MIJIN BUZUWA complete Hausa Novels.txt

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   82 / 144

243K to 246K   out of 431K words

shida ke batun yi.
A wurin ku ma,aurata kikaga saurin hakan mukan ai safiya ya dade da yi ko tunda kinga har nagama aikina yanzu saura naki.
Shiga ki kintsa ki fito a fara zuba masu kafin su tashi mun gama komai dakina na shiga inda ya Amina da anty fauziya suka kwana su mommy na cikin dayan dakin da ban faye amfani dashi ba.
Suna kwance suna barci na shiga na shirya a hankali ina shirin fitowa ne ya Amina ta falka ina kwana nayi mata muka dan tsaya hira.
Maryam ta shigo dakin tana kirana na fita na samay ta a falo tana fada min tana jin hayaniya kamar Nafisa ce ta dawo.
Nace da safen nan kila dai muryan yan uwanta kika ji sai dai kuma ba abin mamaki bane don yace yau za,a sallamo ta dama.
Tace kamar mai tsoron asibiti zata dako wanan sammakon haka ta dawo gida ke ko wake son zaman asibiti idan ba dole ya kama ka ba.
Mun ci gaba da zuba abinci ba tare da mun kara bi ta kanta ba jin muryan su mommy a dakin da suka kwana suna hirane yasa nasan sun tashi.
Dakin na shiga da sallamana suka karba min cikin zubo idon su a kofan dakin fuskokin su a sake tare da fadin khadija kun tashi nace eh mommy ina kaiwa kasa tare da fadin ina kwanan ku mommy ?
Lafiya ya gajiyan da dauwai niya mun kawo maku bakun tan na bazata anty amarya ne ta dan dago daga inda take kwance tana fadin wallahi fa.
Sannu da kokari kinji ina murmushi na mike daga tsugunin da nake nace mommy kuyi wanka abinci na falo.
Kin gani ba haka muke so Alhamdullahi gida ya gyaru yanzu tunda mutun zai zo ya samu tarbo haka ke da ki kara hakkuri don yanzu kishi ko wani iri yin shi zata yi na fili dana boye Alkah dai ya dada kare muna ku.
A raina na amsa da amin na mike zuwa ban dakin wanko masu shi na yi tare da kunna masu ruwan zafi na fito har lokacin magana sukeyi akan gidan ban tsaya na fito daga dakin.
Can na koma dakin kwana na na wanke ban dakin yadda zasuji dadin yin wanka a cikin sa duk da shima ba wani ddatin da yayi.
Muna falo na ce da maryam barin leka shi idan ya tashi in gani na fice daga dakin ina zuwa falo na samu buzaye mazan su da matan su sun saka nafisa a tsakiya.
Nace a, a ashe kin dawo sannu da dawowa ya jikin idan ke dake nesa kin karba min nafisa ta karba min ban tsaya ba nai murmushi ina haurawa sama naji tace Allah waddai cusa kai babu kwarjini.
Sanin muna da baki a gidan yasa ban tsaya ta kanta ba na haye sama abina kofan dakin shi na tura naji kofan a rufe na dan murda shiru.
Harna juya zan fito ina tsanmani ya fita daga dakin naya na sai naji ana murda kofan dakin shine ya bude tare da fadin waye fuskan shi a daure.
Ganina yasa naga ya koma yana bude kofan na mara mai baya zuwa cikin dakin ina shiga yake fadin marasa hankalin na rufe na kofa.
Ina kwance sai ga Samiha min a daki wai Nafisace ta turo ta karban abu wurina ban bashi amsan maganan shi sai kokarin fadin da nakeyi kayi wanka ne ko in hada ma ruwa ?
Banyi ba yanzun dai nake shirin yi danaga baki dawo ba don kwance nake tun dazu na gane may yake nufi amma na basar dashi kamar ban gane may yake nufi ba.
Nagama abinda zan mai na fito daga dakin daya shiga wanka har lojacin suna nan a inda na barsu zaune din.
Ban kula su ba na shige part dina a falo na samu bakina sun fito maryam ta na gabatar masu da abin kari.
Mun zauna ana karyawa ana hira ne ya shigo a cikin shirin fita yana gaida su mommy din da yaya Amina dake mai sarakuta.
Tambayan shi mai jiki mommy tayi yace ai ta dawo da safen nan Anty amarya tace har an sallamo tane yace tadai sallamo kanta dai.
