marairaice fuska na turo baki tare da fadin ni wanan abin ya isheni gaskiya.
Tare da juyowa gare shi na rungumay shi din dayake so a hakali rikene yayi shima yana murmushi a bayan fuskana ya kara rungumay ni na dan wani lokaci ya dan buga min baya tare da fadin take care yana sake ni.
Jikina ne yayi sanyi na fice daga motar ina jin wani irin ba dadi a raina banko juyo ba najiya ta da motar tare da yi min horn ya bar gurin.
Muna shiga school raina nake jin yana min ba dadi har zuwa lokacin da muka fito daga lectures kamar yadda yace lamban drivern ya turo min idan na gama in kirashi yazo ya dauke mu.
Hostel muka shiga maryam ta dauki abinda zata dauka ranan na bayar da kayan amfanina ga wa yanda mukai zaman arziki dasu a hostel din sai godiya suke min drivern na kira ina fada mai mun gama.
Ba a dauki lokaci ba sai gashi ya kirani yana fadin yana bakin hostel din yana jirana muka fito tare da maryam muka shiga ya wuce damu zuwa gida.
Yamma yayi koda muka iso gidan mun samu gida a cike ashe su madam ne suka zo ziyaran ta muna shigowa naji sunyi tsit kamar ba mutanen da mukaji hayaniyar su bane da zamu shigo.
Bamuyi masu sallama ba kai tsaye part dina muka nufa ina dauke da jakkar maryam a hannu na ita kuma tana dauke da ledojin da muka sawo kayan makulashe a cikin sa.
Mun shiga mun huta ina ciki ina cire kayan da ke jikina Samiha, ta shigo tana fadin wai matar gidan tace tana kirana.
Kaina na nuna tare da tambayan ni kuwa tace eh ke tace in kira mata koba kece amaryam maigidan nan ba ta juya ta fita har ta kai kofa na ce mata ki koma ki tambayo ta kila bakiji da kyau bane.
Ta fita ta bar mu ina mamakin kiran da take min yau din maryam na fadin kije kila wani abin ne ya taso na gida zata fada maki.
Nace maryam baki san wannan matar ba inda kike zato daban yanzu bai wuce wani sherin zatai min ba kila amma bari muji har yar sakon ta dawo.
Samiha ce ta dawo dakin tana fadin tace wai bata sanki bane ke take nufi nace Allah ko na dauka ai bata san kalana ba ma kice da ita ina zowa idan na rarage.
Banje ba sai da nayi wanka nasa wani bubu redmaid ne haka yazo da dan kwalin shi na bare chewing gun na saka a bakina na nufi falon gidan inda suke zaune ina tauna chewinggun din.
Ban masu sallama ba ko wanan karon duk da chewing gun din dake bakina addua bai katse min ba a bakin dana tun kare su don yawan jin faduwan gaban da nake ji indan mun hade da ita.
Na karaso na zo har tsakiyan su na tsaya ina fadin gani ance kina nema na gaba dayan su ido suka zuba min suna kallona.
May kike takama dashine a gidan nan da zaki shigo min gida dake da kawar ki babu sallama kina ganin abokan arzikina ba zaki iya gaida su ba kizo ki wuce mutane kina takama.
Sai da na tauna chewing gun yabada kara kasss nace oh ashe abokan arzikin ki ne nan bako sani ba ke da haka ya shafa badai kin gaida su ba.
Na kalle su na ya tsune fuska tare da fadin abokan arzikin ki iyayyenane ko iyayyen mijina da za,a ce dole sai an gaida su.
Gida kuma dana shigo ke idon ki ke ma gizo haka don gidan miji ba gidan uban kowa bane gidan kazo nazo ne bai da mata tabbata ga kowan mu nan.
Ke karamar yar iska karya kike wallahi baki iya fitsara ba koyo kike yi ke wacece da zaki zo ina fadi kina fadi har ki tsaya tsakiyan mu kina bani amsa a cikin gatse tana magana cikin hausanta dake da surkin harshe.
Madam ce ta katseta da fadin tun farko da kun bi shawarana da baku kirata ba wallahi don wanan idon ta a tsaye yake tun farko na fada maku.
