ba sai ni inje maki manene amfanin zaman mu tare da ba zan iya maki komai ba.
Ai kawai ki daina damun kan ki mu za a gwadawa hanyar boka ko malam kuma ko latsandan ne gaba da lahira indai ana zuwa zamuje shi.
Sai lokacin Nafisa tayi ajiyan zuciya taji dadi a ranta tana ganin aduniya bata da kamar su madam dake tsaye a kan ta yanzu.
Tace uwar dakina Allah dai yaja muna nisan kwana tare ni nasan banda kamar ki a duniyan nan yanzu.
Da wanan shawaran hankalin Nafisa ya kwanta nan ta shiga buga waya gida Niger ko an samu wani bakon boka ko malami mai tashe a kasan.
Sai da ya ga komai ya kankama yadda yake so ya bar gidan bayan ya sallami mutanen da sukai mashi aiki duk da yawan samari yan uwan Nafisa a gidan ba wanda zaiyi bugun gaba dashi yayi mashi aiki alhalin biyansu yake duk wata dasunan aiki suke mai a gida.
Bayan kwana biyu su mommy sun gama shirin su tsab ya tura Yusuf ya dauko su zuwa garin Abujan mommy a gutin hajiya mama ta bar yaran ta tazo ita kadai sai iyan Bawa da suka zo tare da wata yar mai masu shara budurwa don taimaka masu da wani abin.
Mommy sunyi waya da Ya Amina tana sallaman ta tace zata gidan Abdulsamad wanda matar shi watan haihuwan ta ya kama zasu dan kwana biyu acan .
Ya Amina sai sulbul da baka tayi tace mommy ashe zaku hadu da Khadija na ke nan mummy tace banda abinki khadija dake makaranta ina zan ganta ni ?
Sai dai idan sawa zanyi a dauko min ita ko akaini in gano maki lafiyan ta idan na samu lokaci dariya kawai ta Amina tayi don ta san gidan su Abdulsamad basu san komai ba a tsakanin mu dashi.
Tafiyan rana sukayi don haka sai da yamma lis suka shigo garin Abuja din direct gidan shi suka nufa yana gida a lokacin don yana dakon zuwan su.
Nafisa wace ke falo tana shan iska ga yan uwanta a kewaye da ita kowa na shaanin gaban shi sai sallaman su mommy da su iyan bawa suka ji .
Gaban tane ya fadi da ganin su mommy din gidan don bata taba zaton zuwan su ba don a wautan Nafisa ta gama da kowa nashi yanzu babu mai marmarin zuwa inda yake.
Zuwan su mommy ba karamin faduwan gaba yasa ta ba sai take ganin ai zancen auren da take zato ko dawowan Fati gidan gaskiya ne.
Shiya fito daga daki bayan sunyi waya da Yusuf ya sheda mai sun iso ya fito da yar fara, a a fuskan shi yayin da ko kallo su mommy basu ishi Nafisa da yan uwanta dake falon ba .
Shi da kanshiyayi masu iso dakin da zasu sauka din bayan dun gaisa sun mashi yaya gida ya fito tare da Yusuf da ya shigo da kayan su ciki da taimakon wani saurayi.
Falon ya dawo inda suka samu Nafisa da yan uwanta sun juye harshe cikin yaren su na buzanci suna maganan zuwan su.
Fuska a daure ya kalle ta yace Nafisa baki san mommy bane da gwago na iyan bawa da baki tare su da zuwa ba ?
Tace a yatsune na san su mana ba matar mahaifin ka bane ita yace OK cikin wani irin kallo har ya fara tafiya sai ya juyo yace tunda kin san ta kin san kuma matar mahaifina ne baki iya taron su ba nima haka ban son in fita yanzu in dawo in samu wa yan nan yan uwan naki a gidan nan yanzu.
Yana fadar haka ya juya ya fara tafiya tace wallahi baka isa ba don zuwan su zakace yan uwana su bar maka gidan ka yanzu yace zaki san na isa idan yan sanda dun shigo sun fitar min dasu.
Idan akwai abin da yan Niger sukaki jini shine dan kakin Nigeria don basu yi masu da wasa idan sun farmake su.
Nan Yanyala ta fara magana tace haba Allaji ai bin baikai can ba daga dan wanan magana har zaikai ka kira muna polizawa kawai dai jira muke su huta mu mika masu gaisuwan mu.