Ikon Allah duk shiru sukayi falon suna mamaki sai Fauziya ne tace wai ko yayan mu Nafisa nada hankali murmushi yayi yana mikewa daga inda yake tare da fadin tana da shi mana tsaban wautane mata.
Da kuma zafin kishi inji Faiza ta badi tana kama yar ta dawowan gida mai zatayi banda zaman saka ido da fitina kana ma kokari wallahi.
Kallin ta ya danyi ya kawar da kai zuwa gareni ban ko dago na kallesu ba ina dan shan tea dake gaba na a hankali.
Zan fita in dawo Allah ya tsare nace dashi tare da kawar da kaina gefe daya akan tea dina bayan ya fita ne suka sa topic din Nafisa a dakin.
Fauziya da Faiza sukace ba zasu gaida ita ba don sai sun nuna mata ba kowa take ba yanzun kan basu shayin rama komai zatai masu.
Maryam nabi a daki nazauna a wurin ta a nan ya Amina ta samay mu sai lokacin nake nuna mata kayan da ya sayo min na lefe fita tayi da kayan falo wurin su mommy tana nuna masu.
Nan suka shiga kallon kayan tare da yaba kyauwon su ashe mu kallon tsoro mukaiwa kayan sai yau muka fahinci may ke cikin akwatunan.
Mommy ne ta jawo sarka da awarwaro na zinare har kala uku da wasu set din agoggaya masu masifan kyau kala uku suma kallon juna mukayi da maryam din na sada kaina kasa .
Su mommy ne bayan sun gama kallon kayan sun sa albarka suka fita waje gaida Nafisa da dawowa basu jima ba suka dawo dakin.
Basu ko zauna ba Faiza ke tambayan su idan nafisa ta amsa masu gaiuwa dariya ne ya dan kamani alokacin haka na kumay shi ba hali in fitar aji.
Haka dai har suka shirya tare da maryam su Faiza da fauziya da Anty amarya suka shiga kasuwa suka barni da su mommy da ya Amina a gida.
Bayan fitar su ne mommy ta fara magana tace dama naki binsu ne don mu samu kyabewa dake Khadija da sauri na dago kai ina kallon mommy din.
Tace khadija nasan irin zaman hakkurin da kike da wanan matan don haka ki kara ga wanda kike dashi kada ki yarda daidai da rana taya ta gane kin karaya da alamarin ta.
Don ta haka zata gano takon ki a gidan nan ki zama jarumar mace a gidan ta kamar sauran jarumai matan da suka sha gwalgwalmaya a gidajen auren su kafin su tsaya a kafan su.
Sannu a hankali idan kinyi hakkuri kuma kikaci gaba da wanan dabiar take zaki cin ma nasaran ki da yardan Allah.
Sai dai abin ne dakamar wuya don akwai tafiya amma sai dai kamar gobe a wurin Allah in dai da rayuwa .
Ba wanda ya tsamani zaki samu sauki a wurin mijin ku haka sai gashi Allah da ikon shi na fahinci biyayyan ki gare shi ya jawo maki mutunci da kima a idon shi.
Bawai kwanciyar aure bane kawai jin dadin aure a, a har da yi nayi bari na bari da gyara da hakkuri da rayuwa ga abokan zama.
Ni a fahintar Nafisa danayi ta ta,allakane kawai da kwanciyar aure a tsakan su ba wai ta damu da kula da rayuwan miji bane.
Shi namiji kana sace zuciyar shi ta fanni daban daban irin kyautatawa da kulawa a gareshi da nuna damuwar ki nasan duk kin san da wa yan nan abubuwa amma sakaci dashi da wasu mata a yanzu sukeyi ne ke yawan jawo masu matsala a gidajen su.
Kinga kamar fati ansan akwai asiri amma asiri ya cin ma hali dama don ko banza haka take kamar dutse babu marmari a tare da ita.
Yanzu daman ki ne khadija da zaki nuna naki bajin ta ga kowa na babangida asan ba auren banza ya kara ba.
Ko wace mace dama da dalilin auro a gidan mijin ta amma dan akasi kadan zai iya bata ta ga kowa ba wai ga mijin shi kadai ba kadai ba a, a har ga kowa dake tare dashi.
Don Allah khadija kin dai ga kannen mijin ki a tsatsaye suke ko gare mu matan uban su wani lokaci sai mun hada da hakkuri da su.
