samu ganin shi ba koda muka shigo
Tace Allah ya tsare ya kare Allah ya dawo daku lafiya suka mike zasu tafi ya juyo yana fadin bataci wanin abin kwarai ba tun zuwan mu garin nan.
A a khadija baki ci komai ba har yanzu kina bakunta ne keda gidan mijin ki idan abinda a girka bai gamshe ki ba ai zaki iya shiga ki girka ko kisa a girka maki.
Ki saki jikin ki nan gidan ki ne gidan auren ki ne kuma mu iyayyen ki ne kada kiji nauyi ko kunyan yin abinda kike so ke tankar diyan gidan nan kike yanzu dama kuma haka din ne ke yar mu ce.
Sun fice sin bar mama na mun wanan nasihan tare da dan yi min nasihan rayuwan aure wanda duk abu dayane duk wani wanda zai mun nasiha akan biyayya ne akan aure zai mun shi.
Suna fita sai ga mommy ta shigo dakin tana fadin gashi kuma su Binta suna school tun safe suka fita gidan nan.
Hajiya Mama tace yanzun yake fada min wai bataci abinci ba tunda suka zo garin nan don haka nasan halin khadija da kunya kwasheta ku tafi can wuri ki ko zata sake dama kece uwar yara.
Haba khadija kina amarya zaki zauna da yunwa a cikin ki haka tashi muje ki samu abinda kikaci don Allah kardai wai har yanzu baki sake a gidan ba kike nufi ?
Nan ta kamo min hannu muka fice daga part din hajiya mama nabi mommy zuwa nata wurin nayi mamakin ganin Ya Amina a dakin mommy da muka shiga ban wani sake ba sai wuri da na samu na zauna a gefen ta.
Khadija kece kika koma haka kallon kaina nayi ina mamakin abinda zata ce na koma nasan dai bai wuce tace na ramay ba inma raman nayi ai su suka kaini ga hakan.
Hawaye na fara daga inda nake zaune hankalin Ya Amina ya tashi sosai tace haba khadija muna murnan ganin ki haka zaki saka muna kuka kuma.
Mommy ne ta kawo min abinci ta aje min a gabana tana fadin bari taci abinci Amina kafin ki fara mata wani magana don mijin ta yace taki ta cin komai tunda suka zo.
Mommy ba gaskiya bane ko yanzu na sha ruwan zafi kafin mu zo nan mommy tace taji amma don Allah in dan ci abincin kafin a gama na rana.
Tabude kulan naga dafa dukan cus,cus da ganye ta zuba min da kanta nan suka tasa ni gaba sai da na dan tsakura.
Bayan na gama ne Ya Amina ke fadin khadija ki natsu ki saure ni ban son ki boye muna komai dake faruwa dake a gidan nan don mu san ta inda zamu bullo ma zancen.
Mommy ta karbe da fadin ki saki jikin ki khadija ko ba zaki iya fada min ba nasan zaki fada ma yar uwar ki Amina halin da kike ciki don hankalin ta ya kwanta.
Don tun ranan da muka barki hankalin mu ba akwance yake ba da barin ki da mukayi a gidan nan da Nafisa da yawan yan uwanta ke ke dai.
Wasu hawaye suka zubo min ban boye masu komai ba har zuwan mu kadunan da mukayi na fada masu kai kawai suke kadawa suna mamaki.
Mommy tace babu komai ke dai ki kara sa Allah a gaba shi zai kare ki daga duk wani sherin da suke kullawa ga kowa a gidan nan.
Saukin abin ma da tayi maki baki bata bashi hakan zai dan kawo shakkun ki a zuciyar ta harta dan rage abinda tayi niyya akan ki.
Kin san dai yanzu akwai hakkin miji a kan ki kada ki yarda ki tauye mashi hakkin ki da Allah ya rataya maki akan ki.
Sanan duk wani abinda kika san yana so ki dinga yin shi a kai kai abincin da yake so shi zaki dinga girka mashi kin san dai dressing na jan hankalin miji ga matar shi nasan baki da wasa a wurin kwaliya da sauran su.
Kinga mijin ki maison jin dadin rayuwa ne shine babban matsalan da suke samu da Fati tun farko nayi nayi ta canza tsarin ta amma bata daukan shawara ko kadan.
