Koda yake ba abin mamaki bane ga wanda yasan mazajen da ke auren irin yan yaren buzaye zai san mazan ne a kasa matan suna sama.
Sai abinda sukace komai su mamaye na miji yazama nasu su raba shi kuma da kowa nasa sai su da yan uwan su zasu dinga bushasha da shi da dukiyan shi.
Sai dai kima sam basu son auren mazan yaren su don irin bakar wahalan da suke sha wurin su amma namu mazajen su ke kwadayin matan buzaye saboda bakar jaraban da suka iya.
Yanzu dai kira shi muji yadda zaku kwashe a tsakanin ku don nasan akwai drama nace ni wanan daure ni suke son yi maryam.
Ban san may yasa suke cewa wai sai nice zan iya masu haka ba bayan yana da kanne mata da yan uwa da zasu iya.
Su iya may khadija ai abin sai da hikima ke fa ba yar uwan su bace kin ga yadda kuke moved dashi kamar saurayi da budurwa ne.
Ke komai zaki iya fada mashi a zauna lafiya wani dan uwa idan yafa da sai inda karfin shi ya kare ke ko sai ki fada mai a wasa bai dauki abin da zafi ba.
Wayan ta na karba ta hanyan yi mata karya wayana ba kudi a ciki tace ai bai san layi na ba don haka ba lale bane ya dauki kiran .
Bari dai mu gwada mu gani idan bai dauka kiran har ya kusa karewa ya daga tare da fadin hello nace dole zama da yan haure ya kowa ma wani akidar banza.
Wake magana please ya tambaya nace wata buzuwa ce ko kana son kari su zama biyu a gidan ka murmushi yayi yace khadija nace ba ita bace.
Kina zaton muryan ki nan zai bace min ne nace marya na yana kama da na buzaye ne ?
Yace ai kamar ma ta baci baki ganin zubin ku daya dasu sai dai yaren da baki ji nasu kai malam ni kiran ka nayi naji ko mommy ta koma ne?
Don nasan ba lale bane buzuwan gidan ka ta barsu su dade a gidan yace idan kina son sani kije gidan ki duba mana.
Ban tashi ba ne da zanje yace ya kike nace ina nan yarda ka sanin a baya ke ba a maganar girma da arziki dake ne ?
Nace banson don ba gaisuwa na kira ka muyi ba ko tambayana yaya ni yace ai kogi ba ki dadi ba ko nace .
Wani kogin ke nan dai wani ko wani ruwa ne ya shige shi in ba nasa bane amansa yake yi don haka ba gaisuwan ka nake nema ba.
Yace becareful nace a nan ko sai kaga mutum har mutum amma a gidan shi sai ka rena mai wayo idan kaga abinda yake yi.
Ta yaya bakin haure har zasu shigo su samu mutum a gidan shi in ba samun wuri ba suce sai abinda suke so zasu mai ni wallahi na dade da raina aya don tsakuwar ta.
Yau hausa kike ji ke nan nace daurowa ne hakan adai ji tsoron Allah kada mutum ya zauna mace ta mayar dashi saniyar tatsan ta .
Ba mai ci sai ita da yan uwan ta kadai yace kina son wani abu ke nan nayi saurin fadin haram wallahi adai ci lafiya.
Ga yan ketare nan suna taya ka ci idan ka wawuro su kuma sai su cafke ranan na zuwa da zan maka irin ku kotu masu ba bakin haure makafa suyi yadda suke so da dukiyar kasan mu.
Yace magana kike ji ke nan dai nace ba wani magana sai fadin gaskiyan da na saba kulun idan naga anyi ba daidai ba.
Ya Abdul ace mutum baiwa kansa adalci kulun sai abinda mace ta dora shi a kai yake bi yace wai may kike nufine don na rasa gane ida maganar ki ya doso har yanzu.
Mafalki nayi naga ka susuce kazama bawan mata sai goyon su kake yi a bayan ka ka manta da kowa na naka sai masu jajayen kunne kasa a gaba.
Murmushi yayi yace ki fito fili kice kin yi kewa na kawai kin tsaya kina dora wa wani laifi kuma ko na kulata ba mata na na kula ba na kula matar wani ne ?
