Allah nima zan taya ki addu,a , Allah yayi maki zabi na alheri.
Nace mama ina yi dama kullun sai dai har yanzu ban kai ga matsaya ba tace Allah yayi muna zabi mafi alheri nace amin mama.
Har ta juya zata tafi sai kuma ta juyo tana fadin sai dai ina ganin kamar mijin buzuwan nan ne yazo fa gidan nan da sauri na dago nace mama bar maganan shi inma shine yazo ni bai cikin lissafina gaba daya.
Allah yayi muna zabi mafi alheri tace ta juya tafita daga dakin nabi ta da kallo ina takaicin AA a cikin raina.
Wayana na jawo na kira nomban shi sai ya nuna min busy yake har dare sosai ina kiran shi wayan na nuna min busy nagane yayi blocking dina ne a wayan shi.
Dasafe bayan nayi sallah ban sake fitowa ba ina daki har saida naji baba ya fita daga gidan na dan fito na samu abinda naci na koma na kwanta a dakina.
Yusuf na nema kira biyu ya daga wayan tare da sallama ya dauka muka gaisa yake tambaya na lafiya na dana iyayayyena nace kowa lafiya yake.
Yayana dama tambaya ka nake son yi don in san gaskiya don Allah kune kuka zo gidan mu wurin iyayyena ko wasu ne.
Sai da yayi dan jim yace mune Khadija munzo ne neman izzinin a gurin su kuma mun ji dadin yadda baba ya karbe mu sosai wallahi.
Do har lokaci ya bamu da zamu dawo nan bada dadewa ba katse shi nayi da fadin why yayana zakuyi min haka yace khadija kin ki tsayawa ku fahinci juna dake da AA akai ga matsayan maganan.
Kashe wayan nayj saboda raina daya baci a lokacin gaba daya ma na kashe wayan don kada ya kara kirana again.
Sai lokacin nake nadama da dana sanin sake masu fuskan danayi har suka shiga rayuwana ban tsaya wani tunane ba na fita wurin mama na samay ta mun dade muna magana daya da ita bamu kai ga mafita ba.
Sai da kyat mama ta samu na sake na dan rage damuwa a raina har da yamma na fita zuwa gidan anty suwaiba na gaida ita na dade a gidan sai gab da magariba muka koma gida.
Sai bayan kwana biyu na kunna wayana maryam na kira ina fada mata halin da nake ciki ssi bayan da tagama saurarena tace dama nasan AA ba kyale ki yayi ba akwai abinda yake shirya akan ki.
Yanzun ke wani shawara ki ka yanke akai nace ban kai ga yanke shawara ba sai dai mama ta ban shawara kamar yadda su ya amina suka fada min in samu wani in tsayar a matsayin wanda zan aura tace shine daidai wallahi .
Abinda ban sani ba shine kan su daya da su AA don haka muna gama waya ta labarta masu abinda na shirya wa zuciya na yanzu.
Kwana biyu da maganan mu da maryam ina daki ina barci kamar daga sama naji muryan ya Amina a kaina da mamaki na bude idona ina kallon ta.
Mikewa nayi daga kwance na yunkura na tashi ina fadin Ya Amina tafiya haka babu sanarwa tace wallahi daurowa ne yayi don nima ban san zan zo ba a wanan lokacin.
Ni dai ban san dalilin zuwan ta don bata fada min ba amma tare muka tashi washe gari muka gyara ko ina na gidan mu da ita.
Fita tayi zuwa gidan ya suwaiba tace zata je ta ganta ta dauki lokaci a can sai da yamma ta shigo gidan irin girkin da naga ana shigowa dashi gidan mu washe gari yasa na tambaya ko baki zamuyi a gidan.
Ban samu wani kwararen amsa ba daga gare su don haka nima na share zancen misalan daya da wani abu motoci suka tsaya a kofan gidan mu kafin bakin su shigo aka fara shigo da akwatuna ciki .
Ina dakina ban san may akeyi ba jin hayaniyan mutane da nake ji a tsakar gidan ya sani tashi in duba ko su waye suka shigo.
Mommy ce na fara tozali da ita sai su fauziya su biyu kannen AA dake aure tare da wasu biyu daga cikin dangin su daban sani ba.
