ki sani banda niyar aikata komay yanzu a gare ki amma ki aje a ran ki time will soon come .
Ko yanzu ke kikaja in maki haka da wanan bakin naki da bai taba mutuwa don ki san irin abinda zaki fada ma mutum.
Fita yayi ya zaya ya bude min gefen da nake zaune na sauko motar a hankali na fito don girman jeep din nasa.
Mun fara tafiya naji ya rada min a kunne anya kuwa ke ma ba buzuwan bace deedar wanan irin gashi da jiki mai dadin tabawa haka fa ?
Hararan shi nayi idon shin kyam a kaina ya sake fadin nayi haka don ki san har gobe nafi wani banzan dake zuwa wurin ki komai.
Banyi magana ba don mun kawo bakin shagon haka muka shiga a jera da juna sayaya nai wa mommy har da gaiya don har yaran ta na zabawa abu.
Ya kalli kayan mai makon inji yayi korafin sunyi yawa sai ji nayi yace kina ganin wanan kayan sunyi ke nan idan kuma kin sai wa yaran mommy ita kadai su sauran yaran anty amarya fa ?
Dole na koma na kara zaba muryan shi ne naji a bayana yana fadin ki zaba ma su ummi da su hajiyan mu kayan suma.
Sosai ya kashe kudi bayan na mommy dana su iyan bawa gana su hajiya mama dana zaba masu super masu kyau su ma.
Mun kai ya biya ko dar nanga yayi ba da akai mashi list din kayan aka saka ga wani katon buhu zuwa inda motar shi take tsaya nayi ban shiga ba sai da ya zauna ya leko yana fadin shigo mana mu tafi.
Nace dashi katafi kawai zan bi taxis in koma ni da sauri naga ya bude kofan motan ban san lokacin da na bude na shiga ba muka bar wurin.
Sai da mukayi nisa naji yace kina zaton abinda ya faru zai kara faruwa a tsakanin mu ne yanzu idan haka kike tunane kinyi kuskure.
Don ni ko matana dake gida sai naga dama nake waiwayan mace do ba haka nake ba kowani lokaci.
Sai dai nayi mamakin ganin yadda kika narke min a jiki kaman dama jira kike in taba ki haka ya nuna min ke nan dama a jirace kike da hakan ya faru.
Ban san lokacin da nace mai mugu mayaudari kawai macuci ba wanda ya taba min haka a duniyan nan sai kai kai kasan wani mace ta narke ma ajiki dan, , , ,
Hannu yakai zai kara kamoni na gwace da zafin nama yayi murmushi yace gobe idan halin ki ne ki kara cika min baki haka.
Ba sai ka kara ganina ba zakace in cika ma baki kaji dadin yaudaran da ka sabayi wa mata a kaina.
Zaki bar Nigeria ne ko mutuwa zakiyi don wanan ne kadai abinda zai hana in ganki in kara kallon wanan suran da kike kasawa a kasuwa in riga kowa kwashewa.
Haushi bai barni na sake magana dashi ba sai juya mashi baya danayi kawai shima bai sake magana ba sai da muka kusa tsayawa naji yace
Wallahi shiyasa kike kara burge ni da wanan halin naki na dan juyo na harare shi yace yes i mean it da wata ce sai tayi nata sayayyan amma ke naga ko tsinke baki dauka a shagon ba naan kuma dole kin ga abinda zuciyar ki ke so a ciki .
Kinga ke nan kin nuna min abin mutum baya gaban ki idan bai baki ba yana da kyau hakan keep on da wanan hali.
Sai dai ai na biyaki ladan ki ko ina ganin ba sai an rubuta maki wani lada ba ko bani wanan lafiyan fresh body din da kika yin kin more ai ke ma.
Ya tsaya da motar na bude najita a rufe na juyo na kalle shi nace bude min in fita hug me for d last time tunda kin ce baza mu sake haduwa irin haka ba.
Malam ka bude min mota in fita ni ba yar iska bace ka sani wallahi ban sani ba zan dai sani nan gaba in Allah ya yarda ban fahinci abinda yake nufi ba bai kuma bude min motar ba yana jiran wai abinda yace.