Mata wai mata matar namu duka dai inji manya mata kan tana kaduna ka barota can wanan ai ta bugi ne .
Khadija you are very stupid matar nawa kike aiban tawa a gaba na nace ko a idon ka sai na fada don gaskiya ake fadi.
Namiji kamar mace baida say a gidan shi sai na mace macen ma abin kyamatar mu gaskiya ka gyara halin ka sai anjima nayi saurin kashe wayan batare da najira amsan da zai fada min ba.
Wanan yarinyar ta ci uban rainin wayo wallahi yace Yusuf da ke zaune gefen shi yana murmushi yace khadija ce halan ?
Wa kasan zai min wanan idan ba ita ba ban san mayeatsalar ta da Nafisa ba ko da yake su mata haka suke dama ko Nafisan da tasan da zancen khadijan Allah kadai yasan iya boren da zatai min.
Kana zuwa gurin ta ke nan har yanzu ya danja tsuki yana fadin wallahi na dade ban ganta ba tunkan naje Lesvegan rabo da na ji daga gare ta.
Yusuf yace ai gashi yau ta kiraka ita yace ta kirani taci min mutunci ba sai nayi maganin yarinyar nan wallahi ta raina ni da yawa I don't know why take min abinda taga dama haka ?
Kun fi kusa ai bani shiga tsakanin ku yanzu ai wani kallo yaiwa Yusuf din yace tunda ka gama hadawa ba ai ka fadi haka yanzu ?
Au ni ma hada ke nan ashe wa ya manna min wanan chewing gun din idan ba kai ba ina zaune kalau abina.
Amma ai tayi muna rana ba kadan ba kasan da hakan dai ?
Tsuki yaja yace ban san ya nakoma ba wallahi yar karamar yarinya ta shige min na kasa yin komai akan hakan ?
Kun dai shige ma junan ku yanzun ne kuma kake neman maraba da ita ko why zaka so ka rabu da khadija bayan kasan tana da amfani a gare ka ?
Amfani fa kace Yusuf yana kallon shi da idon shi da ya kafa mashi sai da Yusuf ya rausaya kai yace kafini sanin haka malam.
Kada ka bari shedan ya rudeka kaiwa kan ka hasara zukekiyar yarinya kamar khadija may kake fadi ne wai Yusuf ?
Kiran kawun shine ya katse masu magana da mamaki a fuskan shi ya furta kawu habu yau lafiya kawu ya kirani haka ?
Ya dauka suka fara gaisawa da kawun nashi wan mahaifiyar shi cikin kunya da nauyin kawun nashi yake amsa mai gaisuwan.
Don ya manta yaushe rabon shi daya kira shi ya gaida shi a matsayin shi na wan mahaifiyar shi da take ji dashi a cikin yan uwanta.
Bayan sun gama gaisawa ne kawun nasa yace dama na kiraka ne idan da hali ina son ka shigo kaduna a cikin wanan satin .
Da mamaki ya tambayi kawun nasa yace kawu lafiya ko yace a, a lafiya kalau sai alheri akwai abinda nake son kayi ne idan kazo amma fa idan ba takura.
Haba kawu ba komai in sha Allahu satin nan zan shigo ranan jumma, a asabar zan karaso zaria in gan ka kawun nashi yace nagode Allah yayi maku albarka ya kara tsare muna ku.
Ya amsa da amin kawu na gode ya aje wayan yana mamakin maganan da kawun nashi ke dashi akan shi Yusuf dake gefen shi ne ya tambaye shi ko lafiya.
Yana mai da kan shi bayan kujeran da yake zaune sama yake fadin wallahi ban san abinda yasa yake nema na ba a yanzu.
Zamu tafi karshen satin nan don haka sai ka shirya muna tafiyan yadda ya kama sai dai ban so tafiya yanzu ba a yadda Nafisa take haka haihuwa yau ko gobe.
Zamu iya zuwa muyi kwana daya idan hakane sai mu juyo idan ka gama ganawa da kawun.
Yace hakan za ayi Allah ya kaimu lafiya gaba daya har ya manta da zancen wata khadija ko don mantuwan da yake fama dashi a yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yan uwa da abokan arziki ba laifi sun zo mashi karan suna sai dai taron ba wani dadi don mai jego ta tsare komai na gidan ta hana mutane suyi yadda suke so.
