Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MIJIN Buzuwa Complete Complete Hausa Novel by Nil

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   55 / 144

162K to 165K   out of 431K words

safe yake fada mata ranan amaryan shi zata tare.
Sai da madam tazo gidan ta ya samu ta natsu daga haukan da take fada sosai su madan sukai mata suna fadin zasu barta don tana son bada su a idon mutane su kuma basu nuna rakin kishiya a fili sanan ta natsu.
Sai kai da koma Yusuf keyi a gidan yayin da yake shige da fice nafisa na daki da yan uwan ta da kawayen ta ana ta faman zugata a gidan.

KHADIJA

Tunda muka dawo lapai da su mama Tani ban kara lafiya ba haka nake zube har washe garin da za a kaini din dunga yadda nake bai sa daddy yayi hakkuri ba har in ji sauki.
Duk wani wanda zai min nasiha akan aure a cikin yan uwa yazo yai min nasiha a dakin mu fada kan zaman aure da sabon yanayi da zan shiga yanzu.
Daddy sai fada yake suyi su tafi kada dare yai masu a hanya motar data dauki kayan da zan tafi dashi daga gidan mu duk da Yusuf yace kada ai min wani tarkace komai zan samu acan amma bai hana iyayyena su saya min abinda ya dace dani ba.
Wani siri da iyayye mata basu sani ba akai min mama ce ta wanke barin jikin ta na gefen dama aka bani ruwan in wanke jikina dashi tare da dauro alwalan barin gidan mu nazo nayi sallah raka,a biyu.
Sannan su Anty Amina da mama Tani suka shirya ni cikin wani lafiyayyen cotting lace mai laushi da daukan ido aka kawo alkyaban aka dora min sama mai hula da gyale a jikin shi irin na matan kasar yamal.
Suna rike da hannu na a guda mutane suka raka ni kofan dakin daddy don muyi sallama dashi ina kuka kamar zan shude mun samay shi shida mama a dakin suna magana muka shigo.
Na tsunguna a gaban su tare da kifa kaina a jikin maman mu ina kuka
Daddy ne yayi karfin halin magana a dakin yana fadin haba khadija ( kijjo) wai mainene a ciki harshen Nufan ci yace kukan ya isa haka mana.
Khadija aure ba yana nufin kin rabu damu bane har abada a, a muna tare dake har abada ga Amina da suwaiba kina gani duk da sunyi aure amma ko yaushe muna tare.
Khadija ni ne dai mahaifin ki na yafe maki duniya da lahira duk abinda zakiyi a gidan mijin ki ina son ki tuna da Allah ki sa Allah a gaba sai kiga komai yazo maki da sauki.
Ki bi mijin ki sau da kafa don yanzu Aljannan ki ya koma karkashin mijin ki nayi bincike da dama khadija kafin in aura maki shi na gane mutumin kirki ne sosai ban ba dake haka ba sai da nayi kwakwaran bincike a kan shi.
Allah yayi maki albarka yabaku zuria masu albarka da amfanin a duniya da lahira mutanen dake wurin suka ce Amin sai mama tani tace maman mu tayi min fada.
Sai da ta fara magana sai ta kasa sai cewa tayi Allah yai maku albarka ya tsare mun ke da tsarin sa na alheri ya kare min ke ga abinki sai kuka ya kubce mata ta dora hannu a kaina tana dan bubuga min kaina a hankali.
Duk wanda ke wuri kuka yake yi banda daddy dake murmushin yake na ciki na ciki mama tani ne ta dago ni tana fadin kin dai ga yadda mahaifiyar ki ke yi a gidan ku don haka ke ma kiyi koyi da halin ta.
Daddy ne yace a fito yana fadin a tafi kada ayi rana a hanyan dare yayi nan aka firfito masu zuwa dama suna a shirye motoci biyar ne za su tafi yan rakiya na sai yan uwan ango daya da suka zo yau da sassafe.
Ni da mama Tani da maryam ne a motar mu maryam na gaba muna baya zaune da mama sauran yan uwa da abokan arziki suna sauran motocin.
