadan nan a gurin ta.
Fauziya tace halin mutum ne ke ja masa so ai don bata so kanta da gidan su ta bar yan uwanta ba nace ni yanzu sai dai idan yaiwa gidan mu alheri su bugo suna fada min amma ban taba bude baki nace kaiwa wani nawa alheri ba duk ko da talaucin gidan namu na rike masu mutuncin su a gurin shi.
Muna ciki motar kaya ta iso gidan nan muka fita zuwa ganin yadda za a sauke kayan sai dai sun bada shawaran a wuce da kayan can gidan Yusuf wanda shima dai a cikin unguwar namu yake.
Sai sauran kayana dake sama suka sauke a gidan na shiga karban key a hannun anty fati na dakin da babu komai ta gama ja min rai ta bani key din dakin akusa da dakin da su laraba suke ciki.
Fita mukayi zuwa gidan Yusuf din dake dan bayan mu kadan aka sauke kayan a gaban mu suna Allah Allah suga kyau kayan.
Sai da na shigo ne zan shiga daki najiyo muryan su na leka dakin ina masu sannu da zuwa ihisan dake dakin tana ganina ta nufo ni sai uwar ta daka mata tsawa .
Kai kina wani shirmay wallahi ina tare muka zo da ita da zan cuta mata da tuni na gama cuta mata ai ba yanzu da alheri ya kawo mu nan ba.
Tace waya sani ko kin cuta mata din don wanan kokarin rabani da diyana da kikeyi haka nace abinda kakeyi shi kake zargin kowa nayi kin gani nan ni ga Allah mahalicina na dogara ba ga wani mutum can ba da shima yake nema a gurin Allah.
Ina fadin haka na juya na bar dakin tare da tunanen yaushe ne wanan matar zata sauya ne tayi saduda tasan Allah dayane a zuciyar ta.
Allah gani gare ka don ina cikin tsaka mai wuya ga Fati babu alaman hadin kai a gurin ta yadda take faman sharewa da basarwa a fuskan ta.
Sai bayan sallah isha,i ne su laraba suka dawo bisa jagorancin momy data rako su gidan sai wani jiji dasu ake a cikin dagi wanda hakan ba karamin dadi yake min ba a raina tunda kowa na son jini na a gidan.
Har umma daba kula kowa take ba momy tace a wurinta sukai magariba zata kwace mata mijin ta don haka take cewa Al,amin.
Washegari bayan mun huta ne naba Laraba tsaraban su ta shiga masu dashi gidan inda babba da yaro kowa ya samu tsaraba na a gidan.
Sai gasu suna layi wurin zuwa yi min godiya tare da sannu da zuwa wanda hakan ba karamin bakanta ran abokan zama na yayi ba sosai.
A raina nace indai kana son a soka ashe gaskiyan Anty hauwa da tace min idan ina son in rabu da kowa lafiya kada in matse hannu na gurin alheri musan man dagin mijina da abokan arzikin su.
Sako har na mutanen zaria dangin hajiya mama sun samu na bada akai mata sai albarka take saka min kan hakan.
Niko da a zatona ban dauka haka abin yake ba don ban so nuna masu haka ba wai don gada su gane ina samu a gurin shi sai take ce min ai matar dake cikin daula ansan tana samu ko yaya ne don haka nuna masu a daula kike don rashin bayarwan shi kan shi matsala ne yin hakan sai yanzu na gane wanda ya riga kwana yana rigaka tashi.
Ban samu shiga gaida sarakaina ba sai washe gari na samu shiga gidan muka gaisa dakin hajiya mama na yadda zango.
Bayan mun gaisa take fadin haba khadija kin dauke kafa gare mu haka har ina murna kin dawo da hankalin mijin ki gida sai gashi ke kuma kina kokarin gudun mu yanzu.
Ina kaduna ina Abuja bafa wani nisa ne a tsakanin mu ba kwarai amma kuke wanan dadewan baku zo gida ba ko yan jikokin nan namu yanzu don su saba damu ai kyazo dasu su san yan uwa ko ?
Hakkuri na bata ban kawo korafin komai ba don taimin uzuri sai hakkurin da na bata akan zamu gyara insha Allahu.
Zancen bukin ta dauko min inda take fadin yara sun zo suna fada min kokarin da kukayi ke da mijin ki sosai an gode Allah yasa albarka ya kara daukaka da nisan kwana a kunyace na amsa da amin mama.
Nace sai zancen gara shine ma ya saka muka zo da wuri don a gudanar da komai yadda ya kamata akan lokaci yace a lissafa abinda ake so gaba daya idan yaso sai ya turo da kudi kafin yazo a saya don shi sai karshen sati yace zai shigo.
Madalla duk da nasan Alhaji ne mai wanan nauyin amma hakan yana da kyau don yanzu lokaci yayi da zasu dauke mai wanan nauyi zan fadawa Alhajin sai ai shawaran abinda za a kai masu.
