asha ai zomu zauna zomu saba sai hakkuri da mun dauka kece babba a gidan don haka zatai maki biyayya a gidan amma tunda kince kowa halin sa yafida shi shike nan.
Wata daga cikin su ta karbe da fadin ai biyayya yazama dole gare ta don mu ta samu a gidan don haka ita ta zama yar bi a yanzu.
Gyara dai, maganan ki don kun riga da kun gama magana kowa tashi tafidda shi dama haka zaman gidan miji yake ai, Allah ya bamu alheri ta mike tare da cewa sauran ku tashi mu tafi.
Kowa daga cikin mu ya mike don barin dakin mun kai kofa mukan har mun fice daga dakin sai wata daga cikin su tace ni fa banga mutum ba a nan .
Sauran suka amsa da ai shine duk da tana rufe amma kamar ba wata mai fasali bace daga cikin mu wata ta amsa masu da fadin ahaka kuma mijin ku ya gani yace yana son ta.
Nafisa zatai magana madam tayi saurin kwabarta da cewa zancen ya isa haka shi dai ya gani yace yana son abin shi ai.
Mu dai Allah ya bada zaman hakkurin ki dai kau da kai kawai tayi hakane don kare Nafisa daga sakin layin da take son yi a gaban kowa.
Don ko a cikin kawayen nasu akwai munafukai nan take Nafisa ta gano maganan madam din sai tayi shiru.
Muna gama fita daga dakin wata ta sake cewa amma dai da kuke wanan maganan kamar kallon tsoro kukai wa amaryan nan ?
Saboda may kika fadi haka tace humm ku baku lura da takon ta ba da tsayin ta kafarta mafa farine sol ji yadda ya sha lalai yana daukan ido anya ba boyon kama tai muna ba ?
Koma dai may nene kinsan dai mun mata tazara ko sai dai bi don gidan nan sai Nafisa suka saka ihu gaba daya su dake wurin.
Washe gari sai ga su fauziya sun shigo da kayan karyawan mu ruwan zafi ne da gwangwanaye madara milo suga da liptop da kuloli dake dauke da kwai da irish a ciki sai turiri suke yi.
Nan aka shiga gaidasu da sa masu albarka ita ko matar gidan ko bude part din su basuyi ba sai bayan mun gama karyawa ne ta aiko muna da wani bussashen doya da bai soyu ba wai shine abin karyawan mu bayan makudan kudin da ta karba a wurin AA din tace za aiwa baki abincin dashi.
Tace ai yan Niger basu da abincin da yafi doya shiyasa na ce a soya masu doya busakakai suji dashi yan kauyen bazan dasu.
Ana shigowa dashi su mama Tani sukace a mayar mata sun koshi don sun karya ko sai da suka gama shiryawa ne suka fito dani zuwa dakin da su mommy suke ciki mun samay su, suna karyawa suma nan dai suka tare mu akai gaishe gashe a tsakani.
Mommy ta tare mu da fara,an nan nata tana ba su mama hakkurin abubuwa da ya faru a gidan mama tace ba komai irin su Nafisa haka suke dama zafin kishi da zugin kawayene ke wahalshe su.
Mama da ya Amina suka kara danka wa mommy amana don shiga cikin su yanzu danayi sai alokacin nasan su Binta da Zainab na gidan da suka shigo daga gidan da suka sauka suna aikin abincin taron bakin.
Nan suka tasani gaba wai sai in bude fuskana su gani mama tace ai zaku ganta don ta zama naku yanzu mintsilar da Binta ke min yasa na jawota zuwa jikina muna maganan siri da ita.
Ba wanda yasan da shirin da suka zo ashe har walima suka hada sai dai kawai ganin mata na taruwa a gidan don zuwa yin walima.
Nafisa dake daki labari ya samay ta tafito da zuman fada don may mata zasu taru mata a gida bada sanin ta ba Fauziya tace malama gyara zancen ki dai gidan ki ko gidan dan uwan mu.
Mommy ne tafito ta kara kwantar da fitinan ta koma daki da tarin bakin cikin da ke cin ta a ranta nan dai malam da aka gaiyato suka fara gabatar da waliman wanda wa,azi ne akan aure sai hakkin miji ga matansa da hakkin mata a gun mijin ta.
Inda nasihan ya shiga mutanen dake wurin sosai anci an sha a wurin an raba calander dake dauke da ayatul qursiyu da suna na dana AA da ranan auren mu.