Uku saura na rana muna cikin garin Abuja direct gidan muka nufa sai dai abin mamakin da muka fara karo dashi shine motar farko data tashi da kayana a ciki tana tsaye kofan gidan na AA a bakin get tun lokacin da suka iso wai an hanasu shiga ciki.
Gwagona da wata yar maman mu sune suka biyo kayan suma gasu waje zaune cirko cirko a bakin get din gidan.
Motocin mu na tsayawa sukayo gurin mu suna fadin kun iso ko wallahi tun dazun muka iso akwai matsala a gidan nan don wai uwargida tace ba za,a shiga da kayan khadija ciki ba.
Kamar yaya baza a shiga da kayan ciki ba mama tani da kawayen ta suka tambaya gwago tace haka dai mai tsaron kofan yace muna da muka iso.
Su mama suka taka har zuwa kofan gidan ta kwankwasa shiru ba a bude ba sai wata kawar aikin mama ta karaso ta fara dukan kofan da karfi kamar zata balla get din shiga gidan.
Nan mata da aka zo suka shiga fadin albarkacin bakin su shiru ba wanda ya bude kofan maryam ne daga inda muke zaune ta daga waya ta kira Yusuf tana fada mai halin da ake ciki.
Yace what kice a bari muzo yanzu ya kashe wayan nan maryam ke fada masu abinda suka ce mama tani tace lallai akwai magana a gidan nan.
Wanan wata irin mace ce yar iska haka da ita sauran sukace yau ko zata ga tsiya don zamu gwada mata mun fita iskanci babu tsoro a gare mu ko kadan.
Sai lokacin dariya ya subbuce min don su ma sunga abinda nakewa gudu yanzu da idon su zasu je su karas a gida idan sun koma.
Maryam dake zaune gaban mota ta gama waya ta juyo tana ce min muguwa may kikewa dariya nace sun fara sheda abinda nake fada maku tun yanzu.
Daga inda muke zaune muna kallon yadda ake rikici a kofan gidan yadda yan kawo ni ke faman halako da tada jijiyoyin wuya aka a budw masu kofa su shiga dani.
Da suka fara dukan kofan iya karfin su gaba dayan su kamar zasu ta da unguwa a lokacin.
Dole aka fito su madam ne suka fito daga ciki suna fadin wai waye zasu balla muna kofa haka ne suna fadi da karfi daga ciki ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kawayen mama Tani da su Ya Amina sukace baki ne na alheri daga minna daga ciki su madam suka amsa nan ba gidan mutanen Niger bane kunyi bata.
Mommy da motar su ya tsaya ta fito da sauri daga motar tana tambayan may ke faruwa ne haka nan matan ke fada mata abinda suka sama a gidan rai bace ta daga waya ta kira Abdulsamad din yazo ga abinda ke faruwa a gidan shi.
Mommy ta kasa hakkuri taje kofan tace ku bude kofan nan amaryan Abdulsamad ne ta iso badai samad bakan don mata daya gare shi Nafisa.
Kun makara don dan zaki ya girma inji wata daga cikin yan kawo ni yau komai tsiyan ku komai kishin ki sai amarya ta shiga gidan nan sai dai ku mutu da bakin ciki.
Yan takife sun so abarsu su haura su bude mommy tace idan kun shiga baku san su nawa bane a ciki don haka kuyi hakkuri maigidan ya taho.
Sai ga yusuf yazo yana zuwa ya shiga dukan kofan da karfin tsiya amma basu bude ba wani layi ya kira sai ga wani mutum ya iso ya balle kofan ta baya.
Mu dai muna daga gefe muna kallon su anata hayaniya a gurin har aka bude kofan gidan matan dake ciki gasu tsaye cirko cirko daga ciki Yusuf ya wagale kofan gidan gaba dayan shi.
Wata daga cikin yan uwa ta sakai gida ta debo ruwa daga cikin gidan a sabon butan da suka riko suka bita da kallo takawo inda nake tsaye tace in fito inyi alwala da shi.
Nafisa ta fito da tana fadin malam ko kamanta nan din ba gidan ka bane da zaka sa a balle muna kofa haka ka barmu sake macucin banza mayaudari.
Ina idar da alwalan motar AA tana isowa gurin ya sa kai ya shiga haraban gidan a hasale Yusuf ne dashi ganin mun tsaya cirko cirko suka zo suna ba yan uwa na hakkuri.
