na manta da zancen Maryam din naci gaba da harkokina a gidan zuwa hudu sai ga maryam din ta shigo.
Bayan mun gaisa ne nayi mata jagora zuwa dakin Nafisa tayi mata gaisuwa inda muka samu suna ta faman shirin tafiya washe gari zasu tafi.
Muna fitowa maryam tace kinga mu kuma sai mu dora idan sun tafi nace wai ke da gaske kikeyi ne don Allah tace insha Allah sai munje munga gidan su muma don mu maida martani.
Ai shege akewa bai rama ba mamaki zamu basu don nasan idan kin fadawa mijin ku ba zai yarda mu je ba don haka kyaleshi kedai kawai ki tambaya muna yadda ake zuwa garin.
Haka akayi dan a cikin hikima na tambayi maigidan yake fada min duk yadda za ayi aje garin washe gari suka tafi tunda asuba mu kuma muka fara shirin tafiya don anty Fati ma tace zata tafi tunda gulma ne.
Momy na fadawa shirin mu tace gata tafe dama tana tunanen yadda za ayi sai gata ta shigo garin da yamma da sunan gaisuwa tazo yi a Abuja.
Muma tunda asuba muka dauki hanyan doso da motar Suraj ya hada mu da sojoji guda biyu muka tafi tun muna tafiyan dadi sai gashi ido ya fara raina fata.
Kowan mu ya gaji da wanan tafiyan shiru mukayi dukkan mu a motar sai da muka fara shiga garuruwan kasar ne muka fara magana muka dauki hanyan tawa inda acan ne zamu nausa a sahara zuwa kauyen nasu.
Ga namu watau mun dauka tafiyan mara nisa ne sai gamu har guraren uku bamu kai garin ba sai da muka bar gari da nisa muka iso garin.
Da tambaya muka samu wanda yasan gidan har akai muna kwatance munga karyan buzaye a wanan garin kowa da dan kitso a gaban kai mazansu da matan su da shiga irin tasu.
Kofan wani gida shi ba gidana ba full ba a kuma kiranshi da bukka gashi nan dai ga kamar shi sai da na raina ma AA ba buzuwa ba kawai.
Yana zaune suna karban gaisuwa muka iso yabi motar da kallo shida yusuf ne yana mamakin motar don daga Nigeria take kuma lamban depences na Nigeria ne.
Momy ce da ta fara fitowa dauke da daddy a hannun ta yana kuka yasa AA dan zabura daga inda yake zaune sai gamu muna fitowa daga cikin motar.
Mamaki zaiyi ko takaicin zuwan mu na wanan kasadan shigo wanan kasar da mukayi hikiman
Zuwa da momy ya taimake mu don bai iya muna wani magana ba a wurin sai cewa da yayi momy kune tafe haka ?
Bayan mun gaisa ya nuna muna hanyar shiga cikin gidan muka nufa kai tsaye kowa na baza idon wurin kallon kwam suna ciki da mutane da ba yawa a gidan.
Mukai sallama sai da ta girgiza momy ce dai gaba sai fati maryam na bi ina bayan su gaba daya matan dake gidan suka dawo da kallon su gare mu.
Fatiha ce tayi karfin halin iya magana tana fadin lalai marhabin kune tafe ashe kuna hanya bamu sani ba tana taron mu a cikin jin dadi.
Ita ko nafisa tayi mutuwan zaune ta zuba muna ido ana kokarin shimfida muna ta barma ina kallon maryam bata zauna ba sai da ta goge tabarman da aka shimfida muna don jan magana.
Nan aka debo muna wani jan ruwa a tukunyar kasa aka kawo muna kowan mu kallon ruwan yayi ya kawar da kai.
Za,a ba dan wurina dake rikici ruwan maryam tayi saurin fadin a,a aida ruwan mu a jakka ta dauko ta mika ma Fatiha fatihan tace ai nasan ba zaku iya shan ruwan mu ba.
Gaisuwa muka fara tare da tambayan mu yaya hanya nice nace ina mama mu gaida ita aka nuna muna wani bukka babba tana ciki Fatiha tace mu zo mu gaisa da ita.
Kai maryam da ta kallama ita da fati suka shiga bukkan sai ni da momy ne muka tsaya cire takalman mu muka shiga dakin .
