MIJIN BUZUWA complete Hausa Novels.txt

Author :  Nil Category :  Romance

Chapter   110 / 144

327K to 330K   out of 431K words

saba mata a hakan yadda yake tsoron alamarin ta aiko hajiyan su baya shaku haka nan.
Tace yar na yanzu ma cikin abi yayi sauki ke nan ai idan dane ai bai isa yai mata hakan ba ma gaskiya kowa na ganin kokarin ki sosai da kike iya fuskantar matsalan wanan matar a zauna lafiya.
Ko can sai da hajiya Fati tai magana ranan ganin kun fita da shi tana zaune bata iya cewa komai ba a kai.
Nace mama ai abin nasa ne sai kaga kamar ya kubuta daga kaidin ta kwana buyu kuma sai kiga ya kara dulmiyewa a ciki sosai.
Ai bata barshi haka ba kullun irin su a cikin tushi aikin su suke yi suyi nan suyi can ko yaushe a cikin kauce hanya ake don dai kawai aga an kuntata ma abokiyar zama ta muzanta a gurin miji.
Aike bata samu yadda take so a kanki ba har yanzu nace Allah kuma ba zai taba bata sa, a akaina ba har ta mutu.
Shiru nayi ina tunane a raina yanzun haka zamuyi ta rayuwa a cikin wa yan nan mutane kai ke nan ba wani rayuwan jin dadi dakai da miji gaskiya nikan da ake cewa wai ka gani ka daure ba zan iya cin fuskan Nafisa ba wani lokacin har da miji.
Juyowa nayi nace mama ina ganin bread din nan tun na jiya ne ba zan iya cin sa ba gaskiya ko zamu fita in samu wani na aike sa ya sawo muna.
Tace bari dai ni in leka idan masu gadin nan su nanan sai in basu su sayo muna ko na mike na shiga na fito mata da kudin bread din.
Shiru shiru zanga laraba ban ganta ba gashi kuma ba wayane da ita ba dole na fito zuwa duba ta na samun har an datse get din gidan ta baya.
Karasawa nayi gurin get din ina tambaya buzanyen waya rufe get din gidan daga ciki ne karfe takwas da wani abu.
Don security din bakin get di basu nan su ma ina ta mamaki a raina babu wanda ya tanka min nasa hannu na bude get din .
Laraba da security din nan biyu ne a waje ina bude kofan motar shi na isowa gurin da mamaki ya shigo yana kallon mu ko kallon inda yake ban tsaya yi ba.
Na ba security din hakkuri muka shige da mama a ciki ina shiga ban tsaya jiran komai ba na jawo akwatuna na nafara hada kaya na da suke nawa sai da na shake akwatunana kaf ina jan zip ya shigo dakin .
Kallon akatunan dana dora a saman godo yake yi ya dago ya kalle ni tare da fadin wanan kayan fa na may ye kuma.
Ban bashi amsa ba na nufi gurin wardrobe na bude na tono handbag dina da nake dasu na fara saka kayan shafe na a ciki yana tsaye yana kallo na.
Yace bake nake tambaya ba ina zaki haka kike hada kaya saida na gama na sauke akwatunan kasa na dauki hijjab dina yace ina kike nufin zuwa bada izinina ba sai lokaci na dago nace gidan ubana zan tafi yau insha Allahu komai dare kuwa.
Murmushi yayi yace a wanan lokacin kin ko san karfe nawa muke yanzu da kike wanan haukan wai ma da izinin wa zaki tafiyan.
Wani kallo da ban taba mai ba cikin bacin rai nace izini izini zan nema a gurin wa gurin mutumin da aka hada kai dashi aga bayana zan nemi izini ko may ?
Cikin mamaki yace aka hada kai dani aga bayan ki akan may nace koma may ye ku kuka sani na fara jan jakkan zuwa falo rike ni yayi daga baya yace zaki bar wanan haukan da kikeyi kosai ranki ya baci.
Ki tsaha ki min magana yadda zan fahinta rashin kunya ya hanaki tsaya kina ganin wanan ne mafita ga komay nene kike shirin yi din.
Yanzu akan idon ka Allah ya nuna maka abinda sukai muna ni zaman su a nan tare daku bai damay ni ba kuma ba zai taba damu na ba din.
Lafiya ta da na boyar Allah dake zama don ni a gidan nan najawa nagaji wallahi nagaji da irin wanan zaman gara na tafi inda ake sona da kaunana ida kansan zafi na yafi min.
