Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MIJIN Buzuwa Complete Complete Hausa Novel by Nil

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   54 / 144

159K to 162K   out of 431K words

da yan uwan Nafisa da alaman rashin mutunci a tattare dasu kuma.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Iya kana dasu ido banda mama da yan uwan ta ban magana da kowa a gidan namu kosu don sun gwada min kulawan su a kaina ne kuma nasan su na sona.
Har maryam da nasan ta zo nan don ni ne ban yarda da ita ba yanzu don bala,in haushen ta da nake ji a yanzu din ita ko bata damu ba sai aiwatar da sha,ani buki takeyi hankali kwance.
Duk shirin da ake iya kata dasu ido ne ban san may suke shiryawa ba ina dakina kwance na sala airpiece a kunne na ina sauraren kira,an malam Ahmed sulaiman kano mama tani ta shigo dakin mu.
Ganin ta yasa na cire airpiece din a kunne na ina kokarin tashi zaune tace daughter tashi ki shirya ki rakani unguwa ba nisa zamu tafi ba nan lapai zaki rakani.
Ba musu na tashi na shirya ba wani dogon shiri nayi ba sosai nafito tsarkar gidan namu da har yau bai rabuwa da mata masu shirye shiryen buki.
Ita da kawar tane a motar dan haka na shiga baya na zauna itake jan motar do mama tani wayayiyar mace ce nurser ce a IBB hospital minna nan take aiki.
Tunda na zauna na kawar da kai gefe ina kallon hanyar ban kara bi ta kansu ba can naji kawar nata na fadin diyata ance kishiyar ki daya buzuwa ce ko ?
Banji taba sai da mama tani tace khadija baki ji bane na waigo su da sauri ina sauke ajiyan zuciya maimaita maganan ta ta sake yi a hankali na amsa mata.
Tace wai akwai aiki ja agaban ki wallahi don buzayen matan nan shegune wallahi akwai su da shiri na siri wanda su kadai suka san abinda suke ma maza kaga namiji ya mutu a kansu.
Mama Tani tace shine abindake ban tsoro ai for god sake mijin yayana kamar wanda baiso yar shi kadauki diyar ka ka mika a irin wanan gidan.
Wallahi mairo in ba don nasan halin shi ba sai in ce kudi yabi amma nasan ba haka bane dan shi mutum ne mai tsatsauran ra,ayi ga abinda yayi niya.
Nurse Mairo tace kada ki yarda da ita ko kadan don itama ba yardan zatayi dake ba ki sa ido da kyau ga komai da kikeyi a gidan do ko ba gida daya za a aje ku ba sai tasan yadda tayi maki aike.
Kuma ki rike ibadan ki muddin kin rike Allah insha Allahu abinda duk zatai maki zaizo da sauki and kina ji kada kiji tsoron ta ko kadan don zatai maki barazana da komai da kika sani tun yanzu ki nuna mata ke ba kanwar lasa bace Ehhe, .
Don haka kadai ne zai kwace ki daga sherin ta da kaidin ta don akwaisu da iya hada tugu gasu duk gayen nan da kike gani sunayi a waje wallahi in kin zauna dasu sai kin raina masu .
Don ko girki basu iya ba bazaki iya ci abincin su ba ko kadan sanan kuma gasu da jaraban tsiya namiji baya taba isan su shiyasa makike jin anace dasu sadaka yallah.
Suna da aure suke bin wasu mazan a waje don bakin shaye shayen su na tsiya sanan kuma wanan bakin tea din dakikaga suna sha ba shayin banza bane hadine na abubuwa suke dirka ma cikin su.
Mama Tani tace diyata ga Allah ta dogara shine zai kare muna ita a duk inda take hakane inji Anty Mairo tace amma ance idan kana da kyau ka kara da wanka ko Allah yace tashi in taimake ka.
Mama Tani tace haka ne shiyasa kika gana dake muzo wurin babakin da ita kafin a kaita gidan mijin ta don a samu abinda aka bata.
Kina ji daughter bance kiji tsoron ta ba ko kadan duk yadda kike jin tsoron ta kiyi kokari kibar tsoron a cikin ranki kada ki bari su gane hakan don da huda ki saudaya akaga wuka ya shiga shike nan baki da sauran shakat a gida.
And don Allah kiyi amfani da ilimin ki kada kije ki biye mata kuyi kishin hauka irin su a cikin ruwan sanyi ake guma masu halin su da tayi maki send her back to sender.
Zaki ga tayi saurin kariya dake tana fadin wai shige shige kike yi da sauran su ke har tsafi sai ace kina nayi da sauran su.
Ke dai daure kiwa miji biyayya don Allah ki fara kamo kan mijin ki shine abuna farko samuwar zaman lafiyan ki a gidan.
Sai kin jajir ce wurin tsabta da iya gyaran jiki kiyi kokari ki san irin kayan da yafi so su zaki dinga sawa idan baki da girki kina kwalliya mai daukan ido da hankalin namiji sai kiga namiji ya matsu ya dawo gare ki.
Girki kafin ya bar gida ranan girkin ki kin hada mai abin karyawa haka kafin ya dawo kin hada mai abincin dare ko dan abin jika makoshi da zai taba.