Mama Tani tace ai gara su mai dani gida don tun yanzu sun gane kalar macen dake gidan shi bazasu iya wucewa su barni gidan ba.
Ganin kamar mama da gaske take maganan ta yasa suka fara bata hakkuri mommy tace su mama suyi hakkuri haka auren da zaiyi albarka ya gada wani lokaci sai anyi rigima aure ke zama aure.
Tacei ba komai alwala muka tsaya amaryan ka tayi yanzun zamu shigo da ita lokacin su mommy sun sa kai shiga cikin gidan duk kunya ya rufe su na abinda ya faru.
Gwagona da mama Tani ne a gefe na sun riko min hannu muna tafe suna fada min abinda zan karanta gap da kofan shiga muka ja muka tsaya mama ta rada min in fara kallon barin dama in yi auzubillahi mina shaitanin rajin sau uku hakama barin hagu na.
Sai in shiga gidan da sunayen Allah ko kulhuwallahu a bakina da yarda Allah duk wani abin ki zai kauce min alheri zai tare ni a ciki insha Allahu.
Wanan abinda suke min yasa hankalin su Nafisa ya tashi sosai muna shiga muka samu sun kai su goma sha a cikin gidan .
Gudan da yan uwana suka shigo dashine ya kara firgita Nafisa din ga bakin labarin da ake bata wai ba a shigo dani gidan ba sai da nayi alwala kuma ana tafiya ana tsayawa dani kenan mun san dai abinda muka taka mukazo mata dashi gidan.
Gefen da aka bani anty Fauziya kaunan shi tayi muna iso zuwa can ina rike a hannun mama tani har wanan lokacin a daidai bakin kofan shiga part din suka tsayar dani a gurin addu,oin kariya da fatan samun alheri sukai ta karantawa duk wanda ke gidan zai iya jiyo muryan mai karatun.
Wannan abin yayi matukar kara ta da hankalin Nafisa da mukarabanta sai fadin suke yi wani sabon sallo sai da wata mai dan sauran imani daga cikin hamshakan matan dake zaune tace sun fimu dubura duk suka kallo ta.
Tace Allah da manzon sa suna son masu koyi da abinda Annabi ya kowa yar damu daga cikin addinin shi wanan karatun da suke da alwalan da aka ce tayi ku baku fahinci manufan su ba har yanzu sun mayar da hankali suna sauraren ta.
Tace wallahi wallahi wanan abin da sukayi ko sarkin aljannu yau muka dauko muka aje a gidan nan yana muna tsafi komai da mukayi ya karye don dawuya duk abinda akayi yai tasiri akan yarinyar nan.
Nufawan nan fa shegun mutune ne sun san addini kamar tsiya yanzu kin ga sun samu lincage din mu shi yasa suka shigo muna da shirin su suma.
Ki dubi idon su duk a bude yake babu wace bata san abin da takeyi ba suma daga cikin su akwai aiki babba gare ku don dai ni na hango hakan.
Kafin ta rufe baki suka shiga fadin magana kowa da abin da yake fadi dakin jikin nafisa yayi sanyi ta fara fadin Samad ya cuce ni wallahi da bai fada min tun farko in shirya ba.
Tana son sake layi madam ta tare ta tana fadin babu komai wallahi koda Alhaji malam zasu kawo ta mun fisu sheri damu suke wasan ba zasu wuce su barta anan bane tare da mu suyi suga su tafi.
Fasawa za,ayi kome yadda ta shigo haka zata koma don ba gidan zaman ta bane nan gidan Nafisa da mijin ta ne ita kadai.
Ihu suka sa suna fadin sai madam mun sanki mun san sherin ki balle an taba maki yar lele ai sai inda karfin ki yakare yanzu kan mun bata sati biyu ayi waje road da yar iska kishiya ko kaya.
Ana zaune kalau yaje ya jajibo muna wani wahala wai kishiya na tsani kalman kishiya balle kishiyan afili .
Wata tace kwadayin namiji dai ne idan ya motsa may zata kai Nafisa dashi kyau ko fari ko tsayi ko gashi nasan babu ko daya wallahi don haka kodon kyau ki dole a daga maki kafa.
Maganganu iri iri ke wanzuwa a cikin dakin tare da kara mata hudubun shegu da kara koya mata tugu da kisisina da kada ta daga min kafa ko na rana guda in samu wuri.

