nazo yi a dakina wanda zanyi amfani dashi amma in haka ya bata ma rai kayi hakkuri.
Kallin mamaki yayi min jin kalman hakkuri ya fito a baki na sai naji baiyi magana ba sai tuki yake yi mun kusa kawa gidan naji yace yusuf yaje kaduna yace su hajiyan mu na gaida ke.
Sai lokacin na juyo nace mai ya koma bayan zuwan mu kuma yace ai yanzu kin san zuwa ya kama shi tunda bukin su ya kusa.
Au har bukin ya zo ne ai na dauka sai ta karasa karatun ta yace ke kin kare ne da kikai aure shiru nayi mashi ya sake tambayana nace ai kafi kowa sanin amsa.
Amsan ki nake son ji kin koya ma zainab ana aure ko ba a kare karatu ba don haka itama zata kwaikwaiye ki ne nace nima ai dole akai min ba da sona ba.
Wa yai maki dole ya fada yana murmushi nace kafi wacce kake tambaya sanin amsa ai na dauka maryam tai maki nasiha ne jin kalman hakurin da kika bani dazun don nasan ba halin ki bane aro kikayi.
Kai har yaushe kasan wani halina tunda ba zama cutship mukayi da kai ba balle ka sani kasan komai nawa.
Wani irin cutship kike son muyi dake bayan wanda mukayi dake a baya ban samu bashi amsa ba motar shi ta shigo get din gidan wani dogon mutum fari kanshi ako yaushe a cikin nadi yana rataye da takobi always a kafadan shi ya taso ya wagale get din muka shiga.
Motar mu na danna kai motar Nafisa na kokarin fitowa a gidan wanda dama ashe ita buzu mai gadi ya bude ma kofar fita daga gidan.
Sau daya na kalleta na kawar da kaina gefe daya ban kara kallon ta ba shima kallon nata yayi ya kawar dakai, ganin shi bai sa ta dawo ba ko ta tsaya sai ta fice a gida.
Kanshi ya girgiza a cikin takaici batare da yayi magana ba ya samu wuri ya parker motar nayi sauri kama kofan zan bude amma sai naji kofar a rufe take.
Na juyo na kalle shi ya zaune yayi shiru yana kallo na nace bude min in fita yace mana yace ban gama dake ba tukun zama na gyara ina sauraren shi.
Iska ya dan furzo daga bakin shi tare da sauke numfashin shi yace kin san yau ranan girkin ki ne ko na juyo na kalle shi tare da fadin ina da ranan girki ne a gidan ka ?
Ko matar ka ta yarda ne a bani girkin ta gama cin ramuwar girkin ta da naci mata ya dan murmusa tare da fadin ko can bata ci wani ranan girkin ba don ni ba jahili bane.
Nasan abinda nakeyi fa khadija wanan haukan da take bawai zai rudar dani bani in afka sherin shedan na daina shiga gurin ki ne don naga kina lalura yasa na daga maki kafa.
Baki na turo gaba tare da kara yunkurin bude kofar motar ina son fita daga cikin ta naji ya danna abu kofan yayi kara yace kin dai ji na fada maki.
Fita nayi ba tare da ns juyo gare shi ba na fice daga cikin motar yabi ni da kallo har na shige ciki da sallama a bakina.
Suna falo zaune kamar kullun suna hiran su babu wace ta karba min sallama na nima kuma ban damu da sai sun karba min din ba na fara wuce wurin da suke zaune.
Suna gani na sai sukai tsit da farko da na dan wuce su sai suka saka dariya irin wanda ke sa mutum ya tsargu din nan haka bai sa na juyo gare su ba sai dana kai kofana na juyo na dawo gare su duk suka maida hankalin su gare ni
Nayi masu kallon tsab gaba dayan su tare da fadin wacece mai share share a gidan nan shiru sukayi suna kallona ga baki dayan su.
Na sake fadin mai shara nake tambaya a cikin ku da wace ke girki don za ai min gyaran daki ne da girki yanzu.
Yanyalace ta amsa min da babu wata mai aiki a cikin mu da zatai maki aiki a karkashin Nafisa muke zaune nan dukan kan mu yarinya.
