ba.
Tana fadin haka tace nagode da kika bani lokacin ki kuma kika aurare ni da fatan zaki kula da abinda nace ma,assalam.
Tana fadin haka ta juya tafita daga dakin ajiyan zuciya na sauke tare da fadawa tunanen abinda tace min din.
Ya Amina ne ta shigo nake fada mata yadda mukayi da yar uwar Nafisa din tace ikon Allah Allah daya gari bambam ke nan.
Gasu uwa daya uba daya amma yanayin su ya bbambamta wurin hali ai gaskiya ta fada maki ba karya a ciki kjadija wallahi kija mijin ki a jiki yanzu ki nuna mai so.
Ba dai inda zaki yanzu kibar wa yan nan yaran wa wata ta rainar maki su da wani tarbiya na daban don haka wallahi khadija ki sa tsoron Allah ga alamarin ki ki bar wanan wautar da kike ki rugumi mijin ki da yayan ki kin dai ji abinda mama Tani ta fada maki ai.
Ga yara kamar diyan larabawa kyawawa dasu kamar mutum ya sace uban sai rawan kai yake yana alfahari da abinsa ko da kike cewa wai bai damu da yara ba wallahi nikan naga ya damu da wayan nan sosai.
Idan ya shigo ko hannun wa suke sai ya taba su kafin ya fito don yaran akwai su da shiga ido shiyasa mama tani tace a dan saka masu zuben azurfa don bakin mutane naji maryam tace zata nema masu sai ki tuna mata.
Hmmm nace nama rasa abinda zance sai na juya da fadin ya Amina ki duba kayan a fitar da wanda zasuyi amfani dashi yanzu zannuwa kuma sai ki cire min wanda kika ga ya dace saura a fitarwa laraba da Altine da mommy sai a cirewa hajiya mama ita ma.
Tace wanan aiki bari har maryam tazo don ba zan iya ba ni kadai wallahi kayan ne gasu nan kamar shago za a bude.
Gaskiya mijin ku yana son ki wanan buzuwan ne dai kawai da tai maku shamaki tsakanin ku da ba karamin abu zakuyi a gidan nan ba.
Wayana dake ruri ya dakatar damu na duba sai da na kalli ya Amina nace hajiya mamace fa ke kirana.
Na daga kiran da sallama muka gaisa tace kun tashi lafiya khadija ya su takwara na dasu momy ku da sauran su nace suna lafiya mama.
Tace dama na kiraki ne in tambaye ki may ke faruwa a gidan ku don Nafisa ta kirani ta kuma kira Alhaji a karo na farko ta kawo karan ku wurin mu.
Murmushi nayi nace mama may tace kuma mun yi tace eh to ke dai lafin ki shine wai kince zaki karbi girki yanzu shi kuma mijin naku wai yai maki abinda bai mata ba idan ta haihu.
Alhajin ya nemi layin shi a gabana ya kirashi yai mashi bayani yadda abin yake wai idan zata haihu jinga sukeyi ashe ya bata kudin komai da komai daya shafi haihuwa.
Yanzu kuma da taga a girin ki ba haka abin yake ba shi yayi komai bugun gaban shi shine take kiran shi da azzalumi da macuci.
Sai naki matsalan yace itace ta fara yin hakana yanzu kuma kema kika ce zaki rama nace hakana ne mama tace to kinga aikin gagawa inda yake kai mutum ai.
A lokacin ita gani take dama ne ta samu na yin duk abinda ta ga dama bata tunanen abin da zai je ya dawo gare ta yanzu gashi tayi a lokacin taji dadi yanzun kuma na wani yazo tana yin korafi.
Abinda nake so daga gare ki shine ki natsu don Allah ki dubi yaran ki kada ki biyewa shirmay ta ku koma daya da ita ki dauke idon ki ga komai da takeyi a gidan kinji ko nace naji mama na gode.
Mun gama wayan na kalli yaya Amina tace wanan bata da hankali wallahi yaya zaki kira sarakanki da wanan magana bayan baki da gaskiya ta ko ina.
Nace ya Amina wuyan sha,ani ke gareta ga wanda bai gane halinta ba idan tayi tana jin dadi yanzu ramawa ai sai taji zafi lokacin da ta karbe kudin ta wa ya sani.
Tace wanan ko yadda yai maki din nan yafi zafi ba don ko kudin daya bata masu yawa ne dole taji zafin ganin abinda ya sai maku don zaku dade kuna amfana dashi .
