kanmalane in kwashe kayan a gurin .
May kike tunane haka Deedar har ina magana baki jini ba ajiyan zuciya na sauke tare da mayar da hankalina a gurin shi.
Abinda ya faru yanzun kika sa a ranki ko mai na dan rausaya kaina tare da fadin abin ne kawai yake ban mamaki don naga babu tsarin Allah a cikin harkan ta.
Murmushi kawai yayi ya dauki tsokan nama dake cikin miyan ya kai a bakin shi ya fara taunawa ba tare da yayi magana ba.
Sai da ya lashe abincin tare da turo min plate din a gabana yana fadin kin sani over feeding yau da yawa don girkin yayi dadi sosai.
Haka nake so shiyasa na bata lokacina na girka mashi don nasan zaka so shi saboda na kula da kana son abincin gargaji ya sosai.
Ashe kin fara fahintar halayena yanzu kwarai ina son irin girkin nan idan zan samu don dashi nayi wayau a gidan mu kin sani.
Mikewa nayi ina hada kayan abincin tare da tambayan shi ya zancen da hajiya mama tace tace ka fada na kawo kayan zainab din idan da hali ina son inje ayi sha,anin dani.
Mikewa yayi shima daga inda yake zaune yana fadin ba fa buki bane ko wani abu kayan lefe ne kawai za a kai masu.
Nace ai yanzu kasan an maida abin kamar buki ne duk wani dan uwa na kusa yakan je a tari kayan dashi sai naga zai yi kyau ace wata daga cikin mu ta tafi wurin.
Ita Fati dake can idan taje bai isa ba sai ku dake nan kunje sai dai idan akwai wani abinda zai kaiki dama ba wanan zancen ba.
Ko daya wallahi ban sa ran zuwa yanzu ba ko don karatun dake gaba a wanan lokacin ganin dacewan zuwan mu dai guri.
Dakin shi ya shige ya barni gurin ina gyarawa ba tare da yai min magana ba na gaba hada kayan a cikin basket na shiga na samay shi a dakin.
Ko da na shigo dakin yana zaune yana latsan laptop din shi har na shigo na kara kawar da komai na dakin a inda ya kamata.
Maimakon in hau gadon in kwants kamar yadda na saba yi a kullun sai yana zauna a gefen shi tare da dan kwanto jikina a saman nashi ina sauke ajiyan zuciya.
Muryan shi naji yana fadin Deedar yau may ke faruwa dake ne haka naga wasu sauyi a gare ki.
Ba wani sauyi da ka gani a gare ni dama can haka nake ko ka manta ne da halina kawai dai irin rayuwan da gidan naka ke ciki ne bai gamshe ni ba.
Sosai magana ta taso bashi dariya amma sai ya daure yace dani cikin juyowa yana kallona tare tare da fadin look at me Deedar.
Kallon nasa nayi kamar yadda ya bukata nayi yace gida na ba halin sa ke nan ba ki dai ce matar gidan da kika sama ce halin ta bai maki ba.
Deedar kin san kowa da yadda Allah yayi sa da kuma irin fahintar shi ita rayuwan ta ne haka da zafin kishi irin na rashin fahinta rayuwa nata kawai ta sani bata damu da damuwar wani ba .
Na karbe da fadin wuri dai ta samu nayin hakan don da kunnen ka kaji abinda ta fadi a baya kuna yi watau da kai da ita kun hade kai kuna tauye ma Fati hakkin ta yasa yanzu da ka canza take ganin muna yaudaran ta ko cutar ta.
Murmushi naji yayi tare da fadin kada ki min mumunan fahinta anan mata suke da alhakin saita gida a tsakanin su idan daya ta bada daman da dayar zata taushe jaruntar ta sai alkibilan komai ya koma ga yar uwarta duk kokarin namiji akan yaga yayi adalci a tsakanin su.
Tunda naji kalaman shi na fahinci abinda zancen shi ke nufi watau idan mace tayi sakaci da daman ta sai abokiyar zaman ta ta kwace komai daga miji har gidan a hannun ta yanzu ke nan dabara ya saura gare ni ke nan akan buzuwa.
Bayan dan zurfafa danayi a cikin tunane na sauke ajiyan zuciya ina kokarin mikewa daga inda nake zaune don tuni tun da muka fara magana na raba jikina da nasa ko.