Kada ki yarda kamshi ya rabu da jikin ki ko yaushe dakin ki jikin ki shiyan ki zama kamahine a koda yaushe.
Kalamai masu dadi su dinga zuwa suna dawowa a bakin ki da irin dan shagwaban nan na mata da sauran su sai kin mai da kan ki karuwan gida da kyau gada ki yarda ki nuna gajiyan ki ko kadan ga miji.
Haka dai sukaci gaba da min huduba iri iri wasu ma ban san may suke nufi dasu ba a kofan wani gida motar su ya ja ya tsaya.
Gidan irin ginan lakan nan ne na kauye mai kofofi fiye da uku ga rumbu a tsakiyan gidan na laka.
Matan gidan suka shiga taron mu suna gaida mu a cikin harshen nufe Anty Mairo na amsa masu .
Sai da muka dan huta kadan wurin matan gidan akai muna iso zuwa wani daki shima dai ginan lakane kamar sauran sai dai shi an mai bugun kwana sai dai kwanon ya tsufa.
Wani dattijo ne baki mai farin gemu zaune saman wani buzu fari ga littatafai nan da yawa a gefen shi ga wani katon tasbaha yana ja a hannun shi sai kamshin turaren mutanen da ke tashi a dan dakin.
Ga hoton iyas a ko ina an manna a dakin wuri muka samu mu ukun muka zauna sai daya gama adduan shi ya shafa san nan ya juyo gurin mu yana fadin sannun ku da zuwa.
Sun gaisa sosai da Anty Mairo sai ta gyara zama tace baba ga yarinyar kawata zatai aure ita muka kawo wurin ka son akwai matsala zata ci gaba yace yana kallona dakata Mairo.
Yace ai bata da wani matsala da kuke tunane tunda naga mijin da ta aura yana son ta sosai a zuciyar shi kuma zasu haihu dashi sosai ai kun ga matsala ya kare ko ?
Da sauri na dago kai na kalli mama Tani muka hada ido tace malam don Allah ko akwai wani abinda za a taimaka mata dashi haka ko da addua, ne.
Don gidan mutumin akwai matsala sosai don kishiryar ta daya ma buzuwa ce ka shige shige da nbin bokaye da malamai da sauran su.
Haka ne na gani ai sai dai shawaran da zan baku shine ko nan gaba kada ku bata kudin ku ko lokacin ku zuwa wurin wani don yarinyar ku tana da tsarin Allah a jikin ta.
Kuma Aljannun ta ma duk musulmai ne bazasu bar wani abin cutarwa ya cutar da ita haka kai tsaye ba don da taimakon Allah har aka kai ga yi auren su yanzu da ba don ita din bace kai ina wane buzun ta.
Da yanzu an mata da labarin ta ai kun dade tare da mutumin ko yace yana mai tsura min idanun shi jajaye irin na nufawan gidi.
Mama Tani ta kara fadin malam a dai dan tai maka mata don Allah da wani abin yace kai bazaku yarda bane amma tunda kun matsa batin bata wani abin.
Sai da ya yunkura yana dauko jakkan shi daga gefen shi yake cewa sai dai don Allah ki dinga hakkuri ko yaushe don hakkuri shine a kan gaban ko wani alamari kin ji.
Nace a sanyayye naji malam yace kada ki kuskura kiwa wani sheri haka kuma wanda yayi maki shima zai girbi abinsa don irin mabiyan da kike dasu.
Wani dan kyale ya bude ya ciro garin magani daga ciki yana fadin ga wanan ki shaka idan kun koma gida yau da gobe sai wanan da zan rubuta maki ki shanye shi a nan gurin na kada kaina.
Sai daya rubuta ya bani na shanye duk sun tsare da ido yace in shafa dan kwakwagin a fuskana na shafa yace Allah ya tsare ya kare a duk inda kike.
Su mama tani suka fara yi mai godiya suka balle jakka suka fito mai da kudi da sauri ya girgiza kan shi yana fadin ina ba zan karbi ku sisin ku ba don Allah nayi mata.
Anty Mairo ne ta bude jakkan ta tafito da kulin goro manyamanya ta aje mai a gaban shi yace to kin ga yar gida tasan abinda nake so fiye da kudi indan kin bani wanan kin gama min komai.
Jikina duk babu karfi haka na fito na tsaya a bakin motar mama Mairo na jingina bayana ga motar ina tunanen duniya tare da bin garin da kallon mamaki kai duniya da fadi yake wallahi.
Ban taba zuwa lapai ba sai wanan karon da dalilin auren ya kawo ni garin ko da muka iso minna la,sar yayi a lokacin.
Haka na shigo na samu wuri a dakin mama na kwanta yayin da suka shigo ciki suma a gajiye suka samu wuri suka zauna.
Ruwa da abinci mama ta kawo masu mikewa nayi don inje inyi alwala inyi sallah Anty mairo ne ta dubeni tace ke kuma fa bazaki zauna kici abincin ba ?
Na koshi nace dasu can kasan makoshina tace gara kici abinci kada kije gidan angon ki ba karfi waima kun fara bata abin gyara jiki ko ?
Ban samu zama ba yau dai nake son mu fita da dare zuwa gidan hajiya Bayi mu san abin yi baki na turo gaba na fice daga dakin.
Bayan sun huta sun ma mama bayan nin komai sai lokacin naga hankalin ta ya dan kwanta taci gaba da dan walwala a fuskan ta.