Haka ke ma nake mai jan kunnen ki a kansu kada ki yarda ki samu matsala dasu ta ko wani fanni na zamantakewar ku dasu don Allah.
Ko dan zaman nan da mukayi tsakanin jiya da yau ya kamata ki fahinci wani abu daga gare su irin halaiyan su da sauran kalaman su zuwa ga nafisa.
To ke sai kiyi amfani da wanan damar ki toshe wanan kafar da ta sake daman ta a gare su ki gyara ta yadda zai zama kin kawar da duk wani shakku na gidan nan a zuciyar su.
Ina fada maki hakane don daukar ki danayi tankar yar uwata ta jini don albarkacin Amina gata nan shawaran Amina har gobe baya wuce ni da kika ganmu nan .
Haka nima nawa bai wuce ta a haka muke zaune muna rufawa kan su asiri ga matsolalin mu .
Akwai canji kwarai da aka samu a gidan nan ta dalilin ki ne kuma sai ki daure ki rungumi Allah da mijin ki banda yawan fushi kan abinda bai kai ya kawo ba a dauke shi da zafi.
Har yar uwar zama ta fahinci kuna da matsala da mijin ki taji dadi ko a bainan jamma, a yai maki abinda ba daidai ba kada ki yarda ki nuna har mutane su gane hakan gare ki.
Ajiyan zuciya na sauke bayan ta kare maganan ta da fadin Allah yai muna jagora ya shige muna gaba da amin.
Nace mommy na gode in sha Allahu zan kiyayye da yarda Allah ya Amina ne ta karbe da fadin don Allah khadi kiyi amfani da maganganun da mutane suke fada maki ko da yaushe ki jajirce a gidan nan ki mai da komai ba komai ba .
Dawowan su Anty amarya yayi daidai da isowan shi gidan ya dawo ya sallamay shi sai da yasa aka cika masu bayan motar su da tsaraba sukai muna sallama suka tafi.
Bayan tafiyan su ne ya dan shigo bai zauna ba saman dakin shi ya shiga bai dade ba ya fito su nafisa na zaune a falon ya dan tsaya da ita yai magana daga nan ya shigo part dina ya samay mu.
Ina gyaran wuri ya gaida maryam dake kitchen tana wanke kayan da mukai amfani dasu ga bakin mu yace dani ya kamata a samo mai taimaka maki da aikin nan haka.
Nace zan sa hajiya mama ta duba min a kaduna idan za a samu a turo min yace ba zaki magana a samo maki a gida ba.
Fuska na ya mutsa nace mai zan dai fi so a kadunan don can gaskiya ban san wata wace za,a dauko min ba yanzu kan.
Ok zan mata magana muji ko akwai wace za,a turo maki din ni ni zan koma office sai yamma idan na dawo.
Allah ya tsare a dawo lafiya nace mai yanzun na dan sasauta daure fuskan da nake mai kwana biyu a gidan.
Na jin zafin abinda yai min ajan nafisa don ni jin zafina shine bai kulani ba kamar ba mutunce ya bari a daki ya fita ba.
Sai kuma fadan da yai min don may na fita school a ranan duk da na fada mai a motar gida na fita kuma yake ganin laifina dayin hakan.
Bayan mun gama komai ne mun zauna da maryam muka danyi hira har barci mukayi after four tace zata koma school ban so ba sai dai ba yadda zan yi da ita don dole ta koma din.
Bayan tafiyan marya sai naji zaman ba dadi ban kuryan daki ban falo a karshe dai na dawo falo na zauna da takarduna ina dubawa a hankali.
Lokacin aiyukane amma sanin cewa ba nice da girki ba sai ban damu da in aiwatar da komai a gidan ba don ba hurmi na bane yin hakan yau.
Waya na dake gefena yai kara na dauka ya Amina ce ke kirana na dauka take fada min bayan mun gaisa wai sun isa tun dazu yanzun take shigowa gida.
Nace sannun ku da hanya su boy dai nasan sai zuwa gobe za a dauko su ko tace nace a kawo min su yau don gidan yai shiru basu.
Nace wallahi haka nake fama da kadaici yanzun haka dazun nan ma bayan wucewar ku yake min maganan ai in samo mai aiki da zata debe min kewa.