Bayan an watse daga walima ne kannen ango suka sai baki sun bada abinda ya sawaka daga garesu gwagona da mukazo da itane ta yaye gyalen dake rufe da fuskana.
Aka sa guda nan maza suka shigo abokan ango suka dinga zuba kudi Nafisa dake dakin ta kamar ta kama da wuta a gidan ta rasa yadda zatayi sai surfa ma AA zagi da yusuf da yan uwan shi take yi.
Uku daidai yan uwana suka fara shirin tafiya zuwa gida ina ganin haka na shiga damuwa sai da suka ce zasu bar muna yan matan anan su kwana min biyu na sake da zasu tafi ne sukace bari suba da sako daga nan ne ban kara ganin su ba har maryam din duk sun tafi.
Shiru ni kadai a dakin da zaman ya isheni ne na mike na shiga bandakin da niyar dauro alwala sai kuma na canza shawara na hada harda wanka nayi.
Ina nan zaune ni kadai a dakin gurin da na sallamay sallah magariba sai naji an turo kofan Binta ne da Zainab suka shigo dakin a lokacin.
Dauke da kayan abinci a hannun su kallo daya nai masu na kawar da kaina gefe Binta na dariya ta aje kayan tana fadin Amarya kina kamshi.
Nace a, a ina wari yanzu ai nasan zama na daku wallahi wai kuna garin nan amma kuka share ni haka kamar baku damu dani ba.
Ke nan kuna bayan dan uwanku kike nufi ko may dariya suke min suka samu wuri suka dan zauna zainab tace wallahi ba share ki mukayi ba khadija.
Aiki ne yai muna yawa can aka kwashe mu aka kai gidan anty maimuna wai mu dinga ma bakin da suka rakoki abunci baki ga yadda muka ji haushi ba wallahi.
Yanzu jiran mu akeyi wai muje gidan mu hado kayan su anty Fauziya yau anan zasu kwana tare dasu mommy tunda an rage yawa a gidan.
Da sauri nace don Allah kada ku tafi dukan ku don wallahi tsoro nake ji zaman nan ni kadai ya ishe ni wallahi.
Da sauri Binta tace haba khadija tsoron may kuma keda gidan mijin ki wallahi ki fitar da tsoron nan tun yanzu a ranki don wanan kishishiyar taki idan ta gane haka zaki sha wuya a wurin ta gara tun wuri ki nuna mata kefa ba kanwan lasa bace.
Nace ni wanan bata a gaba na yanzu amma dai kin san abinda yayan ku yai min bai kyauta min ba wallahi.
Haba khadija kada kice haka mana mijin ki ne fa yaya Abdulsamad yanzu komai yayi maki asai ki yafe mashi ko tunda kun zama daya ke dashi yanzu.
Wani kallo nayi mata nace eh gaskiya ne zainab kin nuna min bayan dan uwan ki kike tun yanzu tace ba hakana bane wallahi gaskiya ne dole a fade ta.
Nace gaskiya akan auren dole don dole yasa iyayyena sukai min a kan shi ba da sanina ba komai ya wakana shine zaki wani ce wai mun zama daya yanzu.
Binta ta karbe ni da cewa dama na fada ma hajiyan mu ba da yardan ki yace wai kin yarda dashi ba har kun shirya mu har muna fushi dake akan kin boye muna komai dake tsakani ku dashi sai dai kawai muji aure daga sama.
Binta wai may yasa ke baki da hankali ne don Allah maimakon ki bata hakkuri ki kwantar mata da hankali zaki kuma zo kina maganan abinda ya wuce.
Binta ta turo baki tana fadin dama ai ke ko yaushe ne magana sai kice ban fadi ba daidai ba tana fadin haka ta mike tana fadin ida kin gama ki samay ni waje.
Khadija sai mun dawo ko ince sai da safe mu hadu idan mun shigo kafin mu wuce makarasa maganan mu tana fadin haka ta fice daga dakin.
Zainab ta juyo inda nike ta dibeni tana fadin don Allah khadija rabu da mahaukaciya nan Binta kin san girman ne kawai badon ta kai ba.
Ban mata magana ba don ina ganin ba sona take ba dan uwanta kawai take so mikewa tayi tabar dakin .