KHADIJA
Da fatiha na saka kai acikin dakin duk da idona yana a rufe bai hana in gane na shigo wani sabon rayuwa ba idona nakara lumshewa wasu hawayen bakin ciki suka ziyarci fuskana.
Ina jin mata na yaba kyan part din da tsaruwan shi wanda ni bashi ne a gabana ba yanzu duk da dai haka kowa ke fatan samu a rayuwan shi amma ni wanan abin da suke fadi tankar guba nake jin shi a raina.
Zaunar dani akayi a bakin gadon dakin mama Tani ce mai rada min komai a kunne sai yanzu na gane ma,anan abinda ake idan za, a kai amarya inga wata mace ta rike ta gap da gap ajikin ta ana magana kuskus da amaryan yau da yazo kaina na fahinci komai.
Sallolin da ake bin mu aka fara gabatarwa a gagauce sai ga su Fauziya da sauran yan uwan su na shigo muna da kulolin abinci lafiyayyu a part din.
Anci ansha aka shiga tsumi fadi akan Nafisa muna cikin uwar daki dani da maryam da wasu yan matan minna a saman gadon nidai sauraren hiran su nake ban magana komai da kowa abinda ya damay ni ya damay ni a raina.
Don ban san ta ina zan fara ba a gidan nan da Nafisa zan fara koda maigidan da yai min yankan baya .
Idan ina wanan tunanen sai huduban daddy na ya fado min a rai inji jikina yayi sanyi sosai don na shirya mashi rashin mutunci sosai a raina sai ga mahaifina ya aza min doka akan AA din.
Ido kawai nasa da kunne ina tsintar maganan yan uwa da suka kawo ni gamay da zaman gidan kowa sai fadan albarkacin bakin shi yake yi.
Part din da akace shine nawa ya ishe mu da yan uwa na sai bayan mun huta mun sauke gajiya ne mama Tani ta shigo tana fadin in shirya zasu kaini wurin uwar gida na mu gaisa a raina nace ashe akwaita kuma.
Ina zaune saman sabon salayana banyi niyar tashi maryam ne tace da mama su bari a gyara mi jiki tsab na fito bayan sun gama min feshe feshen tura da sauran su daganin shigana ba sai an fada ma gogagiyar yar boko bace ni muka nufi part din Nafisa din.
Tana tsakiyan aminanta suna ta tofin Allah tsine ga maigidan dani da yan uwan miji da nawa wata yar uwarta ne ta shigo da sauri tana fada masu gamunan tafe part din ta.
Nafisa ta mike zubur tana haki tana fadin may zasu zo suyi min a shiya ko an fada masu ni sa,ar yarsu ce da zasu wani kawo min ita nan suje can su karata da wanda ya kwaso ta gidan.
Su madam suka rike ta suna fadin haba haba Nafisa ki natsu mana ki kwantar da hankalin ki kiji damay suka zo wanan aladan haka akeyin shi ko ina akasan nan ba yau ne farau ba.
Kada idanun ki su rufe mana akan kishi ki manta da matsiyaci yanzu ki kwanta kiga takon ta tukunna.
Tana huci tana fadin dani zuwa zanyi in dakatar da yan iska da sauri sukace mata dako kin bada kan ki a wurin su may zai sa ki nuna kan ki gare su tun yanzu ai nuna masu kawai ke din ra kwarai ce.
Ki daure ki natsu su shigo muji abinda ya kawo su daga nan mu ga kalar tsiyan da ya dauko maku gaki duk kin kasa controling din kan ki kamar bake bace.
Ta dubi madan ta sauke ajiyan zuciya tana fadin nima ban san dalili ba wallahi sai dai ina mai tsananin jin kishin yarinyar da tsanar tane.
Don Allah manta da kishin nan ki natsu wuri daya da sun shigo su gane kwaruru ba tsaran wake bane kada ki yarda ki nuna komai a gaban su.
Ta zauna kamar mutumiyar kwarai taci jan shadda dinki su na yan Niger ga gwala gwalai a jikin ta suna sheki.
Da sallama muka shiga suna hada baki wurin amsawa muka shigo aka fara samun wuri ana zaunawa inda mama ta zaunar dani a saman wani kujera dake fuskantar inda suke zaune ita da madam.
Nan aka fara gaisuwa a tsakani sai madam tace ina kaunar tamu take ne daga ciki kawar mama tani ta nuna inda nake a kundundune tace a, a baza ki bude fuska muga fuskan kanwar tamu ba.
Anty Mairo ta ce to uwargida ga yar mu mun kawo maku amana kafin Anty mairo ta rufe baki wata daga cikin su tace ai ba a karban amanan kishiya Nafisa tace tayani gani kedai sai dai kowa ya zauna da halin shi.
Anty mairo tace

55 / 144

Chapters