MIJIN BUZUWA complete Hausa Novels.txt

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   49 / 144

144K to 147K   out of 431K words

son mu kalle shi dashi ba fa zai manta da abinda muka fada mai ba.
Nace ni wallahi zan iya yanzu ma ba sai anjima ba zan kirashi in fada mashi maganan da zai sa yaji haushi ya ce ya fasa .
Ke dallah ja can halina dake rashin kunyan tsiya may zaki fada mai wanda zai sa yaji haushi banda rashin wayon ki can .
Ya Amina ne take fadin haka rai bace dani nace wallahi ya Amina idan ba haka nayi mai ba tarko yake son ya dana min kawai ya cuce ni.
Ki daibi sannu maryam dake gefena ta fada tace kin san mutumin da baya magana mugunta na nan tare dashi.
Ya Adam dake zaune yana kallona ya harde hanayen shi saman chest din shi yace kada ki fada mai maganan da zai dawo ya damay ki daga baya don ni nasan ko waye AA don kusan a unguwa daya muka tashi dasu.
Nace cikin bacin rai da damuwa ni to yaya zanyi dashi lalaba shi zakiyi ku rabu lafiya inji yaya adam din yace min .
Kuka nake sosai yace ai ba abin kuka bane don aure dole ne kiyi shi sai dai yanzu idan zaki tsayar da wani ne daga cikin maneman ki sai dai yaji kawai kin tsayar da mijin aure.
Shawaran da yaya Adam ya kawo yanzu yayi min sosai a haka muka tsayar da zancen ya dan dade yana min nasiha kafin ya shige dakin shi ya bar mu wurin da Ya Amina.
Bayan ta wuce ne muna muka shige dakin kwanan mu nan na duba lokaci naga dare bai wani yi ba a lokacin don haka nakasa hakkuri na dauko wayana nakira shi.
Kiran ya kusa katsewa ya daga kiran nawa da sallama na fara yi mai magana maryam na zaune daga gefe na tana sauraren mu don wayan a handfree na sashi.
Ke baki san lokacin kiran mutum bane ya fada a gadarance nace kai kasan wanan a wurin ka ni bawani abu yasa na kiraka ba yanzu.
Sai maganan da ke yawo a tsakanin mu wai kana so na yace wai ne ma ashe nace wai ne mana don kaima kasan ba haka bane zancen.
Don Allah ina son ka fada ma su mama da bakin ka ba gaskiya bane wanan maganan da sukaji don su bar zancen.
Yace ke baki da bakin fada masu ne ko an dinke maki baki ne wanan maganan ke ya shafa dasu da ke son hadawa.
Na dan marairaice nace ina da baki kuma ba a dinke min ba sai dai ba zan iya fada masu bane su fahince ni yadda kai zasu fahince ka.
Murmushi naji yayi yace ke nan kina umurtana da naje masu da rashin kunya ko ke dai da baki so sai ki fada masu su fahince ki.
Na kara marairaicewa cikin muryan kuka nake fadin don Allah yaya Abdulsamad ka taimake ni please ina jin kunyan su mamane ba zan iya fada masu ba don naga sun dauki maganan kamar da gaskiya.
Au ke a wasa kika dauki zancen ashe nace kaima kasan wasa ne wanan maganan yayana yusuf ne yace ke kin san may nace cikin girgiza kai kamar yana kallo na.
Ki daina kira na akan wanan magana do ni baya gabana sam nace a hasale kamar yadda baka gabana nima har abada.
Haka kika ce nace haka di ne dan kawai ina ma magana na fahinta don kaine babba zaka so fada min magana halan an fada ma nayi kwantai ne ko zan auri miji mai mata ba irin ka ba cus ragowan wasu matan da suka gama dakai.
May zanyi da mijin tace wanda baida tacewa a gidan shi wanda duniya ke ma kallon sususun namiji may ke gidan ka banda wahala.
Wayan Maryam ta fisge a hannu na tare kashewa tana fadin kina da hankali kuwa nace ke bakiji rainin wayon da yake son fada min bane .
Tace ke shine zaki biye mashi kuyi sai da hali kin manta da abinda mijin ya Amina ya fada maki ne nace wallahi bai iya min komai sai Allah.
Sai don ina wawiya ina zauna ya fada min maganan banza don ina tsoron shi ko may kai ta girgiza min tace kina da aiki wallahi.
Sai da muka kara kwana biyu a garin muka koma makaran ta cike da kewan su ya Amina da yaran ta don su binta bamu kara haduwa dasu ba tun wanan lokacin da suka zo da dare gidan ya Amina.
Kafin in wuce sai da mijin ya Amina ya zauna dani ya sake maimaita min da inyi gagawan tsayar da wani cikin manema na.
Yace in iya sanin shi aure abune daya shafi fanin rayuwa n mutum saboda haka ina son ki kwantar da hankalin ki kwantar da hankalin ki ki zabi na kwarai ba zabin zuciyan ki ba.
Ki zabi mutumin da zai iya baki kulawa keda iyayyen ki da duk wani naki nan gaba don kwanciyan hankalin ki.
Ya Amina tana gefen shi tace ki fada muna sai mu sanar da daddy cikin maneman ki wa kika zaba kallon ta nayi nace ni wa zan zaba ya amina ?
Sai dai idan mamud zan tsayar ko ismail don yanzu su biyun nan sufi zama serious akaina.
Salati naji ya Amina ta saka min tana fadin wani mamud wanda kuna tare yaje ya kara aure ba ke kika ce baki son mai mata ba da farko.
Nace nace tun farko kin san ismail nake so ku kuka hana tace ki tsinci mai wurin wanan dan karyan mai neman mata nace ni ina son ismail don mun dade tare dashi.
Tace lallai ke yarinya ce har yanzu don Allah kada ki kara min maganan mutum biyun nan idan ina wurin nace ai kulun haka kuke fadi idan ana maganan shi.
Shin wai may shi Abdulsamad din yayi maki da baki son shi da sauri nace don Allah ya amina ki bar min maganan shi don ni bai cikin lissafi na ina fadi na kawar da kaina gefe.
Shiru mukayi falon dukan mu na dan wani lokaci sai can tace yanzu mamud din kika ga yafi maki ki aure nace yafi min gaskiya.
Kallo daya nayiwa ya Amina naga yadda ta hade rai mijinta yace yanzu dai zamu baki lokaci kije ki kara tunane akai nace zan yi yace in bashi layin mamud zai kira shi.
Na tashi na shiga dakin mu na dauko jakka na tare da fada ma maryam ta tashi muje kada rana yayi muna a hanya.
Mun isa makaranta lafiya sannu a hankali na fara mantawa da abinda na baro a kaduna nan ma da muka dawo ban sake kulla komai ba sai karatuna.