Zaki natsu sosai ki fahinci komai nasa ki dinga aiwatar da nufin ki a kan su sannu a hankali ba a cikin garaje ba yadda kika tilasta shi yakai yaran shi makaranta yau da safe hakan yana da kyau sosai wallahi.
Nan suka zaunar dani suna min nasiha sosai akan rayuwan gidan aure har barci ya dauke ni a gurin suka zauna da ya Amina suna maganan abinda suka fahunta a cikin magana na.
Mommy tace don kada ta tayar min da hankali ne bata sanar dani ba don kada hankalina ya tashi.
Tace ba karamin magana bane wanan fa Amina ni abinda na fahinta shine kamar irin asirin da taiwa fati ne ta sake maimata wa Khadija yanzu kuma don Nafisa ba karamar shu,uma bace wallahi.
Saukin abin ma ita khadija ba irin yaran yanzun bane ai da ta fahinci halin da suke ciki da mijin.
Wace amarya za akai yanzu harta share wanan kwanakin miji bai neme taba a zauna lafiya kuma ko da bata son auren ai ba sin shine batayi ba a yadda na fahince su.
AA
Sun isa zaria suka fara zuwa wurin kawu salihu nayan sun gana dashi ya gama jin abin da ya kawo su bai tsaya ba yace suje wurin wanan tsohon malamin nasa.
Sun isa gurin shi sunyi sa,a ba mutane a gurin shi bayan sun gaisa dashi kawu yace malam gamu mun sake dawowa da dana na wancan lokacin.
Nan ya koro mashi matsalan dake addaban shi a yanzu wanda basu fahinci ko maynene ba dan murmushi malam yayi irin na manya yace ai nasan zaka dawo in ka tuna da istiharan da na baka kaje kayi zaka gane wanan matsalan ya fito a ciki amma kai baka gane hakan.
Wani zobe fari ya zare daga hannun shi ya mika ma AA din yace kai zaifi maka amfani a yanzu sama dani.
Yace don naga kana da rauni wurin ibada ta haka ake samun daman cuta maka ta inda baka zata ba .
Ya kara dauko wani garin magani yana mika mashi yace wanan za kayi amfani dashi idan ka koma gida daidai lokacin da kake fara jin yanayin da kake ji.
Don daure ka ake bazaka iya aiwatar da komai ba akan mace zakaji ka koma tankar mace a duk lokacin da bukatan kasancewa da matar ka ya taso maka.
Ya dauko wani dan abu ya bashi yace ya binne a cikin gidan shi indan har ka saka wanan abin a gidan ka da yardan ubangiji duk wani sheri da za a aiko maka bazai yi tasiri a kan ka ba.
Sukai ma malam godiya tare da bashi dan sadaka don bai karban wani abu a gurin su sosai suka juyo zuwa kaduna.
Sun kamo hanya suna magana AA ke fadin wai wake binshi da wanan sheri hakane may ya tare wa mutane.
Yusuf ya kalleshi yace maganar gaskiya shine a cikin iyalin ka wata ke wanan sheri idan ba su din ba wazai maka wanan sherin haka akan iyalan ka.
Huci ya sake daga inda yake zaune yana cewa indan na gane may mani wanan sheri ba zan saurara ma mutum ba ko wanene.
Khadija
Shiru shiru basu dawo ba har nayi barcina na tashi dawowan su Binta na koma dakin hajiya mama sarakuwa na muka kebe a daki dasu muna hira.
Duk yadda suka so su bugi cikina suji zaman mu a gidan na boye masu ban fada masu komai ba sai dai in masu dariya idan suna maganan su.
Can zuwa hudu suka dawo part din Abban shi suka yada zango a wurin shi sun dade a zaune da Abban ya aika in zo in gaida mahaifin nashi don yace bai sanni ba.
Nashigo falon na Abba suna zaune a saman kujera a cikin sakewa da mahaifin nashi na shigo bisa jagorancin mommy .
Kasa na zube kaina yana kallon kasa na gaida shi da wuni yake cewa da mommy eh lallai naga sarakuwan nawa alama ma kawai yanuna min daga inda ta fito.
Don kin san su mutanen Niger akwasu da tarbiya mayne ma sunan ta mommy tace ai uwan tace khadija take Abba yace suna mai kyawo da fatan zaki halin mai sunan da kika gado.
