juyo yana fadin wanan abin naku yaushe zaki gama shi ne ?
Wani abu na dago na kalle shi cikin jin haushin maganar shi yace abinda ke saki ciwon mara mana nace ban sani ba don sirina ne.
Dariya yayi ya fita daga dakin na ja guntun tsuki tare da fara tatara kayan abincin na mike don in kawar dasu a wurin.
Kofana na rufe daga nan tare da bin kusurwan dakin ina tofewa da addu, a don i zuwa yanzu ina matukar jin tsoron lamarin Nafisa ta yadda kowa bai fadin alherin ta sai akasin hakan.
Ina mamaki a raina wani irin kishi ke gareta haka kamar tafi kowa sanin dadin miji nace a raina Allah yaba Anty Fati boyar Allah hakkuri.
Barci ya dan fara daukana can a cikin barcin sama sama nake jin kamar hayaniya a gidan kasa kunne na nayi na kara saurarawa.
Haniya ne gami da kururuwa ke tashi a zabure na mike zaune jin hayaniyar yai yawa yasa na fito falona a tsorace na dubi lokaci naga goma na dare saura.
Ihun kamar babu lafiya na bude kofa na fito daidai lokacin da yake jibganta daga sama suna saukowa kasa tana buga mai duk abinda yazo gaban ta.
Ga sauran yan uwanta tsaye cirko cirko suna kallo sai tsuma sukeyi har zan juya naji sun dauki kururuwa na juyo da sauri inga abinda suke ma ihun lokaci daya haka.
Nafisa ne ta dauko flower vase ta nufe dashi shi kuma ya murde ta ya kwace yana dukan ta na karaso da sauri ina fadin ka sake ta mana kasheta zakayi ne.
Don Allah ka barta hakana zaka biyewa mace ne kayi kisan kai a gidan ka ya juyo ya kalle ita ko bata saduda ba nan yan uwanta sukayo kan su suna batun banbaranta ajikin shi ta yi wuuu dasu dashi ya kara sheke ta tana fadin zai kasheni mugu kawai.
Shakeshi su yanyala sukayi daga baya ya juya gurin su yana fadin ku sake ni sai na fahinci shigar mata sukayi.
Ranan naga tashin hankali sosai a gidan don dukan su ya shiga yi mazan suka yo kanshi suma cikin kuka take yare da ban jin abinda take fada sai naga sun dare nasan warning dinsu tayi da hakan.
Dakina shiga na kira Yusuf cikin tashin hankali nake fadin kazo yanzu don Allah babu lafiya a gidan nan fa na kashe wayan .
Ba,a dauki lokaci ba sai ga Yusuf din ya shigo ban san irin gudun dayayi a hanya hanya ba ya iso gidan yana shigowa kai tsaye wurin AA din ya nufa sai lokacin na karasa kusa dashi nima ina fadin ga jini nan yana zuba ma a hannu da gefen goshin ka yayana kuje asibiti don Allah kabar gidan nan dashi please .
Wurina ta juya da masifanta tana fadin akan ki akai min haka wallahi dake dashi kun nemi rashin kwanciyan hankali a gidan nan kun samu muci gaba da haka dani daku yadda ya zubar min da jini nima sai na zubar maki da naki a gidan nan duk kayan dake jikin su sun yaga su.
Kada ki soma kice zaki kawo haukan ki ga yar mutane kinji na fada maki duk ranan da kikai gigintaba ta sai kin kwana a cell wallahi don ba zan nuna maki sanaya ba.
Tace narin doke ta a gaban ka sai in kwana a cell din tun yanzu tayo kaina a sukwane Yusuf yayi sauri shiga tsakanin mu shida AA din.
Nace barta barta ta gwada haukan ta a kaina yau ta rena kan ta a gidan wallahi ke wallahi ki kiyayyeni kina ganina haka nafiki hauka wallahi don ke ba masifa kika iya ba sai hauka.
Kallona ta kama yi ido bude ba ita kadai ba har dasu dake falon don idona ya gama rufewa da ita a lokacin .
Ke Deedar shiga dakin ki nace karki kara fitowa nan wajen yana fadi cikin bani commad kamar zanyi magana sai kuma na juya na tafi tare da sa ma kofa na sakata na barsu a wurin.
Ranan sai dai barci dayake barawo ya dauke ni ban sani ba amma da zaran na rufe ido su nake gani a cikin yanayin dana gansu suna fitinan.
