take kwana don tasan duk wani gajiya anriga da an sauke ma yar uwarta shi sai dai ta samu ragowa saura.
Mai maganin ne tace balle wanan abinda na baki yanzu ai sai dai ta sha takaici koda ya koma a wurin ta don haka zai jita salaf kamar miyar da ba maggi a cikin sa.
Shewa suka dauka tace nasan tana can yanzu ta tasahi a gaba kamar hoto don babu abinda zai iya tsinanawa yar banza.
Madam tace yarinyar nan tana da dan banzan wayo shiyasa ake gudin auro mace mai ilimin da ta dara ka don komai wayon ka sai ta dan munafince ka gun miji.
Haka nake karantowa gun wanan yarinyar don wanan tarkon da muka dana mata na zancen cikin jikin ki ban dauka zata tare shi da mutunci ba har tana fada akan shi.
Kyale yan iska dani suke zancen komai jarabansu sai dai sukali juna kamar photo don ko hannun ta ba zai rikaba in tace naci ta iya yaya muka kwashe da fati a baya.
Wani irin dariya suka sa sun dade suna tataunawa kafin ta mike tace zata gida taga rawan kan yar iska don sai haka din a tsakanin su.
Har waje mota madam ta rakota tana kara mata bayanin yadda zatayi da maganin da ta karba din tare da fadin sai mun sha labari da safe mutumiyar.
Ta iso gida a gajiye a falo ta zube nan yaranta suka rufa mata suna tambayan ta abinda da ta sayo masu tace ba ta tsaya ba sun rufa ta suna lalaban jakarta inda suka ga babu komai a cikin jakar sai ledan maganin da ta shigo dashi.
Yanyala da su Samiha suka fito daga dakunan su suna gaida ita da dawowa bayan ta gaisa sun zauna take tambayan su samad ya fita ne ko yana gun yar iskan nan har yanzu.
Yanyala take cewa da ita ina ganin baya gidan nan fa don tun safe banji duriyan shi a gidan nan ba tace nasan ai ba zai zauna yasha takaicin yar iska ba tunda ta hana shi ya wala inda yake so.
Hira suke tayi a gurin har akai kiran sallah azahar basu mike ba don sallah dama baya damay su bane.
KHADIJA
Can cikin barci nake jin agogon dakin na nuna alaman biyu tayi tashi nayi a wahalce ina kallon yadda muke kwance dashi .
Duk rabin jikina yana manne da nashi kokarin zare jikina nake a cikin nashi ya bude idanun shi tare da sauke su a kaina kawar da kai nayi gefe ina fadin lokacin sallah yayi fa.
Har lokaci yayi ya fada yana kokarin kallon agogon dake dakin yace shiga ki fara alwala sai kin fito zan shiga.
Adakina zanje inyi na bashi amsa ina kokarin sauka a gadon yace bari ki dan kara gasa kanki anan kada ki fita kina wanan tatatan ana kallon ki.
Mikewa nayi na sauka daga saman gadon na nufi bandakin don shawaran kwarai ya bani nayi kamar yadda yace na fito na samay a zaune yana dakon fitowa na tare da fadin akwai hijjab a wardrobe dina ki duba ya fada yana mikewa daga saman gadon.
Kallon mamaki nake mashi yace kina mamakin hakane na tanadar maku shine don gudun hakan gashi kuma yai muna amfani ko ya fadi yana wani kashe min ido.
Shima shiga yayi ya dauro alwala ya samu har na tayar da sallah ina nafila ina idarwa ya jamu sallah .
Mun idar muna addua sai da ya shafa naji muryan shi yana fadin Deedar ban san godiyan da zan maki ba ga wanan tanadin da kikai min wanda na amsa a gurin ki yau.
Fatana Allah ya bamu zama lafiya a tsakanin tare da samun zuri,a masu albarka da fahintar juna a cikin raina na amsa da amin.
Deedar nasan kinyi hakkuri dani wanda ba kowa ce mace ne zata iya irin abinda kikai min ba batare da anji tsakanin mu ba.
Ina son ki kasance da wanan hali naki na hakkuri da rikon amna ki bani hankalin ki don yanzu lokaci yayi da zamu fahinci juna dani dake .
Deedar kin fi kowa sanin ina son ki don da ban son ki ba zan kawo ki gidana mu zauna tare ba duk da kalubalin da nasan zan samu a gurin ku.