Malalacin Murmushi ya sake tare da fadin akan dawowan mutanen nan kike wanan haukan ashe idona ya ciko da hawaye nace dawowan su gidan nan bai tare min komai ba don a tare na samay ka dasu.
Lafiya ta na jawa don gaba ban san irin abinda zasu iya min ba ina cikin wanan hali gara na koma ida aka san zafi na da ciwo yafi mun sauke.
Kallon yadda nake zubar da hawaye yayi sai naga ya fita zuwa falon yace mama wani abu ya faru ne bayana.
Laraba dake zaune tayi tagumi a takure guri daya tace Alhaji mutanen nan dai ne da suka dawo sin saka mu a gaba da dariya yanzun kuma na fita zuwa sayo mata bread ina ba masu gadi sako suka rufe mu ta baya.
Yace rufewa fa yana fadin haka na fito ya kalle ni baice komai ba ya nufi kofan fita daga part din har ya fita ya dawo ya cire key di dake lake a jikin kofan ya rufe mu ta baya ya wuce.
Zama nayi a gurin ban iya magana ba sai kukan da nakeyi part din nafisa ya nufa suka hade da ita tana fitowa.
Nafisa wa yarufe kofan gidan nan da mama laraba a waje sai da taimai wani kallo tace nice nace su rufe don ko bazan yarda ana fita a wanan lokacin ba tana kebewa da wasu maza a dauka yan uwana ne dake gidan suke haka ?
Nafisa kin san yarda muke da laraba kuwa tace ko ya kuke ai aiki take a gidan nan kuma a karkashin ka take.
Kallon mamaki yake mata don yadda take maganan sai dai yana jin ba zai iya mata masifan daya shiryo yai mata ba suna hada ido yaji wani irin abu a tare dashi ya soki zuciyar shi.
Wanda yazo da fada sai gashi yana maganan lumana haba wanan ai kin san bai dace ba kamar laraba ce za ace ta fita yin zance a waje ko may ?
Samad kaga idan matar ka ta turo kane kai min cin mutunci in sani don bazaka zo nan ka tsare ni ba kana fada min wanan magana.
Zuwa tayi gidan nan ta samay mu bata isa ta ce zata juya kowa yadda take so ba dokane na bayar ko itace ta fita wanan lokacin zance a rufe gidan nan ne.
Ta fada tana wuce shi ya bita da kallo sai yaji bai iya musa mata da komai a lokacin suko yan uwanta sunyi tsit suna sauraron su.
Yaja kafan shi ya bar gurin zuwa part din shi bai iya aiwatar da komai ba don kwarjin da Nafisa tai mashi.
Yusuf na kira ina kuka ina fada mashi yai mashi magana ya bude muna kofa don ya rufe ni ta baya .
Hankali tashe Yusuf yake tambayana abinda ke faruwa nace Yusuf nagaji da auren mijin wata wallahi bazan iya zama a gidan nan ba gaskiya.
Yace yi hakkuri gani nan zuwa yanzu don Allah kanwata kada ki fita a cikin daren nan kin san halin da kike ciki fa yanzu.
Hali ba zai hanani kwatar inci na ba nagaji ne sai kaga abu kamar yai sauke gare ka sai kuma a bulo da wani abin ban iyawa wallahi yace zaki iya insha Allahu khadija ki kara daurewa dai please.
Maryam na kira muna gama waya nace tazo ta dauke ni jin ina kuka yasa taba anty waya tana tambayana ban boye mats komai ba abinda ke faruwa.
Tace wai shi wani irin mutum ne da bazai iya tashi tsaye ba akan gidan shi yanzu kiyi hakkuri khadija dare ya riga da yayi sosai .
Ki bari gobe idan Allah ya kaimu zamu shigo mu samay shi dole ne yasan tsarin da zaiwa gidan shi duk abinda take ji kowa ya iya sa ai.
Da kyar ta samu ta lalashe ni na bar kukan da nakeyi din taita bani magana akan inyi hakkuri in bari har suzo.
Yusuf ne ya iso gidan tun waje ya fara mamakin ganin buzayen sun dawo gidan don bai fada mai cewa sun dawo din ba sai da yazo ya gansu.
Nan ya fahinci inda matsalan take ciki ya shiga ya samu matan sai raha suke a tsakanin su bai tanka su ba ya nufi part din mai gidan kai tsaye.