Shigowan shi a bayana yasa na juya wurin shi ina kallon shi tambayan may ke faruwa ne ya tsaya yi nace kai kace min yan aiki ne su idan ina da bukatan wani abu in kira mai yi tayi min yace kwarai da gaske.
Yanzu ya akayi nace na bukaci mai shara da mai girki sun ce babu a cikin su asali ma su a karkashin Nafisa suke zaune.
Yace haka ne tare da kallon su yace tunda a karshinta kuke ba aikin gidan nan kuka zauna kuyi ba sai ta zo ta sama maku wurin da zaku zauna daga yau din nan ba sai gobe ba.
Yana fadin haka ya juya ya fara tafiya muryan wata daga cikin su ne take tambayan wani guri zasu share min na nuna mata falon gaba daya nace nan nake son a share a gyara bana son daga yau in kara samun falon haka.
Sai mai girki idan akwai zaso ta biyoni taji may za a girka muna a gidan kowa yaci ina fadin haka na juya na fara tafiya ban tsaya sauraren may zasu ce ba.
Na bude part dina tare da addua a bakina na shiga sai dana aje tarkacen takarduna da na shigo dasu na fada bandaki na watso ruwa na sauya tifafin jikina dan karamin kitchen dina dake manne a part dina wanda nake dan yin aikin abinda zanci na bude na shiga.
Motsi na ji a falon yasa na fito wata buzuwa nagani tsaye tana fadin zancen girkin da kikayi ne ya kawo ni.
Nace da ita abinci zaki girka wanda mutanen da ke gidan nan zasu ci ganinan fitowa yanzu zan duba abinda za a dafa.
Ta juya ta fita ni kuma naci gaba da abinda nakeyi a kitchen din nawa na dora komai na fito na samay ta tare da wata nan muka fara aiki dasu cikin dan lokaci kadan muka girka tuwo da miya wanda zai wadaci wa yan da ke gidan.
Ga mamakin su ban tsaya diba ba sai dai na zubawa duk wani dan aiki suna fada min muka gama lokacin magariba yayi ko.
Part dina na koma na samu cow tail din da na dora ya dahu yadda nake so na sauke na zuma warmer tare da dora wutan tuwon alkama nake son tuka mashi sai miyan yauki da zan danyi a hada da ja miyar cowtail din dana dafa kafin takwas da rabi na gama komai naje nayi wanka na fito na fara gabatar da sallah na dan dade a zaune ina addua kafin in tashi in shirya kaina.
Abinda antyn Maryam ta aiko min na bude na karanta bayanin su turaren na shafa tare da bin ko wani gabban jikina na goga kadan na dauko wani Ethopian abaya na saka a jiki.
Sai da na gama na fara tunanen yadda zamu kwashe da buzuwa yau a gidan gashi nabi shawaran maryam nayi yadda tace amma kuma matsalan shine buxuwa yanzu.
Nace a raina dole ne Anty Fati ta kasa jure wanan fitinan na buzuwa tabar mata gidan duk da mijin wanda nai fahince tane ashe ke ganin laifin ta.
Sai yanzu dana shiga wanan tarkon nake kara fahintar dalilin ta na bar ma wata mijin ta da gidan ta gaba daya ta zabi zama a inda bata samun kulawan shi yadda ya kamata acan.
Mikewa nayi yare da fadin Allah ya haudani kan wanan matar shu,uma ta gidan nan kamshin humran da body spary na oud dana shafe jikina dashi ne ya amsa ko ina na gilma a gidan.
Na shirya komai da zan bukata a basket na jawo kofan part dina nayi mashi key turaren ne ya jawo hankalin su inda suke zaune suna cin abincin da muka girka in general na gidan.
Araina nace algungumai ashe suna son cin abincin gashi yanzu duk suna cin abincin da suka tsaya min iskanci.
Sama na haye zuwa wurin maigidan basket din na aje ba tare dana jera ba na nufi cikin dakin kai tsaye inda na samay shi ya fito daga wanka kenan yana goge jikin shi.
Juyawa nayi da sauri zan koma muryan shi naji yana tsayar dani a inda nake yana fadin ina kuma zaki ba kinzo cika ladan ki bane kuma zaki koma.