Na juya naji ya riko hannuna ya rike ba yadsa zan iya tafiya naji yace ina son ki fahinci magana ta da kunnen basiri a yadda nai maki shi a dunkule da fatan zaki fahinci mai nake nufi.
Na fahinta na fadi cikin daurewa don nakai iya wuya a lokacin yace ba ina nufin ki biye mata ku dinga hauka irin nata da sunan kishi bane.
Ina son ki gane kamar yadda na auro ta a gidan nan da sunan so a gare ni haka kema na auro ki na kawo gidan nan da sunan so a gare ni.
Sai dai kada ku mata ni namiji ne ina da wanan daman da zan kara kawo wata agaba ta zauna a cikin ku ku zama ku hudu ke nan a gare ni.
Kallon da nai mashi yadan kara jawo ni a gare shi yace ni mijin mace hudu ne Allah ya bani wanan daman kuma ya hore min abinda zan iya karawa dashi ai kin san aure kuma sunna ce ta Annabin rahama.
Don haka ne nake son ki fahinci zama da hali mai kyau ko akasin haka mafitane a ko wacen ku idan Nafisa tana da wani hali da bai gamshe ki ba a gidan nan.
Kina da daman dake zaki amfani dashi wurin toshe wanan kafan ki dora hakin ki na gari ki gyara min wanan gurbin da taba da kafa a gare shi.
Shiru nayi ina sauraren maganar shi wanda yake min kamar nasiha ko fadakarwa a gare ni kokarin janye hannaye na nayi daga nasa sai naji ya rike ni gam ya ki raba hannuna daga nasa.
Yace Deedar ki sa a ranki wanan ne kaddaran ta farko da kika fara fuskanta da fatan zaki rugumi rayuwa a yadda yazo muna.
Yanayin rayuwan zama na da nafisa kowa ya gani zai dauka ta fi karfi na ko wani abu makamancin haka ni na bar wa cikina wanan dalilin.
Yanzu naga kamar magana ta tasa zuciyar ki ta fara kishina jin zan iya karo wata a bayan ki kuma nan gaba.
Yanzu wanan zancen da zai sa ki lalabanj kina ririta ni duk wata mace dake gidan nan dama wace zata zo ki nuna masu cewa ke din ta daban ce daga cikin su.
Fisge hannuna nayi daga gare shi na haye gadon na kwanta tare da juya baya a gare shi can naji ya gama abinda yake ya hawo gadon ya kwanta.
Hannun shi yakai a jikina na lumshe idanuwa na muryan shi naji yana fadin Deedar badai maganar fahintar a tsakanin yasaki shiga wani yanayi ba.
Na juyo a cikin wani courage dana samu ina fadin na rungumi kaddarana tun ranan da na shigo gidan a sunar matar sunna a gare ka .
Zanso ace na kasance daga ciki diyan albarka masu biyayya ga iyayyen ga duk halin da suka riski kan su a ciki.
Don haka ni na dade zama da shirin duk wani rintsin da zan fuskanta a gidan nan ko wace kallace matukar ban saba wa mahalici na ba da hakan.
Wani kallo yake aika min ina maganan a take idanuwan suka canza launi ganin haka na so juyawa in koma yadda nake da farko naji ya riko ni.
Kokawa irin ta ma aurata muka fara a lokacin nayi nasara haye ruwa cikin shi nan wasan tamu ya canza sallo a dakin mun dauki lokaci a tare muna farauta wa juna rai a inda ya sha mamakina a wanan dare.
Ko da gari ya waye ranan mun makara daga tashi sallah a gurguje na karasa duk wani abunda zanyi na fito bayan mun karya muka bar gidan.
Ban hadu da Nafisa ba a falo ashe bata gidan nan ne tayi asubacin batin gidan zuwa wurin madam kan matsalan da take fuskanta.
Ban makara daga shiga lectures ba a ranan duk da lating da nake gani nayi a lokacin sai dai jikina nake jin yawan kasala yana damu na sosai ga wani barci da nake ji wurin kwantawa kawai nake bukatan in samu.
NAFISA a falo madam cikin takaici take magana kan sauyin da take gani ga madam sai data gama fadin maganan da ke tafe da ita iya son ranta madam din ta karbe maganan da fadin.
Nafisa kema kin san wanan yarinyar fa ba irin ta farkon bace don wanan kina ganin ta duk da tana da karancin shegaru idanuwan ta wallahi a bude suke.