Ya fice zuwa nemo ma su mommy abinda zasu ci a gidan don yasan ba zasu iya taba cin abincin da suka dafa ba.
Bai dauki lokaci ba ya dawo dauke da ledoji iri na restaurant dauke abinci dasu ruwa a ciki ya bayar aka shigo masu dashi har dakin.
Mommy ta idar da sallah sai ga yaron shi isyaka yana shigo da kayan ciki tare da gaba tar masu da abincin.
Sunka ce har da dawai niya zuwa sayo abinci kuma nan dai iyan bawa ta kasa hakkuri tace zainabu may kika fahinta ga wanan zaman ?
Murmushi mommy tayi tace ke dai iyan bawa ai ayi shani kawai wai ancuci na kauye wanan matar bata da hali ko kadan.
Kin dai fara ganin makasudin zuwan mu garin nan ke nan don fitar shi kunyan abokan shi nasan halin matar nan tashi dakilace na gani a fada.
Ba zamu sakar mata fuskan da zata kawo muna raini ko wulakanci ba don nasan tun zuwan mu batayi farin ciki da ganin mu ba.
Sunci abinci sun huta sai ga Nafisa ta shigo tayi wanka ta saka sutura a jikin ta yan uwan ta suna mara mata baya suka shigo dakin.
A falo suka samay su nan ta ja ta tsaya bata zauna ba tana fadin kunzo lafiya ya hanya da mutanen gida ?
Mommy tace lafiya duk suna gaida ku yaya nauyi Allah ya rabaku lafiya tace amin sauran suka shiga gaida su da yi masu ya hanya suka fice daga dakin ba wanda ya zauna.
Shiko bayan ya mika sakon wuri na ya nufa kamar yadda ya saba zuwa man koda ya kirani muna tare da maryam da zarah a dakina kiranshi ya shigo min.
Mutumin ki ne halan yazo maryam take tambayana nace cikin tabe baki shine ai kin san bai tashi zuwa min sai wanan lokaci.
Maryam tace ai kuna daidai dashi in kin isa ki fadi a gaban shi yana da amsan baki indai wanan yaya in love din kine.
Kai maryam kina da wuyan sha,ani wallahi na fada maki ba soyayya a tsakani na dashi sai amin taka kawai na damuwa.
Zarah ta dago kai tace min wani guy kuke magana muje in gani idan ya min in saka shi a layi mu shiga sha,ani dashi.
Zarah wai ke baki jin kunyan fadin fitsrane haka tace in banda abinki wake ta wani wasa da so yanzu khadija bari kiyi wasa da daman ki yanzu yan jami,an nan suyi maki wuf dashi.
Idan banda abinki an fada maki kowane yan matan jamia ke iya wuf dashi kai daya zarah wanan ya wuce sanin ki wallahi.
Dariya tayi tace muje inga guy din nan dai da kuke wani zuzutawa haka dai murmushi nayi kawai don ba zan so a ganni da ita ba.
Duk da ba wani shiga na yi ba amma suna ta yaba kyau da nayi wai na hadu zarah na fadin ashe zaki zama yar hannu haka khadija.
Tare muka fito dasu sun zo su gaida shi tunda muka tunkare shi zarah ta tsunke da ganin motar da yazo da ita tana fadin tun ban ga guy din ba wallahi nasan zai hadu ko don motar nan da nagani how lucky you are da kika iya canko wanan zukeken guy haka.
Mun iso yana ta faman ansa call a wayan shi sai da zarah ta kare mai kallo ta dago bayan ya gama wayan suna gaida shi bai wani sake fuska ba ya amsa gaisuwan.
Tare da kawar da kanshi gefe daya zarah tace dama na sani sai irin wanan guy din khadija wanan jan ajin naki yayi yawa wallahi har ta gama ta wuce bai yi magana ba suna shiga maryam ta nufi dakin ta.
Maganar shi ta farko bayan wucewar su shine ina kika samo wanan kawar kuma ?
Nace a inda ka gan mu yanzu yace No ba girman ki bane da mutuncin ki yawo da irin wayan nan nace kawatace fa tare mukazo karatu daga gida.
Na fada maki bana son in kara ganin ki tare da ita please na juyo ina kallon shi ido cikin ido nace tana da aibu ne komay ?