Mun gaida matar da wahala ya sata tsufan dole tare da mata gaisuwa don bata jin ko zo in kashe ka da hausa sai yaren su na buzaye.
Bamu dade ba muka fito don zamu juya sai lokacin nafisa da bayan gaisuwan da mukayi bata kara magana ba tace ashe yanzu zaku juya ?
Eh don ba kwana zamuyu ba anan nice a kofan su muke magana da Fatiha nake tambayan ta ko zamu samu ninon rakumi a wurin su.
Tace sosai kuwa ai yanzu lokacin sa ne ma na bata kudi akan a samu muna idan ba zai dauki lokaci ba tace nan bayan su akwai inda zata samo muna.
Shije ya dan bata muna lokaci har muka dan makara mun fito zamu tafi inda naba uwar su kudin mu na Nigeria masu yawa da su Fatiha sai godiya suke zabga min muka fito .
AA da ransa in yai dubu ya baci yace ma momy badai juyawa zaku yi ba yanzu momy tace munzo munyi gaisuwa ai gara mu juya komai dare insha Allahu yau gida zamu kwana.
Baiso tafiyan mu ba yaso akaimu cikin gari wai mu kwana da safe mu dauki hanya sai sojojin nan sukace ba damuwa tunda muna tare dasu ai don suma basu son su kwana a kauyen.
Bamu muka kawo Abuja ba sai daya na dare suka sauke mu gida suka tafi wanka nayi na rama sallah dake kaina na kwanta.
Don gajiyan da muka debo sai dai AA yana kiran mu har muka shigo abuja hankalin shi ya kwanta da safe ban fito ba don gajiyan da muka debo acan ko tsaranban da muka saya ban bi ta kanshi ba.
Kwanan shi uku da akai sadakan ukun ya dawo a cikin dare sai dai ba kamar namu tafiyan ba na dare sosai jin dawowan shi ne na fito don har lokacin ina da gajiyan zaman mota a jikina.
Yana waya na shigo ganin yana waya yasa nayi mai sannu da zuwa na juya da zan fita ne yake cewa dakata na juyo dani yake din yace hada min ruwan wanka.
Banki ba na hada mai na fito na samu ya gama wayan yace ku yan kasada may yakai ku Niger ne da mamaki nake kallon shi nace kai may yakaika don Allah ?
Ni kike tambaya nace naga dai abinda ya shafe ka ya shafe mu ai ko zuwan namu kuma laifi ne idan kuma bamu je ba a ce bamu tafi ba don bamu damu ba tunda ba uban mu bane ya mutu.
Bakin nan naki ai sai ke ni dai ban son hakana kuma banji dadin zuwan ku ba tunda baku sanar min ba idan muyi laifi kayi hakkuri bamu sake hakan na fadi tare da barin dakin waini nayi fushi.
A raina nace mun dai je munga abinda ake boye muna din idan shine ba a son mu gani ashe bayan tafiyan mu sai da sukayi kaca kaca da Nafisa a can .
Wai ya munafunce ta bai fada mata zuwan mu ba sai ganin mu tayi kwatsan yaja mata abin fada a gurin mu ke nan shima ya rufe ido yayi mata cin mutumci a gurin sai da aka raba su.
Shine karin takaicin shi damu fati ma da ta shigo sai da sukayi fada tace baka son muje ka hada mu yace gulma dai ya kaimu tace in ma gulman ne mun dai tafi din.
Haka yai ta shan mur shi kadai ba wanda ya kula shi a cikin mu dama momy ta koma tin kan ya dawo don haka bai samay ta ba a gidan.
Ya gaji donn kan shi ya sauko ta nemi shiri damu ni kuma na hau ranan nice da girki sama sama nake dashi na aje mai abinci zan fita yace wai ke mai kike shawa wanan kamshin ne haka.
Nace kamshi akan may inma kamshi ne aikai ka fara sha muda muka sadaukar da ran mu muka bata lokacin mu zuwa maka kara baka gode ba sai ganin laifin mu .
Ashe zuwa gidan kishiya baida dadi ka bari taje namu gidajen sai itane don munje mata abin arziki zakace bamu kyauta ba.
Kin san yadda mukayi da ita dans san taje nifa akan yaran da kuka wahalar min nake wanan ba don komai ba in ma ba gaisuwa kuka tafi ba ai kanku kukaiwa.