Irin wa yan nan ba ta wanan hanyar ake fito maku ba nace who d hell are da zaku kirani kuna son raina min wayo na juye harshe cikin turanci na shiga surfa masu zagi har da hauka.
Tasowa Nafisa tayi wai zata mare ni madam ne ta riketa ta bayan ta tana fadin Nafisa mu ba munzo don tashin hankali bane farin ciki ne ya kawo mu gidan ku.
Na samun cikin da kika yi na juya tare da tafa hannuna nace Allah sakone to za a fada masu ashe kin samu karuwa ne Allah dai ya raba lafiya.
Ciki ai yanzun ba abin kuri bane adaiji da wahalan shi tukun nan baku fada ma kowa ba don ni ko a jikina wallahi inkin iyama ki haihu duk sati don ko a jikin khadi.
Na juyo nabar wurin ina jin suna hayaniya ban juya gare su ba na shige abina madam ta juya tace wanan yar takai fitsarara wallahi jifa zancen cikin nan ko a jiki ta ma.
Wata tace karya ne wallahi ba zamu gane hakan ba sai idan Samad ya dawo munga bata dauki wani mataki ba sanan zamu san bai damay ta ba.
Ina shiga daki na zube a saman kujeran falon ina maida numfashi maryam ta kalleni tace ban taba jin kalar kishin gidan ku nan ba khadi kishi haka har da su hauka.
Nace ashe kina jin mu tace ba dole in bi bayan ki ba kada su maki na jaki ke kadai wai har da ciki har sai anyi wa mutum gatsen shi kuma.
Nace sunyi ma banza wallahi inya iya ya bata ciki duk sati ko a jikin dije don haka yake gareni ban damu da shirmay su ba ni daga shi har ita shi kuma munafukin zai dawo ai ya samay ni.
Idan ya dawo may zaki ce dashi ai yadda kika nuna masu nan koshi haka zaki nuna mashi idan kin bi ta nawa shida kanshi zai ji kunyar haka wallahi.
Don dama sunyi hakane don hadin hasumi a tsakanin ki dashi tunda sun san sherin da suka kulla a kan .
Sun hana wani mu,amula a tsakanin ku dashi ita ta samu ciki a hakan zasu nuna maki ke ba mace bane a gurin shi wallahi sai yanzu nake ganin gaskiyar Fati uwargidan shi khadija.
Ina zata iya da wanan abin haka kishi harda mutanen waje bayan yan uwanta dake gidan ana gwabzawa dasu.
Wayana dake ringing ne ya dauke min hankali ina duban mai kirana a wanan lokacin slnomban South Africa na gani da mamaki na daga wayan da sallama a baki na muryan shi naji yana fadin my Deedar mun iso yanzu muna south africa sai lokacin na gane baya kasan ma gaba daya don ni wautana bai barni na tambaye shi inda zai tafi ba.
Maryam ne ta kalleni tana min signal da ido nace kun sauka lafiya yaya hanya naga tayi ajiyan zuciya daga inda take zaune.
Ya amsa min da lafiya ya muka barku I hope ba matsalan komai dai nace lafiya muke ya tambayi maryam nace gata zaune tana assingment .
Ba wani hira bane sai dai fada min wahalan hanyan da suka sha wai jirgin su ya masu dely din lokacin da zasu sauka.
Bayan mun gama wayan ne maryam ta kalle ni tace ki tafi haka dashi har ya dawo khadi kada ki yarda korafi na fitowa a gurin ki sai abinda idon shi ya ganan mashi ko yaji.
Saukin abin ma kina da baki da baki magana ne abin zai maki yawa ya cuta maki kuma ba ganewa mutane zasuyi ba.
Waike maryam duk a ina kika san wanan rayuwar hakane kamar wata matar aure tace wallahi zama da yan uwa yasani sanin haka.
Na fada maki ai nice auta a gidan mu koda yake kin ki zuwa ma balle ki san gidan mu gidan mu gidan yawa ne khadi so nasan irin wanan rayuwan ne ga zamantakewa a cikin yanuwa kowa da tashi kalar kaddaran dakan zo mashi.
Kuma nima da kike gani fa na taba aure sai dai zaman baiyi ba don ko tarewa kishiyar bata bari nayi gidan mijin ba aka watse.