Na sake cewa da kai fa nake magana ka kyali ni yace even peck kiss yana lumshe ido kamar zan kai kiss din sai na cije shi a kumatunshi.
Yana shafa wurin yana fadin wassh ko hakan ai na gode zan tunaki watarana na taba haduwa da wata manya yar Niger mai zubin half cas.
Ya bude motar tare da fadin thanks ki kula da kan ki don Allah don kin bar min tarihi nace mugu kawai azzalumi mayaudari da sauri na fita do kada ya kara rufe kofan yana dariya yaja mota tare da min horn ya tafi .
Ko da na shiga hostel na samu har martam ta kwanta ina shugowa tace kun dawo tare da duban time tana fadin ban dauka zaku dade haka ba ai.
Zama nayi jagwal a wurin fuskana kawai zaka kalla kasan ina cikin bacin da sauri ta mike zaune tana fadin wani abu yayi maki ne.
A takaice nace may ye bai mun ba yau maryam AA ya cuci ni ya shammace ni sosai wallahi da sauri naga ta fida ido waje.
Nace ban taba sanin dan iska bane sai yau wai nifa AA ya ruguma maryam har da taba min kai kiji min dan iskan banza.
Ajiyan zuciya naji ta sauke tare da fadin wallahi har kin saka gaba faduwa na fa dauka ko raping dinki yayi wallahi wani irin harara nayi mata nace ya ma isa.
Tace cikin dariya yadda kikai maganan ai dole mutum ya tsorata yayi zaton hakan ne ya faru a tsakanin ku.
Nace may ye marabin wanan da hakan don Allah bada hakan ake farawa ba har aje can daga magana kawai sai naji ya rungumay ni don kawai ya nuna min dan iska yake macuci kawai.
Tace akan kayan dazu ko na kada mata kai nace ashe kin san abinda zai min kika bari nabishi ke nan tace kema kin faye baki wallahi .
Ai gara da kika zabi law don kin iya bakin ki don Allah bani labari nikan in sha dariya don nasan yau ashe yasha zagi a gunki.
Nace ban sani ba cikin hararan ta ina mike tace indai gulma kuka kai shi ke dashi kuna son juna kuna wani noke noke .
May zanyi da wanan dan iskan ni bakiji ba ma wai shi ko matan shi sai yaga dama yake kara waiwayan mace idan yaga dama.
Dariya mai karfi ta kwashe dashi tana fadin ashe akwai aiki kuwa kuma yake sha, awan kara mata fadi dai yayi wallahi.
Toni ina ruwana da rashin kula matan shi ko ya kula ko kada ya kula duk uwar su daya a gun khadija don ba abinda ya shafe ni da hakan na fada mai.
Nan nabarta tana min shakiyanci alwala na dauro ina son yin waka don kada ta zarge ni haka na fito na tayar da sallah na gama na kwanta banci komai ba ranan.
Sai dai ba barci nayi ba don tunane ya hana ni shakat a zuciya na don da zaran na rufe ido abinda ya faru tsakanin mu ne yake zuwa min.
Har dai barci yazo ya dauke ni ranan na makara da sauri na mike ina shiryawa sai ga wayan shi ya shigo min.
Kamar ba zan daga ba kallon da maryam ke min yasa na daga wayan murmushi naji yayi tare da fadin nasan dai kamar yarda banyi barci ba kema hakan bazaki barci ba daren jiya.
Akan may zan hana idona barci nace mai, yace akan dan gidan mommy mana kema kin sani , nace Allah dai ya sauwaka kana ganin kayi wani abun gwanewa kenan, mutumin da ko runguma bai iya ba sai ta hanyar karfi, zai sa na kasa barci na kashe wayan.
Yayi kiran duniya naki daga wayan sai ga text din shi ya shigo min kamar haka.
Saboda kin san kin zuba min dahin ki a jiki daren jiya yasa kika fara garani ko may ?
Niba macijiya bace ai, balle in zuba ma dafi
Na tura mashi, ba a jima ba sai ga amsa shi kamar haka ,
Kin fi macijiya dafi karfa ki manta ke mace ce, mace ko shu,umace ko wace iri ce ita tasan sallon sheri ga da namiji.
Kai dai ka sani da kayan sherin ka in ma dafi ne kai kazubawa kan ka bani ba ya karanta yana dariya bai san shigowar Nafisa ba dakin.
