MIJIN BUZUWA complete Hausa Novels.txt

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   53 / 144

156K to 159K   out of 431K words

dayan su mamakin ganina ya kamasu na dan samu gefen kujera na zauna ina fadin ina kwana anty Nafisa , ?
Ke ta nunani da hannu tare da waro idanuwanta gare ni tana fadin wai dama kece ko dai wani abin ya kawo ki kuma gare ni yanzu.?
Gyara zama nayi nace eh nice ina kwana anty tace cikin hasala waye anty naki garama tun wuri ki canza salon ki ashe ke yar akuyace wallahi samad ka cuce ni karasa wace zaka dauko min sai wanan yarinyar mara mutunci ka cuce ni daka dauko min wanan a matsayin kishiya a gare ni.
Bari kuji daga kai har ita nafi karfin ku nafi karfin wanda ma ya dauko ki gidan nan har ke kin isa kizo min har gidana ki kwana min da mijina a matsayin mijin ki ke ma.
Bari kiji idan kina son kanki da lafiya tun wuri gara ki tatara naki ina ki kibar gidan nan ki barni da mijina tun duniya suna shedaki.
Murmushi nayi tare da mikewa tsaye nace waki ke da suna ne buzuwa kike kowa ake kiran ki idan junin ki iya shege yanzu kin samu mai tayaki yi agidan nan.
Idan kuma kurin ki kiran mijin taro da sunan mijin ki ke kadai to yanzu ki gyara zancen ki, bakin ki ya saba da kiran mijin mu, mu uku, Fati uwar gida sai buzuwa yar tsaka sai khadija amaryan tsakiya don bansan ko akwai wata zuwa bayana ba don haka bazan kira kaina amaryan gidanan ba.
Na kara takawa zuwa gaban ta nace duk wani abin da kike takama dashi ko yanga da zakiyi ko kike yi yanzu ki shirya yin shi tare da wata a gidan nan don bake kadai bace mamalakiyar wanan gidan ba yanzu.
Ki sani ni nan da kike gani ba fitina yashigo dani gidan nan ba don ni tsakani da Allah na auri mijin ku badon wani abinshi ba ko kudi ko kyau shi ko sabar shi, a, a na girgiza kaina nace Allah ne ya hadani da mijinki don haka ni dake mu zuba a gidan nan kamar yada kika furta yanzu.
Ina fadin haka na hankade su na fice daga dakin na koma dakina ido na rufe da abinda ya faru yanzu tsakanin mu da Nafisa.
Allah ya gani ba haka naso mu fara da ita a gidan ba sai mamakin kaina yadda na iya kallon su na fada mata magana son raina har dakinta nafito.
Binta da zainab nake tunanen ina suka shiga haka banji duriyan su ba a gidan har wanan lokacin.
Cikina ne ya fara neman agaji daga gare ni sai lokacin na tuna da abinci fita nayi zuwa kitchen don in ceci kaina zan halaka da yunwa kawai a gidan nan.
Kitchen din na shiga sai na tsayawa ina karema kitchen din kallo yadda aka tsara komai a cikin sa gwanin ban shawa, a dashi sai da na gama duban kitchen din.
Komai na aiki akwai acikin sa ga freze nan da sauran na,urorin kitchen a kune suna ta aiki a ciki fridge din na bude wani tururin sanyi ne ya daki fuskana.
Ledan da nagani sama ne na bude naga kaji ne a ciki da sauran drinks a cikin kwalayen su ga kuma danye kajin da ba,a gyara ba nan zube acikin sunyi kankara.
Ledan kajin na jawo na dauko daya na sa a oven ina gasa kazan hawaye ne ke zuba a idona saboda irin rayuwan da na riska tun yanzu a gidan.
Sai da na kammala na dauka zuwa falo na na zauna ke nan zanci sai ga shi ya shigo part din nawa tunda na dago kai nayi mashi kallo daya na duka naci gaba da cin kaza na a hankali.
Karasowa yayi a cikin dakin daga inda nake zaune nace dashi ina kwana a ranshi yaji dadin haka ya amsa min a sake da kin tashi lafiya ?
Ni zan fita zuwa office yanzu don yau ina da aiki sosai a office sai dai wanan aikin da naga kinyi yanzu akwai masu aiki a gidan sai idan na dawo yau da yamma zan hadaku in sanar dake komai na gidan don ki sani na gaba .