Bayan Yusuf ya kaishi asibiti an mashi dressing din ciwon ya dawo dashi gida sun dade a mota suna maganan dashi yana fada masu wai murde mai gaban shi Nafisa taso tayi yana barci.
Gaskiya wanan matar taka bata da hankali kasheka taso tayi ne ko may idan taja maka wani matsala fa kuma ?
Nifa wanan matar tsoro ta soma bani AA gaskiya kasan nayi tun wuri yace haukanta na banza ne ya motsa kawai wai tana zargin naje na sadu da sauran matan nawa shine duk wanan haukan da kaga tanayi fa.
Da mamaki ya kalleshi yace da may take nufi ita kadaine mace ko may yace ban san wanan haukan ba nima shike damuna ai.
Lalai akwai matsala kuwa ina ga taga khadija ta fara haihuwa a gidan nan ai sai ta hade ranta ke nan.
Na gama komai a part din sai dai na kasa bude kofana har lokacin zaman kadaici kuma ya damay ni jinayi ana kwakwasa min kofa part din.
Tashi nayi naje na bude kofan shine a tsaye a saka mai plaster a gushin shi da kuma inda yaji ciwo a hannun daga kofan ban kauce ba nace ina kwana hannu ya mika ya jaye ni a hanya ya shiga part din kamshi ne ya daki hancin shi mai dadin shaka.
Daga kofa zaki gaida ni ko kina korata a dakin naki ne nace ba koranka nakeyi ba ina dai guje ma abinda zai kawo fitina ne a tsakanin ku da matar ka tunda mune bata son taga ka mame mu.
Wanan ne dalilin ki na dakatar dani daga waje kuna da banbanci ne da ita ko may nace ai yadda ta nuna akwai banbanci sosai kuwa don kai nata ne ita kadai don haka don Allah ka kula.
Yace damay ko shiyasa da suke duka na naga kin damu kin so ki shigar min don baki sona ko ?
Kallon shi nayi sai na rasa abinda zance dashi har na juya sai kuma na waigo nace mashi saura kiris ai su kashe ka da baka fisu karfi ba kan ban san yadda zaku kwashe ba.
Uhhmm yace ashe na baki sha,awa,ke nan ko na burge ki tunda har kika fada nace fada da matan shine burgewa komay kayi ?
Gaskiya idan haka zaka biye mata kuna wanan fitina kamar gidan wasu madanbata aibin baiyi ba wallahi ya girgiza kai yana fadin kin san may ta aikata min har na doketa haka.
Nace ban sani ba wanan tsakanin ka ne da matar ka ban kuma son in sani don ba abinda ya safe ni bane.
Nasan zaki tunanen haka halina yake dama dukan mata akan may zanyi tunanen hakan ai da kana dukan mata da zanji tun baka aure ni ba.
Bincike kikayi akaina ke nan akan may zan bincike don banda aikin yi ko may maganar duniya ai bai boyowa kamar yadda naji a kan matar ka gashi Allah ya nuna min.
Wanan bakin zanso inga ranan da zai mutu nace akan fadin gaskiya ko may ya dan jima a dakin muna fafatawa wanda shi hakan yana mashi dadi.
Yai ta zolayana niko in hakikance ina mayar da martani kamar gaske ya gaji ya fita yana dariya dake ban haushi.
Maryam ne ta shigo da sallamanta a dakin tana fadin Khadija kunyi accident ne ko may naga AA din ki da plaster a goshin shi.
Kai gulma ajali shiya kawo ki ko duba ni tace wallahi abin ya ban tsoro ne wallahi ke dallah can ni barmin wanan zancen kinji nayi missing din ki zaki zo min da wani zance kuma.
Khadija don Allah ina fatan bake kikai mashi wanan abin ba wani kallo nayi mata tare da fadin may kika maidani wai nifa nasan abinda nakeyi can tsakanin shi da matar shine.
Nan dai na kora mata iya abinda na sani tace duk saboda ya tafi kd dake tayi wanan abin haka ko may, ?
Nace wa ya sanar mata don ni ban damu da in sani ba ba abinda ya shafeni da rikicin su ni yanzu zancen karatuna ne a gaba na don ban san may yake nufi dani ba.
Khadija kibi shi a hankali shima ai yasan kina karatu koda ya aure ki kawai halin su na mazane sai yaja maki aji akan hakan tunda yasan kina so.