NAFISA

Tunda ya haura sama bata kara bi ta kan shi ba ranan ko runtsawa batayi ba ta rasa may zatayi taji sanyi a ranta.
Ta tsani Yusuf da iyayyen Samad dan tana ganin su saka shi wanan auren bawai yin kan shi bane a ganin ta.
Maganan wata daga vikin kawar tane ya tsaya mata arai da take cewa wai yar minna wa yan nan gogaggun matane fa su ma ga iya tsafi don mayu ne.
Gasu da kyau tsiya kamar su sukai kansu ga ilimi da jin kai sai kinyi aiki babba gaskiya amma sai wata kawar su tace mata ko yaya take dai ki san batai kamar nafisa ba dai ko ?
Don haka karkiji komai a ranki karaf daya zaki ma shegiya wa ya aiko ta cikin mu ai ba sani ba ragowa ga kishiya yanzu.
Ire iren magan ganun da take ta tunawa kenan har gari ya waye tunda safe tabar gidan bata ko tsaya bin ta kan maigidan ba don bata da lokacin shi yanzu kallon mataudari take mashi so take ta gama da karamar yarinyar da take son shige mata hanci kafin shi ta waiwayyo shi.
Hanya suka dauka sai maiduguri su ukku sun sha tafiya a hanya kagin su isa maidugurin ta koro bayanin komai da wa yanda take so a illanta mata mutumi yace zai mata akan kudi masu yawa kuma ta yarda.
Yabasu abinda zai basu suka kama hanya inda yai masu alkawarin khadija ba zata shiga gidan nan ba ko ta shiga ba zaman lafiya a tsakanin su.
Suna hanya a gajiye madam tace aini dama na sani akwai abinda yarinyar nan ta taka muna kwance an muna nasari a inda bamu zata ba.
Ji irin kudin da muke narkawa akan wanan mutumin amma wai ace yau shine yai muna abinda bamu zata ba haka.
Nafisa taja tsaki tace kin san ba kullun ake kwana a gado ba suma nasan ba don sun iya asiri ba haka da wane su da Samad.
Kin san fan Niger din nan akwaisu da maganin tsiya wallahi gasu da mugayen malamai da kudin ki kadan bukatan ki sai ya biya.
Barsu kawai madam wasa suke dani wallahi basu san ko cikin buzayen suna suka tara ba yanzun dai in samu in karya asirin tukun in koma kan su da kyau babu yar iskan da ta isa ta aure min miji ina kallon ta.
Ni kishiya kota lahira in ba dole ba bani son ta ai balle ta duniya bazan yarda ina kallo ba wata tazo shimfida da mijina ba ina kallo ta lasar min zuman miji.
Wanan kayan nawa ne ni kadai ba wata yar iskan data isa takai wurin nan ko Fati a kullun shine bakin cikina da ita bakar manya kawai.
Dariya madam yayi sosai tace Nafisa baki da kyau wallahi ke wanan ne kawai abinda kika tsana kar wata ta lasa zumar bindin ki tace bari madan ina bakin ciki da hakan wallahi yafi komai kona min rai da kishiya.