Wani kallo nayi mata tare da tambayan kin taba aure fa kikace maryam shine duk zamana dake baki taba fada min wanan zancen ba.
Dariya tayi tace ba maganar da zaka fada bane tunda ba dadin ji zancen ke dashi ba wataran zan zauna in baki labari kada ki damu.
Washegari da muka tashi da safe bayan mun shirya ne muka zauna mu karya lokacin na kira malam musa driver ina sanar mashi da mun shirya.
Sai dai wayan shi bai shiga a wanan lokacin ana fada min wai not reacherble nace babban magana wayan mutumin nan baya shiga fa maryam.
Gamu kuma da test ranan da safe tace mu gama sai mu fita waje mu gani ko yana nan yana jiran mun kin san kila matsalar services ne.
Bayan mun gama mun fito motar shi baya waje sai motocin maigidan na alfarma da suke rufe a cikin innuwa.
Kallon juna mukayi da maryam tace mu koma tunda bayanan nace akan may zamu koma wa yasan lokacin da zai dawo gidan kawai muje titi mu shiga mota takarasa damu.
Don ba zan yarda in rasa test dina yau ba hayan fita get din gidan muka nufa kamar ance in juyo baya Yanyala ne da Samiha a tsaye suna kallon mu suna yare suna dariya ban wa maryam magana ba har muka samu mota muka tafi.
Shidda daidai na kira malam musa ga waya na ringin sai dai bai daga ba raina ya baci nace ma maryam mu tafi titi mu samu mota.
Mun dawo gidan suna falo kamar kullun ranan har da Nafisan bata fita ba suna ganin mu suka kwashe da dariya suna yare can cikin hausa naji tana fadin.
Matar permsec ne yau a motar haya haka shine daidai da yar tallakawa dama an ga motoci a gida an biyo banza kamar in koma in bata amsa maryam tace ba banza a jiyar ta dama nasan da manufa haka ya faru bandai maki magana bane.
Nace na sani tun ganin su da nayi da safe suna muna dariya tace ashe kin gansu kema abin ya kona min rai sai dai na kyale tun wanan ranan ban sake gigin kiran malam musa ba ya zo ya dauke mu ba.
Kullun da safe wani mai Napep zai zo ya dauke mu ya kuma je ya dauko mu don muna bashi kudi masu yawa.
Mun dawo muna daki da maryam da dare nace da ita ina zuwa kitchen na shiga na dauko yuka da gishiri na fice gidan.
Allah ya taimake ni hankalin mazan dake waje yana kan butar shayin da suka dora a wuta hankalin su ya dauke dashi ga kidan yaren su sun saka suna bi suna rayawa.
Da karfin halina na suce tayon motacin dake aiki a gidan tare da zuba gishiri yadda ba zasu moru ba sai an zuyarci kani kawa.
Na juyo cikin duhun na koma part dina ba tare da na bari wani ya ganni ba da safe ko da muka fito suna gurin tsaye cirko cirko cikin tashin hankali bamu bi ta kansu ba ko kallon abin bamuyi ba muka fice gidan.
Sai da muka dauki hanya nace suma suji inda dadi abinda mukaji maryam ta juyo tace may ne wai nake fada mata abinda nayi baki ta rike tace khadi kin kai can ban sani ba.
Har na wuce nan ma itama ta iya sheri balle wani kafin mu dawo maigidan ya kirani hankali a tashe yana tambayana ashe abinda ya faru ke nan ?
Nace may akayi yace wai an shigo gidan jiya da dare an taba motoci nace banda labari don ni yanzun haka ina school.
Yace da wani mota kika je nace wanda na saba zuwa dashi dashi na tafi yana fadin bai gane ba na kama fadin hello hello ban jin ka fa na kashe wayan.
Bayan mun fito ne muka dan ratse sayayya a wani shago muna gab da gamawa ne naji ance wanan ba matar oga AA bace ban tsaya ba sai maryam ne ta ba mashi amsa ashe tare yake da matar shi .
Maryam ne ta tsayar dani tana fada min tare da nuna matar a gareni yace aishi yaron AA ne ya taba ganin tare shiyasa ya shedani.