Muryan Nafisa ne daga inda take zaune take fadin kai waye da zaka shigo min gida haka kai tsaye ka wuce sashen maigidan baka nemi iso ba.
Ya juyo da zuman ya fada mata bakar magana wani iri yaji a ransa da sauki ya ambato Lah, illah,ha illah muhammadan rasullilah sau uku yaji wasai a ranshi yace ke baki isa ba wallahi kuma sherin ki yayi kadan a kaina.
Yana fadin haka ya wuce part din azaune falon sama inda ya ke zama ya huta ko yaci abinci ya samay shi zaune.
Lafiya na ganka a wanan lokacin Yusuf yace ba dole in taso ba kanwa ta takirani hankali a tashe zata bar gidan ka.
Sai yanzu danazo kuma na fahinci abinda yake faruwa a gidan AA yaushe ka dawo da mutanen na gidan nan baka sanar dani ba.
Yusuf ashe abinda ake fadi gaskiya ne kakai kanka inda ka wuce iyakar ka matsalan na nida iyalina harshi dole sai ka sani ko may ?
Kallon mamaki Yusuf yake mashi yace gaskiyane na wuce iyakana a gare ka amma kayi hakkuri nayi kuskuren yin hakan.
In Allah ya yarda kuma hakan ba zai kara faruwa ba don nima na sani matsalan iyalin ka baidace in shiga ba.
Amma ka sani matsalan wanda ya shafi khadija ya zama dole in saka baki a cikin shi don matsalanta a gidan nan ya shafeni.
Yusuf ya fadi a kakausar harshe yace ban min gidana tun muna sheda juna dani dakai a gurin nan matsalan Deedar ya isheni nima.
Tunda na aureta ban zauna lafiya da matana ba kullun a cikin jidali muke a gidan nan ba wani kwanciyar hankali dana samu a cikin gidan nan.
Yace naji wanan kuma kai kajawa kan ka haka tunda baka iya tsayawa kayi adalci a gidan ka ka bar mace ta shige maka a gaba kan komai.
Ni ba zaka fada min wai khadija ta shigo ka rasa kwanciyar hankali a gidan ka ba don nafi kowa sanin gudun mawar da shigowan ta gidan nan ya baka.
Tun kan khadija ta shigo gida ka baku da kwanciyar hankali da matar ka haka ta shigo ta samay ku da tarin matsalan ku a gidan nan.
Yusuf ka tafi ka barni a yadda nake jin din nan idan ma zaka tafi da ita ne ga key can ka dauka ka kwashe ta ku tafi duk inda zaka kaita da daren nan sai kun dawo.
Inda ya nuna mashi key din ya dauka ya fice baiko kalle shi ba ya ja tsuki a kofan suka hade da Nafisa tana shigowa tace mu zuba dani dakai agani.
Yace ko mun zuba indai ni Yusuf ne baki kwashe komai wallahi don nafi karfin tsafin ki ko wani shirka daga inda AA yake zaune yace Yusuf ka fice min a gida nace maka.
Yusuf ya fice bai ce mai komai ba part dina ya nufa ya bude muna falo ba wanda ke magana a cikin mu inajin an bude kofan na mike a zatona shine ya shigo.
Sai naga Yusuf na zauna naji wasu hawaye suna zubo min na takaici da kunan rai yace khadija yi hakkuri ba sai kin fada min komai ba na fahinci duk abinda ke faruwa a gidan nan ko.
Daga wurin shi nake yanzu wanan shu,umar matar ta riga da ta asirice shi da sihirin ta yanzu maganar ta wuce yadda ma kike zato ga AA din.
Kuma dan dawowan nan da kukayi ne komai ya faru ina kuka nace ni ba zan zauna ba yayana dama can zaman hakkuri nake don ba sona yake ba har ga Allah.
Yace ki bar fadin haka khadija don so wallahi ni nasan AA yana son ki fin karfin shi da asiri ne kawai akayi yanzu kuma insha Allahu zamu kwatoshi daga halakan ta.
Sai dai abinda nake so dake yanzu don Allah ki jaye wanan maganan ficewa daga gidan nan da kike fadi idan kinyi haka kamar kin nunawa Nafisa nasaran ta a fili ne.
Kin ga kina dauke da tsohon ciki haka tare dake sai taji dadi dama nasan akan abinda akai wanan aikin ke nan yadda yai masu din nan nasan ba zasu kyale shi ba nasani .