Tunda ya fara magana ban dago kai na kalle shi ba ya karaso inda nake zaune saman kujera na tasa kaza a gabana yana turiri ina ci.
Wuri ya samu ya zauna a kusa dani yana fadin ina nawa kazan ko haka zaki bar angon naki yafita da yunwa don nasan ba haka akace ki min ba idan kin zo.
Wanan matsalan kane kai haka akace kayiwa bakon gidan ka kabarshi da yunwa idan gari ya waye .
Dariya yayi yana kai hannu ga kazan dake gabana yace ai ke yanzu kin wuce bakuwa a gidan nan tunda har kin gabatar da kanki ga matan gidan ko tasan ko wata kalane ke tun yanzu.
Nace eh don a haka kuka ja in gabatar maku da kaina ko ni wacece a gare ku ya kara kai hannun shi ya dibi naman yana fadin.
Ke may yakai ki shiyan ta a yanzu da sauri na dago kaina ina fadin kada ka dauka shishigi naje maku ni har ga Allah gaida ku da kwana naje yi amatsayi na karama a gare ta.
Yace na sani kuma nasan manufar ki sai dai ki sani ba iri Nafisa akewa wanan shishigin ba don a yanzu duk abinda kikayi gani take da sheri kikazo mata don bata da yarda ko kadan.
Shiru ne ya biyo a gurin dagani harshi babu mai magana shi ya kawar da shirun da fadin barin bar maki abinki kada kice na cinye maki.
Nace kaci ni ya ishe ni su Binta nake jira su shigo mu shiga kitchen mu girka abinda zamuci yau a gidan.
Hannu yake gogewa da tissue, ya kallo ni yace au ban fada maki sun tafi ba kina barci mommy tace abarki ki huta kada a tadake sai kunyi waya dasu .
Wani iri naji ba dadi a raina har na kasa boyewa a fuskana ya mike yana fadin kar kiji haushin hakan don ba da wani manufa suka tafi basu sallamay ki ba.
Sunyi hakane dan a zaton su kin kwana da angon ki daren jiya kina cikin gajiya da wani hali yasa mommy tace su kyaleki ki huta haka.
Hararan shi nayi yana murmushi zai fice daga falon yace amarya mai rowa zan kira daddy in fada mai barci kikazo kina min a gida.
Kai kadade baka fada mai ba tunda baka da kunya au da wasa kika dauka ke nan sai ya ciro waya a aljihun shi yana kiran daddy na.
Kira daya gana biyu daddy ya dauka da sallama a bakin shi, shi yafara gaida daddy din tare da tambayan shi baki sun isa gida lafiya ?
Banji amsan da daddy yabashi ba a lokacin sai dai naji yace ma daddy gani nan yana kokarin mika min wayan.
Na karba ina gaida daddy din cikin sanyin murya mai ban tausayi don jin muryan daddy ya sakani a wani hali a lokacin gida ne ya dawo min sabo a raina.
Da kyat nake iya bude bakina ina amsa ma daddy amin kan adduan dayake kwararo min a wayan wanda nake ji kamar in fashe da kuka a lokacin.
Wayan na mika ma AA din ya amsa yaci gaba da magana da daddy cikin sakewa kamar sun dade da sabawa dashi tun farko.
Suna gama magana dashi ya kashe wayan yana kallon yadda nake zubar da hawaye daga inda nake zaune.
Takowa yayi a hankali zuwa inda nake zaune yana fadin kuka kike don kin ji muryan daddy a yanzu suma fa sun fi son zaman ki anan yanzu da zaman ki a wurin su.
Dago kai nayi na kale shi nace rashin sanin zai sa su soni a inda ba a sona da sun san da wanda suka hadani dashi ba sona yake ba nasan da bazasu yarda su dauko ni su kawo ni inda rayuwana zai shiga tangariri ba.
Ba,a son ki fa kikace da ba a son ki da baki shigo gidan da bakin ki ka fadi gidan mijin kine ba.
Nace dashi ka dogara ashe yace dashi din kowa yasan kina zama gidan yanzu nan gida miji ki ne uban "ya"yan ki masu zuwa.
Uban wasu dai a ina zan haifi diyan da uban su bai taba sona ba balle ya furta min wata kallama mai kama da hakan.