Yadan muna nasiha a tare har lokacin ban dago kai na kalli Abban ba yace mutshi mu tafi Allah yayi muna albarka araina nace amin don irin su bakin su karba ake idan an dace.
Zan fita naji AA na fadin ki fito mu tafi gida don ina son tafiya yanzu ban amsa shi ba nafita muna shiga mommy ta kara min nasiha ta rakani na sallami sauran mutanen gidan muka fito suna waje suna jirana a lokacin.
Barin mu gidan nasu kafin mu karasa gidan su kira ya shigo a wayan shi ya dauka tare da sallama bata karba ba tace Samad idan baka dawo ba wallahi zanzo garin nan in samay ku.
Watau kai ga mai amarya ka dauke ta kaje can kuji dadi da ita ni ka barni nan yace ke ban son wanan haukan naki ya kashe wayan shi .
Nikan mota na tsayawa na bude nafice daga ciki ban tsaya jiran su ba tunda yanzu nasan hanya ba sai an nuna min ba.
A falo na samu su Anty Fati da sallama nashigo ganin su yasa na tsaya ina gaida su da wuni tace kun dawo ya su hajiyan suna lafiya ?
Lafiya suna gaida ke na wuce zuwa sama inda dakunan suke na bude na shiga dakin na nan a yarda na barshi tubewa nayi na fara gyara dakin sai dana gama na sauko kasa don shirun da yai min yawa.
Basu falon motsin su naji a kitchen na nufi can bayan Anty Fati na fara hangowa na karaso ina fadin ashe kuna nan ne ?
Eh ta fada tana juyowa gareni karasowa nayi cikin kitchen din ta dan kauce min na shiga daga ciki nace anty may za a dafa sai inyi mama laraba yau ta huta ita.
Haba dai ki barta tayi ai aikin ta ne hajiya ki barshi zan iya ai laraba tace nace ba komai nagaji da zama guri daya ne ina son in dan motsa jikina.
Anty Fati tace na rasa may za, a girka yanzu kin san shi dan matsalane wallahi azo ma ayi yace ba shi yake so ba.
Nace ina ga kamar tunda dare ne ai zai fi kyau a girka tuwo tace dare baiyi ba nace idan akwai kayan aiki ai za a iya yi.
Tace to shike nan ta juya ta fita daga kitchen din nan muka fara aiki da mama laraba wanda kusan aikin nice may yi tana miko min abinda nake bukata.
Bayan magariba mun gama komai da muke bukata har mun fitar dashi a falo nan dai na shige daki inyi wanka naga period yazo min.
Wanka nayi na gyara jikina na fito dama ina expecting din zuwan shi nazo da pad dina na shirya na feshe jikina da musk mai kan shi na samu wurina dan kwanta tare da bude datan wayana.
A take sakonni suka fara shigo min wanda kusan yawanci yan makarantan mune suke tayani murnan aure tare da yi min korafin rashin fada masu suzo.
Ina cikin basu amsa ne ya shigo dakin ya sauya kayan jikin shi kallo daya nayi mai na mayar da hankali na ga abinda nake yi din.
Takowa yayi zuwa bakin gadon abinci fa madam na dago nace mai naci kafin in shigo taso muje falon yace min.
Nace amma kasan haka baida kyau don itama tana son kebewa dakai yanzu tunda ita kazo yiwa weekend don may zan dinga takura maku haka.
A binda mutum baiso kada yayiwa wani don shima in an mashi bazai ji dadi ba ashe malama na kawo gidan ban sani ba.
Ba zancen malama sai gaskiya matar ka tana bukatan ka a kusa da ita banga dalilin da zan takura ma rayuwan ta ba ina da hankali fa.
Fitan ki shi zai sa mu takura mu fasa abinda zamuyi yallabai ba zan fita ba gaskiya ka bar ni please ?
Sunan da na samu kuma yau ke nan a gurin ki nace ai naga kamar kafi yallabai din mulki ne yanzu.
Yace lalai kan tunda ina a gaban gimbiya ai na zama yallabai din kaidai ka sani kana dai gaban matan ka ni may ye nawa a cikin wanan.
Ya juya yana fadin idan fa baki fito ba bazanci abincin ba nima yana fadin haka ya fita abinda ya fadi yasani tunanen kadafa su zarge ni idan banci abincin ba tunda nina girka.