Ita karshe ma kila kudin a banza zai tafi gun bokaye da malamai nace tun yaushe wallahi ni abinta ma yanzu ya daina bani mamaki sam.
Ita fa yanzun na fahince ta gaba dayan mu bata son kowa ya rabe shi ne sai ita kadai ko uwar da ta haife shi tana kokarin nisanta shi dasu ne dan kowa bata son ya raba shi.
Yanzu ai sai dai ta mutu don karshen rabuwa har da rabo biyu a tsakani ai kinga dole ta ganku tare munyi hiran sosai karshe muka koma hiran maryam tana yaba kirkinta gare ni.
AA ne ya shigo dakin ya Amina ta fice wurin su momy yanayin shi ya nuna daga barci ya taso lokacin nace ina kwana daga inda nake bai amsa ba sai da yazo kusa dani ya lakutan min hanci yace .
Shine kika shayani jiya ina jiran amaryan jego tazo tayani kwana in sha karni murmushi nayi nace wane ni in ka ganin dakin ka mun yi arba,una ne.
Yace kai mata nace ai itace ta fara don haka kar kaga laifi na yace banga laifin ki ba ga hakan tunda bashi kike biyan .
Dan kallon shi nayi nace haka ka dauka ko yace tunda anci gashi zaki karba kuwa tunda kin iya daru ke ma.
Nace ni har wani daru gare ni ka san dai inda daru yake yace darun ki a cikin ruwan sanyi kike abinki babu fada balle hayani don haka yanzu nake tsoron fadawa tarkon ki.
Murmushi nayi nace sunan da na samu yanzu ke nan kuma aina gode tunda shedan mai sauki akai min.
Ya dan jima a dakkin muna magana akan sunan da taron da akayi muna kafin ya fice a gurina a falo ya samu Nafisa da yan uwanta zaune suna duban waya.
Jin motsin shi ya fito yasa su daga kai suna kallon shi Ihisan ne ta mike zuwa wurin shi uwar ta daka mata wani irin uban tsawa sai da yarinyar ta kado.
Da mamaki ya kalleta yace don may zaki hanata zuwa wurina tace don ni ke da yata ba wani ba yace ok ashe yar taki ce ke kadai kin san inda kika samo ta ke nan ?
Yau ka fada min abinda dana dade ina jiran ji daga bakin ka kamar yadda yan uwanka suke fada min game da yarana a gidan nan.
Fatiya ce tayi gyaran murya ta katse lazumin da take yi tace wanan wani irin abu kuke haka gabsn yara ko da yau kuke na kulluyaumin gidan ku babu zaman lafiya sai anyi fitina kamar kananan yara.
Yanzu ina amfanin wanan abin kece fa kika fara jan maganan nan ya baki amsa kince ina yafito kima kanki fada don Allah yaran ku girma sukeyi suna ganin abinda kuke yi.
Tace oya Ihisan jeki gurin Abban ki kinji yarinyar tana kallon uwar su don tsoro yace ta zauna abinta fita zanyi ya kalli nafisa yace kin kaini bango yanzu kan ya fita.
Tace ba laifin ka bane laifina ne dana yarda na nuna maka son kwarai har cikin zuciyata yanzun kam ya kare ai.
Kai Fatiya ta girgiza mata ta hau yar uwan da fada a cikin yare don laraba dake falon tana gyaran bangaren mu.
Zama tayi tana tunane a ranta bayan fitan shi wai itace kuwa Nafisa ita nafisan da suke rayuwa kamar ba gobe da mijin ta tana juya abinta yadda take so.
Ya gwada ma yar da tazo dashi gata har zuwa Ihisan dinta yanzun tana kokarin zama dodo a gare shi akan wata wai ita ake wa haka akan kishiya da take ma kallon bata kai mace ba.
Yau tana kallo ba dan ta rasa kudin yin sihiri a gareta tana ba kuma rashin masu mata aikin ba sai dai gani take abin baya tasiri a kan su ne yanzu gaba dayan su har samad din.
Maganar da zatai mashi da ya bata hakkuri akan shi yanzu kafin ta gama fadi ya bata amsa gaskiya dole ne ta kara danmara a gidan ta ta gasa masu kwakwa a hannun su.
Ya zama dole ta dauki mataki akan wanan yarinyar data shigo jiya jiya gidan nan tana kokarin ta taushe ta da karfi da yaji a gidan.