Fati dake zaune a falon su tana kallo zaune da balaraba mai aikin su wayan tane yayi kara ta dauka bata sheda mai layin da ya kira ta ba.
Tana dauka tare da sallama taji ance ke Fati wai ke wata irin kaska ce mai bakin naci mara zuciya wawiya mara wayo dabaki san ciwon kan ki ba ?
Ta sheda muryan nafisa don inda sabo ta saba don wanan ba shine karo na farko da takan kirata a waya ta zage ta ba tas akan mijin ta.
Har yakai ta daina daukan layin ta idan ta kirata shine wanan karon ta canza layi saboda tasan bata daukan nata din bai ma shiga don ta sakata a black list.
Idan kin gama haukan ki zan kashe Fati ta fada cikin bacin rai tace wallahi sai nayi ajalin ki idan kin ce bazaki fita hanyan samad ba baza karya kawai.
Allah yabaki daidai dake ni banda lokacin ki don don ga Allah na dogara kece duniya take rudin ki har kike ganin anan zaki tabbata a cikin sa.
Eyyeh ke har kinyi bakin da zan fadi ki fadi wallahi zaki san da wanda kike zance don kin sanni na san ki.
Sanina na alheri ta ja tsuki ta kashe wayan tana tunanen wanan halin kishin hauka na nafisa da bata daukanta a mai hankali.
Hajiya wanan matar tana da kai kuwa inji laraba take tambayan Fatin taja tsuki tace ita kuma nata kalar kishin ke nan na hauka.
Laraba ban iya wanan haukan kishin na Nafisa shiyasa mutane ke ganin laifina akai tunda ko nace zan dauki mataki shi ba yarda zaiyi sai yace nice banda hakkuri.
Hajiya kin sani ba aikin kan shi bane idan da abin na kai sake ne da yanzu ya isa ya gane halin ta amma matar da bata zauna ba kullun tana hanya bin bokaye da malamai da bokaye.
Ranan ma fa da tazo ina jin tana tambayan su jummai da suka shigo wai akwai wani malamin dake tashen aiki a garin nan zataje akan maganan yar ta ne.
Allah dai ya kyauta laraba ni nagaji wallahi ai abin yanzu ma da sauki tunda ba guri daya ake ba zaune hakan yafi min alheri ranan da ya tuna mu yazo shiya sani.
Hajiya ki dai kara hakkuri don hakkuri bai faduwa kasa banza wata rana dadin ki yana tafe insha Allahu.
Murmushi fati tayi tace kin ce Allah da sai in ce yaushe kuma ko sai lokacin da karfi na yakare zaizo din tace kin san fa buzayen nan haka su ke.
Duk gidan da suka shiga wanan gidan sai ya girgiza ke makin yi arziki ta barki a cikin diyan ki kin zauna ai ta gidan Alhaji garbati ai duk ta watsa matan gidan baki dayan su da baki halin ta.
Hajiya ai badon in fada maki wani abu ba hankalin ki ya tashi dana fada maki wallahi da sauri fati ta juyo tace may zai sa inta da hankalina laraba wani dare ne jemage bai gani ba.
Tace ai shine na gani don ke abin ai kamar ma saukin ki ne laraba tace fati ta sake tambayan ta may kike son fada min ne laraba.
Laraba ta gyara zama kamar mai son gulma tace wani magana najiyo a gurin anty Amarya dazun dana shiga.
May kika jine wai tana kallon ta take tambaya tace abin ne da wuyar fadi ai amma ai dole ne kiji ko a wani gurin.
Wai ji nayi suna magana da kawarta wai maigidan ku zai kara aure kwanan nan tace aure kuma laraba tace abinda naji suna fadi ke nan wallahi.
Gaban tane ya fadi sai laraba taji tsoro tace niko a ganina hajiya wanan bai shafeki ba kamar sauki ne a gurin ki ai.
Don yanzu akanta wanan buzuwan zata koma kinga ke kin samu hutu wani abin ke nan sai dai ki zama yar kallo a tsakanin su.
Sai lokacin tayi ajiyan zuciya tace zata koma kanta amma laraba tunane na kowa cece zai aura din yanzu kuma oho ?
Don itama kin san da nata sallo zata shigo kishiya fa kishiya ce ba ko yaushe ake samun ta Allah ba a wanan zamanin.
Gaskiya ne hajiya Allah dai ya hauda ke kansu duka baki daya don zamanin nan sai a hankali.
Shiru tayi tana tunane a ranta tanajin wani bakin kishi na taso mata a zuciyan ta ace kuma yanzu aure zai kara kenan ba batu su ma yakeyi ba ke nan.
Can kuma wata zuciya tace mata ke maiye naki a cikin karin auren shi duk tsiya dai tana zaune a cikin su can kuma tace kai may zai sa in damu haka ai bani za a kawo wa kishiyan ba.
Ita ma maynene bata gani ba akan nafisa a gidan nan don dai da rabon sai ta zauna a gidan ne take ciki har yanzu amma da ita da babu duk daya ne a gidan.

