zata iya insha Allahu.
Suna shiga falon gidan sai da sukai mamakin iri hamshakan matan da suka samu a falon ko wace ka kalla tayi murtuk da fuska kamar suna zaman makoki a gidan.
Suna gani shigowan su ko wace ta sako masu na mujiya don dama ba sani AA din sukayi ba sai faman jijiga kai sukeyi kowa da abinda take rayawa a zuciyar ta.
Cikin karfin halin ya fara masu magana tare da fuskan ta su yana fadin lafiya nagan ku haka a wanan lokacin.
Nafisa da tai wani wujiga wujiga da ita a tsakiyan su ce ta fara magana cikin bacin rai sai madam ta tare da da fadin haba Alhaji kai muna laifi mun taru kuma har kana tambayan mu ko lafiya ka gan mu a nan ?
Wani kallo yayi mata da ga haka bai kara furta komai ba sai kokari ciro wayan shi da yake yi daga aljihun shi yana duba lamba.
Hello IG Fam sec ne na FLAS ke magana ina son yanzu a turo min yan sanda gida nane zubar suka fara mikewa tsaye suna fadin ai abin bai kai can ba daga zuwa abin arziki abu zai zamo tsiya kuma.
Kafin haka sun watse sai madam ta rage nafisa ko tana kan bakin ta tazage shi ta zagi Yusuf da iyayyen su zagi na fitan arziki take aika masu.
Madam ne tai magana tana fadin suyi hakkuri ran Nafisa ne ya baci da ya fada mata tun farko ta san da maganan ta shirya da haka bai faru ba tunda tana da masaniya.
Yusuf ya watsa mata kallo daga inda yake a ranshi yace kaga shegiyar kilaki maikai mata ga halaka watau a fada muku ku shiga ku fita ko kafin a farga zancen ya rushe .
Sai dai a fili cewa yayi banda abin Nafisa may ye na tayar da hankali haka kan kishiya tunda ba a kanki zata zauna ba.
Gidan ta daba naki daban maye na damuwar kan ki haka da fitina a hasale tai saurin fadin wallahi babu inda zaku kaita nan dai zamu zauna tare da ita.
Ko wace shegiyace zata shigo ta samay ni anan in ga damay zata zo wani kallo ya watsa mata lokacin da take fadin haka na.
Maganan da madam ke masu a cikin lalama yasa suka zauna don a sulhunta magana a tsakanin su ta nuna an mata laifi don ba,a fada mata ba don haka an munafuce ta.
Yusuf ne yabata hakkuri yace nan kan anyi kuskure gaskiya kuma ko su daurin auren yazo masu a bazata ne ta sake cewa don may bai fada mata tun farko yana neman aure ba.
Yusuf yace wanan kuma ba dole bane saboda kwanciyar hankalin ku yasa ya boye maki ne man tace dashi munafuki ai duk shirin shi don ai mata haka yace ya dauka shine ya hada auren.
Zata fara hauka AA yai magana yace ke dakata idan abin da kuka zaunar damu ke nan kuyi muna bazan lamunci haka ke uwata ce ko ubana da dole sai na fada maki komai nawa aure na nakara idan zaki zauna ki zauna in baki zama kofa a bude yake maki ban tsare ki ba.
Ke ba wata kika shigo kika sama a gidan ba ko nayi maki alkawari cewa bazan kara aure bane nan gaba tace eh lallai samad na yarda sun gama dakai.
Tunda ka dubi idona yau kana fada min magana haka so ranka madam ne ta katse ta gada ta sake layi a gaban su yadda taga ta burkice komai tana iya fadi.
Tace ya isa haka Nafisa ki kwantar da hankalin ki ai magana na fahinta a tsakanin ku in ba haka ba zan tafi in barki bazan iya ba gaskiya.
Sai lokacin ta natsu don tasan da gaske madam keyi zata iya wucewa ta barta dasu kamar yadda tace din.
Yisuf ne yace yanzu may kuke so ayi Nafisa tayi caraf ta sake fadin ban yarda a kaita wani gida ba can a nan zamu zauna da ko wacece a gidan nan .
AA din yace haka yayi maki tace eh sai kuma motar da zaka can zamin ka kuma sake mi sarkoki na da sauran abubuwan bukata na.
Dama yasani maganan ta da haukan ta ba zai wuce kudi ba yace bayan wanan fa tace idan kai haka sauran zai biyo baya.