Murmushi yayi a baiyane yace kalman so kike so a furta maki san nan ki yarda ana son ki na dago na kalle shi na kawar da kaina daga kallon shi.
Gap dani ya matso kamar zai shige min jiki sai da na dan ja da baya na makure a gefen kujera ya ce koya min abinda zan fada maki yanzu a shirye nake in fada maki matukar zaki yarda dani idan na fada maki din.
Sauran yaya kayi ka fada masu kana son su har ka zauna dasu a gidan ka zai yi magana mukaji sallama a kofan shigowa part din kafin mu amsa maishi har ta shigo falon ko.
Ba sai an fada min cewa buzuwa bace itama don yanayin su dana gani a tare da ita ba gaisuwa ko wani abu sai cewa tayi Alaji yayan mu tace kafito yanzu tana magana dakai.
Yace kice da ita gani nan tafe ya na shirin mikewa tsaye itama ta juya zata fice tana wani harare hararen da tsage ranci nace ke buzuwa.
Daga yau idan zaki shigo wuri ki bari idan kinyi sallama sai an baki iso zaki shigo kada ki kara fado min a shiya haka kamar kafira.
Ta juyo tana kallona kamar zatai magana sai kuma ta kalli fuskan shi yace kije nace ina zuwa yanzu .
Ya juyo ya kalle ni na tsura mai idoina kallon yadda zai fita daga dakin ina ganin ya gane may nake nufi sai ha kalli agogon hannun shi yana fadin malamata kin sa na makara zuwa office yau gashi kuma ban dauki komai ga darasin ki ba har zan wuce.
Harara na aika mai nace je kada kai laifi gun madam yanzu ta turaka waje ba shiri dariya yayi yana buga kafan shi kasa ya fice yana fadin zan kiraki idan naje office inji lafiyan amaryana, na bishi da harara ina jan tsuki nace a raina akwai aiki a gaba na ja kuwa.
Mikewa nayi daga inda nake zaune na fara gyara falon duk da bai wani yi dattiba amma sai da na kara gyara shi na koma kuryan dakin dana gyara tun kan in fita da safe na kara gyarashi shima.
Misalalin sha biyu namike nayo alwala nazo zanyi nafila wanda dabi,anane hakan tun a gida idan ba uzuri ya fitar dani waje ba zanyi sallah a wanan lokacin idan ina gida.
Aka turo kofan dakin aka shigo wasu mata ne su uku ko wace daga cikin su taci ta koshi tana tafiya da kyat da ita na mike daga inda nake zaune ina masu sannu da zuwa don ban san ko su waye bane a lokacin.
Gaida su nake suko sai kallo na suke suna kada kan su cikin gamsuwa da ganina Nafisa ce ta shigo dakin a karshe .
Tana wani ya tsune kamar mai jin wari wani abu a part din nasan salon iya shegen tane haka yasa ban wani tsargu ba.
Tace ashe har kun shigo ko taja tayi tsaye a bayan kujera daya daga cikin su ne take fadin eh lalai kuwa mun ga amarya itama gata da zubi irin naku na buzaye ai ba a raba ku da ita don kusan zubin ku daya da ita.
Daga inda take tsaye tacevkin sani ko farin mai ne do yanzu akwai fari a shago sai yadda kake son ya tsaya maka zai tsaya.
Nace ai kin san tun kafin ai farin shago akwai na asali wanan da kike gani daga Allah na samay shi ba saye nayi ba kamar wasu.
Madam tace a, a Nafisa kardai kishi yasaki yin maganan nan amma ai wanan fari ke ma kin san na asaline jin haka da madam ta fada yasa tayi shiru tasan katse ta tayi daga yin katobara a gaba mu.
Ina zuwa tace kasu ta fice daga dakin na gane mutanen tane don haka ban wani sake dasu ba a dakin.
Nafisa na fita waje madam tace dama mun shigo mu gan ki ne kuma muyi maki nasiha ku zauna lafiya a tsakanin ku ki biyayya ga mijin ki da matar gidan da kika samu.
Kada ki wuce matsayin ki garesu kamar in bude baki in ce mata akwai wani matsayi ne da ya wuce in shiga a gidan sai dai nayi shiru inji karshen maganan ta.
Tunda ba sa,ar yina bace don dukkan su ukun sun manyata ga ido bazan iya masu rashin kunya ba a yadda suke.