Ganin haka ne tu sha biyu suka buga min waya suna tafe gurina don basu ga amfanin zama gidan da suke yi ba gara kawai su fita suga gari.
Da waya har suka iso gidan da muke zama inda ake kira da up k na mata inda a nan nima nake da dakin na da aka kama min tun zuwa na Abuja.
Ranan nayi mayan baki don karshen ta dole suka samu gaba wai mu zamu nuna masu gari shigan dai guda ne don ko yau wani abaya baki mai kyau ne ke saman lace din da nasa.
Shigan yayi min kyau matuka don ya mayar dani kamar wata yar bukuwar haure dani munje wuse market mun dan leka gura re sai yamma lis muka bar SAHAD zuwa inda gidan yayan nasu yake inda suka zo suna.
Don nace dasu ni ban sani ba can ko sai faman tambayan su ake don wata ta bar yar ta karama na barci a gidan ta biyo mu yarinyar ta tashi tana kuka sosai don haka ake tambayan ina suka je.
Har shi kanshi maigidan da kukan yarinyar ya damay su yake tambaya akace mai suna gurina bai tsaya mamaki ba ya fara fadin may suka je yi wurin yarinyar dake makaranta.
Mun shigo suna falo an gama rikici ke nan da buzuwa matar shi da Fauziya kanwar shi da su mommy don komai da ake shigowa dashi gidan buzuwa ta hana aba mutanen Abdulsamad sai idan kaje wurinta munafunci zata baka ko matan abokan shi haka bata ba abin sai taga dama.
A daidai lokacin da suka gama rikici da Fauziya da tace sai an raba an basu nasu, ranan ta murje ido tayi ma buzuwa tas a gidan abinda a da suke tsoron mata.
Shigowan mu ne gidan ya dawo da hankalin mutane a gare mu su tambaya ina suka shige haka ne ni da zainab ce da Binta sai maryam muka shigo daga karshe gidan ina tako dadaya duk kan mu kwaliyan mu ba laifi.
Tsaye yake yana magana a cikin fada muka shigo da sallama falon sai da ya so rudewa a lokacin da mukai arba dashi nayi saurin kawar da kai na mommy da na hango zaune na nufi gurin ta har kasa na zube ina gaida mommy ta dafa ni tana fadin khadija kina garin nan nazo na dade a nan ban ganki ba.
Yanzu ma nasan don su Binta ne kika zo gidan nan da bamu gan ki ba na san har mu koma Nafisa dake zaune ta cika ta batse sai huci takeyi tana kokarin son tuno a inda ta san fuska na amma ta kasa ban dade ba muka ce da su zamu koma ko dakin bamu shiga ba.
Binta na fadin ba wani abu a basu mommy shi kuma maigidan ns fadin Fauziya tashi ki hada nasu snack din nan da aka yi da drink's lokacin har mun kai kofan fita daga katon falon nasu ko.
Binta da zainab dake bin mu a baya ne ke fadin ku tsaya don Allah a kawo maku abin buki kutafi dashi na juyo nace da ita.
No ku barshi kawai dama mommy muka zo gaidawa a a yan mata ashe kun samu shigowa bukin ku ma ?
Muryan Yusuf ne dake fitowa daga cikin motar da ta parker a gaban mu yake fadin haka maryam ce ta bashi amsa da fadin wallahi fa.
No ba buki ya kawo mu ba munzo mu gaida mommy ne tsaye Binta tayi tana kallon mu da mamaki tafiya na fara yi zan wuce wurin Binta tace don Allah ku tsaya ku karbi abin buki mana.
Nace a barshi kaya zai muna yawa idan mun tsaya daukan wani abu kuma ke khadija wani kaya ke gare ki banda handa bag da kika rika nace shima ai kaya ne ko.
Khadija ya kira suna na da karfi na juyo tsaya mana ku amshi kayan bukin maryam tace ya Yusuf muna sauri ne mu samu abin hawa kasan unguwar nan naku idan yamma yayi akwai matsalan abin hawa.
You known each other ne dama ?
Zainab ke tambaya cikin mamaki No ya dade da na san su ba irin familier din nan ba dai na fada ina yatsune fuskana.