Haka dai sukai ta bugawa har ta yarda ta dan lafa haukan ta barsu a zauna lafiya yace madam itace sheda don idan sun tayar da wani fitina daga baya zai dauki mumunan mataki akan su.
Bayan ya raka Yusuf ya tafi ya dawo dakin shi ya na rage kayan jikin shi tare da neman abinda zai kora ma bakin shi.
A dakin Nafisa kuma madam ne tare sa ita dasu Yanyala madam ke fadin ke kina da hankali da zaki ce a kawo ta gidan nan tace madam nasan halin samad sarai don haka bazan yarda yakai ta wani gida ba tace da ita tunda ke kika zabi hakan shike nan ai.
Amma ina ji maki tsoron abinda kaje ya dawo tace madam nine fa ban tsanmani akwai wata mace a kasan nan da yanzu zata girgizani ba kai ko a cikin jinsin mu na buzaye ta fito banji zata iya kai ni a gurin samad.
Barni dasu daga shi har ita har wa yanda suka bada goyan bayan yin haka gare ni sai nayi maganin su daya bayan daya wallahi.
Haka dai suka rabu da madam din tana kara karfafa mata abinda zata sun aje kan washegari zasu maiduguri suga malamin su idan sun dawo sai su shirya su ketara camaron inda sukaji labarin sabon malami mai tashe.
Allah ka shirya shirya muna zukatan mu kasa mufi karfin zuciyar mu musan Allah keyi ba mutum ba ya bamu ikon dogara da shi.
Nafisa ta raja,a da boka da malam suke yi suke iya sa aso ka ta ko wani hanya ansan asiri gaskiya ne amma kuskuren ne mace ta kauce da yawa irin haka ba abinda zata kai kukan ta ga Allah sai dai gurin wanin Allah din.
Shima kuma wanin ga Allah subbahanahu wata,ala ya dogara don ko sihirin da sa,an ubangiji bokayen ke yin shi don may ke ba zaki zauna kiyi a cikin dakin ki ba sai kinje gurin wani .
Yanzu wasan ya fara yan uwa ku biyo ni kuji zaman kishin da buzuwa da mijin buzuwa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU.
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Mun dauki lokaci da maryam a dakin muna magana guda kan zaman gidan AA din ida maryam ke fadin ni ke nike jiyarwa a gidan nan.
Nace nima tunanen da nake kenan wallahi don abinda nagani jiya ya matukar ban tsoro wallahi.
Shiyasa nake son mashi magana ko in koma hostel in zauna ko kuma ya sama min wani guri na daban da zan zauna kada yazo bai nan su sameni su illanta ni a banza.
Dariya tayi tace kina haukane da zakice zaki koma hostel da zama da auren ki ko an gaya maki shi mahaukacine irin ki kidai zuba ido muga matakin da zai dauka akan su.
Ai shi ba jahili bane sun mashi haka ina gake dole yai wanan tunanen nasani cikin ranshi nace wallahi maryam bari kiji indai ba zai dauki wani mataki ba akan haka da sukai mai ni zan daukarwa kaina don zaku neme ni ku rasa a gidan nan.
Tace ina zaki nace nina sani ai don ba zan zauna wasu banzayen fulanin su illantani ba ga banza dariya ta kwashe dashi tana fadin.
Wallahi sai kin zama jaruma a gidan nan tunda kinga sun fara haka don dai ba wai ba wata rana zai zo akanki ranan ko da mun sha dariya .
Hararan ta nayi ina fadin Allah ba zai kawo ranan ba balle ku sha dariyan muguwa kawai kofan falon aka turo nasan shine don babu mai shigowa inda nake in ba shi ba.
Maryam ta dan shiga kamay kamay tana gaida shi yace maryam yau kin leko mu ne gidan tace na yi kewar mutumiyar tawa ne nazo ganin ta.
Dan murmushi yayi ya kalleni fuskana a daure yake tamau don haushin abinda ya faru jiya nake ji a rana har wanan lokacin .
Kimun list din abinda kike buka za,a shiga kasuwa sayayya yau ya fada yana kallon cikin fuskana ban bukatan komai idan ma ina bukata ga maryam nan sai ta sayo min.
Maryam kina kallon yadda nake fama dai da mutumiyar taki ko har yanzu ita bata dauke ni da wani matsayi ba.