Samad ban gane may kake nufi ba da zakaje kaduna ka kwashe har kwanaki hudu wurin wanan gajar matar taka da bata da wani amfani.
Zaune yake a bakin gadon shi ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki a ciki bai dago kai ya dube ta ba don tunda ya dawo fushi take dashi wanda shi bai san dalili ba.
Yayi lalashi taki ta sauko jin abinda ta fadi ne yanzu yasa shi gane abinda take ma fushin dashi.
Iska ya furzo yace da ita a gurin ki ne bata da amfani ni a wurina tana da amfani don uwar yayana ne kuma yar uwata ce ita.
Yaya wasu yayan baidai wa yan nan masu kama da kama ba yayan nawa kike zagi haka babu nauyi ko kunya a idon ki nafisa.
Yayana ne daba zan zagesu ba wani kallo yayi mata yace ok tace kuma kudi zaka ban do da bakanan nayi lalurar kudi a bayan ka.
Yace idan na baki kudin za a zauna lafiya wani zaman lafiya idan baka daina bibiyan wanan matar taka ba mai busashen gaba ta kaduna.
Dariya maganar ta bashi yace ashe sai in nemo wace take ajike ku dinga jikani a tare da sabuwar da zan dauko.
Baka isa ba wallahi idan ma mafalki kake ka falka don babu zancen karin aure a gare ka don na shigo ke nan a gidan nan zaman lafiyan ka shine ka sallami fati shine zamu zauna lafiya don ni ka sani ban zama dako wace kishiya wallahi.
May ka rasa a gurina may kake nema a gurin wata mace wanda ni banda shi ko zaka kewaye kasan nan naku kaf ba zaka taba samun mai zubina ba.
Kaiko a Niger kaje a yanzu da wuya ka samo irina acan don haka kaba kan ka lafiya da zancen wata mace a duniyan nan.
Kai ya girgiza mata kawai shi dai bukata shi shine subar wanan zaman doya da manjan da sukeyi a gidan shi da ita na kwanaki da suke yi.
Kudin ta kara tambaya yace nawa ne tace dubu dari biyu ya mike zuwa wurin da yake aje kudi a gida ya kirgo ya mika mata ta fice daga dakin.
Kai ya girgiza yana mamakin halin Nafisa din da kanta kawai ta sani banda wani agaban shi yanzu ta aibanta diyan shi daya haifa da cikin shi.
Sai lokacin ya tuna da khadija yaja dogon nufashi ya sauke yar matsala ko tana ina yanzu waya sani.
Ya tuna wayan mu na karshe dashi yayi dariya tare da fadin yarinya zanyi maganin ki ne kwanan nan don ba zan tsaya jin haukan ki ba.
Sai dai matsala daya daya tsaya mai arai shine anya kuwa khadija zata iya zama da Nafisa jifa irin ikirarin da tayi yanzu akan shi.
Kada fa ya jawa kanshi wani sabon tashin hankalin da ba zai iya magance shi a gidan shi gaskiyan nafisa ne bata rasa komai ba a tare da ita namace da ake so namijin ya samu.
May kuma zai kai shi wani karin aure a yanzu ya ja wa kanshi matsala hajiya mamane ta fado mashi a rai yadda suka rabu da ita take ta nanata mai ya nemi son khadija a gurin ta don aure a tsakanin ba fashi saboda taga dacewan hakan a tare dasu.
Yanzu yaya zaiyi yace a ranshi shi dai gaskiya ba zai iya tsayawa wani soyayya ba a yanzu kan wata mace dole ne ya nemi shawaran Yusuf don yafishi sanin irin wa yan nan abubuwan.