Kwana biyu ya Amina ta tafi sai momy da Altine momy ma sati biyu kacal Abba ya bata da kyat ya yarda tai muna satin biyun ta dawo.
Tafiyan ya Amina ya saukar min da kadaici sosai don kwana biyun da mukayi a tare ba karamin dadi nake ji a raina ba.
Wucewan ta yasa momy ta dawo dakin ita da Altine muna zama Laraba ko ance ta shigo bata sake jiki a cikin mu sosai tafi gane ma zaman falo ko tana wani aikin.
Gashi idan tayi wankin yara bata shigowa sai kayan sun sha iska take dawowa part din don dai kawai tsaron lafiyan su da take yi.
Na samu hutu sosai don idan suna falo barci nake samu inyi sosai sukan kyale ni har lokacin dana tashi ko yaran suna neman nono.
Maryam ko cewa nayi ta bude kayan ta dauki duk abinda ranta ke so ba wani kaya ta dauka ba sai turmin zani guda daya wai shine ya bata sha,awa a cikin kayan.
Madam kafa ya kiya har lokacin tana kwance a asibiti tana jinyar kafan basu sani ba ashe daurin da akai mata bai dauru ba da kyau dole aka samce aka gyara wani sabon dauri din iya wuya ta ci shi.
Ga rashin ganin kulawan da take Nafisa batai mata da takan shigo sau daya ta dubata har ta koma bayan kwana daya take shigowa gidan.
Ya kai yanzu sai ta share kwanaki bata leko ta ba sun dinki da sabuwa aminiyar madam din na baya da sukai fada tana kwance labari yazo mata.
Ta kudurta a ranta zatai wa Nafisa magana akan hakan duk ranan da tazo dubata din sai bayan kwana uku tazo a gurguje tana sauri tana wani sham kamshi.
Bayan sun gaisa take fadin akwai ida zata sauri take yi madam tace dama ina son magana dake don naji wani maganan da tsamace shi ba a gare ki Nafisa.
Tana wani taunan chewing gun tace ins jinki ai yanzu nafisa ki rasa wanda zaki hurda dashi sai sabuwa makiya na zaki dinki da ita.
Nace tace may ye a ciki madam business ne fa dama tsakanin mu ba wai haka kawai kike min ba yanzun kuma kina kwance kina jiyan zama kike son inyi kar in nemi wanda zai haska min hanya ko may ?
Ita ma sabuwa abinda kike min take min a yanzu kema idan Allah ya baki lafiya sai mu dora a inda muka tsaya ko ba shike nan ba.
Matsalan ku da sabuwa ku ya shafa bai shafeni ba kowa kudi nake bashi yadda ya bukata yaje min guri ko ya rakani inje.
Madam ta ce haka kikace tace ai haka maganan yake madam sai idan kin so juya shine a wani tsigar kuma wanan kam.
Tana fadin haka ta aje mata dubu biyar a gefen filon ta tace sai anjima don ni akwai inda zan tafi daga nan kallo madam ta bita dashi tana kallon takon ta tare da kutawa .
Ta raya a ranta sai ta dauki famsa in har ta mike akan Sabuwa da Nafisa kan abinda sukai mata din tace ai in kun san wata baku san wata ba dani kuke wasan.
Tana fita ta samu sabuwa a mota suka dauki hanyan zuwa jos ranan suke son zuwa su dawo a ranan kuma a gida dai ta bar yan uwanta da yara tace dasu zata dan je wani wuri ta dawo.
Bayan fitan da kamar awa daya sadiya ta fara kuka sunyi lalashi taki yin shiru tun suna lalashinta da girma da arziki har abu yafi karfin su.
Sai ga Fatiha dauke da ita ta nufo ni ina falona lokacin ina cin abinci tace Dija ko zaki duba muna yarinyar nan uwarta ta fita yau dai sai kuka take muna mun rasa gane kanta.
Karbar yarinyar nayi daga hannun ta ina lalashi ta muka samu ta dan yi shiru nace ina abincin ta tace bari ta dauko.
Ta dawo dauke da feeder ta ta miko min a na dan bata taja kadan sai kuma taci gaba da kuka nace yau halima lafiya kike kuwa na fara dan taba mata jiki zuwa kai naji kan yai zafi sosai.
Na dago nace mata ina ganin yarinyar nan bata da lafiya ne yau ina maganin ta yake a bata tace sai ta tambayi Yanyala.