Taci gaba da fadin kada ki zaman to cikin irin matan nan masu shiga gida su tarwatsa zaman lafiya agida.
Ki maza ke ma ki sama muna yan dugwidugwi ki cika muna yaya a gidan koda yake ancd ba son shi kikeyi ba ma aka aura maki shi.
Sai lokacin nayi magana tunda ta fara nace cikin dariya ai hajiya zancen rashin so ya kare gareni yanzu tunda na shigo sai a fara damawa dani nima.
Kallon juna naga sunyi dana fadi hakan ta gyara zama tana fadin yawa yad gari ai zancen so ya kare kan tunda an shigo ta sake kashe murya tace kin ga dai kishiyar taki ai.
Don haka ki bita a sannu don muke tare da ita mu muka san halin ta ba son kishiya take ba don haka nake fada maki kibi a sannu kada ki shiga sha,anin da ba naki ba.
Ki kwanta kikaga gudun ta kafin ki aitar da komai garesu don sai kasan kan gida kake kafa naka ikon nace ai gidan tane hajiya don tare na samay ta da mijin ta may zai sa in sa mata ido ga alamuranta bayan tare nazo na samay su.
Ina kallon su suks kalli juna suka daga ma junan su gira cikin sytle suka mike suna fadin to amarya min gaida ke mu zamu tafi muna maku fatan alheri .
Nagode halin ku na alheri gare ni ya rakaku suka kali juna suka fice a dakin naja tsuki suna fita sai dakin Nafisa suka shiga.
Tana zaune tana jiran shigowan su taji yaya akayi madam na zama tace Nafisa wanan amaryan taki ido ta a bude yake wallahi naga kamar kar take kallon mu ta gane plain din mu fa.
Hajjaju tace aini amsan da take bakine ma ya firgitani wallahi yarinya da an fadi magana sai ta bada amsa daidai da maganan mutum.
Wallahi shegiya ni kyau tane ma ya rudani wallahi dole samad ya rikice muna haka a kan ta babu namijin da zai samu wanan ya bari ta kubce mashi.
Yadda suke zuzutani a gaban ta yasa ranta ya kara baci taji wani irin kishi da hassadana ya kara shiga ranta a lokaci daya.
Taji in akwai wanda ta tsana yanzu a duniya bai wuce ni din ba sai a lokacin take tunanen ina ta fara sani na don ita a zaton ta anan abuja ta sani.
Gani sukayi ta mike zubur suka mai da hankalin su gare ta suna kallon ta tace tsaya hajjaju yarinyar nan kamar itace wace mahaifiyar samad ta taba hado mu da ita wani lokaci mu rage mata hanya daga kaduna.
Nan dai ta koro masu yadda abin ya faru take madam tace duk yadda akayi da sanin mahaifiyar shi wanan abin ya faru.
Sun dade suna magana akan zancen suna neman mafita yadda zasuyi su kawar dani a gidan cikin dan kankanin lokaci.
Hajjajune tace ni anawa ganin dan bakan nan zata fara dana masu ya zamanto babu abin da ya wakana a tsakanin su don babu shegiyar da zata zauna haka tana kallon namiji kamar samad bai taba ta ba.
Madam ta juya wurin ta tace ba mutumin nan na maiduguri ya bamu shi tace ai tun ranan da aka kawo ta na fito da shi yanzun haka akan shi na dogara in ga iya gudun su kafin in shiga masu Niger din kansu.
Don nafi gane ma asirin mutanen kasar mu don na nan sai ya dauki lokaci kafin kaga fa,idan abu.
Yinin ranan ya kirani har sau biyu ban daga waya ba sai ga na uku ne na dauka cikin basarwa nake amsa mashi maganan shi ba wani magana bane sai zolayan da yake min da fadin.
Amarya na ya na barki kifa shirya idan na dawo darasin mu zaici gaba daga inda muka tsaya don kin san dalibin naki ba kan daukan magana yake dashi ba.
Kaidai ka sani na bashi amsa a hasale tare da fadin wanan ne sallon yaudaran ka ashe idan ka saba yaudaran matanka da dadin baki anan kan kayi kuskuren yin haka.
Dariya dake bani haushi ya soma na kashe wayan tare da jan tsuki na koma na kwanta naci gaba da tunane a raina ina tuna yadda zaman mu zai kwashe dasu a gidan shi.
Gashi na fahinci gidan cike yake

53 / 144

Chapters