Ina son ki sani ni ba mutum bane mai son yawan hayaniya amma sai Allah ya hadani da mata masu son rashin zaman lafiya a gida.
Zanso ace kin san ko waye Nafisa yanzu da yan uwanta dake gidan nan wanda kulun a cikin kwaso min su take sai dai idan bataje garin su ba.
Don Allah kiyi hakkuri ki yaki zuciyar ki ki kawar da idon ki akan alamuran su ki dan bani lokaci har zuwa lokacin da na gama shirina akan su.
Ya kare da fadin ina fatan kin fahinci may nake nufi da magana na kai na gyada mai tare da fadin insha Allahu zaka samay ni mai biyayya ga abinda ka umurce ni dayi matukar ba shiga harkans sukayi ba wanan kan ban maka alkawarin shi ba don zan maida martani akan hakan.
Yace wanan kina da daman yin hakan mudin kina da gaskiya akan maganan nima a shirye nake da daukan mataki akan hakan.
Dan shiru ne ya biyo baya ya gyara zama yana fadin yunwa nake ji zan dan fita na samo muna abinda zamuci don kin sa ni yau cin abinci sau biyu a wuni.
Hararan shi nayi ina fadin nasan maryam zata girka muna abinci tunda taga ban fito ba har wanan lokacin.
Kai maryam tana da kirki sosai wallahi tun farko na karance ta da tana da matsala da tuni na rabaki da ita ai ba kamar waccan kawar taki da na taba gani ba yar garin ku.
Mikewa nayi ina gyara dankwali dake saman gado ina kokarin daurawa a kaina nace ni zan sauka sai ka fito.
Yace kibi a hankali don kin san idon kowa yanzu a kan ki yake kamar in ce dashi kai kuma kana tsoron hakan ne sai dai na wuce ba tare da nayi mai magana ba ina tunane a raina.
Ba dama mutane su sake a gidan ke nan mutum yayi abinda yake so sai idon jamma,a ya sauka a kan shi kamar gidan haya.
Karan bude kofan danayi ne ya jawo hankali su a falon suka bi hanyar stairs din da ido a hankali nake saukowa daga saman yayin da idanuwan su yake a kaina.
Fuskana ya nuna daga barci na tashi a lokacin har na sauko basu dauke idanuwan su a kaina ba tare da kallon yanayi na.
Ban kula su ba nazo na wuce su tsuki naji aje tare da jin muryan nafisa na yare da yan uwan ta banji may take fadi ba don ba yaren nake ji ba nasu.
Na dai ga ta mike a fusace ta nufi saman ban tsaya ta kanta ba na shige part dina inda na jishi a rufe gam kwakwasawa na tsaya yi abinda ya dan dakatar dani a wurin ke nan na dan wani lokaci kafin maryam ta bude kofan.
Tambaya ta tsaya yi nace don Allah bude nice matsoraciya ta bude tana dariya na shige ta mayar da kofan ta rufe.
Wani kallo take min ban tsaya ta kanta ba na fada kan doguwar kujeran dake falon ina fadin maryam kin cuce ni yau wallahi.
Dariya ta koma sakewa tare da guda tana fadin amarya ta ango yar shagali yar biyan bukata yar garali makulin mota ke aka ba harara na aika mata tare da fadin.
Idan ba a bani makulin mota ba ai an bani na wahala daga haka na mayar da kaina saman kujera tare da kara hannuna saman fuskana.
Don wani yanayi nake ji na zazzabi nason kamani a lokacin in kawo maki abinci kici ne kai na girgiza mata tare da fadin banjin cin komai yanzu wallahi.
Shidai yace yana jin yunwa yanzu zai sauko yazo yaci yace daga haka na rufe idona dan ban son yawan magana a lokacin.
Zama tayi tana fuskanta tare da fadin wallahi yau kun burgeni sosai wallahi ko ba komai mun nuna ma buzuwa karya take wallahi.
Allah ya fita yafi sherin ta sai dai taji a salansa yanzu kan shetin ta ya kare a gidan nan wallahi daga yau kun zama daidai da kowa a gidan nan abinda bata so ya faru ko.
Tana magana bance da ita kanzil ba jin nayi shiru ne ta fahinci ina cikin wani yanayi wasa wasa ko zazzabine mai karfi ya rufe ni a gurin.