Dan dariya tayi tana cewa haba tama isa haka dai halin mutumiyar taka yake ai dama da sannu zata bar wanan halin ta juya wurina tana fadin ki fadawa mutane abinda kike bukata kin tsaya jawa mutane aji.
Maryam idan ina bukatan wani abin sirina dole sai wani yaji abinda nake so saboda ban san ciwon kaina ba komay wani zai tafi sawo min abu.
Au kin fi bukatan abaki kudin komai da zaki saya a hannun ki ke nan ya tambaya yana tsaye nace idan dai bakai zaka da kan kaba hakan yafi mun sauki.
Murmushi kawai yayi ya sake gaida maryam din ya fita daga part din maryam ne ta kalle ni tana fadin wallahi ban taba zaton haka yake da saukin kai a gidan shi diba yanzu lokaci daya ya gano nufin ki.
Kuma har ya yarda shi isa buzuwan nan take yadda take so a gidan nan kema gashi yanzu kin fara shimfida naki mulkin na gani.
Don Allah khadija ki bi mijin ki asannu ki gama fahintar halin shi amma hankan da kike cikin garaje ba daidai ne ba.
Nace maryam could you believe cewa itace yanzun haka mai bada sakon zan zaune kishiya irin wanan yar renin wayon ta sanan sirina watarana mafa ai sai tai min gori akan hakan.
Gara tun wuri in kwatar wa kaina yancin haka yafi min alheri tace badai kina nufin har sun shirya ba ne ?
Nace gashi kin gani a zahiri zai masu sayyan suci suji karfin kara dukan shi gobe idan yai masu ba daidai ba.
Kai wanan abin akwai daure kai a cikin sa wallahi yana da saukin kai sosai wallahi nace na dole ba ba dolen shi yayi saukin kai ba tunda ya zama mijin tace.
Inba shi ba zaizo ya tambaye ni wai may za a sayo mi nace dashi ina bukatan wani abin shine.
Nauyin dake kan shi ne na hakan yake son saukewa khadija banda wani nauyi a kasa da zai sauke min tace tunda baki dandani zumar shi bako, kin san kuma abinda buzuwa kewa kishi ke nan.
Nace kuma ba zan taba dandanawa ba in dai haka zamu zauna wai Khadija may ke damun ki ne ana gabas kina yamma.
Wallahi ya kamata ki shiga karatun na natsu tun dare bai maki ba ki rungumi mijin ki ki jashi a jikin kin ki kinunawa diniya ke din diyace ta halas.
Ta ko wani fanni ido aka saka maki aga takon rawan ki ko so kike ku koma daya ke da buzuwan da Fati ya rasa tundun dafawa a gidan shi duk ku ukun ku zama iri daya.
Maganar ta ya fara shigana ta sake cewa so kike ki watsa ma iyayyen ki kasa a ido su da akai sha,awan hada iri dasu don ganin ya Aminan ki da sukayi.
Ko so kike su da sukaji suka gani suji kunya dayin wanan hadin khadija kina da wayon ki kin san abinda ya kamata ba sai na tsaya fada maki komai ba.
Daga irin nau,in magana da miji, kwalliya, iya girki taron bakin sa ki tararaye su yan uwan shi da iyayyen shi su zama tankar naki, ladabi da biyayya shine kawai banbancin ki da wanan buzuwan.
Ta dago kai ta kalleni taga ina sauraren ta cikin sanyin jiki tace koke fa khadija wallahi dana shigo irin yadda muka fara dake yasani jin tsoro da farko.
Yanzu maryam yaya kike son inyi don Allah wallahi ni har yanzu bai kwanta min a rai bane ban san may yasa ba na kasa yi mashi biyayya.
Tace ki sa a ranki daga yau zai ga canji a gurin ki ki koma khadijan ki ta ainihi da kowa ya sani kiga yadda zaku kwashe dashi da buzuwa a gidan nan.
Na sauke ajiyan zuciya tare da fadin ban san ta inda zan fara bane nima abin yana damuna don nasan hakan ba halina bane.
Nan dai ta dinga bani shawaran da ya dace har bayan uku na rana mukai sallama akan zan roke shi idan ya yarda zata zo muje wurin gyaran kai da ita don kaina ya tsufa yana damuna yanzu.
