Kai kasan wanan nace dashi ina kokarin kwace jikina daga rikon da yai min din kamar mai rada yake magana.
Idan mun idar da sallah zamu zauna daku a falo don haka ki zauna a cikin shiri zan kiraki naji nace dashi kawai ya sakeni yana gyara hannun rigan dake jikin shi.
Ya juya nace dashi dama sai kuma nai shiru yajuyo tare da takowa zuwa inda nake yana fadin dama may sunkuyar da kaina nayi kasa tare da fadin.
Idan na gama abinci a ina zan kaima naka yayi murmushi tare da kallona a cikin mamaki abinda bai samu a gidan shi yau ya samu ana mai tayin abinci dare da zaici.
Haka gaisuwan da nayi mai yaji shi wani iri don bai saba aimashi ina kwana ko wuni ba idan ya tashi.
Yace kin san ban saba cin abinci a gidana ba sai dai zaki iya kai min a dining din dake sama anan zan samu inci hankali kwance don wanan dining din na kasa ya zama na kowa yanzu.
Nace ko in aje maka anan idan ka shigo sai kaci yace hakan ma yana da kyau nagode ya fada daga haka bai tsaya ba ya fita.
Ajiyan zuciya na sauke bayan fitar shi daga part din nawa ina mamaki mutum da gidan shi baida daman ya wala yadda yake so komai a make zaiyi shi don wani akida nasu na daban.
Gaskiya akwai aiki ja a gabana yadda zamu zauna da mutanen nan su da yawa ni kadai a cikin su ya zama dole gare ni in jajirce sosai in kwatar wa kaina inci garesu.
Wanka nayi na saka atamfan zani da riga a jikina sai da na zauna na gyara fuskana a jikin mirrow nakawo dan kwalina na kafa daurin ture kaga tsiya nayi sai daurin yai min kyau sosai ya kara fito dani.
Ga gashina dsa yasha kitso a baya daure da ribon ya fito fili yana sheki karan wayana naji daga inda nake zaune na mike zuwa inda wayan ke jikin caji.
Sunan da nayi seving din nomban shi dashi nagani a wayan sai da ya kusa katsewa na daga wayan muryan shi ne yana fadami in fito ni suke jira tundazun.
Nace naji kawai na kashe wayan turare kusan kala biyar na feshe jikina dashi kafin in fita nakawo takalma masu hill na saka a kafana kamar mai shirin fita unguwa sai kara suke sakewa na tada hankali .
Tun fitowa na naga kallon da matan buzaye dake zaune a falon gidan sun tasa wani abu ga buta sama suna rike da kofuna a hannun su, suna min wani kallo kamar sun ga abin mamaki a tare dani.
Babu wace taimin magana daga cikin su nima haka na nuna ban san da zaman su a falon ba nabi kwatancen da yai min na haye sama dauke da basket din abinci a hannu na.
Da sallama na shiga falon da baikai wancan dake kasa girma ba zaune na hango su saman three seater kamar su manne ma juna dashi da ita.
Na karaso da sallama mana ta dago ta dubeni daga samana har kasana ta kawar da kanta gefe daga kallona dining din na nufa na fara jera abinci a sama dining ne na glass mai kujera shida.
Sabanin wanda nake gani babba a falon kasa wanda kujerun shi zai kai takwas ko fiye da hakan gaba sai faduwa yakeyi amma na dake don in nuna mata ban damu dasu ba.
Sai da nagama na juyo inda suke zaune nace ga abinci nan na shirya maka yayi murmushi tare da fadin sannu da kokari na gode.
Wanan godiyan da yake min tsakani jiya da yau yasa na kasa fahintar halin ko zan iya kiran shi da mutum mai saukin kai ko akasin hakan.
Ya dubi inda Nafisa take a gefen shi zaune yace bissimilah mu fara cin abinci ko ina ganin zai fi sauki kafin muje ga abinda ya tara mu a nan.
Kallon ta na danyi da gefen ido na dauka zatace wani abu sai naga ta rigashi mikewa tsaye ba tare da tayi magana ba ta nufi gurin table din.
Tana isa ta fara bude kulolin abincin tana tabe baki har tagama ta jawo kujera takai zaune shima ya taso ya ja daya ya zauna a kusa da ita.