Ni ki zauna ki zuba min abinci naci don yunwa nake ji yanzu nace bakai bane a raina, ina zubawa ne yake fadin ya kamata ku koma haka na don karatun yaran nan kada ya lalace.
Kofa wata daya kwakwara bamu cika ba ina gani gaskiya nikan ba yanzu zan koma ba sai nayi wata uku a gida kafi in koma wanan kasan.
Zance dai kike so don naga ke karatun yaran bai damay ki ba ko kadan in ma ya damay ni sai na tauye kaina don su.
Ban kara magana ba na zuba naja kujera na zauna tare da fadin yarinyar da zamu da ita tananan ta iso yace ok Altine din ba zata koma ba ke nan.
Nace naji kamar momy tace aure zata daura fa don tunda muka dawo ta bugo min waya sau daya sai ko da mahaifin nafisa ya rasu ta kira bata kara kirana ba.
Yayi murmushi yace ita tana ganin tayiwa kanta mafita ke nan duk da dai ba a hana aure amma auren ta nawa idan tayi wanan don tun ban karasa cika saurayi ba take aure.
Don ma bata haihu da yawa bane jikin ta bai nunawa aida yanzu ta ragwabe suma mazan dake auren nata ne basu da aikin yi ai.
Nace bakaji masu iya magana sunce guban wani zuman wani kai ke ganin ta ta tsufa sukan shar suke ganin ta ai.
Hiran yasa gaba dayan mu muka mata da zancen fushin da mukeyi da juna muka buge da zancen Altine har wani lokaci.
Zaman mu da fati akwai fahinta sosai don ina guje ma abinda zai kawo wani baraka a tsakanin mu don haka ne muke zaune lafiya da ita bani shiga zancen ta idan ba itace ta sakani ba.
Satin nafisa biyu ta dawo abuja da yan uwan ta gidan ya koma cike kuma sabanin da muke mu kadai sai yaran mu nidai ba a samu matsala dani ba sai dai da AntyFati ne suke dan tabawa akai kai.
Sai da maigidan ya dan tsawata masu kan hakan suka dan bari amma suna dan tabawa a boye don Nafisa ta tsani zaman fati a Abuja.
Na fito da safe mukai kicibis da wasu mata sun fito gurin nafiss ban son tankasu ba sai da naji dayan tace min hajiya khadija mun tashi lafiya ?
Na dakata ina kallon matar kamar na taba sanin ta sai tayi murmushi tana fadin nasan baki gane ni ba ko ?
Nace na dai sanki amma wallahi na manta inda nasan ki tace kin manta da madam mai zuwa gurin Nafisa a baya can.
Nace a, a mama kece wallahi mun dade bamu hadu ba tace wallahi kwanaki nazo akace yanzu waje kike zama da maigidan.
Nace hakane yaya bayan rabo tace sai Alheri dama ina tason mu hadu in rokeki gafaran akan abubuwan da suka faru a baya.
Mota zan shiga don har na bude ne na tsaya muna gaisawa dasu nace baki min komai ba mama in makin min to na yafe maki.
Sai ta fara sharan kwalla nace tafiya zakuyi ne in rage maku hanya don fita zanyi tace dako mun gode don wurin nan naku ba a sanun abin hauwa wasan dadi.
Mun dauki hanya har lokacin tana dan sharan kwalla a fuskan ta sai naji dayan tayi magana tana fadin ki fada mata gaskiya don baki san ranan da zaku kara haduwa ba.
Dan juyowa nayi nace wani abune mama datan tace wai gafaran ki dai take son roka akan abinda sukayi a baya akan ki.
Sai madam ta karbe tana fadin don Allah hajiya kiyafe min nasan alhakin ki na cikin abinda ke bibiyana yanzu don tun wanan ranan dana fadi a gidan ku ban kara lafiya ba har yau din nan da muke magana.
A ranan ma mun yo daukan asiri ne da zamu shafawa diyan ki sai abin ya juye a kaina nan dai ta shiga bani labarin abinda ya faru a ranan da ita.
Tace yanzun ma tazo don nafisa a baya ta gujeta sai yanzun kuma ta nemay ta wai tana son suci gaba da harkan su na baya.
Tana son a illanta yayana dani kaina da kuma fati a rabata da gidan ga baki daya sai dai na fada mata yanzu ba da bane bazan koma wanan harkan ba shine tayi muna koran kare kona mota bata bamu ba.