Nan dai su anty Faiza suka samay ni gurin hajiyan mukaci gaba da shirin da zamuyi dasu haka dai zuwan ya zama min busy bamu da hutu na kan mu sai dare.
Duk yadda nasu in zulle masu indan huta hakan bai samu ba a gare ni don a cikin kwanakin ne akaje yiwa zainab gyaran dakin ta sai dai ina kokarin leka ya Amina na duk wanan ritsin.
Abin gidan yawa sai abin ya koma gulma kuma wai dani kadai suke shawara sun bake sauran yan uwana basuyi dasu.
Yau ya kasance ranan kamun zainab yan uwa da abokan arziki sun hallara a gidan gida ya cike da yan uwa zainab tana gidan mu ana shirya ta don mai makeup tazo.
Wasu yan mata da matasa a gidan namu suke zaune duk wace akacewa zainab tana gidan mu nan suke shigowa.
Sai abin sha dana dan tauna baki muke rabawa wanda Yusuf ne ya sawo ya kawo muna a raba ma baki don Binta ta kirashi take fada mai komai.
Wanda ya rage na sa a dayan dakin muka rufe muka fito zuwa gurin kamun wanda kafin in isa har mun iske an fara program din ko.
A daidai wanan lokacin ne AA ya shigo kaduna ranan yammacin alhamis sai dai yayi mamaki ganin dandazon mata a kofar gidan iyayyen sai gashi ya iso gida ya samu Fati a gida.
Ya haura sama nan ma su Nafisa da yan uwanta suna gida zaune a binsu sai shan bakin tea suke saboda sanyin da akeyi a kadunan lokacin.
Ihisan da ta fara hangoshi tayo wurin shi da murna tana taron shi fuska ba saki ya rikewa yarinyar hannu yana fadin .
Ihisan ya baki je gurin kamun gwagon ki ba ke tace Abba Amin mu tace kada in bi momy ne ya dago kai ya kalle ta daga inda take kwance baiyi magana ba ya wuce dakin shi ya dan jima a ciki ya fito daga kofa ya tsaya ya kwalawa yarinyar kira ta fito.
Ya rike mata hannu suka fita tare zuwa gidan duk yawan matan dake gidan haka ya kusa yana rike da hannun Ihisan zuwa dakin mahaifiyar shi.
Ya samay ta zaune da wasu dattijan mata a dakin yan uwanta da abokan arzikin ta bayan sun gaisa ne hajiyan tace da yarinyar ashe suma sunzo akace yake fadin basu shigo gaida ku ba ke nan tunda suka zo?
Tace mun dai ga khadija da yaran ta don su ko yaushe a nan suke tare damu koda uwar bata gidan har sun saba da mutane hajiya ina Deedar take ya tambaya.
Yanzu kan ai tana cikin wanan taron don sune keda bukin ai wanan yarinyar na kawo mata na samu uwar ta ta hanata fitowa wai.
Hannu hajiya ta mikawa yarinyar duk da tana da wayau sai taki zuwa tana shigewa jikin uban tace ina zata zo tunda bata san mu ba.
Tsawa ya daka mata cikin harshen turanci yace taje gurin grandma don tsoron shi ta taka a sanyaye zuwa gurin ta.
Ai daka barta tunda ba sanina tayi ba daya daga cikin matan dakin ke fadi akan may zai barta ai gara a nuna masu ku su sanku ko.
Wani irin ba dadi AA yaji a ranshi sai yanzu yake dana sanin auren bare wanda babu wani alfanu a cikin sa sai jin dadin rayuwa karshen abin ba kyau yake yi ba ga mutum.
Wai ace yayan shi basu san mahaifiyan shi ba haka kamar an jefo momy dakin tare da su yan biyu dake gurin ta don zata fita ta shigo da yaran gurin hajiya su zauna.
Suna ganin uban zube a kasan carpet din dakin mahaifiyar shi sukayo kan shi da murnan ganin shi aka dauki dariya a dakin.
Ihisan ta baro wurin hajiyan zuwa wurin da suke tana kiran sunan su tare da dariya suma dayake sun saba da juna sai gasu suna wasa a jikin uban da junan su.
Yanzu kan kin san yan uwan ki ai gashi kije gurin su ba tayi anan ya barsu ya fice daga gidan ranshi yana mashi ba dadi.
Ya rasa dalilin matan nashi na kin shiga sha,anin bukin shi sai da zai fita ne yaga shigowan Fati gidan ita da wasu yan uwan ta ya dauke kai kamar bai gansu ba.
Mota ya shiga ya nufi inda su Yusuf ke jiran shi sai dai kafin yaje yayi tunane kala kala tare da hango abinda bai taba yin tunane a kansa ba sai yanzu.