Barin sauke ku mana Yusuf yace da sauri nacevka barshi kawai zamu karasa ai na fadi ina ci gaba da tafiya na nufar get din zuwa waje.
Da sauri ya shiga babban motar Abdul din yana fadin ku shigo in sauke ku nasu in ki amma Binta na ta kaudi motar yayan sune ai in shiga a kaimu hostel din .
Zainab tace friend ku shiga don Allah bari muje tare a sauke ku sai yaya Yusuf ya dawo damu abubuwa ake fitowa dashi daga cikin gidan wai duk namu .
Mommy ne ta fito waje lokacin da zamu shiga motan tana magana dani tace ga abin buki nan yayan su Binta yace a baku kuje dashi wai angode nace lokacin shima ya fito wajen.
Yusuf ina zaka ne yace zan sauke su khadija ne hostel in dawo barin bi ka mu fita daga can zan tafi gidan MD dayani.
Ga mommy tsaye ta kura muna ido dole na yarda muka shiga motar a tare dashi dasu Zainab da binta ya juyo yana fadin ku kuma ina zaku sukace zamu raka friend din mu ne yaya.
Ba yanzu zamu dawo ba fa ku fita don Allah rike zainab nayi nace a tare zamu fita ke nan don saboda su nazo nan din da kuma mommy.
Sun yi mamakin jin maganan da na iya fada ma yayan nasu wanda suke matukan tsoro da girmamawa su.
Sun dauka zai yi wani abu sai sukaji yayi shiru bai sake magana ba sai tsawan da ya daka ma Yusuf akan ya tsaya mana su sauka kokarin sauka nike yi zainab tace ki bari gobe zan shigo wurin ki da safe ai.
Ta fice daga motar da sauri ta rufo kofan da mu a ciki yusuf ya kama hanya ya tafi daga gidan ba wanda yayi magana a cikin motar.
Ya Yusuf ka tsaya dan Allah in sauka ko sauraro na bai yi ba sai tukin mota yake a hankali kwance abinshi.
Tsuki na naja daga inda nake zaune muryan shi ne naji yace kibi a hankali fa kada ki bata muna rai a nan sai kace wace aka ce za a sace ta.
Nace ai in ma kunyi niya zaku iya hakan don iya yaudaran ku dariya sosai Yusuf yayi yace munyi kama da mayau dara ke nan khadija.
Kasan ta iya shirme wani lokaci mu sace ki muyi may dake ai ba irin ki zamu sata ba har in muna satan yan mata.
Yusuf yace nikan irin su zan sata don yanzu suna danyun su shar ai kaga daidai sata ke nan nace ai dama nasan zaku iya haka ba sai kun fada ba.
Yace Yusuf ya tsaya a wani guri da ake sai da kaji ya mika mai kudi ya sayo muna da abinsha mai sanyi Yusuf ya fita ya barmu a motan tare dashi.
Naji dadi da maryam ke cikin motar a lokacin ba a barmu mu biyu ba ko kallo gefen da yake ban yi ba maryam ne ta dan zugure ni wai in yi mai magana.
Na kawar da kai kamar ban gane abinda take nufi ba tunane nake ta yadda zan fita motar nasu a lokacin Yusuf ne ya dawo dauke da ledoji a hannun shi ya shigo motan yana aje kayan a gefen shi ya ta da motar muka tafi.
Ban akara ba sai gamu bakin hostel din mu da sauri nayi niyar fita daga motar amma motar tana rufe har lokacin ga sanyin A C motar daya damay ni.
Suna zaune ba wanda yai magana a cikin su har dan wani lokaci can naji Yusuf yace daidai lokacin da nake fadin ka bude mu fita mana.
Shikuma yana fadin gaskiya khadija ba a kyauta maki ba a kyauta maki ba da sauri ya dago kai yana kallon Yusuf din dake magana.
Yusuf fitar masu da tsaraban sunan su su sauka don Allah zaka tsaya wani magana kuma yace ya zama dole mu bata hakkuri don bamu kyauta mata ba.
Da akai mata may kuma ya tambayi Yusuf din cikin tsare shi da ido yace ai kaine mai lafin yaya zaka saka ta saba da kai daga baya kuma kazo ka share ta haka ba dadi wallahi irin haka