Banyi zaton ta shigo gareki a banza ba yanzun dai matsalar mu ai wanan cikin da kika samu ne gashi yazo maki da lalurar rashin yin motsi mai karfi da sai mu bazama mushige duniya can kasashen yarbawa da iyamurai kin san su aikin su tsafi ne kamar yanka ne.
Nafisa ta kalli madam tace ke nifa ciki ba zai hanani yin komai ba wallahi idan zamuje a shirye nake ko yanzu kan wanan yar iskan.
Wai fa a gaba a kan idona na samu wai tana balle samad anineyar rigan shi shiko yayi tsaye kamar wani soko dashi.
Dariya madam tayi tana fadin ke makin san halin maza ai idan suka samu sabon sauyi sai fa kinga abinda ba daidai ba a idon ki.
Ni yanzu shawaran da zan baki shine ki bari har ki haife sai mu san abin yi don yanzu koda munyi wani abin walahi barnan kudin ki kawai zakiyi.
Keda, keda dama yanzu da zaki ta karban kudi da suna cikin jikin ki kina tara ma tafiyan mu kin ga kafin nan kinyi muna tanadi mai kyau da zamu ci kaniyar su da tushe.
Jin maganan kudi ya shigo yasa Nafisa washe baki tare da fadin kin kawo magana madam don ni ban ko kawo wanan ba a raina ina dan banzan hauka kamar yadda yake kirana dashi.
Madam tace kin fahince ni mutumiyar ai ba karamin shiri zamuyi wa shegiya ba sai ta raina kanta da ta shiga ragan da ba nata ba.
Wallahi madam na tsanin wanan yarinyar ban taba dauka samad zai ga wata mace har ya ta so rikita shi ba haka.
Madam ki duba min may na rasa a jikina wanda yasa samad yin aure madam tace ikon Allah kin fasan halin namiji fa nafisa.
Balle shi da iyayye suka bada tasu gudunmawa ga auren shi baki ga sai da suka darje suka zabo mashi mai irin zubin ki ba ta yadda zai iya fudewa a kanta ya barki ba .
Basu san wasa suke damu ba jin mu suke basu san sherin mu ya wuce haka ba ke zan iya cewa gara da yai maki ita yanzu ba sai daga baya ba lokacin girma ya kama ki baki da moriya sosai ba.
Ai babu auren nakasa ga mace kamar sai lokacin da girma ya fara kama ka a auro maki kishiya da zata zo tana haihuwa kina kallon ta.
Badon kin ma yar iska wanan dan bakan ba ai da yanzu tana nab da kunshi a gaban ta wai ciki.
Da sauri nafisa tace dakun daure ni ranan don bansan inda zan saka raina ba shiyasa na haka ma yan iska shi ban sake bi ta kanshi ba.
Shine daidai wallahi don gudun bacin rana kizo baki haka ba azo a samu akasi ya haye yar iska tazo ta dauki ciki asirin mu ya tonu .
Ina ai ba zan ma yarda haka ya faru ba a tsakanin sai dai gani da hange badai wanan ba nasan don haka ne ai yake lalaba shegiya don kada ta tona mashi asiri mutuncin shi ya zube a gane shi mace ce.
Kin gane ke nan amma ya kamata fa ki duba bakan nan don kin dade da haka shi ko yana a haken har yanzu kada azo a samu matsala kuma.
Zan duba yau din nan dana je gida amma inda na aje shi ai banyi tsanmanin wani zai iya ganin ba ma ga kuma kwalban dan agadas shine ma banga wani tasirin shi ba koda yake ai yau suka fara kwana dakin tare.
Dan iskan kamar yasan abinda nasa ranan sukaki kwana a dakin sai dakin ta suka je suka kwana shiyasa nake fada maki ai da shiri shegeya ta shigo maki.
Sun dade suna magana daya a karshe dai ta yarda da shawaran madam din na sai ta haihu kafin su yi wani yunkuri a kaina da maigidan.
KHADIJA.
Tunda nayi sallah nakai kwance sanan carpet din masallacin ina jin dadin yanayin wurin na dan shiga na a hankali.
Maryam ta idar da sallah ta juyo gare ni tana fadin yau yaya dai madam nace wallahi maryam wani irin barci nake ji sosai jikina duk kasala sa nakeji.