Nace wallahi bai isa yace zai hanani karatuna ba maryam tunda a haka yaganeni ya aure ni banji zan iya bari ba kuma.
Idan yace ki bari ai dole ki bari din shine saukin ki ki dai lalabashi don Allah ya barki ki koma nace ina ruwana dashi maryam zaman dai kawai nake a gidan wanda ni banga dalili ba kawai dai don ya kuntatamin ne yai min haka na karasa cikin bacin rai.
Tace da amfani mana tunda yana hutu a jikin ki wani kallo nayi mata tare da fadin wani hutu cabdi jam yana dai hutu a wurin matan shi.
Kina nufin har yanzu komai bai shiga tsakanin ki da shiba komay komai kamar yaya dama ance maki sona yakeyi ne don fa ya kuntata min ya kawo ni gidan shi yaga yadda zanyi niko bazan taba karya ba har yagane mu tafi a hakana dashi.
Gaskiya khadija ban taba zaton haka ba wallahi don nasan AA yana son ki kuma shi namiji ne da ko wace mace zata so kece dai kike mashi rowa shi kuma ya biye maki yaga iya gudun ki.
Anya khadija ba sherin wanan buzuwan bane kuwa nace kamar yaya tace tai maku asirin akan haka mana khadija wanan fa yana faruwa a tsakanin kishiyo da basu da imani .
Da zaran namiji yazo ga matar shi sai yaji shi ya koma tankar mace ba zai iya tabuka mata komai da dai sauran abubuwa da zai gusar mashi da sha,awanta gare shi.
Shiru nayi ina sauraren ta tunda ta fara bayanin ts sai da ta nace haba dai tana iya yin Abin da Allah bai tashi yi bane kawai dai hakan ra,ayin shi ne maryam.
Nace kuma fa maganar ki yana da kamshin gaskiya don abubuwan dake faruwa a tsakanin abin akwai ayan tambaya.
Nan dai na koro mata labarin komai tun zuwa na gidan ban boye mata komai ba har hiran da naji mommy da ya Amina sunayi sun dauka barci nake a lokacin.
Tace Khadija gaskiya kibar sakaci da ibadan ki idan ma kinayi to ki kara duk da sherin ta kada ki bari ta fahinci halin da kuke ciki dashi.
Ki nuna mata ke fa kin san kan ki ta ko ina ba kishin hauka irin nata zaki tsaya yi da ita kamar wata bagidajiya duk da ansan asiri gaskiyane.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Naji dadin kasancewa da maryam a dan wanan lokaci kamar yadda ta fini da shekaru haka ma na fahinci ta san hikima irin ta matan zamanin nan sosai.
Bayi mamakin ganin haka daga gare ta ba don fada min auren da tayi a baya inda ta hadu da kishiya yar bala,i da bata ko barta ta tare a gidan mijin ba.
Cikin hikima take hada min komai da zai inganta jikin mace da cikowan ni,ima ban san kaiba don haka sai nake dauka kayan kwadai ne kawai take ban da kuma na tsari.
Na ciki sosai a cikin dan sati biyun nan da mukayi da ita a gidan ba tare dashi ba ni kaina ina jin dadin zaman mu a haka ni da maryam sai dai muci musha muje makaranta mu dawo.
Buzuwa kumz ko yauahe bata rasa fitinar da zata takalo min dashi a gidan sai da nagaji muka saka mata ido itama ta kyale mu a haka .
Bata fita da motocin don maigidan yace abari har yazo yaga abinda ya faru da motocin dole yanzu duk wanda zai fita sai a motar haya hakan yasa Nafisa ta rage yawan fitan da takeyi ko yaushe akai akai.
Cikin hikima da dabara maryam ke kawo min hiran iri daban daban da har naji zuciyata ta natsu da abinda take koyar dani.
Haka yasa na raya a raina da zaran ya dawo zai samu canji sosai daga wurina sai dai a can kasan zuciyata ina kwankwanton anya kuwa zan iya haka a gare shi.
Mutumin da bata kaina yake ba ta matar shi yake zama nake dashi a gidan kamar kiwo na yake yi.
Yau mun tashi da niyar zuwa gyaran jiki don maigidan yace zai dawo daga tafiya a karshen satin nan gidan yar maryam muka fara zuwa gaida ita don ta dawo da mura daga Dubai.
