karfe bakwai yake jin yanayin yana ziyar tanshi.
Hakan bai sa ya kawo komai a zuciyar shi ba sai dai abin ya dan damay shi a cikin ranshi haka ya kare min wuni na a dadafe.
Haka yaci gaba da wakana a tsakanin mu saidai baiga damuwan hakan dake faruwa dashi a fuskana ba don haka ya dan rage damuwan shi.
Don ni ko kadan abin bai damay ni ba ban kuma daukeshi wani abuba rawan kan da take tana wani hura hanci ita a dole ga mai miji haka zai wuni bai shigo part dina ba.
Batasan ni mijin bai damay ni ba don da ina son shi a lokacin duk wani rawan kanta bai razana ni shiko idan ya dan samu ya shigo ya fara dan kame kame irin na mazan da basu da gaskiya.
Ya samu Yusuf da ya dawo daga tafiya da zancen tun shigowan shi wurin AA di yana mashi ba,a yaga ya koma so silent wuri Yusuf din ya samu ya zauna.
Yana tambayan shi may ke faruwa ne ko sun fara caza maka kaine a gidan gaka ka fada a lokaci guda.
Dan murmushi yasake tare da girgiza kan shi yana fadin ba wanan ba Yusuf wani bakon yana ne ke ziyarta na kusan wanda nake ji a baya idan ina tare da Fati sai dai wanan akwai banbaci sosai dana bayan.
Don da zaran ina dakin khadija akace bakwai na yamma yayi zan wuni lafiya kamar bani na amma da zaran bakwai yayi sai in fara shiga cikin wanan bakon yanayin nawa.
Zan din gajin jikina yana sake min sai in koma tankar mace ga wani mugun sanyi da kaduwa da zan kwana dashi bani zan samu kaina sai gari ya waye watarana kai in gajarce maka a haka zan wuni da wanan yanayin a jikina.
Kai kawai Yusuf ke iya kada mashi yana sauraren bayanin da yake mashi din sai da yakai karshen maganan shi Yusuf yace wanan magana fa kada ya zamo gaskiya.
Da sauri AA yace wani magana ke nan kake nufi zai tabbata yace yanzu dai ba wanan ba neman mafita ne a gaban mu don wanan ba karamin magana ba da za,ayi wasa dashi.
Ita khadijan ta fahinci hakan ne ko may yace ban dauka ta fahinta ba don kasan har yanzu ba wai ta sake bane irin haka.
Zaka iya barin garin nan na wani dan lokaci tare da khadijan kamar yadda mukayi akan Fati ta daga daga garin nan ita ma.
Kai ya girgiza ma Yusuf din yana fadin kasan haka ba zai samu agare ni ba yanzu naso sai zuwa next week ko upper week mu leka kaduna mu gaida su su gane ta taga yan uwa.
Yace ya zama dole ku dan daga ma garin nan muga abinda hali zaiyi daga can mu shiga neman magani akan wanan matsala don zai yuyu abinda nake hasashe bashi bane ko shi din ne.
Yanzun ba zamu iya gane hakan ba sai kun dan daga ma garin nan na wani lokaci zamu san abin yi akai.
Ina kwance a falon dakina karatu nake barci ya dauke ni a gurin yadda ya samay ni shiya kara kidima shi yazo dap inda nake kwance yayi min kallon tsab yau ba inda bai kalla ba a jikina sai inda yake rufe a cikin rigana kallon shi ya tsaya cak akan kirji na da ya dan taso ya tsaya cak da sauri ya mayar da idon shi a fuskana.
Da sauri ya juya zai bar falon nawa yaji na motsa ya juyo yana fadin na shigo na samu kina barci ki tashi ki shirya yau zamu shiga kaduna.
Mamaki ne yakamani ba wani shiri ace wai tafiya da rana tsaka ba kai aure ma dai matsala ce wallahi don banda yadda zanyi dole in bi umurnin shi a hakan.
Ya fara tafiya ya juyo yana fadin ba wasu kaya masu yawa zaki dauka ba don bai wuce muyi kwana uku ba mu juyo ban iya bashi amsa ba don raina ya baci.
Kaya kala ukun dayace na dauka sai wanda na saka ajikina ya cika hudu koda muka fito Nafisa bata gidan don haka ko sallama ban samu yi da ita ba .