Yau ko zamu samu leka anty salbiya ke nan nace zamu bari dai in dan kara hutawa gashi kuma yau ina son attending din last lectures dina wallahi.
Tashi mukayi muja shiga gun lectures din yana fita muka nufi gidan salbiya din don jin dan karuwan da zamu samu a gurin ta.
A gidan anty salbiya ma kwance nake ina sauraren bayanin da take min ka kwalliya da yadda zan dinga shiga wai ko wani lokaci ya kamata ace mace tana yabayin shigar da takeyi tundai idan oga yana gida tare da iyalin shi .
Ta juyo gare ni tana fadin idan kin bi wanan hanyar zaki ci galaban kishiya sosai wallahi don ko wani kasa suna da kalar tufafin da suke jin dadin sakawa a jikin su.
Ashe kin ga ku matan kasar nan ko wani shiga kukayi yana daukan jikin ku sosai don baku dogara yanzu da kayan aladan ku ba.
Kin ga kuma su mazan yanzu abinda ke kara ingizasu kenan gun wasu matan sai ki dage wurin saka tufafi masu jan hankalin namiji nasan ko tace zata koye ki abin ba zai dore ba gare ta don ko bata saba ba da hakan idan ma ta saba ke zaki iya kirkiro naki sallon kiyi.
Yanzu dai kinga ko anan ai mun samu wani babban mafita akanta ko mukace hakane anty sannan ta juya da fadin sai gyaran muhali.
Yazanan to part din ki yana da wani kamshi da sai a gunki za a ji wanan kamshi naki ne ke kadai komai na gurin ki ya karba da wanan kamshin.
Ina mai tabbatar maki duk lokacin da yaji wani kamshi makamancin haka zai tuno dake a ranshi haka nau,in abincin ki ya zaman to kina canza shi lokaci lokaci ba kulun abincin ragayen mata ba irin su indomie taliya da sauran su din nan.
Ke koshi miji fa yana bukatan gyaran kansa daga gare ki kamar kula da tufafin sa da undies din maigida da sauran abin amfanin shi irin su takalma da sauran su bawai sai tufafin jikin shi ba kawai zaki kula akan su ba.
Wani amai ne ya taso min na toshe baki na da sauri na nufi toilet din dake falon su banyi wani abin kirki ba na dawo idanuwan su a kaina har na zauna.
Tace ikon Allah anyah amarya bakin halbu bane kuwa wanan irin amai kuma haka fa nace anty ina ganin rashin karyawa ne da bana yi sosai ya jawo min ulcer.
Dariya sukayi anty salbiya tana fadin Allah yasa ulcer mai tushe ne ya samu to yanzu barin barku kije gida ki huta don kina bukatsn hutu a tare dake.
Don tun shigowan ku na fahinci hakan ki daure dai ki adana wanan sirin idan son samu ne sai idan ya fito a gani a jikin ki.
Don shi ciki kamar hasken rana idan ya haska babu abinda ke boye shi ko mijin ki ki bari sai ya gani da idon sa .
Don wasu mazan yawan doki na saka su jawa mace matsala akan sauran al,umma basai kishiya kawai ke kishin haka ba.
Idan baki yai yawa gun abu sai kiga abin na zuwa da matsala sosai don baka san bakin wani ba don baki dafi ne sosai wallahi.
Nace ba komai yanzu anty hasashen kune kawai hakan amma dai zan kula din idan haka ya faru maryam kan bata samu bakin magana ba sai kallo na take yi.
Mun bargidan ganin banjin dadi yasa maryam ta biyo ni gida yau tunda ba nice da girki ba mun huta ina zaune a falo ya kira layi na.
Nakai hannu na da kyar na dauki wayan tambayana yake idan mun gama lectures din a zo a dauke ni na amsa mai da kyat da gani nan na dawo gida yau banjin dadin jikina ne.
Yadda yaji murya na yace da sauri may ke damun ki nace ulcer ne yace kin gani ba dama nasan haka zai iya faruwa ai na fada maki ki dinga cin abinci bakya ci.
Nace da kyat bafa rashin cin abinci bane ulcer ciwo ne kawai yace yanzun dai ke dayane kuma gashi aiki nakeyi nace muna tare da maryam ne ta rakoni gidan sai ta zauna dani.
Ok maryam ta kyauta ki samu