Sai jin muryan tana tambayan shi kaidawa ke waya haka kake dariya ?
Dakewa yayi duk da kaduwan dayayi cikin ranshi amma a fili cewa yayi da ita nida Yusuf ne don yasan ba karatun boko ta iya ba balle ta amsa ta karanta.
Ba don ta yarda ba ta kyaleshi kawai tana zargin shi a cikin ranta don yanzu ya fara bata tsoro gaba daya don ya daina sayin ta da yake yi a da can baya.
Daga haka ya sauka kasa yana yana kiran yaran aikin gidan shi ya shigo mashi da buhun da ya dawo dasu jiya.
Ya sa akai masu dakin da su mommy suke tare dasu iyan bawa a gidan daidai lokacin Nafisa ta sauko kasa tana fadin Sabel wanan kayan haka daga ina kuma ?
Yaro gidan dan yaren su na buzaye yace maigida yace ya dauka yakai dakin dabakin shi suke ciki tabi buhun kayan da kallo nan ta so sanin abinda ke ciki.
Don haka tabu shi a baya wai taje da sunan gaida mommy yau da kwana yana zaune saman kujeran dakin suna hira da iyan bawa ta shigo tana gaidasu idon ta akan buhun dake gaban shi nan ya fahinci buhun ta biyo a lokacin don ganin may ke ciki.
Idon ta ya gano mata atamfan da ya fara fitarwa kasa yana son fitar da sauran sai gata ta daure fuska tamau idan da dane da ya shiga hankalin shi ga yadda ya ga ta daure fuskanta.
Sai ci gaba da fitar da kayan yake yana bin sunaye su yadda na rubuta ajikin ko wani ledan kayan yana ajewa gaban mommy bai fara bayani ba ta juya ta bar dakin a fusace cikin bacin rai.
Sai bayan fitan ta daga dakin ya fara yiwa mommy bayanin kayan tare da dora ma ko wani kudi a saman kayan yace suyi dinki sai Allah ya dawo dashi lafiya zai shigo yayi masu ban gajiya.
Kallon shi mommy tayi da kyau bayan ta gama sauraro shi tace wanan hidimar yayi yawa haka babangida don haka kabar kudin nan abin kuma ya koma biya , ?
Mu da mukazo aikin lada zaka saka muna da wanan irin alherin haka mai yawa gaskiya hakan bai muna dadi ba gaba baka son inzo zama da diya ta ke nan in Allah yayi abin.
Murmushi yayi yace ko baku zo nan ba mommy zan iya maku fiye da hakan don haka wanan ba komai bane Abba yace a tura ku gida yau kafin in wuce.
Nasan ya kiraki ya fada maki komai ai don haka idan da sauran wani abin sai ku fada min a sayo maku kafin ku wuce na kuma gode kwarai da kokarin ku a kaina.
Sai dai ayi hakkuri da yanayi matar gidan don Nafisa sai hakkuri nima dai kun ga shinakeyi.
Ka dauki kudin nan ko ka rage dawainiyar yayi yawa haka abin ya zama kamar biya mu kayi ke nan ya mike yana murmushi yana fadin ba komai iyan bawa ai yima kaine.
Na shirya driver da zai sauke ku idan kun gama sai aimin waya zan dan leka office don tafiyan mu sai dare zamuyi shi akwai dan sauran lokaci zuwa yanzu.
Godiya sosai sukai mai ya fita nan dai mommy suka fara shirin tafiya don ba a ketare maganan Abba a gidan.
Yana fitowa bai koma ciki ba ya nufi hanyar fita daga gidan muryan Nafisa yaji a bayan shi tana fadin dama nasan abinda ya zaunar da su ke nan a gidan nan tun bayan suna basu tafi ba kamar yadda kowa ya wuce.
Suwa ke nan kike nufi wanda kasai wa kaya bada sani ba yanzu Allah ya tona ma asiri na gani do baku so in gani ba.
Wai nafisa kina da hankali kuwa iyayyen nawa ma bakin ciki kike dasu akan nayi masu alheri tace ai ba su kadai suka wahala a gidan ba har dasu Yanyala sun wahala .