Yusuf yana zaune a gaban motar da zamu shiga yana jiran fitowan mu har lokacin cin bacin rai nake fuskana ba wani walwala a tare dani gaida shi kawai nayi na shiga motar.
Tunda muka fara tafiya su kadai ke firan su a motar hankalina yana a wayana da nake duba tafiya naga saurin shi don ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba sai gamu garin kaduna.
Lokacin magariba ya gabato sosai muna shiga layin su daidai get din gidan ya Amina ko kallon wurin basuyi ba suka nausa shiga cikin unguwar kai tsaye.
Babu abinda ke raina sai irin tarban da zan samu gun anty Fati ga nauyi da kunyan ta da nake ji a raina na yadda zan hada ido da ita a matsayin kishiyar ta a yanzu.
A hankali na furta da kun sauke ni gidan ya Amina in sauka a nan nace dasu ko kallona ba wanda yayi daga cikin su sai da Yusuf yake karya kwanan shiga get din gidan yace min yanzun ai kanwa ta ke da gidan antyn ki sai dai ziyara kuma.
Wani iri naji a raina don ni gaskiya an dai takura ma rayuwa na don ban taba kawo haka a rayuwa na ba a yanzu.
Bayan motar ta tsaya ban fito ba muryan AA naji yana fadin ki fito mana ko dadin motar ne bai isheki ba a baki key ki koma abuja a yau.
Sai da Yusuf ya fita ya zagayo ya bude min gefen da nake zaune yana fadin kaga aboki na kada kai mata laifi kuma ka koma zolayan ta yanzu.
AA yace nidakai wa yafi laifi a gare ta yanzu yanzun nan fa ta gama tambayan ka ka sauke ta gidan antyn ta kaki.
Banyi magana ba sai fitar da kafa na daya da nayi waje bakina yana dauke da addua na dauko hand bag dina na fito daga cikin motar.
Tsaya wa nayi daga gefen da nake ina kallon su Yusuf ne yace bissimillah mana khadija mu shiga welcome to yaur house ki saki jikin ki don gida kika zo.
A hankali na fara takawa ina gyara mayafin kaina sai kuma na ja na tsaya guri daya sai da suka karaso driver dayan motan ya fara shiga da kayan cikin gidan na bisu a baya.
Falon muka shiga babu kowa a cikin sa shiya hau sama inda dakunan kwanan su yake ya shige ya bar mu a gurin.
Labara ne ta fito daga kitchen tana muna sannu da zuwa tana ganina tace ashe da amarya ake tafe sannun ku da zuwa ga wuri ki zauna.
Taron da matar tayi min yasa na dan fara sakin zuciya na saura na matan gidan mu gani yadda zata tare ni can sai gata tana saukowa daga saman fuskan ta babu yabo ba fallasa a cikin sa.
Itama sannu da zuwa take muna na dan duka ina gaida ita vikin mutunci a daidai lokacin ya sauko daga saman yana fadin ku basu ruwa mana.
Cikin muryan ta mai kamar taka da basarwa tace laraba kawo masu ruwa don Allah ta kai zaune tana fadin ashe tare kuke tafe.
Na dan dago kaina a kunyace nace eh anty mun samay ku lafiya ta wani ya motse fuska tana maida kanta bayan kujeran da ta zauna take fadin wallahi lafiya.
Goran ruwan da laraba ta dire a gaban mu Yusuf ya dauki dayas ya balle ya kafa bakin shi ba tare daya zuba a cup ba.
Yana gamawa yace zan tafi gida yanzu don su san nazo ya dago yana fadin kanwata ahuta gajiya ko ?
Dan murmushi nayi daga inda nake zaune a tsawala AA ne ya mike yana fadin bude mata dakin dake kusa da nawa ta zauna ciki.
Daga haka ya fice daga gidan laraba ta umurta da taje ta bude dakin ta nuna min dan kallon ta nayi ina fadin anty don Allah sallah nake son inyi.
Ok zaki iya shiga dakina ki hau sama ai kin san dakin ko na dan gyada mata kai a hankali na tashi ina daukan hand bag dina dake aje saman kujeran..
Tace baki sha ruwan da aka kawo maki ba zansha nace na dauki gora daya na fara tafiya dashi na kai saman sai gata ta biyo ni tana fadin.