Nace ni bashi ya kawo ni ba zuwa nayi in gyara ma guri daku abinci dana kawo yana tsaye na nufo inda yake ya tsaya yana kallon na a zaton shi gurin shi zan zo sai yaga na wuce na shige bathroom din na rufo gyara nayi sosai ban so yi da dare ba amma banda lokacin yi don na makara gayin hakan.
Koda na fito na samu ya gama ya sauka kasa na gyara mai dakin na goge ko ina ina gap da karasawa ya shigo dakin dauke da jakar da ya ke fita aiki dashi yana fito da laptop din shi ciki.
Na gama nace dashj abincin fa don ni zan koma part dina dayake shi dan zolaye ne a noke sai cewa yayi wanan kwaliyan da kamshin wa zaki kai ya shaka ko ya gani.
Kaina nayiwa kwaliya ba wani ba yace karya kike wallahi ni ki kawai kuma ban gama gani ba da shaka don ban biya ki ladan yi ba.
Kaidai ka sani na fada na kara dacewa kai dama ba,ayi ma abin arziki ai a wanye lafiya sai ka samu abinda kace wa mutum.
Yanzu kuma laifine don naga abin sha,awa a matata na yaba ko ba yabon baki kike so in maki bane ?
Fita nayi ban bashi amsa ba sai da nakai kofa nace idan ka gama abinci yana danning yana jiran ka ni sai da safe na gama nawa yace kada ki soma ki bar part din nan don baki gama ba.
Fita nayi zuwa dinnig din na jera mai abincin ina cikin jerawa ne ya fito daga dakin ban ji fitowan shi ba sai jin hannuwanshi nayi saman weast dina yana min chakulkuli da wani irin zabura na dago na watsa mai harara tare da fadin ka bar min haka please.
Zama yayi yana fadin ina da doka ne ajan abina kuma karki manta fa kayana ne a gurin bansan may yasa yake son min irin maganan nan dake sakani jin kunya ba.
Bandago kaina ba don na fahinci shi baisan kunya ba ganin ya zauna na jawo plate din na fara zuba mai abincin yana zaune yayi balance saman kujeran da yake zaune yana kallon abincin da nake zuba mai baiyi magana ba jin bai tanka min ba yasa na dogo kaina ina kallon shi tare da fadin ya isa ko in kara ?
Yace idan zamu iya cinye wanan din ki barshi hakana ko kuma ki kara idan ba zai ishe mu ba don tare zamuci.
Da sauri na dago kai nace dashi nifa na koshi don naci abinci a gurin maryam dazun.
Yace wanan ba reason bane ki zauna kici abinci nace ban cin abinci sau biyu a wuni haka ka,idana yake ki koyi ci daga yau ya fadi.
Gani nayi kamar bai yarda dani bane yasa na je kura daya na zauna a kusa dashi tare da wanke hannu na soma ci yana zaune ya harde hannayen shi saman chest din shi ya kura min ido.
Dago kai nayi na dan kalle shi ganin bai fara cin abincin ba bakin shi ya bude min sai na dan harara shi.
Yace baki son in ci abincin ke nan ashe nace kai ni wallahi kana takura min har abuncin ma na girka ci ma bazakayi da kanka ba sai anbaka a baki ?
Ganin da gaske ba zai ci ba na debo katon loma na nufi bakin shi dashi sai da yayi murmushin ganin loman dana debo din ya bude bakin shi da nufin in sa mai.
Nafisa ce ta shigo tana watsa muna harara dagani har shi tace karuwancin da ake ma ke nan tun a waje har ya rude ka ashe , ?
Eh yace mata ashe kema kin gane yanzu akwai wace ta damu da cina dashana a gidan nan tunda gashi kin gani kinyi magana.
Loman da ya barni dashi a hannu na mika mashi ya bude baki ya hade abincin takai ma kallo tace wanan karyan bai rudani.
Nazo ne jin dalilin da matar ka zata sa min yan uwana aiki haka a gidan a wani dalili nata zata saka su suyi mata aiki.
Yan uwan ki ko yan aikin gidana kike nufi don biyan su nakeyi kuma inda suke zama tasa su gyara abinci kuma naga suma sunci da suka girka sai kuma may ya saura.