AA mutum ne dake da yawan sakaci yasan halin matar shi amma shi bai damu da neman kubuta daga sherin ta ba zan kira hajiyan su yanzu insanar da ita abindake faru ta kara baki hakkuri takuma dage gurin yi masa addua itama don yadda na fahinci abin aikin gagawa aikai masa.
Nan kafin in magana ya fara neman layin hajiyan ta dauka suka gaisa bai boye mata komai ba ya sheda mata harda abinda ya faru yanzu a tsakanin su.
Hajiya sai innalillahi take maimaitawa yace ga khadijan hajiya kuyi magana tace kana gidan ke nan yace eh don ban fita ba ina gurin ita khadijan yanzu haka.
Miko min wayan yayi bayan tace ya bata hakkuri ta shiga bani ba abinda nake sai kuka sai fadin take don Allah in rufa mata asiri kada inje ko ina zasu san abinda sukayi tace in ba yusuf din wayan don kuka da yaci karfina na bashi ban san may tace mai ba naji yana fadin in Allah ya yarda hajiya zan shigo din.
Sai kuma ya mikawa laraba wayan ta karba itama sai fadin take insha Allahu hajiya ina tare da ita ko wani lokaci zan bata hakkuri in Allah ya yarda.
Ya dai dan kara min nasiha da nuna min kuskuren tafiyan da nake son yi din tare da ban shawaran in kara dagewa wurin mika lamarina a gurin Allah.
Karshe dai yai muna sallama ya fita muka rufe kofan part din nan laraba itama ta shiga bani baki tana lurar dani illan da fitar mace gidan mijin ta ke jawo mata a gurin kishi.
Da barin ta fahinci halin da muke ciki kamar nuna mata samun nasaranta ne a kaina kukan ma da nake ya daina zo min sai tunanen maganan da Yusuf ya fada ma hajiya sunyi a kaina nakeyi.
Ranan sai dai barci barawo ne ya sace ni ban dade ba na falka gajikin ba dadi abu gamai ciki haka na daure na gabatar da nafila na dade zaune ina mika kuka na a wurin Allah da fatan ya sauke ni lafiya.
Washe gari tunda na tashi nayi sallah na gaida laraba na koma na kwanta ban fito dakin ba barci da ya soma dauka na laraba ta shigo tana fada min ina da baki a falo.
Nafito na samu anty Hauwa da wata kawar tane da nake gani tare da ita ko yaushe ina fitowa tace khadija badai kuka kika tsaya yi akan wanan kishiryar taki ba.
Dayan matan tace ai kuka baima irin matan nan ki dake ki nuna mata duniyan ci in kin yi kuka har ta gane ai abinda take son gani ke nan dama daga gare ki.
Duk namijin da kikaga ya zauna da mace so ne yasa ya kawo ta gidan shi kinga zomu zauna zo mu saba idan ita tana asiri ke kuma ki nuna mata karfin Allah a kan ki.
Anty Hauwa tace bamun zo nan bane don mu hadaki da mijin ki muyi magana yin hakan yanzu gare mu kamar tonuwar asirin ki ne tsakanin ki dashi a gareta.
Shawara mukazo mu baki babu inda zaki kinji na gaya maki a gidan nan dai da bata son ganin ki zaki zauna ki haihu lafiya lau a dakin ki.
Idan kinji na kuda daure ki kirani ko ban gari akwai matar da zan turo tazo nan gida ta karbi haihuwan ki haihuwar ki a cikin gidan nan shi zai kawo nasaran cin galaban ki a gurin wanan matar.
Don matane basu gane ba sun dauka zuwa asibiti a haihu wani abin adone yanzu haihu yanzu ga saporters nan suna zuwa har gida su karbi haihuwa jinin nan da zaki zubar a cikin gidan nan shi zai karya duk wani asirin da ta binne a gidan nan.
Sai abu ya gagara ne ya kama aje asibiti da mata sun sani irin haka ko sau daya ne da sun daure sun haihu a dakunan su don samun sauki a rayuwan su.
Sun min magana mai tsawo wanda har naji na fahinta da zancen su nayi masu godiya anty hauwa ta mike tana fadin mu zamu tafi dama na zo ne don nayi maki alkawarin zuwa yau din.
Matar tace zauna ki gyagije adakin ki kamar ba ayi ba kuma kada ki biyewa ciki ki zama raguwa a gurin miji.
Ki nuna masa dashi da ita basu

110 / 144

Chapters