Bari in dan gyaro ban dakin kafin ki shiga nace ba komai zanyi hakana a tare muka shiga dakin nata da ita.
Na aje jakkana da gyale na na nufi bandakin ko dana tura saida tsikan jikina ya tashi gurin na dan gyara do naga abin gyara a je gefe daya na wanke nayi abinda zanyi na fito don akwaini da kyankyami.
Na samu ta shifida min abin sallah na gabatar da sallah na zauna a gurin ina jiran a kira magariba ta sake shigowa dakin lokacin nace da ita su AFFAN fa anty.
Sai lokacin naga ta danyi murmushi tace suna cikin gida sun je islamiya ne sai zunyi sallah zasu shigo.
Kiran sallah da agogon dakin yayi yasa na mike na fara gabatar da sallah na a gurin sai da nayi ishai na dako wayana na kira ya Amina.
Tana dauka ta fara fadin Amarya mai batun hankali yau na samu an kirani ne fushi ya rage ke nan nace su Nasir na nan gidane ?
Sunanan wani abin ne nace ki turo akawo min shi don Allah da sauri naji tace ina da mamakin ta gani nan gidan Anty Fati dazun muka zo.
Khadija kin zo garin nan shine baki sanar dani zuwan ku ba sai da na bata rai cikin gajiya nace nima ban san zamu zoba yau sai da ranan nan yake fadin in shirya.
Tace gaskiya yanzu ba zan samu turo su ba dare yayi da safe zan shigo nace Allah ya kaimu na kashe wayan.
Shine ya shigo dakin yana dadin ba,a gyara part din bane ta koma ciki tace ba sakin fuska an gyara sallah ta ke yi.
Deedar idan kin huta zamu shiga mu gaida Abba ya fada kai tsaye to kawai nace don naga anty a tsaye dakin.
Yana fita na mike tsaye tare da tambayan Anty Fati wani daki zan shiga tace muje in kaiki yana nan kusa ai tayi gaba nabi bayan ta zuwa dakin .
Sauran dakunan duk a rufe suke sai wanda zan shiga ne ta tura kofan muka shiga tace wanan ne dakin nagode nace mata.
Har ta juya zata fita ta juyo tace min idan kina bukatan wani abu sai ki min magana to nace tare da fadin nagode.
Tana fita nabi dakin da kallo komai na dakin Fati akwai shi dakin sai da wanan bai tsufa ba don ba a zama cikin shi yana nan sabon shi fil.
Sai dai dakin yayi kura sosai ba zan iya zama a cikin sa haka ba gyale na na cire tare da aje hand bag dina na fara gyara dakin.
Kayana Laraba ta shigo dashi dakin tana fadin a, a baki huta ba da sai da safe nake son shigowa na gyara maki nace kada ki damu mama ai gyaran ba wuya don na gyara.
Bayan fitan laraba ne na shiga wanka na dan dauki lokaci a bayin kafin in fito ina fitowa AA ne zaune a bakin gadon dakin ya tsurawa wayan shi ido.
Gashi da daura gaba na fito bayin don ko tawul babu a dakin na rasa yadda zanyi shi kuma ya dago kai ya kafe ni da ido na rasa yadda zanyin in karaso gashi zaune a dakin.
Dan komawa nayi kamar zan shiga bayin can kuma naja na tsaya wuri daya nace don Allah dan fita in gyara jikina kamar mai jira inyi magana ya mike daga zaunen da yake yace idan kin gama ina jiran ki a falo bazamu fita ba sai gobe don yanzun dare yayi.
Cikin sauri na shirya jikina jin bazamu fita na saka dogon rigan da na dauko don shan iska tare da dora hijjabin sallah na akai.
A falon na samay su zaune da anty Fati da yaran su lokacin yaran sun dawo daga babban gidan su wurin kakanin su.
Karasowa nayi inda suke ina dan taba kan karamin daga ciki ina fadin kun dawo ba tare da ta dago kanta ba tace bazaku gaida anty da zuwa ba.
Yaran suka dago suka kalleni sai kuma suka maida hankali wurin uwar su suna tambaya mama wace anty.
Kyalesu ta yi nidai na samu wuri na zauna ba tare da nayi magana ba tace kai Affan jekace laraba ta fito da abinci.