Mu shiga gidan tana bedroom din ta maryam tace mu samay ta a dakin naso tsayawa falon sai taja hannuna zuwa saman inda dakin yar nata yake.
Shigar maryam har ta fara fada da maryam din tana cewa wai sai yau taga daman zuwa ta dubata bayan ta fada mata ta dawo da matsanecin mura daga tafiya.
Ganin da tayi min na shigo a bayan maryam da sallama yasa ta tsagaita da fadan nata ga maryam tana fadin yau amaryace a gidan namu.
Nan muka shiga gaisawa da ita yadda naga suna yi da maryam din suka ban sha,awa sosai don sai kace itace ta haifi maryam din
Kallona tayi bayan maryam ta mike zuwa wurin kayan da ta dawo dashi din tana fadin khadija gaskiya aure ya karbe ki sosai.
Kaina na sada kasa ina murmushi ta sake fadin ance ana gane bikin mace indan yayi kyau a cikin satin da ta haihu ne kamar yadda kuma ake gane kyau dakin mace idan ta dace a jikin ta.
Daga inda maryam take tana daga kayan tace wani kyaun daki tayi anty wanan kanwar taki ai sai kin hada da bulala kila don bata daukan shawara .
Kallona tayi sosai tana fadin ban gane ba khadija abinda take fada da gaske ne saurin kada mata kai nayi ina fadin bs gaskiya bane anty kada ki dauki maganan maryam.
Maryam din ta sake cewa wallahi anty gatanan dai yau a gaban ki gaki gata har yau din nan fa babu abinda ya taba shiga tsakanin ta da mijin ta .
Da sauri ta wani waro ido tana fadin Khadija kina da lafiya kuwa kunya naji sosai nayi kasa da kaina dan shiru tayi sai can tace dani Khadija dago muyi magana dake ta fahinta ina son ki dauke ni tankar yar uwar ki ta jini a gare ki kai na gyada mata.
Fada min may nene matsalan ki don idan irin haka ya faru dole akwai matsala a ta wani bangare walau a gurin ki ko a gurin mijin naki.
Murmushi nayi ina fadin anty ni banda matsalan komai wallahi a bangare ne a iya sani na ko yana tare dani ina iya tursasa zuciyana wurin ganin na mashi biyayya da ya dace dashi.
Sai dai ban san dalilin shi ba na kyale nin da yake yi wanda nima hakan ba damuna yake ba don nafi jin dadin hakan da muke dashi.
Subbahanallahi ta fadi da sauri a hankali cikin hikima irin ta matan da suka san kansu take min tambaya ina bata amsa har muka kai inda take son fahinta.
Naga ta wurgar da hannaye ta biyu saman gado tana fadin shike nan ta cuce ku yar iskan mata mara imani maryam ai ki bar ganin laifin kawar ki don matsalan ba daga gare ta yake ba.
Asiri akai masu wanda in ba wanda yasani ba ba zai iya fahintar komai ba anan sai irin matan dake wanan asirin suka san haka.
Tace wani asirine da ake hadawa da kaucen albasa da jijiyan dabba idan anyi wanan abin aka haka a ranan girkin macen da ba a son miji ya kwana da ita sai wani akasi yazo ya gitta masu wanda zai ji ba zai iya kaiwa ga matar shi ba komai kuwa sha,awan da ya motsa mashi na matar.
Irin shi ke sa sai zargin miji ya shiga zuciyar dayan da akaiwa asirin taga yar uwa da miji ta suna sha,anin su ita kuma an bake ta a gefe sai kaga kishiyar wani lokaci ita kadai zata dinga samun ciki.
Maryam tayi saurin fadi wallahi ko kamar kin sani anty don yanzun haka har da kiran khady tayi suna sheda mata wai ciki ke gare ta nan dai ta kora mata labari komai da ya faru harda hana mu shiga motar da yadda nima nayiwa motoci gidan illa babu mai amfani a yanzu .
Dariya anty tayi tace ta koya maki kema kin iya ke nan don gashi har zaki jawa maigidan hasara a lokaci daya.
Ta dago ta kalleni tana fadin ki kwantar da hankalin ki khadija wanan ba wani matsala bane insha Allahu yau din nan zanyi waya a sama muna makarin wanan abin.
Ai idan tasan wata bata san wata ba komai shu,umancin ta kuwa ta samay ki yarinyace shi yasa har abin ya dade yana tasiri a kan ku.
Daga