Zaki iya fadin wanan maganan a gaban maigidan mu mama na katseta da tambaya don jin may zata ce zan iya idan har hakan zai sa Allah ya gafarta min .
Don nasan koda banyi mata ba wata zata nema tayi mata wanan aikin nikuma nasha alwashin fada maki gaskiya dama don ko ban ganki a yanzu ba zanyi kokari in nemay ki.
Ni mama ga Allah na dogara babu ab
inda zata iya min da yardan ubangijina duk abinda take nufa akaina na sheri akanta zai koma.
Tace kawarai kuwa niko nasan hakan don irin daukan da muke a kan ki kina katarewa abin akwai mamaki don ba karamin tsari ke jikin ki ba.
Yaran nan naki ma saai ince sun fiki tsari don su kila kokuwan su na tagwaye ne ya hade danaki yake aiki a kansu.
Kada kiji komai mama ni ina tare da Allah ko da yaushe don gare shi na dogara ga duk alamurana ban shigo gidan mijina da wani sihiri ba ko magani da ayar Allah dai na shigo a bakina.
Na sauke su bayan nayi alkawarin zan nemay ta ta bani nomban wayan ta na bata kudi zai kai dubu hamsin nace tasha magani dashi tana tayi min godiya da fatan Allah ta tsare ni da diyana.
Na wuce gidan maryam ina tunane a raina kan Nafisa wai ita wata irin mace ce kamar dutse wurin tauri ita watau mutuwar mahaifin ta bai shige ta ba ke nan ko.
Ina shiga gidan maryam tunanen yarana da banyi warning kada a bari su fita ba ya fado min a rai nan nakira laraba ina tambayan ta yaran.
Take fada min wai suna waje gurin security suna wasa nan na hauta da fada maryam na falin na shigo ina fada da laraba tana saurare na.
Bata taba jin ina daga ma laraba murya haka ba irin yau bayan na gama ne na aje wayan take tambayana.
Nan nake fada mata abindake faruwa dani duk abinda madam din ta fada min dan lokacin daya wuce tace wai wanan matar may take nema a gare ku ne da har yanzu batai saduda ba.
Nace may ko take nema banda ran mu dai take so maryam idan ta lalata min yara ko tayi masu wani mugun abu wa gari ya waya.
Wanan katon bazan yarda ba maryam idan matar nan tayi comfention bai yarda da ni da kaina wallahi zan dauki mata a kan su.
Wa zai ji wanan abin bai dauki mataki ba sau nawa ake wanan maryam wani mataki kika taba ganin ya dauka a kanta koda ma ya dauka din ai na dan kwana biyu ne ya bari.
Na dade a gidan maryam kafin in dawo gida na samu yaran na falo suna kallo kan su na shafa kagin in zauna ina fadin.
Laraba kin jini hankali a tashe na kiraki ko nan dai nake labarta mata komai ta rike haba tana salati tace haba ina nan ina fadin may na nayiwa hajita yau.
Sai na koma ganin bakin nafisa ko maganan ta ban son a dauko a gidan sai dai ban gama yanke shawaran abinda zanyi ba akan abinda madam din ta fada min.
Ranan dana karbi girki ne ina gurin shi ne muna hira na jeho mashi zancen nace kasan matar nan madam aminiyar nafisa ta da lokacin da ina amarya.
Yace wanan bakar matar wai tana inane yanzu nace ranan na ganta a gidan nan ta fara fada min wasu magana da ban fahinta ba nace ta bari zan nemo ta ta fadi a gaban ka gamay da yaran nan.
Yara kuma may ya samu yaran ya tambaya cikin kura min ido yana son jin ba asin maganan nacw wani magana take fada min wanda ni ban fahince shi ba.
Yace ki gayyato ta gobe tazo karfe biyu zan dawo mu saurare ta muji abinda zata ce amma ina mamakin may ya hadata da yaran kuma.
Nifa ban yarda da wanan matar ba tuncan bata a cikin tsarina haye jayen nafisa ne kawai ta dauko muna ita amna dai ai ka bari tazo muji may take son fada muna ne , .
Na fada maki gobe tazo karfe biyu sai dai don Allah ki una min gobe din idan Allah ta kaimu don gudun mantuwa karna manta da zance.
Allah ya kaimu nace ina kokarin tashi daga inda nake