Au ke baki ga aibu ta ba wanan bata da kamun kai ba girman ki bane yawo da ita nace ka taba ganin mu a tare ne ko yanzu ma daurowa tayi ka gan mu da ita.
Har ya bude baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru nima shirun nayi ba wanda yayi magana daga cikin mu.
Can naji yace idan na fada maki wani abu zaki yarda dani ?
Zaki yarda gaskiya nake fadi.
Murmushi nayi nace idan maganar ta kama gaskiya mai zai hana nayarda tunda nasan gaskiya ka fada.
Kin yarda dani khadija ?
Nace na yarda dakai mana yaya Abdul fati da mijin buzuwa ina fadi ina mashi dariyan shakiyanci cikin gatse.
Shima murmishin ya dan yi wanda sai wanda ya sanshi zai iya fahintar hakan daga gare shi yace kin san kamun kan ki yasa muke tare da ke har wanan lokacin.
Kasan ni ne da zaka wani ce ina da kamun kai bayan iyakar mu dan wanan haduwan da muke yi.
Na tsinci muryan shi yana fadin niko na sanki khadija you are classic baby da na taba haduwa da ita a rayuwana.
Katse shi nayi da fadin may ke faruwa daksi haka ne wai ke irin wanan magana yanzu a kai na ko last zuwa da kayi haka ka dinga min wanan maganganun.
Ya girgiza min kai tare da fadin ba komai cikin lumshe idanuwa shi sai kuma ya bude su ya sani gaba yana kallo na.
Shirun motar na kawar da fadin yau ba fita ke nan yace ina kike son muje nace inda ka saba zuwa mana mu zaga gari kawai kana barnan man motar ka.
Haka kika dauki fitan namu dama nace hakane mana tunda ba wani guri muke zuwa ba.
Ke ce baki fahinci muhinmancin fitar namu ba kila amma ni yana da ma,ana masu yawa a gare ni matuka khadija.
Don kasan cewan mu a tare you have change me now na fahinci su abubuwa da dama da ban taba fuskantar su ba a baya.
Maganan gaskiya yau kin dawo min da farin ciki rayuwana har iyayyena sun zo gida da sunan kwana biyu a wuri na.
Da sauri nace cikin murna wai da gaske kake yi yace kwarai kuwa deeda don yanzu haka mommy da gwagona iyan bawa na gida maganan nan da muke yi dake.
Taya kike ganin bazan maki godiya a wanan kangin da nake ganin kin fitar dani wanda a da nake dauka da shirmay irin naki na yara kike yi.
Sun kuyar da kai nayi kasa ina tunane hankalina yayi nisa bani jin abinda yake fadi tsoro na daya ne kada mommy tasan ina tare dashi ta fasara haduwan mu a wata manufa.
Ban sauri maganan shi ba na katse shi da fadin zan roke don Allah kada ka bari mommy tasan kana zuwa inda nake don bansan da wani ido zan kallesu ba har hajiyan ka.
Ya lura da irin rudewan da na shiga sai dai baice min komai ba ganin bai yi magana ba yasa nace please yaya Abdulsamad ka boye wanan a matsayin siri a tsakanin mu don Allah.
Kallo na yayi ya sauke murmushi yace saboda may kike son kada su san ina tare dake nace dashi wayyo Allah kana son su dauke ni yar cin amana ne ko may ?
Cikin sanyi murya nace kasan su ba zasu gane mutunci ke tsakanin mu ba sai su dauka muna tare da wani manufan da bashi ba.
Hakan kuma yana nufi na ci amanan su ke nan gama yadda suke son Fatin ka a gidan yanzu kuma sai su gan mu tare yaya kake ganin zasu dauki abin.
Kai tsaye yace zasufi kowa farin cikin da hakan na sani tunda sun san ki sun san halin ki zasu yi farin ciki da hakan.
Daga yau magana ya kare ba sauran wani abu a tsakanin mu tunda bukatar mu ya biya ka shirya tsakanin ka da yan uwan ka.
Mamaki magana na ya bashi yace juyo yana kallo na sai can yace ai deal namu bai kare ba tukun ko kin manta baki karasa aikin ki ba akan fati ?
Na amsa da fafin kwarai bamu kai nan ba cikin takaici nace wana kuma yanzu ya rage gare ka sai kasan yadda ka shirya da matarka.