Bayan tafiyan maryam ban zauna ba don nasan nice da girki da yamma don haka na shiga kitchen na dora muna girkin abinda zamuci da dare semo na tuka sai miyar agushi da nayi wanda yayi kauri sosai banda fresh vegetables don haka nayi amfani da bussashen shuwakan da nazo dashi don akwai ni da son miyan shi.
Daga nan na wuce part din shi na gyara mai ko ina na wanko bathroom tare da saka kamshi na sake mai zanin gadon dake saman gadon nashi dakin ya dauki kamshi da kyali.
Nagama nazo na gyara part dina na saka mai kayan kamshi tare da kuna AC din falon wanka na shiga na gyara jikina na fito na shirya a cikin wani dogon riga na Afri Abaya dinkin rigar yai mutukar karban jikina sosai.
Don fashin sallah da nakeyi yasa ina ganin magariba tayi na dauko tasbaha na ina ja daga inda nake zaune a falon.
Tun fitan da yayi muna tare da maryam bai sake shigowa part din ba, don haka abin ya damay ni sosai a raina don ban san halin da yake ciki ba.
Har wurin nine bai shigo ba don haka na yanke shawaran bin shi da abincin a part din shi sai dana gama jera abincin na nufi dakin in gani ko yana ciki.
Turan kofan nayi a hankali bakina dauke da sallama kwance yake rairai saman gadon shi ya dora hannu daya saman fuskan shi.
Ciki ciki ya amsa min sallaman na karaso inda yake kwance na karaso gaban shi tare da fadin mun wuni lafiya.
Ya dan sauke hannun shi tare da fadin lafiya kalau ya kika wuni na amsa da lafiya sai na dan tsaya ina kallon yadda ya kara maida hannun shi saman fuskan shi.
Zanyi maganan da ya kawoni naji ya rigani fadin yau ban jin dasin jikina tun dazun nake kwance fitana ke nan zuwa asibiti kika shigo kika gyara min dakina.
Sannu nayi mashi sai naji ba zan iya fadin abinda ya kawo ni wurin shi ba a lokacin don ciwo ya kawar da komai.
Allah ya sauwaka nayi mashi tare da fadin abinci yana falo na ajema yace ya gode na juya zan fita daga dakin mukaji karan fashewan abu da sauri ya daga yana kallon kofan nima wurin nake kallo.
Karan muka kara ji kamar ana wurgi da kaya aka bankado kofan da karfi duk muka sake kallon kofan a razane nafisa ne ta shigo tana huci tare da fadin.
Ke karamar yar iska may kike nufi da mijina ne wai kina nufin in saka maki ido da mijina kina yadda kike so to ki sani duk kwanakin da kuka je kukayi dashi a kaduna sai ya rama min shi a gidan nan.
Watau ke mai wayo ko kin dauke shi kun tafi kaduna kun gama iskancin ku dashi yanzun kin dawo kin wani kwaso dan iskan abincin ki kin kawo mashi.
To sai dai uwarki ta nemi wani kulan ta kawo maki ba dai wanan ba kuma bari kiji sai na rama kwanan ki da kuka yi a can tunda nasan ba zai kwana da fati yana kallon ki ba.
Wai ku masu wayo kun gudu kunje can ku huta to in kun gudu nan ai baku guje ma sheri na ba abinda zai taba wakana a tsakanin ku har abada sai dai ku tabbata a hakan.
Zata ci gaba yace ke Nafisa wai kina haukane komay kike haka ne yarinyar nan bata kula alamarin ki amma duk da hakan ke sai kin san yadda kika shiga alamarin ta.
Ya ishe ki haka na tun baki kaini bango na maki abinda ban tashi yi ba a gidan nan kin isheni nafisa kin fara kaini bango ya fada da karfi .
Daidai lokacin na bude dakin na fita tare da kallon kayan abincin nawa da ta watsar a karamin falon nashi inda yake cin abinci da hutawa.
Wuce kayan nayi zuwa dakina zuciya na yana tafarfasa badon huduban maryam da nake son amfani dashi da ranan taga kalar nawa fitinan .
Don sai nayi mata hasaran da yafi na kulan data nana min a kasa suka watse ina shiga dakina nayi mashi key ban kara bi ta kan su ba nagama abinda zanyi na kwanta.
Sai da safe bayan na tashine nayi wankan tsarki na fito na fara tsefe kaina da nake son zuwa gyaran kai kofa naji ana