Don may ba zaka saya masu tare ba ka ware naka kadai watau sune ka sani ke nan kai ya girgiza cikin kunan rai yace ba laifin ki bane sai kawai yaga ta sha mai gaba ta inda zai wuce ta.
Hayaniyar su ne ya fito dasu mommy waje ganin su mommy ba sa ta fasa ci mai mutunci ba mommy ce ta hana shi magana.
Duk ta hade dasu mommy tana zagi tare da fadin tayi ma kowa nashi iyaka da gidan tun da ba zuwan arziki suke yi ba jifa samun wuri a gurin wanan matar ita ha gida taf da yan uwanta kullun sai kara yawan su takeyi a gidan.
Kowa yazo da sunan ganin ta sai ya nemi wuri ya zauna ba maganan zuwa gida kuma gare su an shafe ke nan.
Haka ya fita gidan ranshi bace ranan su mommy sun ga fitsara a gurin Nafisa inda tayi ta aiban ta su suna ji suna gani ba abinda zasu iya yi tana gani taci gaban su.
Ranan haka dai ya wuni cikin bacin rai halin Nafisa ya jutayin irin zaman da suke na rashin jin dadi a gare shi kuma bai jin zai iya rabuwa da ita ko kadan.
Bayan su mommy sun gama shiri suka kirashi yace gashi nan zuwa ya samay su a shirye don haka basu bata lokaci ba suka fito da kayan su Yusuf suka loda a mota sukai sallama dasu suka tafi suna kara bashi hakkuri.
Da yamma ya fito cikin shirin shi ya samay ta a dakin ta tana zaune tana waya ganin shi bai sa ta katse wayan ba sai data gama yake fadin su zasu tafi.
Wani sabon lalura ta kirkiro mashi aladole kudin da take hasashen ya kashe ma iyayyen nashi sai ya kashe mata su bayan ya riga da ya sallamay ta da safe ta lissafa mai abinda take so ya bata.
Nafisa wai may zakiyi da kudin da kike karba ne haka ya tambaye ta wani kallo tayi mashi tace idan zaka bani ka bani ba sai ka tsaya ka tambaye ni ba kuma ina sin idan ka dawo zan tafi gida inyi gyaran gidan mu na can.
Dole ya bata daga cikin kudin da zaiyi amfani dashi don kawai su rabu lafiya da ita.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Wanan magana ya tsaya min a rai sai dai gaskiya ban aminta da maganar maryam ba don ba zan iya bude baki na in roki namiji koda kwandala ba balle har mota.
Ina zan kai mota idan ya bani a gida ince dasu ina nasamo mota kana wa yaban motan akan wani dalili zai min kyautar mota haka inma har zai bani din.
Gaskiya maganar ta bai karbu ba a wuri na sam zandai gwada mata nima ba kyale bace zan mata abinda sai tarena kanta da kanta anan na aje maganan azuciyata.
Sai dai ban fada ma maryam abinda na yanke a zuciyana ba nabar abin a raina don ita maryam ba abinda ya damay ta wanan nake ganin a gurin su ba komai bane hakan sai abin alfahari.
Washe gari na mike kamar komai ba faru dani ba ajiya ganin yadda na sake yasa maryam dauka ko na dauki shawaranta ne.
Ban damu da fita ba don yanzu karatuna shine a gabana ranan mun dawo maryam ke tambaya na wai har yanzu taji shiru mana ko ban buga ma AA waya bane akan batun motar.
Banza nayi da ita kamar badani take magana ba sai da ta sake tambayana nace mata don Allah maryam ki bar wanan zancen .
Don bashine a gabana ba yanzu abinda nazo yi nake fuskanta ban son abinda zai raba min hankali ko kadan.
Amma dai khadija kin kwabsa wallahi don kawai kin tambayi AA abu shine kike ganin rage ajine a gurin ki wanan ai ba komai bane wallahi.
Yan mata nawa samari ke sayawa mota kuma a zauna lafiya so maye bai sakawa a yi wanan ai kara ma kanki daraja ne ba wani abuba.
Wani kallo nayi mata nace rokon shine karin daraja ga mace rokon ma irin na rashin hankali haka wai ma idan har ya bani motar ina kike son in kai mota yanzu.