Sai da na bari sun kai zaune na karaso gurin na ja wanda ke dayan gefen shi na zauna muka sashi a tsakiya.
Kallona tayi kamar zatai magana sai kuma naga tayi shiru ta fara zuba abincin da plate idin dake gaban ta.
Ganin haka sai na mike na bude kulan na jawo plate din gaban shi na fara serving din shi na sai da na kusan rabin plate din da abincin nace akara ko ya isa hakana ?
Yace is ok wanan yayi min sannan na zuba kadan a plate don kada suce banci ba na koma na zauna nayi bissimilah na fara ci a hankali.
Saici yake ya na wani lumshe idanuwan shi ban sani ba ko haka yaba ta haushi sai ta turo plate din ta da karfi tana jan tsuki ya dubeta yace ya akayi ne bazaki ci abincin bane ?
Ta wani yamutsa fuska tana fadin dama tun farko kamshin abincin bai mun ba kuma dandanon shi babu dadi.
Yakai loma a bakin shi zaiyi magana nariga shi fadin saukin abin wanda na girka kan shi yayi mashi dandano don naga yana kai hannu baka hannu akushi.
Yayi mashi na dole ko kamar yadda akai mashi dole a kanki ya kwaso yakawo min ke cikin gidana ke naga zubin ki na marasa kunya ne fa.
Murmushi nayi sai da nakai lomar da na diba a bakina na kora da ruwa nace saukin abin dai shine kin gani da idon ki ai kowa akaiwa dole a cikin mu.
Kin taba ganin inda aikawa gwabjejen kwato kamar mijin mu auren dole kuma namijin ya kalli macen dole nan take.
Enough don Allah ya isa haka bashi na dauko nan kuyi min ba abinci dai bai maki ba bakici shikenan ya isa haka ban son jin hayaniyar nan kuma.
Shiru nayi ban kara magana ba itako tana saman bakin ta sai abinda ta manta gurin fadin bakar magana don in nuna mata nazo da shirin biyayya ga iyayyena da wanda yayi sanadin zuwa na gidan ban sake kulata ba har muka kare na tattara kayan a cikin basket tana kallona kamar ta shake ni.
Bayan ya gama ya mike ya dawo saman kujera ya zauna ta taso ta dawo inda yake da sauri ta zaina sai da na gama hada kayan na dawo saman three seater din da suke zaune yana ganin haka ya gyara min wuri nima na zauna.
Nafisa irin matan nan ne da basu iya danne kishinsu sai ta fitar a fili angane nufin ta a take na fara gane takon ta.
Yayi gyaran murya ya soma magana Nafisa gadai kawar ki nan na kawo maki gidan nan sai kiyi hakkuri da ita ku zauna lafiya.
Ban son in, , , tare shi tayi da fadin kanwa ta ko kishiya ta kace ga kishiya ta ka kawo yan uwan ka sun auro maka mata da zata zo ta ci min mutunci muna zaune kalau.
Wanda su kuma shine basu son su gani a gare mu ni kuma ba wanan ba ko goman ta zaka dauko bazata taba girgizani ba indai Nafisa ce.
Murmushi yayi a cikin rashi yace mudai samu mu iya da wanan din mai gira saman ido tukun.
Ya juya gefe na yace Khadija kinga yar uwar zaman ki Nafisa ina fatan zakiyi mata biyayya a matsayin ta na wace kika sama gaba dake a gidan nan.
Sanan akwai masu aiki duk wanda kika gani a gidan nan da sunan aiki yake zaune nan tare damu babu abinda zakiyi hatta gyaran daki da wanki bayin ki duk sune zasuyi maki daga cikin su akwai masu girki sai dai duk abin da kike so kya iya sanar dasu su girka maki.
Zan sa a saka maki waya da duk kike bukatan wani zaki iya kiran masu aiki suzo saboda bukatan ki.
Ko in kinyi baki haka kodai wata matsala aikin ki daya ne a gidan nan shine gyara min dakina watau shifidana don ban yarda wani dan aiki ya shiga min daki saboda sirina.
Zaici gaba da magana tace Samad wai kana nufin yan uwan nawa kake kira da yan aikin da zasuyiwa wanan aiki ko may ?
Yace yan uwanki ba a matsayin mai,aikatan gidana kika dauko su nan ba ina biyan su duk wata kuma da albashi mai tsoka ban cutata masu ba ko kadan.