Ya rasa gane may yasa Nafisa bata son zancen yan uwan shi bata mu,amula da kowa daga cikin su duk da kokarin da yake na ganin ya kokarta ma yan uwanta a koda yaushe.
Amma haka baisa ta dauki nashi da mutunci ba kokari ma take ko yaushe ta nisanta shi da yan uwan shi sai lokacin yake tuna wasu abubuwan da suka faru a baya kai ya girgiza yana furta kalman innalillahi har yakai wurin da zai tafi din.
Ya samu su Yusuf din na shirin zuwa wurin kamun ba yadda zaiyi duk da zainab kanwar shi ce yasani amma zuwa wurin ya zama mai dole don kokarin Yusuf a gare shi.
Wuri ya dauka ga angwane sun iso ban san da zuwan shi ba don na dauka sai washe gari zai shigo sai dai kawai na hango shi yana ma Yusuf da zainab liki a tsakiyan fili.
Daga inda muke tsaye ina rike da mami sai Alamin dake hannun laraba ihisan tana tsaye rike da hannu na daya, muna hango shi na kare mai kallo har na shagala ban san ya karaso inda muke tsaye ba sai ganin shi nayi yana muna liki kallo ya dawo gare mu mata nata kokawan kwasan yan dubu dubun da yake manna muna.
Abokan nasu har Yusuf suka dawo kaina da yaran suna manna muna kudi ina kare kaina don kunya ya jawo mu ya rugumay wuri ya kara rudewa.
Ya fice yana muna dariyan keta don ya gama bani kunya a bainan jamma,a ya wuce nan kannen sa da aboka wasa suka shiga min sheri a gurin.
Sai bayan magariba muka dawo gidan ina daki ina cire kaya Alamin yana kukan da ban san may ke damun shi ba don haka yake kwana bibiyu da ciwo shi macen tafishi dama.
Ya shigo dakin shima da ganin shi a gajiye yake lokacin yake yaron dake kuka ya kama sai ga laraba ta shigo da madaran da ta hado ma yaron daki.
Yana tambaya may ke damun shi nace nasan sanyin garin nan ne ya kama shi tunda acan ba fita suke haka ba ko yaushe.
Yace ki bashi nono ba wanan abin ba yaya zaki gane halin da yake ciki baki mamay shi ba a jikin ki ban ki ta nasa ba na dauki yaron ina kokarin zama dagani sai zanin da daura gaba a jikina.
Yana tsaye yana kallon yadda yaron ya kama nonon ya sauke ajiyan zuciya ya juya ya fita daga dakin .
Bakai dakin shi ba Nafisa dake dagon shigowan shi ta tsare shi a hanya tace dama kai nake jira ka shigo inji idan kai ka ce kada a fitar da komai abawa kowa nasa don ban san dalilin matar ka na kule kayan da aka zo dashi ba a daki tana amfani dashi ita kadai don samun wuri.
Wasu kaya ya tambaya da mamaki karara a fuskan shi tace kayan da ka saya aka zo dashi mana ko wani sallon wulakanci ne ka dauko kuma haka yasa kace sai munzo .
Ke ban san zancen kayan da kikeyi ba don haka ban son wanan haukan naki idan cin mutuncin ki ya taso ne in sani.
Idan ma na sawo kayan tayi amfani dashi ke bukin ne ya kawo ki nan ko may ina gida kike baki je gurin abinda ya kawo ki din ba.
Yana fadin haka ya wuce tana fadi cikin daga murya may zanje yi gurin mutanen da basu sona sai dai suga bayana shine fatan su.
A cikin daren nan taje gurin Abban su AA da korafi wai ya hanasu komai sai ni kadai ce nake gudanar da komai a gidan kan bukin.
Abba yace ta koma zai nemi AA din yaji kan maganan idan haka ne kuma bai kyauta ba ya dai bata hakkuri ta wuce zuwa gida.
Washe gari da safe Abban su AA ya tako zuwa gidan mu ya samu su laraba yace a sallama mashi dan nashi sai da AA yayi mamakin jin ga Abba a gidan nashi yau yazo da kan sa.
Yana kiran wayan shi don su laraba sun fada mai cewa basu tashi ba a lokacin yasa shi kiran wayan shi.
Ya sauko da sauri zuwa kasa ya samu mahaifin nasa a kasa ya zauna don girmama mahaifin nashi da yakeyi yace ya tashi ya zauna magana zasuyi dashi.
Bayan ya zauna ne mahaifin nasa ya fara mai da nasiha da wa,azi akan zama da mace fiye da daya sai daga baya yake cewa dashi jiya matar ka ta samay mu da korafin kana tauye masu hakkin su.
Ya dago kai da mamaki yana kallon mahaifin nasa yace kamar ya Abba yace eh kasan maza wasun mu haka suke wani lokaci hankalin su sai ya raja,a agurin mace daya ya manta da hakkin sauran matan nasa.