Gabana ne ya fadi take naga wani duhu na neman rufe min ido da baya baya na koma saman gadon mu tare da dafe kaina.
Sun shiga dan falo gidan mu inda ana aka saukw su tare da gabatar masu da abinsha dana ci gidan gaba daya ya kaure da gayaniya babu wanda ya koma ta kaina kuma.
Barci ne ko tunane naje ban san yadda akayi ba ni dai na falka naga mama zaune a kusa dani tana fadin kin tashi khadija ido na bita dashi ba tare dana mata magana ba wai ashe suma nayi a dakin ban sani ba.
Ki sha tea gashi nan na hada maki kada ya huce kuma ki natsu don sarakuwar zata shigo dubaki yanzu tana fadin haka ta fice daga dakin ta barni kwance ina binta da ido.
Ya Suwaiba ta shigo dakin tana cewa khadija sannu akan wanan abin kike son daga hankakin ki haka wurin kayana ta nufa tana fadin wasu zan dauko maki ki saka don zasu shigo su dubaki kafin su tafi.
Ya Suwaiba don Allah kada ku shigo min dasu ni yanzu ma gidan zan bari wallahi don bazasu ganni ba har su tafi kuma ku basu tarkacen su su koma dashi.
A daidai lokacin mommy ta shigo dakin da sallaman ta saurin yunkurawa nayi don in tashi don daga ni sai wani dogon rigar danasa ne a jikina kaina babu kitso gashina ya zubo ya kwanta min a bayana wani kuma ya fado a goshina.
Haba khadija ki kwantar da hankalin ki kina natsu akan wanan zancen zakibi ki tayar da hankalin ki haka idan kin halaka kanki fa badon Allah ya gyara ba.
Mu bamasu cutar ki bane kin sani mu ba masu cutar ki bane masoyan ki ne mu don haka kika ga muna kokarin wanan abin ya yuyu.
Nasan Babangida bai kyauta maki ba tunda bai nemi so daga gare ki ba yasa muka kwaso jiki zuwa nan ba tare da sanin ki ba don da kin sani baki yin hakan da kikayi.
Ki natsu don Allah kada wanan zancen ya koma kunnen mutane don bamu bari sun fahinci halin da ake ciki ba don idan hajiya mama taji a yadda take son abin nan ranta ba zaiyi dadi ba wallahi.
Fadawa nayi jikin mommy din ina fadin mommy ki taimake ni ya jaye wanan kudurin nashi a kaina don ba sona yake ba ya fada min shima yayi hakane kawai don ya kwatar maku da hankalin ku.
Nasani tace tunda shi namiji ya iya daurewa yayi haka ke mace mai zai hanaki nuna ke mai tarbiya ce kema kibi maganan iyayyen ki ki masu biyayya.
Mommy wallahi ba zan iya ba AA mugu ne babu komai gidan shi sai tarin fitina da bakin ciki kuma kun sani mommy may zai sa kusani a cikin wa yan nan hali bayan kun sani.
Na sani khadija nasan komai da kike tunane akan babangida sai dai ina son ki sani wanan abin da kike tunane insha Allah ba zai faru a kan ki ba da yardan Allah.
Don sanin ki da nayi jarumar mace wace zata iya tsayawa ta kwatar wa kanta yanci a gurin ko waye har nafisa dake tunanen ta mallake kowa dake kewaye da shi.
Mommy wallahi bazan iya ba nidai ku rabani dashi ban son shi wallahi ni akwai wanda nake so tace naji yanzu tashi ki shirya sai ku gaisa da mutane daga baya zamuyi waya dake idan na koma gida.
Da wannan magana na mommy naji karfi gwiwan tashi na kimtsa jikina cikin wani lace sabo dana dinka na dora abaya a saman kayan tare da daura gyalen abayan akaina.
Da jagoracin ya Amina da anty suwaiba muka shiga falom inda suke zaune sun sake jiki kamar yan gida su ma ba wani takura a tare dasu.
Ina shiga naji matar daya da ban sani ba tace masha Allah wana ita ma kamar buzuwan ne ai lalle na yarda da zaben dan nawa ya iya zaben tankar da dubu.
Kaina na kasa na durkusa har kasa gefen kujera ina gaida su daya tace a a gaskiya da alama yanzu kan babangida yakai ga matan nunawa tsara ga kyau ga tarbiya ga natsuwa masha Allah.