Ta sake duban shi da mamaki kamar zatayi magana ya rigata fadin ko kina nufin duk wanan taron haka zasu zauna damu a gidan nan a yadda suke so.
Tace to wallahi baku isa ba daga kai har ita baku kai min can ba babu wacce zatayi ma wanan aiki a gidan nan aure tazo yi tayi aikin ta da kanta zamana suke a gidan nan kuma ni kadai zasuyiwa aiki idan ina so.
Murmushi ya yi kadan yace ashe ko idan har ba zasuyi wa matana da na dauko aiki ba sai tayi da kanta zasu ko bar min gida kada kice ban fada maki ba.
Yaci gaba da magana yace sai kuma zancen kwana idan khadija ta gama satin ta na addini da aka tanada namiji yayi a dakin matar shi ina son jin yadda zaku raba kwana a tsakanin ku, ?
Don in sani saboda shiga hakkin wani ya kare da cewa ina sauraren ku shiru dakin yayi don ita wani gurin take kallo da alama ma hankalin ta bai a girin lokacin ta lula duniyan tunane.
Ya ce uhumm ku nake saurare fa dare nayi ina son in je in kwanta ne don magaji da yawa hidimar bukin nan bai fita jikina ba.
Sai lokacin ta kallo shi tace kana nufin har kwana bakwai zakayi a gurin ta ko mai ?
Yace haka addine ya kidanya muna tunda ba bazawara bace ita mikewa tayi tsaye tace baka isa ba wallahi ta nuna mu ds yatsa tace dukkan ku kunyi min kadan.
Wanan ai son danne hakkin wanine ya girgiza kai yace bani fatan in danne ma kowace daga cikin ku hakkin ta don kowa son shi nake na kawo shi nan mu zauna tare dani.
Ganin zancen yana ta nisa a tsakanin su yasa nayi magana nace idan zancen kwanane a barshi a kwana bibiyu ina ga hakan zaifi sauki.
Ta juyo da sauri tace ke wacece da zaki tsara muna yadda zamuyi kwana a gidan nan na bude baki zanyi magana ya daga min hannu naja baki na nayi shiru.
Yace idan na kwana biyu zakuyi ba kwana nawa kike son kuyi ba wani nauyin baki tace mashi daya.
Yace dayan yayi maki hakana yana kallo na nace yadda kuka tsara duk dayane a gareni banda matsala ni agurin haka.
Yace idan haka yayi maku kuna iya tafiya Allah ya kauda shedan a tsakanin mu nace amin sai dai banji ka fada muna wani magana daya dace ace mun san dashi ba.
Da sauri suka kalloni a lokaci daya duk su biyun yace may ke nan na manta nace a cikin maganan ka ka manta ka fada muna lokacin da zaka dinga tafiya kaduna ziyaran uwar gidan ka uwar yayan ka sai nake gani ya kamata musan da wanan yanzu.
Daga inda Nafisa take zaune ta watso min wani kallo shi kuma gogan murmushi yayi a ranshi yace kin fara baiyana min manufar su hajiya mama akan ki ke nan.
A fili kuma cewa yayi hakan ma shawara ne mai kyau zan iya zuwa karshen kowani wata in duba su shike nan ko ya tambaya na gyada mai kai badon hakan yayi min ba yace Allah ya taimakemu ya bamu sa,a yana shirin mikewa.
Ita ta rigashi mikewa batare da tayi magana ba ta nufi hanyar fita daga part din nashi rai a bace nima mikewa nayi don in bar gurin da tunane kalakala araina.
Na sauko saman a hankali ban samu kowa a falon kasan ba lokacin da na fito na shige part dina na rufo kofana, .
Abinda ya soma dagawa Nafisa hankali shine zancen yan uwan ta da yayi sai kuma zancen Fati da taji a baki na yanzu nawa iskancin tana daukan shi wasa don har taga ta magance shi ko a wurin ta.
Tun wanan lokacin da akai maganan ni ban ma gwada kiran kowa ba daga cikin su don ba yarda nayi dasu ba har cikin raina.
Koda ya shigo dakin har na gama abinda nakeyi na kwanta a can cikin barci na naji shi a bayana kamar karamin yaro yana karkaduwa alaman baida lafiya.