Ba wani sauran magana yanzu a tsakanin mu kuma na fada cikin tsiwa ya juyo da kyau ya kalle ni yace don mommy tazo duk kike fadan wanan magana ko may.
No ba don tazo ba in ma don tazo din ne haka ne bana son su dauki abinda wani fassarane kawai.
Ya zura min idon sa yana kallin yadda duk na rude yace a ranshi ashe karyan rashi kunya nakeyi a da gashi yanzu daga jin mommy tazo duk na bi na birkice lokaci daya.
Motar tayi tsit kowa da abinda yake tunane a ran shi sai da ya shafa kan shi naji yace relax deeda wace dake mommy zata san da wanan maganan dake tsakani mu wai ?
Wata zuciyane ta bashi shawaran ya min wayau kawai don yadda na rikece din nan daga jin mommy tazo zai iya sa komai ya faru idan ya biye min.
Kawar da zancen yayi da fadin zuwa nayi ki ban shawara yaya zan yi da Nafisa don batai farin ciki da zuwan nasu ba yanzu haka.
Da sauri na dago kai na kalle shi da idona da suka sauya kala nace baka fada mata zancen zuwan su bane dama , ?
Kai ya girgiza min yace ban fada mata zasu zo ba tunda ba itace ta aje ni ba yan uwan ta dake zuwa ai ba fada min take yi ba itama.
Kada kaga laifinta a yanzu don kai kai sake har haka ya kasance tun farko saboda tsoron ta da kake nuna kanayi da farko.
Ba tsoran ta nake yi ba deeda kaunane kawai na tsakanin miji da mata wanda ita ta dauka tsoron tane yasa nake mata hakan.
Sai yanzun kasan da wanan yana iya faruwa ka manta a lokacin da take saka abu kana mata shi koda kuwa baka son abin ?
Ya gyara zama yana fadin shine babban kuskure dana tabka a farko wanda nake nadaman yi shi a yanzu haka.
Duk abinda zakayi ko zatayi kada ka bari rainin matarka yakai ga iyayyen ka don ko zaka iya canza mata amma ba zamu iya canza iyayye ba.
Wai ke wake koya maki wanan hikimar haka nr ya tambaya cikin son in bashi amsa nace baka son maganan ke nan.
Yace No idan ban so ai ba zan fada maki zuciyana na ba a yanzu don da zuwan su abinda tayi masu yaci min rai sosai ba zan boye maki ba don yanzu ke ce abokiyar shawarata shiyasa nazo maki da zancen.
Yaya zanyi khadija ina son in fita daga cikin dana shiga a bayane gida na yanzu bana son su mommy su fahinci sakaci na a gida na.
Nace na yaushe kuma saidai kada a kara muma makwabta ku mun sanni balle su mommy dake gidan tare ku.
Ina son mata na khadija shiyasa har haka ya faru da ni kallon shi nake cikin mamakin kalamin shi na wai yana son matan shi da yace.
Shin shi wani iriin mutum ne wai nace nafisa dai kake so amma baka son fati kowa ma yasan da hakan ?
Haka kuke tunane ya fadi cikin zafin zuciya amma ita ai tasan ina sonta halin ta ne kawai baizo daya da nawa ba shine matsalan mu.
Kalon shi nake sororo kamar na samu tv da alama yarasa yaya zaiyi da damywar shi ne ya tsinci kanshi cikin fada min sirin zuciyar a matsayi shi na mutum mai shekaru kamar shi.
Tausayi ya bani don na fuskanci bayan Yusuf da suke tare baida wani wanda zai fada ma zuciyan shi ya fahince shi shiyasa yazo gare ni.
Nace wallahi rayuwan ka na cikin hadari ya kamata ka koma ga Allah kayi abinda Allah yace shine kawai mafita a gare ka.
Lokaci ya duba yace zai tafi lokacin sallah ya gabato zai dawo gobe tunda ba school mu karasa tataunawa mukai sallama ya tafi ya barni cike da tausayi shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tunda ya je office ya kasa aiwata komai a office din ga Yusuf bai shigo ba har lokacin ranshi ke kara baci idan ya tuna da kalaman nan daya dana fada shi yafi bata mashi rai ko yaushe.
Shigowan Yusuf office din tun daga nesa