Allah yasa muce gwama da akayi anty Fauziya tace daga inda take zaune dako kai muyi hoto in nuna ma hajiyan mu zaben dan ta.
Kaina na kara nokewa ina zagi a cikin raina nace matar shi nacan inda take badai ni ba kan.
Nan dai sukai ta magana a kaina ina duke sai da mommy ta tasu ta daga ni tana fadin ku barta hakana don Allah kun san sarakuwan nawa alkunya ke gare ta kun damay ta.
Jan hannu na tayi muka fice falon ina rungumay a jikin ta tana rada min kin gani kowa na farin ciki da shigan ki rayuwan babangida khadija .
Sai da ta zaunar dani a dakin take fadin kwantar da hankalin ki babu komai sai alheri mun san abinda muke hangowa cikin wanan auren naki.
Zamu dinga waya dake ina sanar dake komai da ya daure maki kai wanda baki gane bama zaki iya bugomin ki tambaye ni a shirye nake da in fitar dake a duhu.
Ke dai ki rike addua don shine makamin mumini nace a sanyayye mommy na gode insha Allahu zan kira ki tace haka nake son ji diya ta
Komai zai zo da sauki da yarda Allah sai hudu da rabi suka kama hanya komawa abuja suka barmu da tarin kaya da suka zo dashi wai sun gani suna so har kuma daddy ya saka masu ranan da zasu zo a tsayar da lokacin buki shi da yan uwan shi.
Ban fita ba don haka ban an wani tarkace suka zo dashi ba sai dai ina jin mutane na shigowa yan uwa da abokan arziki suna fita suna yaba irin kamun da nayo.
Wai nayi dace mijin na gwada ma tsara babu wanda yayi min tunanen irin halin da zan fada ciki don idon su ya rufe sai mahaifiya ta ce ke tayani jimamay.
Ina mamaki a yadda nasan daddy bamai kwadai ba yadda yayi saurin yarda da AA din a lokaci guda sai nake ganin kamar bai bincika komai akan shi ba suke kokarin cusa ni a gidan shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Da sauri na kwace daga tabanin da yake son yi daga inda na makure saman gadon naji idona suna fitar da dan siririn hawaye.
Ba zaki yi sallah bane ko a gidana kike son ki karfita sai dai ba zan so muyi haka dake yanzu ba nafi da son sai munfara koyi da sunnan ma,aikina SAW.
Da sauri na kallo shi yace don haka ki tashi mu gode ma Allah a tare don falalan dake cikin wanan ranan mai albarka a gare mu.
Ya juyo guri tare da kafeni da ido yana magana cikin tsigar lalashi tare da karashewa da please yau ba rana bace da ta wasa a gare ko ms may kike ji zaki iya boyoe shi har mu idar da wanan sallah.
Kin dai san biyayya mata ga mijinta , saboda nasan gida an fada maki komai idan har da farko baki sani ba ,
Wani hararanshi na karayi sai kuma zancen iyayyena daya sako, ya fado min a rai don nasiha kan iya nasiha na sha kafin in bar gidan mu zuwa nan.
Jikina yai sanyi kamar zanyi magana sai kuma na fasa sauka nayi daga gadon ina gyara zanin da na daura tare da shimfida salaya da kyau abinda ya ban mamaki sai yadda yake jan surorin alkur,ani mai girma a natse cikin taushin murya.
Raka,a biyu mukayi sai dai duk dogayen sura yake ja abin ya bani mamaki don ban taba sanin yana da ilimin adini haka ga yadda nake ganin shi.
Bayan mun idar da sallah ina batun mikewa ya juyo inda nake tare da dora hannayen shi a kaina ya dinga kwararo min addua idona suna rufe sai naji yan siraran hawaye suna fita min daga idona muryan shi ne naji yana fadin tashi kije ki kwanta.
Ban ko bi ta nasa ba na mike nabar wurin da sauri zuwa saman gadona ban sake bin ta kan shi ba da tunane na kwanta don haka ban san lokacin da barci ya dauke ni a hakan da nake kwance.
Tunda na kwanta ban falka ba sai da naji kamar ana buga wani abu na bude idona firgigit a inda na barshi nan na sake ganin shi zaune abin ya bani mamaki.