Kamani tayi zuwa ciki ta rufa min wani bargo tare da tambayana maganin da zansha tasan ban son magani haka kuma allura don haka nake ciwo na idan ya tashi a wahalce.
NAFISA
Wani irin bugun zuciya take ji a ranta har ta isa dakin nashi ta tura kofan da karfi ta shiga don tabbatar da abinda take zargi da idon ta ya ganan mata.
Yarinyar nan wai may take nufi danine a gidan nan duk da hanasun da nayi sakewa sai ta iza min bakin ciki take nufi ko may wallahi bata isa ta walla a gidan nan ba yadda take so.
Jin yadda aka turo kofan yasa shi juyowa da sauri yana kallon kofan yaga mai shigowa don bai tunanen nice na dawo a lokacin.
Ganin ta yasa ya daure fuskan shi don yasan abinda ya kawo ta ba alheri bane bai wuce taga fitowa na daga dakin ne tazo masifa.
Idon ta a saman gado ya sauka ta ga yadda gadon yake sequzing ya nuna alaman wani abu ya faru saukin abin ma data gani mun canza zanin gadon kafin mu kwanta don sai dana matsa mashi ya yarda na sauya tare da taimakon shi.
Samad samad mai idona ke shirin gani ta fadi tana karasowa a cikin dakin cikin wani irin yanayi na da bata san inda kanta yake mata ba.
Samad dama kana dakin nan tare da wanan shegiyar yarinyar a gidan nan ban sani ba may idona ke son nuna min ne wai ?
Yace abinda idon ki ya nuna maki haka ba matana bace matar wani ne kikaga na kebe da ita komay ?
May kake nufi da maganar ka yace yadda kika dauke shi kinga ban son wanan shirmay naki idan shi ya kawo ki ki bace ki bani guri hutu nake so yanzu.
Ido waje take kallon shi tare da fadin watau hutu ma kake so yanzu may kaiwa yarinyar nan yanzu da rana tsaka yace may ake dake idan kin shigo.
Bata bari ya kare maganan shi ba ta saki wani ihu tare da fadin karya kake wallahi ka fada min don ban fahince ka ba.
Yace may kuma kike son in fada maki uwata banda wanda kika ce idon ki ya gane maki kuma na fada maki hakane.
Ya juya yana son daukan wayan shi shaka yaji takai mashi tana fadin wallahi karyane baku isa kuyi komai ba a gidan nan.
Juyowa yayi a hasale tare da kwashe ta da mari yana fadin kina da hankali kuwa ni zaki rikewa riga ta baya haka duk iskancin ki na fada maki ya daina zuwa a jikina don zan saba maki.
Wallahi baka isa ba daga kai har ita wallahi ita takai wata mace ce da zakace wai ka huta da itane har kana bukatan hutu yanzu.
Ta kara yowa cikin shi ya kawaice wa rikon da tayo mashi tare da fadin idan kika taba again zan saba maki a gidan nan.
Wallahi sai ka fada min dan iska mayaudari azzalumi watau gani sakarai ashe kana ciki kun kule da ita uwar wa zaka nema a gurin ta.
Shine manufar ku na yi min wayau kuce in zabi guda ashe kasan sharin da kuka kulla da ita muna fuka yau zamu hadu a gidan nan ko ni ko ku wallahi .
Har ina macen da za a huta da ita a gurin nan mace haka da fari kamar zabaya yace ashe kin san tana da farin bari kiji idan kika kuskura kika taba yarinyar nan yau a gidan nan raki zai matukar baci wallahi.
Kamar kada ya fadi haka ta juya a sukwane ta nufi dakina sai dai kafin ta sauka ya riko ta ta baya yana dakatar da ita.
Fisgewa take yi tana fadin wallahi yau sai naci uban ta a gidan nan ita har ta isa ta kebe dakai cikin wanan yanayin ta bata min rai.
Ko kuwa ne ya kaure a tsakanin su sosai har ya jawo hankalin su yanyala a garesu suka mike da yare suke mata magana akan ta sake shi.
Yanyala ta hadashi da Allah ya kyale ta ya sake ta yana huci yana batun komawa dakin shi yaga ta nufi part dina a sukwane ya bi bayan ta.