Zubur na mike tare da kunna wutan dakin ina binshi da kallo idanuwan shi suna a rufe nace baka da lafiya ne kai kawai ya gyada min alaman eh.
Nace wani taimako zanmaka yanzu yace ki kara rufa min wani bargo don Allah mikewa nayi na sauka a saman gadon na jawo bargo cikin wardrobe dina na rufa mashi ina mashi sannu.
Na koma gefe nakura mashi idanu kawai ina kallon yadda yake kaduwa a cikin bargon tare da tunanen wai yau nice a gado daya tare da AA a matsayin miji da mata dadai naga tunane ba zai fitar dani ba na fara yi mashi addua daga inda nake zaune .
Ayyatulqursiyu na fara karanto mashi sanan falaki da nasi da kulhuwallahu na tofa mai tare da gyara mashi rufa.
Da kyat barci barawo ya dauke ni na koma barcin alam din da nayi setting ne ya tayar damu daga barcin.
Ina tashi nagashi zaune kamar bashi bane ke kaduwan sanyi da dare na kalle shi ina kokarin tashi nace ya jikin da sauki yace yana sauka saman gadon ya shiga bandakin.
Sai da yafito na shiga na kewaya ruwan zafi na watsa ma jikina na dauro alwala nafito na samu ya na sallah .
Ban bi ta kanshi ba na fara gabatar da nawa sallah sai da muka idar ya tashi ya koma saman gadon ya kwanta ban koma saman gado ba anan inda nayi sallah na dan kwanta bayan na gama azakar din da zanyi.
Sai takwas ya falka lokacin har na hada mashi abin abin karyawa ina jiran shi ya tashi yana falkawa yakai kallon shi ga agogon dakin yana fadin khadija shine baki tayar dani ba don zuwa office.
Nace gani nayi daren jiya bakai barci ba yasa na kyale ka kadan runtsa kafin yai wani magana nace dashi ina kwana ya jikin kuma ?
Lafiya yace yana sauka saman gadon na sake cewa ga abin karyawan ka nan idan ka shirya nagode yace barin dan je in watsa ma jikina ruwa in shirya zan dawo yana fadin haka yafita daga dakin.
Ni abinda ke ban mamaki a cikin kwanakin da yayi a dakin sai dare yayi a haka muke kwana dashi a wahalce ba sauki sai gari ya waye zai tashi kamar bashi ba sai dai ban kawo komai a raina ba na dauko yanayin ciwon ne yazo mashi a haka.
Gashi a dadafe yakai sati daya a wurina don nagaji da gorin Nafisa da kawayen ta dake shigowa ganin amarya suzo su karanta min haukan su su wuce do ni na dauke shi haukane sukeyi.
Abinda ke daga ma Nafisa hankali bai wuce kullun tana saka kunne taji fada a tsakanin mu da maigidan sai taga in gari ya waye shiru mun tashi kamar babu komai dake faru damu.
Idan ta kira madam tana fada mata sai tace nafisa baki da hakkuri wallahi komai ba asannu ake binshi ba.
Tace madam ni sai ina ganin kamar abin bai aiki yana kwana da itane a fake tace zan shigo gidan zan dan bugi cikin ta muji.
A nawa bangare duk da babu wani abinda ya taba shiga tsakanina da AA kuma bai taba nuna min yana bukatan wani abu a gurina ba.
Hakan bai taba damuna ba a raina don ban kawo wanan a tare dani ba yanzu abinda yafi damuna shine karatuna don shike cikin raina.
Yadda naga yana nunawa hakan nima nake nunawa a gidan zai shigo da rana mu gaisa yadan min wasan zolayar daya saba ina mashi tsiwa inyi mai girki yaci yana min godiya.
Tun zuwa gidan yaune karo na farko da nake son shiga dakin maigidan don in gyara mai kamar yadda ya umurta ai mashi don ban ke daya a hannu na.
Wani super nawa ne da mijin ya Amina yai min last sallah a jikina wanda akai min dinkin buje da riga din yana min kyau sosai a jikina.
Na dauko wani dan gyale na yafa tare da zura takalma a kafana nafito na rufe part dina do ban yarda koda wasa in bar part din a bude idan zan fito.
Sai da na kwataci bai gida na nufi part din suna zaune falo duk suka bini da ido caaa na wuce ba tare da nayi masu magana ba kamar