AA
Tunda ya falka daga barci baiji duri ya ta ba yasan fushi take dashi don haka bai nemay ta ba kuma bai fito daga dakin ba.
Sai da Yusuf yakira shi yake sheda mashi gashi a waje ya fito ya fito ya samay shi a wajen bayan sun gaisa ne suka fara shawaran inda zasu gyara min .
Yace kasan yanzu sama kusa da dakina Nafisa ta koma ita so sai dai idan kasan za a gyara mata ita khadijan .
Wani kallo Yusuf ya jefa mashi yace kana iya adalci agidan ka kuwa may nene na rashin adalci anan yace dashi kai kaga yadace ace kuna sama kai da Nafisa ita kuma khadija na kasa kayi adalci ke nan ?
May kake son yan uwan ka su dauki hakan da kayi tun yanzu ka nuna masu irin zaman da yar su zatayi a gidan.
Yace kai mata problem ne wallahi yanzun may ye a cikin haka ba na bata daki zama ba ita a gidan yace look A A wallahi idan zaka gyara iri halaiyar nan da nafisa ta koya ma ka gyara tun wuri kasan dai khadija ba irin Fati bane da kuja samu kuna cuta mata bata magana.
Yace don Allah ya isa yanzu yaya kake so yace ko gaba dayan su ka gyara masu dakin saman ko kuma su dukan su dawo kasa tinda akwai dakuna part din sunanan basu komai ba.
Ok dama fiti Nafisan ne ya isheni nasan ko a wanan sai mun taba fitin don yan uwanta ne a dakin kai kai Yusuf yace.
Yan uwanta a dakin ba yan uwan ta bane idan zasu zauna da ita su zauna idan taga tana iya zama dasu sama dai ne kan ya haramta mata har abada.
Murmushi yayi yace ai kun fi kusa zaka ita da ita yace barin je in fada mata ta kwashe ta dawo kasa jerin dakunan su na da.
A tare suka shiga gidan zuwa falon yace a kira mai Nafisa wace ya tura tace tun safe tafita gidan bata dawo ba.
Kallon juna sukayi suna mamaki Yusuf da kanshi ya zaba min inda za a gyara min nan yabar AA yana tambayan su inda taje.
Gyara sosai ake ma gidan har dare an kwashe tsofin kujerun gida da sauran abubuwa an shigo da wasu har dare mutanen suna aiki gidan duk da gwanaye ne amma sai da aikin yakai su dare kafin wani lokaci gidan ya sauya kamar ba shi ba an kawata ko ina na gidan.
Sai biyu da wani abu na dare ta dawo gidan kai tsaye tayo ma falon tsunke tana kunna wuta indon ta ya sauka ga sauyin da gidan ya samu na dan lokaci kadan.
Sai da ta gama bin ko ina da ido kafin ta ankara da maigidan tsaye saman steps yana kallon ta.
Zata karaso yace ke dakata nan daga ina kike yanzu kamar bata ji shi ba tana kokarin haurowa sama yace cikin daka tsaya nace daga ina kike yanzu a wanan lokacin.
Tace cikin tsiwa naje samun mafita ne akaina abinda zai fitar dani don ba zan zauna ka dauko ni ka kawo garin mutane kaso ka wullakan ta ni ba ko ina akwai mutanen arziki a duniya.
Zaki fada min ida kika je ko sai ranki ya baci tace wani guri muka je kuma dare yai muna sai yanzun muka dawo ta fadi tana kokarin haurawa sama.
Yace dakata dakin ki yanzu ya koma kasane dukkan ku a kasa zaku zauna ku bar min part dina dama nawa ne ni kadai na gina.
Ranan yaga hauka da tonon asiri a wiein ta sai da ya nuna mata namiji ne shi ma ta kyale shi sai da

54 / 144

Chapters