Ina kwance a daki hayaniyar su ne ya falkal dani daga barcin wahalan dana dan samu din maryam ma hakali a tashe take kallona daga inda take a zaune gefe na tana charting.
Ina ganin fitina suke akan ki fa khadija nace kyalesu suci kan su ni ba abinda ya damay ni da shirmay su ta kaina nake yanzu na kara jan bargo na rufe kaina dashi tare da lumshe idanuwa na.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
KU SAKANI GA ADDU,AN KU A DAREN YAU DON ALLAH YAN UWA MUSULMAI.
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tun ina jiyo hayaniyar su sama sama bandai fita ba har wani barci ya kara daukana na dade ina barcin a dakina.
Kwance ya samay ni rijib a cikin bargo na rufe har zuwa kaina sai kaduwan dari da nake yi.
Muryan shi ne ya tayar dani a cikin barci yana fadin subbuhanallahi tun yaushe take haka maryam na bashi amsa tana fadin tun shigowanta dakin nan take kwance.
Tambayar maryam din ya sakeyi da dama bata da lafiya ne ko may tace gaskiya yau daine ta tashi da wanan zazzabin haka amma lafiya lau muka tashi.
Ji nayi yana taba min goshina har zuwa jikina da nake ji kamar garwashin wuta a lokacin ga wani irin sanyi dake damu na.
Tallaboni yayi ina tashi da kyat saboda ciwon da jikina ke yi, idanuwa na sun kada sunyi jawur dasu .
Wayan shi ya lalubu yana kiran Yusuf tare da fada mashi yazo su kaini asibiti banda lafiya sosai Yusuf din yace subbahanallahi da sauki dai ko yace da sauki ka dai zo yanzu.
Ba, a dauki lokaci ba Yusuf ya iso har lokacin yana dakin zaune bakin gadona ya tsura min ido sai tunane yake a zuciyan shi.
A hankali ya lumshe idanuwan shi ya fara tunanen abinda ya faru a tsakani mu ya san ba banza Allah ya dora mashi sona a ranshi ba.
Don yarinyar tana da wani baiwa da Allah yai mata ta zai amfana daga gare ta ya kara bude idon shi ya sauke su a gare ni ina kwancen ban san inda nake ba nikan a lokacin.
Wani shu,umin murmushi ya sake yana godiya ga Allah da ya mallaka mashi ni a wanan ranan ta jumma,a yana godiya ga Allah tare da fatan samun zuri,a masu albarka daga gareni.
Karan wayan shi ne ya katse shi Yusuf ne ke kiran shi yana fada mashi isowan shi tashi yayi da sauri ya fita falon maryam na zaune yace ta gyara min jiki muje asibiti.
Suna zaune a falo da tawaganta madam na tsakiyar su tana bata magana duka ga fitowan mu daga dakin yana tallabe dani a jikin shi.
Ido suka zuba min madam ne cikin kisa tana ganin mu take fadin lafiya kuwa yallabai samad yace bata da lafiya ne zamu asibiti ne da ita daga haka muka fice daga gidan.
Kallon Nafisa tayi tana fadin baga irin ta nan ba ashe ma ko lafiya yarinyar bata dashi shiyasa suka shige daki yana jinyar ta.
Ke ko da baki da fahinta kishi ya rufe maki ido kina naki haukan kishi haukane wai Nafisa ke bazaki bar abin kunya ba kullun danbe da miji akan kishiya.
Yanzu don Allah duba ashe wace kikewa haukan ma ba lafiya ne gare ta ba baki tsaya kin bin cika ba kin hau fadan hauka..
Ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin wallahi madam ban san abin haka yake ba wallahi don idona ne ya rufe a lokacin.
Ta ja tsuki tare da fadin yanzu ai sai ki san yadda zakiyi ki gyara don kin ji irin hukuncin da ya yanke akan ki da yan uwan ki gyara ya saura gare ki.
Don dole ranshi ya baci kina mashi zargin abinda ba shine ba.
Da wani kike son yaji don kinsan dama yana cike da haushin rashin samun matar shi da baya yi sai suka sa dariya harda tabawa.
Yanzu hanya guda ne ya zama dole gareki ki kwanta mashi ki nuna kin sauko sosai kinyi nadama idan sun dawo yana dakin kije ki gaida ita in ma da hali ki yafe mata shi na yau tunda kin san ba komai ne zai wakana a tsakanin