Ta fita da yarinyar kasa cin abinci nayi na wanke hannu na samay su a falon suna tambaban wanda zasu bata daga ciki.
Karba nayi na karanta na mika masu paracetamol si bata ina tsaye ina kallon yadda suke bata maganin sai kuka yarinyar ke yi.
Su goyata nace ko zata yi barci Yanyala ta fara fadin ko sun goya ta kanta ba tsayawa yake yi ba ai nace haba dai sai kusa abu ku tare kan ta baya mana.
Fatiha ce ta goya ta na nuna mata yadda zata tare kan sai kan nata ya tsaya tana dan jijigata har tayi shiru barci ya dan dauke ta nace Allah ya sauwaka.
Na koma part dina na shige bayan kamar rabin awa ta falka kuma kukan ta muna ji har part dina muka fito dasu momy falon muka samay su.
Nan ma munyi munyi taki shiru momy tace su kira uwan mana wai sun kirata wayan baya shiga sai momy ta kira layin AA take fada mai abinda ke faru yace gashi tafe.
Kafin yazo yayi ta gwada layin ta ana fadin not reachable sai ya kashe ya iso gidan ya samay mu a kanta ya tambaya may ke samun ta ne ?
Suka ce haka kawai suka ga ta fara kuka momy tace jikin nata ai ya gashe ma ya dago yana tambayan Yanyala ina Nafisa taje ne tace tace masu zata nan ta dawo ta fita.
Momy a shirya mu kaita asibiti yace a dubata momy ta shiga ta fito tare da yanyala suka tafi likita yace zazzabi ne da kuma karancin jini ke damun ta.
Take aka bada gado ranshi idan yai dubu ya baci sai gwada layin ta yake faman yi baya zuwa shi ya dawo gida daukan abinda zasu bukata asibitin.
Yana shigo yace wa Fatiya bata dawo ba tace ,a,a har lokacin bata dawo yake fada masu an ba yarinyar gado wai bata da jini a jikin ta.
Tace duk kwanan tun da suka dawo gida yarinyar bata cika lafiya ba sosai ga uwar bata zama koma ta zauna ba nono take bata a kan lokaci sai taga dama.
Ya shigo wurina yana fada muna an aba yarinyar gado mukai mashi Allah ya sauwaka ya dauki abinda zai dauka ya bar gidan ranshi a bace.
Tara ya shigo gidan ya kara tambaya still bata dawo ba ya fita ya kira wayan ts yafi a kirga bai samu layin nata ba har wanan lokacin.
Altine dasu Fatiya suka shirya zuwa asibitin don kaiwa su momy abinci tunda har wanan lokacin basu dawo gida ba shir shiru har guraren sha daya da rabi suka shigo har lokacin ba Nafisa ba labarin ta ba a san inda ta tafi ba.
Tun yana jin haushi har ya koma fargaba idan ba wani abin bane ya samay ta can wurin bakin yawon ta don bai dauki wanan abin na kai sake ne ba.
Inda momy tayi sallah ta kira hajiya mama tana fada mata halinda ake ciki ranta ya baci sosai ta kirashi a waya tayi mashi tas ranan .
Sai ga su Altine sun dawo muna da labarin har yanzu ba a ga Nafisa kuma wayan ta baya shiga idan an kirata nan muka zauna jigun jigun damu a falona.
Nafisa sun samu layi a gurin boka haka yasa suka bi sahun masu jiran su gana dashi din sai biyar suka samu ganin bokan shirgegen mushiriki dashi yana zaune daga shi sai lagen bakin zanin daya yafa a jikin shi.
Ta fara bayani ya dakatar da ita ya kora masu abinda ke tafe dasu Nafisa irin su take so dama tace hakane boka shine mukazo wurin ka idan da taimakon da za a bani kanta.
Boka naki jinin in bude ido in ganta a gidan nan yace kada ki damu tunda kinzo nan zamu diba mu gani a cikin karfin tsafin mu.
Yadan yi surukullen shi ya dago yana dubanta tare da fadin kai haba dai gaskiyane kina aiki kamar bakiyi don wanan yarinyar itama hatsabibiyar kanta ne sosai.
Nafisa tace haba nikan na sani idan ka ganta kamar ta Allah da ita ni dama nasan ba banza ta barni ba ya kada kai yace a, a ba yadda kike nufi bane.
Ita irin masu baiwa din nan ne