Mun gaisa dasu zai biya muna kudi nace ya barshi mun gode muna da kudi mun fito zamu shiga Napep ne suma sun fito ya gan mu yana mamakin shigar mu napep ya hana dole shi da matar shi suka kawo mu gida.
Muna zaune a dakin mun barbaje kayan da muka sayo muna kallo aka turo kofan dakin hankalin mune yakai ga mai shigowa dakin.
Kayan dake kasa a barbaje ta kare ma kallo yayin da muma ita din muke kallo muji may ya kawo ta dakin a wanan lokaci.
Tace ban san ke muguwa bace muke zaune dake sai yau abu ya samay mu a gidan ki nuna muna halin ko in kula.
Nace au da ke sai yau kika san ni muguwa ce komai ai halin ki ne nake koyo ba wani ba don kin san ance dan koyo yafi mai hali iyawa.
Sai dai har kullun ina garga din ki da shigo min shiya haka gaba gadi don haka kowa ya tsaya iyakan shi.
Ke uwatace ko may da kullun kike min kallon wace zaki ba commad a gida ke abin ya shafa ni bai shefe ni ba kin ji koma may nene tace dama nasan ba son shi kike tsakani da Allah ba anga dukiya an shigo aci banza.
Nace kamar yadda kika biyo don jin dadin wuri kika kwaso yan garin ku kaf azo a sauke yunwa a nan ko.
Dani dake sai ki tunanen waya biyo dukiya yanzu ni da nazo ni kadai ko wanda ya kwaso yan uwan shi ya cika a gidan miji babu kunya ba tsoron Allah kin kakace gida da komai na gidan.
Bakin cikin ki yanzu shine kin samu wace zaku raba daidai da ita ke kuma baki son ki bude ido kiga haka din a gidan.
Sai dai kare ya mutu da haushin kura don na shigo ke nan ba fita gareni wanan kuma damuwan kine can .
Lalai wanan yar iskan ana zuwa dake haka dama nake son ganin karamin kwazon ki a fiki wanda bai kai ko cikon cukali ba a wurina zaki gane kin shiga hurumin da ba naki ba kwanan nan ta juya ta fice daga dakin .
Maryam da ke kallon ta tun shigowa tace wai khadi haka kuke kullun da wanan matar ashe da gaskiya ne da ake fadin bakin mitar tsiya gare su kamar mayu.
Allah ya taimake ki kina da baki da wanan ai ko sati ba zakiyi a gidan nan sai kin gudu don wanan kishin harda na hauka a cikin sa.
Nace na fahince ta so take ta juyani kamar wata yar cikin ta bata san ta makaro ba duk sirin iskancin ta yana a tafin hannuna.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Shida da wani abu ya shigo part din nawa a lokacin ina kitchen ina karasa miyan da na dora a kan gas wanda zai isheni ci na kwana biyu.
Banji shigowan shi kitchen din ba sai ji nayi mutum ya rugumoni ta baya na tare da dora kan shi saman bayana yana fadin may malaman tawa take girka muna ne?
Zabura nayi a firgice ina batun sake cibin miyan dake hannuna yace relax baby nine wa kike tunanen zai shigo makinan in ba niba.
Nace na sani tunda gidan cike yake da garadan kati nagani ko wani ne yai min shige tunda sun ganni bare a cikin su.
Da naci uban maishi kuwa duk wanda yayi gigin shigo min part din amaryana bada izinina ba basai ka masu haka ba tunda gidan baida security na gani ni dai zan daukarwa kaina mataki tunda kai baka saba daukar masu ba.
Juyoni yayi muna fuskan tar juna dani dashi kawar da idona nayi daga gare shi sai lokacin na gane.
Ya sauya kayan jikin shi zuwa jallabiya fara kal a jikin shi hakan yasa na gane cewa ba shigowan shi gidan ke nan ba a lokacin.
Rikoni naji naji ya kara yi a jikin shi kallon sakeni nayi mashi maimakon ya sake ni din sai ma ya kara rikoni a jikin shi yana shakan kamshin jikina a hankali.
Wani turare kike amfani dashi ne haka mai kamshi kamar banji mai yake fadi ba nace malam sake ni don Allah.
Idan na sake ki ai dana shiga uku nace don ka sakeni zaka shiga uku yace tun ban furta maki kalman da kike son in furta maki ba zan sakeki.