Yaron ya sheka da gudu zuwa kiran laraba din na sake mika hannun gun karamin nace bazaka zo ba mu gaisa a hankali ya tako zuwa wurina.
Hannun shi na kama ina tambayan sunan shi gaba daya na mayar da hankalina ga yaron Affan na dawa ganin karamin a gurina shima yazo inda nake.
Laraba tazo da abinci tana jerawa a kasan carpet gaban shi ta gama ta wuce yace ina wanan maganin da na bari nan tace kai Affan je daki ka dauko ma babban ku maganin sa a kwalba.
Yace kai enough dawo ka zauna idan ke ba zaki tashi ba ki bari komai yaro ko wata zasu yi min ke bazaki iya motsa jikin ba ko kadan wanan son jikin naki baida amfani wallahi.
Dan dago kai nayi na kalleshi sai naji nauyin abinda yai mata a gabana ta mike zuwa dauko maganin .
Cikin harshen turanci nace da shi haka fa baida kyau kana mata tsawa a gaban diyan ta da ni don ko nice bazan ji dadi ba.
Bai min magana sai zama da yayi kasa ya fara bude abincin da aka aje din tsuki yaja yace daidai tana kawo wa wurin amma dai kin san bancin shikafa da dare ko.
Shina dafa tunda rana na dauko da wuri zaku iso rufe abincin yayi ya koma ya mayar da jikin shi ga makarin kujera tare da mai da hankalin shi ga tv.
A dauka kenan bazaka ci ba yace bai ci tace amarya kefa nace zanci anty na gode sannu da aiki tace ba komai.
Sauka nayi tare da yadon a hannuna na zauna a kasan ina fadin Affan zakuci abincin in zuba daku?
Yaran sukace eh anty tare na zuba muna suka zauna muka fara ci a tunane na tunda yace bai ci zata shiga kitchen ta girka mai abinda yake so.
Amma sai naga ta koma ta zauna tana sakatan hakoranta tare da mayar da fuskan ta ga tv tsakuran abincin nake don ba dadi amma haka nake kokarin turashi a cikina.
Wayan shi ne yai kara yana kallo bai dauka ba har kiran ya katse ba a kai wani lokaci ba kiran ya kara shigo mashi ya dauka ba tare da sallama ba.
Sai dai mun ji yana fadin zaki fara wanan haukan naki ko kina wurin yawo ki zan tsaya jiran sai kin dawo in fada maki zamuyi tafiya ko may , ?
Ban ji abinda ta fadi ba mashi ba mun dai ji yace saboda ke kika aje ku ke kika haife ni ne Nafisa kina fa son wuce gona da iri nagani yana fadin haka ya kashe wayan shi.
Aka kara kira sai da ya kallo inda muke kaina yana kasa naji yaja tsaki ya kashe wayan tare da jefata gefen shi.
Baba gobe zaka kaimu makaranta da kanka kullun abokan mu babban su ke kaisu school kafin ya bada amsa nace zaikai ku mana tunda yana gari.
Kuma, asan baban ku yazo ko ?
Uwar tace kada ma ku sa rai don kun san ba kaiku zaiyi ba nace haba anty ki barsu su roke shi mana tunda gashi a zaune.
Murmushi tayi kawai ta kawar da kanta gefe bata sake kallon su ba nace jeka gurin daddy ka rokesa ko zai kai ku yaron yana makewa na turashi dole yaje gaban uban sai ya kasa magana.
Daga inda nake zaune nace dashi ana magana da kai ya juyo fuska a daure yana kallon yaron yace maynene ?
Wai suna son ka kai su school gobe don Allah shine ya kasa magana ns bashi amsa yace
Ke kuma da baki jin tsorona ko kunya kece mai iya fada ko ya tambaya yana kallon fuska na ?
Shi zuwa school din ka kai diyan ka ne abin jin kunya kuma ko tsoro ina fadin haka naja bakina na daure fuskana ban kara magana ba kuma ban ci gaba da cin abincin ba.
Kai ku tashi kuje ku kwanta dare yayi gobe ba kuna shiga school ba yace cikin daure fuska, yaran sukayi saurin mikewa tun bai rufe bakin shi ba don tsoron shi da suke ji.
Mikewa nayi na fara kwashe kayan da mukaci abincin nakai kitchen ban zauna ba ina batun wucewa naji yace ke