Ina zaune dawowan mu daga lectures ke nan jikina ba dadi nake jin shi maryam bata dawo ba a lokacin sai four zata shigo.
Wayana ne ya dauki ruri a lokacin na duba mamud ne a layin sai da na dan ja tsuki na dauki wayan don ni haushin su nake ji baki daya yanzu na tsani kowa.
Bayan mun gaisa ne ya dinga min kamaykamay rashin zuwan shi gurina nace wanan kuma ai na saba idan da sabo mamud.
Ya kira sunana khadija na amsa yace a gaskiya yau nayi farin ciki da jin wani dan uwan ki ya kirani akan maganan mu dake.
Don haka yanzu zan daina wani daridarin da nakeyi akan ki in Allah ya yarda zantura magabata na suzo su gana da iyayyen ki akan maganan mu.
Nace ka dakata mamud ba yanzu ba sai na gama karatuna za fara maganan aure yace a, a haba khadija nace shine ra,ayina .
Yace to babu komai zan yi hakkuri ayi yadda kike so sai dai idan kin dawo zaki min iso mu dinga gaisawa da iyayyen ki don su san dani nace wanan ba matsala bane.
Mukai sallama ya kashe wayan yana mai jin dadi don gani yake kamar har ya mallake ni ko yanzu.
Nace wawa a fili kaje gaba ka nemi matar ka ba nan ba ina mai jan tsaki tare da gyara kwanciyana barci nake son yi a lokacin sai dai tunane ya hana ni.
Nace kuyi gaba yaushe kuka gama da matan ku na gida balle ku dauko wani wahala kuma tunowa da AA nayi tunda mukai wayan nan ban kara ji daga gare su ba kuma.
Kuma ban kara ganin ko daya daga cikin su ba don haka na dauka ya yi fushi da abinda na fada mashi ne ranan dama ya dauka ko ni kanwan lasa ce zai fada min magana son rashi in kyale shi don yana takama da kudi ko mukami.
Abinda ban sani ba ashe Yusuf da AA duk sun bi kowa nawa sun nuna kansu garesu wurina ne kawai basu kula

49 / 144

Chapters