Don haka na mike na fita ina saukowa ya tsura min idon har na karaso wurin na samu wuri zauna yaran suna gefe suna cin nasu abincin.
Affan kun dawo ya makarantar nace lokacin da nake zama na mayar da hankali a gun yaran daidai lokacin Anty Fati ta fito har wanan lokacin tana daure da zanin da ta wuni dashi a jikin ta ne.
Ba tare da tayiwa kowa magana ba ta samu wuri ta zauna batai magana ba shima bai mata magana ba sai ni da yaran ke dan fira a falon.
Karamin yace min yau anty yan school din mu sunga daddyn mu nace ashe kaji dadin hakan ya gyada kan shi dariya ya bani nace idan daddy na gida ashe shi zai dinga kaiku school ke nan kuna jin dadi.
Ke fa nake jira ki ba ni abinci yace mata ta wani juyowa tace ga abincin nan ai an gama tun dazun mikewa nayi daga in da nake zaune na dauko plate uku na jera a gaban su na fara zubawa.
Na aje mai yace min thanks na zuba mata nata na aje mata a gaban ta na dan zuba nawa kadan na koma gefe na zauna ina tsakura don ban jin ci.
Ina gamawa na mike nabar wurin tare da kwashe kayan da mukaci abincin da na su Affan daga can na wuce zuwa daki na ban koma wurin su ba.
Barci ya fara dauka na ban riga da na rufe dakin ba yashigo dakin da sauri na zabura na tashi ina tsoron ya aikata min abinda ya aikata min jiyan.
May ye haka ba barci kike yi ba ne nace barci nake ji dai na mike zaune ya karaso har inda nake zaunen ya samu wuri ya zauna shima.
Yace akan may zaki girki ba na hanaki wana aikin hakaba may ye amfanin masu yi din da aka dauko.
Kallon shi nayi nace don girki kuma shine aiki nayine kawai don in dan motsa jikima ba don wani abuba.
Yace au motsa jiki kike so ashe barin dan tayaki motsawa da saurina yun kura zan tashi ya rike ni na kasa tashi a inda naken.
Kokuwa muka dan fara yi dashi ina kokarin kwatar kaina daga gare shi amma na kasa danne ni yayi tare da raba hannaye na biyu ya shige tsakiyana.
Ban son haka don Allah ka sake ni please kasan haka baida kyau fa nake fada mai cikin wani murya yake cewa may nene baida kyau don miji ya rike matar shi ?
Zanyi magana ya hada baki na da nashi ya fara tsotso ina kokarin kaucewa amma na kasa don yafi karfina.
Jagwalgwala ni ya fara yi yadda yake so tare da cusa hannuwan shi cikin kirjina da karfi na zubura ina kokarin kwatar kaina.
Har kasan mara na yakai yana jin ya tabo pad naji ya sakeni yana fadin na manta lokacin ki yayi fa naga ya mike yana gyara rigarsa daya takure wurin kokuwa dani.
In kin fitar ubangiji yabi min hakkina a kan ku yar uwa don ba zan yafe hakkina ba
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Idan kin fitar min da novel waje ubangiji yabi min hakkina akan ki din na fada maku online novel ne na kudi da kuke cewa kun biya kuna da iko dashi kin san ai ba takarda kika saye ba.
Ki karanta nan ki barshinan idan kuma bakiyiwa Allah da Annabinsa da na hada ku dashi wanan kuma sakkayan na hannun Allah
Kada ki karanta min novel idan baki biya ba don ban yafe maki ba har ga Allah.
Allah yagani ban ji dadin zuwa kadunan da zamuyi ba saidai banda yadda zanyi don yan zu a karkashin dokar wani nake.
Wani abinda ya fara kula dashi shine sabon canjin yanayin jikin shi daya samu yanzu don tun randa ya gama min sati dayana a dadafe ya samu kwanakin suka cika mai.
Shikan shi bai san dalilin dayasa ya kasa aiwatar da komai a kaina ba amma a ranan da Nafisa ta karbi girki lafiya kalau ya kwana babu wanan sanyin da yake ji idan dare yayi ko nauyin zuciya yaji shi ya koma tankar mace ba namiji ba.
Amma saidai may da gari ya waye zan karbi girki tun da