Mikewa nayi na ninke salayan da nake zaune akai na dauko wayana tare da kunna kira,a a ciki turare na dauko na feshe ko ina dashi kamshi ya gauraye dakin har falona na koma na kwanta batare da na bude kulan abincin da suka shigo min dashi ba.
Kwance nake sai dai ba barci nakeyi ba ina bin kira,an a hankali idona suna a rufe luf nayi hakan ne don in kawar da damuwan dake damuna a lokacin.
Duk da kamshin dake tashi a part din nawa ina shaka ina jin dadi a raina amma hakan bai hanani shako kamshin turaren AA dayafi amfani dashi ba ko wani lokaci.
Banyi shakkan jin haka ba don a cikin gidan shi nake yanzu don haka ban bude idanuwa na ba har lokacin da nake jin kamshin na karuwa a hancina.
Dan babban yatsan kafana na dama ya kama yaja a hankali zubur na bude idona tare da mikewa zaune AA nagani zaune a gefena.
Cikin wasu fararen shada sai maiko su ke daukan ido da sauri na mike zaune ina jawo hulan da na saka akaina ya zamay na barshi saman filo.
Murmushin shi mai tsada ya sake min tare da mikewa daga inda yake zaune yana fadin kinci abinci kuwa ?
Shiru nayi ban bashi amsa ba sai sakon harara da na aika mashi daga inda nake zaune din ya sake cewa wallahi yunwa nake ji khadija tashi muci abincin nan.
Tsam na mike na nufi falo na zauna nan tare da barin shi cikin dakin can ya fito falon ina zaune ya kalleni bai min magana ba yasa kai yafita daga dakin.
Yana fita nabi bayan shi da kallo tare da jan tsuki sai kuma na dawo da kallona falon ina kallon yadda aka tsara komai gwanin ban sha,awa a raina nace dama ace da wanda nake so yake sona ne falona yake haka danafi kowa morewa a duniya.
Can sai gashi ya dawo dakin wanan karon ya sauya kayan dake jikin shi zuwa na shan iskan maza na zaman gida.
Kallon na yayi na sauya kayan jikina zuwa rigar barci saidai na dora zani a saman kayan ya rufe min daga sama zuwa cinya na.
Kamar badani yake magana ba yace ki tashi ki dauro alwala kizo muyi sallah godiya ga ubangijin mu da ya nuna muna wanan ranan gare mu.
Ai kasan ban sallah sai dai in a gidan ka zan koya yanzu dan dariya yayi a baiyane yace a iya sanina dai ba lokacin fashin sallah ki bane wanan lokacin .
Au sa idon ka da shishigi har yakai ka ga sanin lokacin fashin sallah na ashe sai yanzu na kara sanin kokai waye .
Yace ni waye cikin rankwafowa inda nake kwance ina kokarin zama zaune nace mugu mayaudari maciji wanda bai iya gina ramin kan sa.
Wai duk ni daya ke da wanan sunan yau khadija nace sunan kama yafi haka a wurina indai kace shishigi ka iya.
Kara matsowa yayi kusa dani ta yadda zamu iya jin numfashin junan mu tare da dora hannun shi saman kaina nayi saurin kaucewa daga tabanin da yake yi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zaune yake ya harde hannayen shi saman kitjin shi yana sauraren bayanin da Yusuf yazo mashi dashi na tafiyan su mommy zuwa Minna gidan mu.
Sai baysn ya gama bayanin ne ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin ban tsamanin abin zai zo da sauki haka ba Yusuf ne ya dan kalle shi tare da fadin don baka san irin yadda mukai tsaye dani da mommy ba har haka ya faru ko ?
Kallon Yusuf din yayi yana fadin kasan wanan auren da zanyi naku ne kaida su momcy din da mama so don kun wahala ai wanan ba komai bane ko ?
Au mune ma keda auren ke nan ba kai ba yace Abdulsamad sai kuma ya kasa magana ya girgiza kan shi cikin takaicin shi tare da mikewa tsaye don ya bar office din.
Juyowa yayi ya kalli Abdulsamad din yace ban ganin laifin Khadija har kullin don ta karanci ko kai waye kalamin ta bai min zafi a kan ka don halin ka ne take fadi ba sheri ciki .
Kai ya rausaya wa Yusuf din tare da fadin zata ko sha wahala idan tazo min a haka ka sani dariya Yusuf yayi yace a naka tunanen ke nan amma ni banga wani wahalan da zata sha ba don tana da basira magance matsalan ka.