Ni kuma nace ba wadda zan samo sai dai yaima hajiya mama ko mommy su sama muna tace kina ganin a dauko maki wata ta fanin su zaifi.
Nace ni haka nake gani anty don kin ga irin korafin da akeyi akan nafisa da yan uwan ta a gidan ko yaushe to sai kuma ni inje in dauko nawa in kawo gidan anty ?
Ke diban hauka zakiyi irin nata ai ba zai wuce mutum biyo ko uku ba ko nace wai anty na kaisu ina data ma ta isheni ai ya Amina ina zan kai har mutum uku haka anan.
Tace yanzun dai zamu tatauna da mommy muji inda ya dace a sama maki din amma ai ko can gida ba za a rasa irin yan kauyen Doko din nan ba masu neman aiki.
Munyi sallama da ita na kashe wayan tare da tunane a raina mikewa nahi na shiga daga ciki don in watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi.
Misalin takwas ya karaso gidan nan falo ya samu nafisa da iyalan ta zaune tana waya gaida shi suka danyi bawani cikin kulawa ba.
Kare wayan tayi tana dago kai gare shi yace da ita ya jikin naki tace da sauki tana kokarin mike kafar ta a kan dan stol dake gaban ta.
Bai tsaya ba yace barin shiga daga ciki in watsa ruwa ya sa kai ya fara tafiya ta kira sunan shi da fadin Samad ya juyo yana kallon ta.
Tace banji kayi min maganan kudin dana tambaye ka ba dazun da zaka fita yai mata wani irin kallo tare da sauke nauyayan ajiyan zuciya.
Cikin bacin rai ya dan runtse idon shi na dan dakikoki sannan ya bude tare da kallon su gaba daya da yan uwan ta yace.
Nafisa na sha fada maki ban son irin wanan dabiar da kike min ke wai kullun baki da zance ga mutum sai na maganar kudi shi kudin nan ko ginar shi mutum ke yi ai yana wahala gurin gina ko ?
Tace idan ban tambayeka ba wa kake son in tambaya ya bani in yi lalurar gabana dashi yace saboda ke baki da wayau ko ya watsa mata hara ya barta gurin.
Har ya shiga wanka yana tunane a ransa alamarin Nafisa yana daure mashi kai ya rasa abinda take yawan yi da kudi haka don kullun cikin jero mashi lalurar kudi take a gidan.
Babu abinda ke cikin zuciyar ta sai zancen kudi bata san ta sauke hakkin ta na aure ba gare shi.
Duk kokarin da yake yi a kanta da yan uwanta a gidan ya lura Nafisa bata ganin haka may ye amfanin bata kudin matar da batasan kimar shi ba.
Ganin alamarin nason damun shi a rai yayi gagawan cire tunanen ta a ran shi ya watsa ruwa agurguje ya fito bai tsaya dogon shiri ba ya nufo part dina don ganin halin da yake ciki don baiji motsina ba a gidan.
Kai tsaye da ya fito part dina ya nufa nafisa da ke zaune tabishi da mayattacen kallo cike da jin hayshin shi da zargi a fuskanta.
Shigowa yayi lokacin ina falo zaune a kasa tv na aiki ga cup din tea da cake a gefe ina rike da takarduna ina assignment.
Kaina na dago ina kallon shi tare da mashi sannu da zuwa ya samu wuri ya zauna tare da fadin dauko min abinci in ci anan.
Kallon shi nayi cikin mamaki nace ba nan kake ba yau ai shiyasa banyi girki ba yace kenan baki girka komai ba ?
Nace cikin girgiza kaina gaskiya banyi komai ba yanzun ma tea na dan hada kada in kwana da yunwa a cikina.
Yace amma kin san dai nafisa jinya take yi ko don haka ba hujja ba ne kice baki girka min abinci ba inba ba, a nan zaci ba ke cikin ki bazaki ci bane ?
Najira ya gama fada in fada mashi dalili na na kin yin girki danayi don yin zai kawo wani fitina tunda dai ita batace ba zata iya yin girki din ba saida ya gama.
Nace ina gujewa abinda zai haifar da wani fitina ne agidan nan tunda ba ita tace ba zata iya hidima da kai ba kuma ni naga ni kadaice yau shiyasa ban girka komai ba tea din ma zai isheni in kwanta ai.
Yar gurin Nafisa ce ta shigo babu sallama ya daka mata tsawa

82 / 144

Chapters