Samad da bakin ka yau kake fada min haka akan yan uwana a gaban wanan fitsarariyar mara kunyar yarinyar mai son katsalan dan to bari kaji
Ban dauko su gidan anan don wata shegiyar matar ka cen ta dinga saka min su aiki ba don bukatan kaina na kawo su nan ba nawani ba can daban.
Yace idan dai zasuci gaba da zama gidan nan ya zama waji bi su yi duk wani abinda kowa na gidan nan zai saka su suyi mudin kina son zaman su a gidan nan kuwa.
Wallahi wanan ba zata saka su komai ba daga yau su sake mata ko wanan da sukayi don bani gidan ne aka samu yin hakan.
Yace ashe ko karshen zaman su a gidan nan yazo ke nan don muddin ta saka su wani abin basu yi ba zaman su ya kare a gidan nan na fada maki.
Tace akan matar ka kake fada min haka bazasuyi ba kuma ba zasu bar gidan nan ba sai dai ita tabar min gidana wallahi.
In ba haka ba sai dai mu tafi tare dasu idan ma korar su zaka yi daga gidan kaji na fada maka yace da ita haka yafi nono fari a gurina idan zsku tafi duka har dake.
Ido waje take fadin Samad akan wanan abar kake fada min wa yan nan bakaken maganganun haka har da cewa sai dai muta tare dasu din.
Kwarai kuwa mudin ba zakubi abinda na umarce ku dashi ba kuwa nima a shirye nake da matakin da zaki dauka din.
Tace ke kuma bari kiji Samad a tafin hannu na yake idan kina takama da guntun asirin da kukayo mashine na baki kwana bakwai a gidan nan.
Idan kin taba zama kin zauna in baki taba zama ba baki taba dashi don wanan dandana haukace na bari kikayi na zana dashi din.
Yace tana barin gidan nan ki tabbatar da tare zaku barshi don kin san ni ba saki ko wani abu a gidana duk wani abin da zaki mata ki tabbatar da kafin ya samay ta kece ta farko da zai sama.
Kai na girgiza ina murmushi nace bude baki kaci abincin kada yai sanyi ka tsaya kana magana akan abinda bai da ma,ana .
Bude bakin yayi kamar wani yaro naci gaba da zuba mai abincin yana ci ta dan tsaya tana kallon mu sai masifa take surfa mashi ni dai ina murmushi ta nufo wurin yace idan kika kuskura kika taba wani abu anan bakin auren ki kenan dani wallahi.
Ido waje take kallon shi sai ta juya ta fita a fusace ta bar gurin tana fita na tsamay hannu na ga abincin ina wankewa tare da mikewa kai ya girgiza min tare da fadin nace dake na koshi ne ?
Nagama baka ka karasa da kan ka wanan masifar taku ya isheni haka wallahi mace kamar a kanta aka fara kishiya.
Na fara tafiya sai naji ya kamomi hannu na zuwa jikin shi wani irin shock ne ya ziyar ce ni a lokaci daya cikin karfin hali nace dashi ka sake ni don Allah.
Murmushi naji yayi na kara jin haushi a raina nace a fili kasan ba ka iya gidan haka ka dauko ni don ku bata min kurciyana komay ?
Jawoni yayi na kara fadawa saman jikin shi da kyau ina kokarin zilewa ya matseni har ban iya motsin komai .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ina kara rokon ku da ku taimaka ku rike min amanan wanan novel din da albarkan Allah da Annabinsa.
Wace kuma ta yi sakaci da amana na roki ubangijin mu Allah alfarman wanan rana ta jumma,a ya hanata farin ciki a rayuwan ta har abada kwantan kwancin abinda na roke ta dashi taki darajan Allah da Annabi.
Tunda na tashi na shiga kitchen goge nan wanko can har na gama na dora abin breakfast duk laraba bata fito ba har matar gidan.
Na kusa gama abinda nake girkawa ne laraba ta shigo kitchen din tana fadin a cikin barci nake jin kamshi a hannci na ashe ke ce a kitchen din hajiya.
Gaida ita da kwana nayi ta amsa cikkin jin dadi tana godiya tare da kallon kitchen din