Ya fada yana kallon shi ido cikin ido tare da dan buga tabur din shi da hannu har yakai kofa yace sai ka zauna a cikin shitin zama angon Khadija mijin buzuwa.
Harara ya bishi dashi ya fice ya bar mashi office din a hankali ya sauke ajiyan zuciya ya kalli files din dake gaban shi ya ja tsuki.
Tun fitan Yusuf wurin shi bai iya aiwatar da komai ba wunin ranan hudu daidai ya mike don barin gurin zuwa gidan shi ya huta.
Shigan motar shi gidan yayi daidai da fitowan Nafisa zuwa unguwa kallon ya bita dashi yadda tasha gaye kamar mai zuwa gasan kyau.
Sai da tazo inda yake yana fitowa cikin motar shi ta tsaya da motar ta da sai kidan yaren su ke tashi a ciki tana fadin lafiya ka dawo yanzu ?
Lafiya ya bata amsa dashi tare da fadin ina zaki a wanan lokacin yana kallon agogon hannun shi fita zanyi zuwa gidan madam akwai abinda nake son yi a can ne.
Tana fadin haka taja motar ta don barin gurin batare da ta saurin abinda zai fada mata ba ta sake mai horn din motar tayi gaba.
Binta yayi da kallo kawai yana girgiza kan shi ya sa kai zuwa cikin gidan nashi a falo ya samu yan uwan ta zaune sun dora butan shayi a dan karamin abin da suke dafa shayin dashi sai kidan yan kasan su ke tashi a falon .
Ta bayan kujerun falon yabi ya raba don takaicin da yake na ganin haka a gidan shi kuma bai iya yin wani abu akai don ba fasawa zasu yi ba.
Sai da yakai sama ya tura kofan dakin ya shiga dakin na nan yarda ya barshi yau kwana uku ke nan yana son ya samu time ya gyara dakin bai samu ba duk dakin a hargitse yake mai.
Zubewa yayi saman gadon shi don ya huta sai karan kira ya shigo mai a waya a kasalance ya mika hannu yana daukan wayan.
Mommcy ya gani a wayan yasa shi dana received da sauri tare da sallama ta amsa mashi tana fadin sun sauka lafiya tun dazu.
Yace Alhamdullahi tace tafiyan namu akwai nasara sosai a cikin shi don babu wani miskilan da muka samu sai dai ita khadija din da taso ta zautu lokacin da ta ganmu.
Babangida yakama ace ka zama namiji wanda sai ya nemi so a wurin mace kafin wani abu ya wakana a tsakanin ku amma sai gashi munje ta nuna muna ita still bata san da zancen ka ba balle na zuwan mu.
Da kyat na samu na shawo kanta don kada yan uwan tafiya na su fahinci hakan zancen ya kama yawo ga yan uwa har maganan ya koma kunnen matan ka duk da nasan cikin kin mu babu wace ba ta jinin ka bace.
Mommy ita fa wanan yarinyar haka take da rikici ba zata taba kwantar da hankali tayi abin mutane ba a daidai sai takawo matsala a cikin abu.
A a babangida ba haka ake neman aure ba kamar abin wasa ko wani abin saye can ina son kasan wanan auren ba fa tursasa ma zamuyi kayi shi ba don ra,ayin mu.
Yarinyar nan tana ikirarin baka taba nuna mata so ba daga gare ka yanzu kuma na tabtar da hakan don kasan suma khadija tayi lokacin da ta tabbatar da zuwan mu akan maganan ku.
Haka ya nuna min khadija ba kudi ko kyau ko nasaban ka ya damay ta ba illa soyayyan ka take nema a gare ka.
Mommy suma tayi a kaina don ta gan ku ya tambaya cikin mamaki mommy tace wallahi shi nake son ka gane khadija ta daban ce.
Da wata ce murna da farin ciki zatayi don abinda mukazo mata dashi hankalina ya tashi da kalaman yarinyar da take rokona akan na lalashe ka kajenye kudirin auren ta akan ka.
Na lura mahaifan ta nason mata dole ne ga abinda bata so sai da muka zauna da uban na fahinci halarci yai muna na ba da ita don Amina da muke zaune da ita cikin salama anan .
A yadda ya nuna muna yayi haka ne don dankon zumuncin dake tsakanin mu ya karu mutuncin hakan suka duba zasu ba da