Nace cikin raina ko ina ya kwana oho da sanda na shige ban dakin tare da duba jikina ko ina a bandakin kafin in dauro alwala in fito.
Inda ya idar da sallah nan nima nazo na tayar da sallan daga bayan shi har na idar yana bin yadda nake sallahn a hakali da idon shi ta gefe har ya gane abinda yake son ganewa a gareni din .
Ban idar da addu,a ba naga ya mike yafita daga dakin nawa inda ya fita ya barni a wurin na kwanta saman sallaya sai barci mai nauyi ya dauke ni ban falka ba sai wani lokaci mai tsawo na falka da sauri namike ina dube dube a dakin.
Ganin kofan kamar yadda yake a rufe na mike zuwa bandaki daga nan na tsaya nayi wanka na fito na gyara jikina a cikin wani cotting lace dark blue mai duwastu kanana a jikin shi ko ina.
Wani bakin abaya na dora a sama wanda bayan shi kawai keda kwaliya sai gaban hulan tare da dora gyalen abayan saman dan kwalin da na daura.
Ga kumshin kafana da mama Tani ta matsa min sai da akai min yana ta sheki kamar yau aka zana min shi a hannu na da kafafuwana.
Flat shoes na saka a kafafuwa na part din da su mommy suka sauka na nufa sai dai part din yana rufe na dauka basu tashi daga barci bane sai na nufi wanda nake tsamanin na Nafisa din ne.
Tun daga kofa na jiyo musayan maganan da sukeyi kamar a cikin tashin hakankali ita da maigidan ina ta sallama ba a karba min ba.
May kake nufi da zuwa dakin Amarya ka kwana tun mutane basu watse daga gidan ba kana nufin tun yanzu zaka fara wulakantani ko may har wani auren kayi wanda kakewa dauki haka ?
Kana nufin ka auro wata mace don kaji dadi ne ko ta baka abinda ban dashi a tare dani ko haihuwa ka auro ta zo taimaka a gida maganan nake ji kamar fada shiyasa na daina sallaman ina sauraren su
Nafisa tace to bari kaji lndan kaji dadi ka auro ta ka sani babu wani dadin da zataji a gidan nan wurin ka.
Idan kuma an aura maka ita ne don tazo tai haihuwa maka a gidane kamar bera ko kaza don ni nazama juya to itama ba zata taba haihu a gidan nan ba muddin ina raye,.
Kasani tsakanin ka da ita daga yau sai kallo nan naji muryan AA a dakin yana cewa ai baki kamar Allah ba Nafisa duk wanan maganan da kike yi a shirmay nake daukan shi da zafin kishi.
Kuma bari kiji ninaga Khadija da idona nace ina son ta karki sake zargin wani dan uwa nawa don su abinda nake so ne suke tayani so ko may nene na dauko gare su kuwa zasu fini son abin nan indai alheri ne.
Kuma diyar mutane tafi daga bakin ki don ba yadda zaki yi da ita don ta riga da ta shigo ko yanzu matsayin ku daya a wurina .
Don ta riga tafi karfin ki tunda har ta shigo gidan nan ta ture zancen ki da kike fadin ba macen da ta isa ta shigo gidan muddin kina raye.
To ita ta kauda wanan burin naki tun yanzu ta nuna maki ke ba kowa bace face baiwar Allah kamar kowa.
Oh watau taga mai kudi ta shiga tafita sai da ta kutso kai ta shigo gona na ko ai zakace nace indai nice dani kuke zancen wallahi.
Taga mai kudi ta biyo ka to ta sani ta biyo wahala a rayuwan ta don yadda ta shigo haka zata fita don ba gidan zaman ta bane gidan nan.
Ke kudi ya dama Nafisa don ita kudi ko wani abina ba shine a gaban ta ba nata take kokarin nema ko yaushe don ita duk wanan bai gaban ta.
Don haka ni naganta nace ina son abina don ita ba sona take ba ko wani abina keko ke kika ganin kiga abinda nake dashi kikace kina sona don shi.
Don haka kinga akwai banbanci a tsakaninku don nike son ta don nasaban ta ke kuma ke ke sona don abina.
Dadai naga basu da niyar barin musayan maganan da suke ma juna nayi sallama da karfi na shiga falon nata
Gaba